bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:49:43
daga cikin muhimmman ayyuka nagari mafi falalar ibada tsarkakakku ma’abota mukami mai girma da gwaggwaban lada da samun aljanna Firdausi mani’imciya da tsira daga azabar jahannama shi ne yin kuka kan musibar da bala’in da ya samu shugaban shahidai Imam Abu Abdallah jikan manzon Allah Ta'ala (s.a.w) furen Fatima Batula (a.s)
Lambar Labari: 141

Da sunan Allah mai rahama nmai jin kai

Ubangiji madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma da hikima mai zartarwa da tabbatar da maganarsa yana cewa

﴿ اللَّهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ الْمِصْبَاحُ ﴾.

{Allah shi ne hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar misalin taga ce da aka ajiye fitila a cikinta}

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: cikin daman Al'arshi anyi rubutu da koren launi cewa Husaini ne fitila shiriyakuma shi ne jirgin tsira

Bayan haka: daga cikin muhimmman ayyuka nagari mafi falalar ibada tsarkakakku ma’abota mukami mai girma da gwaggwaban lada da samun aljanna Firdausi mani’imciya da tsira daga azabar jahannama shi ne yin kuka kan musibar da bala’in da ya samu shugaban shahidai Imam Abu Abdallah jikan manzon Allah Ta'ala (s.a.w) furen Fatima Batula (a.s) `dan karamin zakin Aliyu Almurtada `dan'uwan Hassan Almujtaba mutum na biyu cikin mutanen cikin bargo dubun dubatar gaisuwa da yabo da aminci su kara tabbata gare su, lallai cikin haka masu rigengeniya su yi rigengeniya, masu aiki su yi aiki tukuru, lallai babu mai samun wannan sai mai babban rabo

Lallai Allah matsarkaki madaukakin sarki hakika ya kebanci Husaini (a.s) zinariya kasantattu dayantacciya, babbar ayar Allah, mafi girman sirrin samuwa da wasu falalloli kususiya da wasu Abubuwa da fifita da su koma bayan dukkanin halittu, babu banbanci cikin tsarin halitta ko na shar’antawa.

Daga farko: hakika Allah ya sanya waraka cikin kasa mai albarka wadda cikinta aka kashe Husaini (a.s) kamar yadda ya sanya waraka cikin ruwan zamzam.

Na biyu: haramun cin dukkanin kasa face kasar Imam Husaini (a.s) domin neman waraka, sannan makaruhi ne sanya bakin tufafi da yin raki face kan musibar da ta samu shugaban shahidai cikin watannin safar da Muharram da Safar, kan wadannan matakai biyu daga shaidu da misalai masu tarin yawa

Shin ma kasan cewa kacokafAllah ya halicci aljanna daga hasken Imam Husaini (a.s) shi ya kasance sababin samuwarta cikin duniyar yiwuwa ya yinda cikin aljanna akwai abin da wani ido bai taba gani ba wani kunne ba ta ba ji ba. bai kuma taba darsuwa cikin zuciyar wani dan Adam ba…

ya kake tsammanin sababin samuwar aljanna shi kuma zai kasance tunda dai ka ji kadan daga labarin aljanna, shi kana tunanin akwai wani mutum da zai iya tsinkayar hakikanin yadda Imam Husaini (a.s) yake, lallai dukkanin abin da muka sani dangane da shi tun zamanin farko zuwa wannan zamani da muke ciki kai har zuwa tashin kiyama kaso daya ne daga cikin `dari ne wanda ragowar kaso casa’in da tara na wajen Imamul Hujja ma’abocin zamani (a.f) abin da ke gare mu kamar misalin cikin tafin hannu ne da muka kwarfa daga tafkunan falalolinsa da darajoji kai a hakika ma dai abin da ke gare mu wani Abu ne da yake daga gere su zuwa gare su yake komawa kai da ba don su ba da har abada ba za mu taba iya saninsu ba

da za mu karanta tarjamomin malamanmu kan manya-manyan masana ilimin fikihun mu ma’abota girma daga magabata da wadanda suka biyo bayansu har zuwan wannan zamani da muke ciki muka bincika halayyarsu lallai babu makawa za mu gano sabubban samun dacewarsu da tsinkayarsu da shahararsu kamar misalin shaik `Dusi da Shaik Mufid da Sharifai biyu Sayyid Murtada Alamul huda da Sayyid Sharif Radi, da kuma irin su Sayyid Mahadi Bahrul ulum da shaik Abdul karim Ha’iri da Allama majalisi da Sayyid malaminmu Najafi Nar’ashi (ks) da ire-irensu daga manya-manyan malamai lallai mafi bayyanar sababin samun dacewarsu shi ne dangantakarsu tsarkakakka tsaftatta da lamarin shugaban shahidai Imam Husaini (a.s) da kuma rige-rigensu cikin raya bukukuwan ta’aziyyarsa da dukkanin yanayinsu da launukansu saboda girmamawa da raya ibadun Allah matsarkaki

An karbo daga Imam Rida (a.s) cikin wani hadisi da ya yi bayani dalla-dalla: (lallai tunawa da ranar da aka kashe Husaini ya na sanya idaniyarmu tayi radadi yana sanya mu zubda hawaye yana kaskantar da madaukakinmu)

an karbo daga majibancin lamarinmu Imamul Hujja da zamani Hujja ibn Hassan Al’askari Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja yana cewa: ya kakana zan kiraye ka safe da yamma zanyi maka kukan jini mayin kukan hawaye.

Lallai Imam Husaini (a.s) hasken Allah ne kuma fitilarsa cikin duniyar samuwa, lallai shi cikakken mutum ne kammalalle wanda sunan ubangijinsa mi girma ya yi tajalli cikinsa, da kuma hakikar kansa mai mafi girma, hakika ya bayyana cikin dabi’unsa na zati da juyin juya halinsa na kawo gyara madawwami matukar dawwamar zamani.

Lallai jahilai sun nuna masa kiyayya da dukkanin siffofinta, gafalallu da makiya sun tadar da fitina da shubuhohi kan rayar da tunawa da kisansa da yunkurinsa daga wannan lokaci zuwa wancan lokaci suna son dusashe hasken Allah da bakunansu da shubuhohinsu da kafofin sadarwarsu sai dai cewa kuma shi Allah zai cika haskensa cikin Imam Husaini (a.s) har zuwa bayyanar Imam Hujja (af) Almahadi wanda zai cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya.

Imam Husaini (a.s) zai dawo karo na biyu tare da sahabbansa masu daraja dawowa tabbatatta da Hujja da hankali da nassi wanda hakan ya kasance daga Abubuwa da aka sallamawa cikin mazhabar Ahlul baiti (a.s)

Sannan yin shakka da mukamomin Ahlul baiti (a.s) da zantukansu bawai bakon Abu ba ne wanda zamani da muke ciki ya kagar ya farar, bari dai ya kasance hatta a zamanin Imamai (a.s) kai har lokacin Annabin rahama akwai cikin mutane mutumin da yake nuna wani nau’in daga jayayya da kin yarda da zantukan Annabi (s.a.w)

An rawaito daga Imam Sadik (a.s) da ingantaccen isnadi cikin littafin Alkamilul Ziyarat ya ce: Imam Husaini ibn Ali (a.s) wata rana ya kasance cikin dakin annabi (s.a.w) suna wasa tare yana sanya shi dariya, sai A’isha ta ce: ya manzon Allah menene ya fi tsanani daga yadda wannan yaro karami ke burgeka? Sai ya ce: mata: kaiconki ta kaka ba zon shi ba ta kaka ba zai burgeni ba bayan shi ne kayan marmarin zuciyata sanyin idona? Amma da sannu al’ummata zata kashe shi duk wanda ya ziyarce shi bayan wafatinsa Allah zai rubuta masa ladan hajji daga hajjin dana halarta

sai ta ce: ya manzon Allah (s.a.w) hajji fa daga hajjin da aka halarta?

Sai ya ce: eh ladan hajji guda biyu daga hajjin dana halarta

Sai ta kara cewa: ya manzon Allah (s.a.w) hajji biyu fa daga hajjinka?

Sai ya ce: na’am hajji guda hudu.

Ba ta gushe ba tana kokawa da mamaki shi kuma yana karawa kan kokawarta ya ninninkawa har sai da yakai ga adadin hajji ya kai 90 daga hajjin manzon Allah (a.s), tare da Umararsa

Daga cikin mafifitan kwanakin ziyararsa mai albarka cikin ranar Ashura daga mafi falala ziyara da hadisi ya zo kanta ita ce ziyarar Ashura. Hakika cikin shekaru biyu da suka gabata cikin watan Muharram mai alfarma mun yi muhadara kan tafsiri da sharhin ziyarar Ashura da bayani wasu nukdodi cikinta, domin ta kasance karin haske mai haskaka cikin rayuwar mu ta ilimi da aiki da zamantakewa da daidaito

bai buya ba cewa ishkaloli da shubuhohi wanda ake tayarwa game da ziyarori da bakukuwan ta’aziyya wanda a zahirinsu ba baki bane, bai gushe ba akwai wadanda suke ta ruruta wuta da yin huri cikin kura, sai dai cewa ya tabbata a bayyane a gaban idanu yin hakan babu abin da yake janyowa masu yi face kunyata da tozarta da haramtuwa, domin shi Allah madaukaki hakika ya yi alkawalin azaba da cewa babu makiya lamarin Husaini (a.s) za su karu da shi face faduwa da tozartuwa da rashin nasara da kaskanta, shi kuma raya lamarinsa zai ta bayyana da kuma samun daukaka.

Umar Alhassan Salihu

Faroukumar66@gmail.com

+989335382587

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: