bayyinaat

Published time: 25 ,April ,2018      17:43:27
Sa’annan sai ya fuskanci ‘yan Dahriyya ya ce da su: Me ya sa kuke cewa abubuwa ba su da farko ba su da karshe?. Kuma ba su gushe ba kuma ba sa gushewa?.
Lambar Labari: 112
Sa’annan sai ya fuskanci ‘yan Dahriyya ya ce da su: Me ya sa kuke cewa abubuwa ba su da farko ba su da karshe?. Kuma ba su gushe ba kuma ba sa gushewa?. Sai suka ce: Domin mu ba ma hukunci sai da abin da muka gani, kuma ba mu samu farko ga abubuwa ba sai muka yi hukunci da cewa ba su gushe ba tun farko samammu ne, ba mu gan su suna karewa ba sai muka yi musu hukunci da cewa su madawwama ne. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Shin kun same ta Maras farko ko kun same ta Mai wanzuwa har abada ba za ta gushe ba?. Idan kuka ce: Kun same ta hakan, to kun tabbatar wa kawukanku cewa ba ku gushe ba a kamanninku da hankulanku ba ku da farko kamar yadda ba zaku gushe ba a halinku kamar yadda kuke, kuma idan kuka ce haka, to kun yi musun hakikanin zahiri kuma masana wadanda suke ganinku zasu karyata ku. 
Sai suka ce: A’a, mu ba mu ga farko gare ta ba kuma ba mu ga karshe gareta ba. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Saboda me kuke hukunci da rashin farkonta da rashin karshenta har abada ga ku ba ku ga farkonta ba, kuma karewarta shi ya fi cancanta ya wakana fiye daga bayanin da irinku yake yi game da ita, sai a yi mata hukunci da faruwa da karewa da yankewa domin ba ku ga dadewa ko wanzuwa gareta ba har abada.
Ba kuna ganin dare da rana ba?. Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin kuna ganinsu ba su gushe ba kuma ba zasu gushe ba? Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin yanzu ya halatta ku yi hukunci da haduwar dare da rana waje daya? Suka ce: A’a, Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ashe kenan kowannensu rabe yake da dayan sai daya ya riga daya ya zama duk inda daya ya yanke dayan yana gudana bayansa. Suka ce: Haka yake. Sai ya ce: Kun yi hukunci a nan da faruwar abin da ya gabata na daga dare da rana alhalin kuma ba ku gan su ba, saboda haka kada ku musa wa Allah ikonsa.
Sa’annan sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Shin kuna cewa duk abin da ya gabata na daga dare da rana yana da karshe ko ba shi da karshe? Idan kun ce: Yana da karshe, to kun sami karshen da ba shi da farkonsa, idan kuma kuka ce: Yana da karshe to an sami lokacin da babu wani abu da ya kasance daga cikinsu. Sai suka ce: Na’am.
Sai ya ce da su: Shin kun ce Duniya Dadaddiya ce ba Fararriya ba kuna sane da ma’anar da kuke nufi da furucin da kuka yi da kuma abin da kuke musawa? Suka ce: E. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Wannan halittu da kuke gani sashensu suna bukatuwa zuwa ga sashe, domin kowanne ya dogara ne ga samuwa da daya sashen nasa kamar yadda zaku ga gini sashe yana bukatar sashe, in ba haka ba, da bai yi karfi ba bai hadu ba haka ma sauran abubuwan da muke gani. 
Ya ce da su kuma: Idan wannan bangaren da sashensa yake bukatar sashe domin ya yi karfi ya cika shi ma Dadadde ne to ku bani labari da ya kasance Fararre da yaya ya kamata ya kasance? kuma yaya siffarsa ya kamata ta kasance?. 
Imam Sadik ya ce: Sai suka dimauce suka san cewa ba yadda za a yi a samu Fararre da sifa da suke siffanta shi da ita sai sun same ta ga wannan abin da suka raya cewa Kadimi (Dadadde) ne. Saboda haka sai suka tage suka ce: Zamu duba al’amarinmu tukuna.


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: