bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      21:59:03
Ya zama wajibi kan kowannenmu da dukkanin abinda Allah ya bashi da tashi ya raya lamarin husaini da dukiyarsa da alkalaminsa da kafafuwansa da dukkanin ikonsa domin ya karu cikin da lada da dacewa
Lambar Labari: 143
Da sunan Allah mai rahama nmai jin kai

Daga cikin hakkin dukkanin musulmi da musulma da duk wanda ya yi Imani da manzon rahama da ya yi koyi da shi cikin raya zaman makokin ashura da girmama ibadunsa ka da ya damu da shubuhohin da ake kawowa ciki domin nufin suka da kawo ishkali kan ta’aziyar husaini da masu ta’aziyya da masu ganagra maukibinsa.
A bayyane yake cikin tabbatattun lamurra kamar yadda bakin ciki kan shaugaban shahidai baban Abdullah Husaini (a.s) da ta’ammuli cikin lamarinsa da girmama ibadunsa da dukkanin hidima cikin tafarkin raya majalisin ta’aziyya da musibu, lallai digon hawayen da ya zuba kan husaini(as) tana kashe fushin Allah mai girma da daukaka hakama akasin haka, lallai yin tawaye da isgili kan raya lamarinsa da wulakanta masu raya lamarinsa da raunajna su da sanya kaya kan hanyarsu ta husaini yana jawo ukuba mai girma da kunyata duniya da lahira, saboda haka akiyaye akiyaye  daga shiga azabar wuta da nadama da hasara a ranar da nadama bata wani amafani.
kada ka sake ka bar raya lamarin husaini wadda cikinsu akwai ziyararsa baban Abdullah (as).
Ya zo cikin littafin alkamilul ziyarat babi na 40 sh 116 da isandinsa daga imam sadik (as) cewa: kada kabar ziyarar kabarin imam husaini (as) saboda tsoro lallai wanda ya bar ziyararsa zai ga daga hasara abinda zai fatan inama ace kabarinsa ya kasance kusa da kabarin imam.
Idan ya zamanto wannan shi ne halin wanda ya yi kasa a gwiwa ya takaita kan sha’anin ziyartarsa ya kake tunanin halin wadanda ke kawo shubuhohi da cikin sha’aninsa da yin tawaye da jayayya kan rayar alamominsa da bukukuwansa tsarkaka, sannan bomi bomi ga wanda ke yakar wadancan bukukuwa da alamomi yana ta’addanci kan maziyarta husaini (as) yana mai kokarin dusashe hasken Allah da yake tajalli cikin fitilar imam husaini shiryayya,sai dai cewa Allah yaki yarda sai ya cika haskensa koda kuwa kafirai da munafukai sunki.
    Ya zama wajibi kan kowannenmu da dukkanin abinda Allah ya bashi da tashi ya raya lamarin husaini da dukiyarsa da alkalaminsa da kafafuwansa da dukkanin ikonsa domin ya karu cikin da lada da dacewa.
 Na’am ya zama dole ai gyara da sauye sauye a wuraren da ke bukatar hakan ya zama dole a kyawunta niyya da kyawuntar mai aiki da kyawunta aikin, kyawuntar niyya bai isarwa tareda rinjayar aiki da barnarsa lallai kyawuntar niyya bata isarwa cikin ta’ammuli raya al’amarin  husaini (as) lallai dole shima rayawar ya zamanto anyi shi cikin kyawawan yanayi, lallai mafi kankantar kuskure koda kuwa bada ganganci akayi shi ban a iya tasiri mara kyawu cikin raya lamarin husaini(as).
Wajibine kan dukkaninmu gwargwadon sha’anin kowannenmu kamar yadda malami ya mallaka da iliminsa mawaki da wakens `dan kasuwa da kasuwancinsa sarayi da karfinsa mace da rayuwarta mai huduba da hudubarsa kai kowanne nau’I daga cikinmu ya zama wajibi su kara sadaukarwa cikin wannan hanya ta Allah da kuma abinda ya fi falala da kamala da tsarkaka da yawa da girma da iklasi suna mai tsarkake niyya da izinin Allah madaukaki.
Ya zama dole mu kayyadantu da hukunce-hukuncen Allah da tsantseni daga bayyana ra’ayi matukar mu ba ahalin hakan ba bane bamu cancanci ba da ra’ayi ba da ijtihadi kamar misalin maraji’ai ahalin haka, lallai wajibi ne mu mayar da lamari zuwa ga ahalinsa wadannan masana fikihu ma’abota girma da wanda suke da hakki cikin fitar da fatawa da alkalanci, ka da mu sake mu ketare iyakokin Allah gwargwadon silin gashi lallai su hukunce-hukuncen Allah suan da gman gaske daga waliyansa, shin shahadar husaini (as) wani abu ne da ya wuce raya addinin kakansa musdafa (s.a.w) lallai daiann har addinin muhammadu bai tsayuwa sai an kasheni to yaku takubba ku kamani.
ashe manzon Allah (s.a.w) ba shi ne mafi darajar halittu ba kuma ba shi ne dalili samuwar duniya da fadinta da cikarta ba, da shi aka farab da shi aka rufe, lallai shi yana kyawawan dabi’u, ya kasance tsakanin zira’I biyu ko kuma mafi kusa daga haka daga madaukaki mafi daukaka, ai dai lokacin da lamari ya isa ga hukunce-hukuncen Allah to Allah madaukakin sarki ya ce:    
 
﴿ وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الأَقَاوِيلِ (44) لأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ (45) ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ (46) فَمَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ ﴾
          da ace zai kirkiri ba’arin wasu maganganu kanmu* da mun damkeshi da dama* sannan da mun yake masa laka.
Yana daga cikin sanannen al’amari cewa labari da akaima sharadi gasgatacce ne tareda rashin gasgatuwar mukaddima da kuma natija da zata zo bayansa a ilimi mandik. Lalla babu kokwanto cewa manzon Allah (s.a.w) bazai aikata haka sai dai cewa Allah madaukaki ya yi nufin bayyanarwa da bada labari cewa kan lamari mai muhimmancin gaske ba komai bane wannan al’amari da ya wuce girman hukunce hukuncen Allah madaukaki da girmamar alfarmar fatawa da haramcin yenta ba tareda ilimi da ma’arifa ba.
Lallai raya ashura cikin kowacce shekara na nuni zuwa ga rayuwar mazhabar ahlul baiti (as) da wanzuwarsa daga nan kuma mu’amala treda da la’amarin imam husaini (as) da dukkanin shakali da yanayi lallai Allah zai bada lada mai yawa ga wanda ya yi haka, kamar yadda dukkanin wanda ya tsaya gaban yaduwar lamarin husaini Allah zai masa ukuba da ukuba mai radadi zai kuma dusashe ambatonsa wannan sunnar Allah ce kuma bazaka taba samun sauyi daga sunnar Allah ba.
Idan ranar ashuara ta kasance a shaekara 61 daga hijra rundunoni biyu zasu gwabza da juna rundunar yazidu da rundunar imam husaini (as) to haka lamarin yake cikin kowanne zamani runduna biyu na kwamawa da juna, duk wanda ya kasance cikin hanyar imam husaini (as) zai amu lada da kuma rahamar Allah, wanda kuma ya kasance kan hanyar yazidu ba’umayye lallai ya cancanci ukuba da fushin Allah     
 
و﴿ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ ﴾
Ranar ne zasu rarrabu.
Irin wannan rarrabuwa za ta cigaba har tashin kiyama.
Hakika habibu ibn muzahir ya kasance daga mutanen kufa kamar yadda shimru ibn zul jaushin ya kasance daga mutanen kufa, dukkaninsu daga gari daya suka fito sai dai cewa makomar kowanne daya daga cikinsu tayi nisa daga dayan a ranar Ashura, hakika shi habibu rayuwarsa mai albarka tayi karshe mai kyawu cikin sahun imam husaini (as) shugaban shahidai jagoran rundunarsa, amma wancan tsinanne wanda ya kasance daga gayyar makiya imam husaini(as) daga makasansa jagororin munafunci da kafirci.  
nawa ne daga mutane daga wadanda sukai ta’ammuli mai kyawu da al’amarin husaini da alamominsa da ta’aziyyarsa sai ya zamanto ya garar rahama ya azurtu cikin makomarsa da karshensa.
  misalin zuhairu ibn kainu sananne da kasantuwarsa a farkon sha’aninsa ya kasance mabiyin usman masoyinsa ya kasance ya na imanin cewa lallai na kasha usmanu bisa zalunci kuma sarkin muminai ali (as) yanada hannu cikin kisansa, ga irin misalin wahab wanda shi kacokan da kirista ya kasance sai dai cewa su biyun sun kai ga matsayin samun ceto da martaba mai girma a ranar Ashura kai hatta kowanne daya daga cikinsu ya kasance kamar ragowar shahidan karbala miliyoyin maziyarta na kai ziyara kabarinsu tsarkakka domin su karanta musu(raina dana mahaifana fansarku) maziyarta sun kasance suna karbar fansarsu da mahaifansu, cikin wannan maziyarta nasu zaka samu manya manyan malamai  da masana fikihu da manya-manyan maraji’an taklidi da muminai masu falala.
Lallai imam husaini (as) ya kira zuhuiru sai zuhairu yam kiransa ya azurtu duniya da lahira, haka ma ya kirayi ubaidullah ibn hurru ju’ufi don tallafa sai ya ki amsa kiran imaminsa ya wayi gari cikin asararru ya yi hasara duniya da lahirarsa.
Imam husaini (as) da bukukuwan juya yinsa cikin zamaninmu kadai sun kasance ma’auni majarrabta masakar sanin gaskiya da banbanceta daga karya da tantance haske daga duhu da alheri daga sharrri da falala daga kaskantuwa. , akwai daga waliyan Allah da shi’ar imam husaini da masoyansa da zasu fitinu cikin imam husaini (as) ya kasance yana musu addu’a a cikin kunutun sallarsa yana rokon ubangijinsa ( ka tsare waliyyanka daga fitinuwa cikina).
Lallai ita Ashura itace masukar jarrabwa da gwaji. Lallai daga mutane akwai wadanda suka rabauta cikinta suka samu riba, akwai kuma wadanda suka fadi suka asarantu, haka lamarin zai ta wakana har zuwa tashin kiyama.
Akwai wanda ke hidima da dukkanin abinda yake da shi daga karfinsa kuma ya sadaukar da rai mai tsada cikin tsayar da raya bukukuwan juya yin husainiyya zuwa ga bayyyana ibadojin Allah, ya kasance daga rundunar imam husaini (as) cikin sahun habibu da su zuhairu da wahab da hurru ibn yazid rayahi, akwai kuma mai tada fitina da kawo shubuhohi da sanya kayoyi da shinge kan hanya da dawwamarta sai ya dinga kawo shakka da yin isgili ga masu raya bukukuwan to wannan mutui ya kasance cikin sahun su shimru ib zul jaushi da harmala da umar ibn sa’ad da yazidu ibn mu’awiya sai ya fadana cikin fitina, sannan addu’ar imam husaini(as) ga waliyan Allah wadda yake yinta cikin kunut ba zata tattaro da shi ba.
 Shin kasan kuwa cewa mutane dubu suka kasance cikin maukaibin imam husaini (as) a kan hanyarsa zuwa karbala kafin wayewar garin goma ga muharram sun kuma ka suna sallah a bayansa suna sunbatar hannayensa masu albarka suna tamabayarsa ilimin addininsa da mas’aloli sai dai cewa ranar Ashura basu ci jarrabawa ba sun fadi yasassu babu wadanda suka rge daga cikinsu face mutane saba’in da `yan kai, domin su sun nemi duniyar imam husaini (as) ya yinda suka tsinkaya suka gano cewa imam shahada zaiyi wayewar garin goma ga muharram sai suka kunyata shi suka warware mubaya’a suka koma zuwa ga duniya yazidu ibn mu’awiya tsinannnen Allah. lallai sun kasance bayin duniya addini wani abune da yake damfare a fatar bakinsu. Suna karkata duk inda rayuwarsu ta karkata, idan an jarrabce su da bala’i sai ma’abota addini su karanta bawanda suke ragewa face kadan daga bayin Allah masu godiya. adadinsu yakai mutum dubu talatin koma fiye da haka basu fusknata basu ganewa kamar dabbobi koma ace sun fisu bata wadancananka suna daga gafalallu. sai ku sanya idaon basira ku lura yak u ma’abota hankali. bafa mai rabauta da samun nasara daga wannan jarrabawa face `yan tsiraru, sai agargadu agargadu hakika Allah ya tsaresu daga fitinuwa cikin shugaban shahidai (as)
   Wajibinmu muyi addu’a da kuma aiki nagari da kiyaye kawukanmu da tseratar da iyalanmu da kiyaye `yan’uwanmu cikin Imani daga faduwa cikin wannan jarrabawa, ya kamata muyi watsi da tada fitina da kawo matsaloli da shubuhohi, sannan cikin duk wani abu karami ko babba mu komawa masanansa mu je wurin maraji’ai masu girma domin samun fatawa daga garesu cikin kowanne batu gameda raya batun Ashura, kada wani ya yi fatawa ba tareda ilimi ba, lallai yadda al’amarin yake shi ne duk wanda ya yi fatawa babu ilimi to tya yi sauri ya nemawa kansa matsuguni cikin wuta, ya zama wajibi muyi taka tsantsan daga bayyanar da ra’ayi cikin hukunce-hukuncen Allah mu lazimci komawa masana fikihu wanda suke da hakkin yin fatawa da bayanin hukunce-hukuncen Allah, wannan shi ne abinda  lafiayyen hankali ke karba da dayantattaar halinta da da dabi’a wayayya da kur’ani mai girma da irfani madaidaici, menene bayan kin gaskiya da wuce bata.
Kan kowanne dayanmu wajibi ya yi addu’a yana mai tsarkake niyya da Allah ya datar da shi da tsayar da raya juaya yin shuagaban shahidai imam husaini (as) Allah kuma ya kimsa msa karfi da hakuri da Karin juriya da dauriya kan wannan hanyar, sai muyi koyi dan majibancinmu imam sadik (as) cikin haka a cikin addu’arsa da yake maziyartan kabarin imam husaini (as) (Allah ka jikan wadancan fusake da suka sauayasaboda rana* ka jikan wadancan iface iface da ta kasance saboda mu)
Lale lale ga ma’abota ni’ima data ni’imcesu, farin ciki ga wadannan wadanda basu banbance darensu daga ranarsu cikin hidimar imam husaini (as) da tsayar da raya juya yinsa da shirya ta’aziyya da mimbarori jaje da ciyarwa da shiryarwa da sakafantarwa, Allah ya gwabunta ladanmu da naku kan musibarmu musibar da ta su majibancinmu shugaban shahidai imam husaini (as) Allah ya kyautata mana ta’aziyya ya sanya mu da su daga cikin masu neman fansarsa tareda magajinsa abin taimakawa imam mahadi ma’abocin dawowa daga iyalan muhammadu (s.a.w)
`yan uwana cikin Imani da akidar gaskiya abinda yake wajibinmu shi ne mu yi shimfida ga daular imamin zamanimu (as) wanda zai cika ksa da adalci da bayan ta cika da zalunci da danniya, sai mu tashi da aikata wajibinmu kan yadda aka bukaci muyi, mu karu da ilimi da ma’arifa saboda Allah matsarkaki  da kuma muslunci wanda bai da karkata, musammam ma cikin kwanakin watannin muharram da safar, ya zam wajibi kanmu mu karu cikin ilimi da ma’arifa da kara karanta lamarin imam husaini (as) da juyin juya halinsa madawwami, Imani ya kasance kammalalle da aiki nagari tsarkakkakke cikakke kan hasken ilimi da ma’arifa da yakini.
Shin kuwa kasan cewa shin yakini cikin sakafar muslunci cikin makarantar ahlul-baiti (as) ya kasu zuwa martabobi uku, ana kidayasu da jigon martabobi cikin yakini sune: ilimul yakin da ainul yakini da kuma hakkul yakin.
Sannan shi yakini na da ma’anar ilimin da babu shakka ko kokwamto cikinsa, bai girgiza lallai shi kamar misalin kafaffen dutse ne iska da guguwar shubuhohi da ishkaloli da fitintunu da jita-jita da sauye-sauyen yanayi da surutai basu iya motsa shi.
Bara in baka misali cikin sanin wadannan martabobi guda uku:
Duk wanda ya hangi hayaki daga bayan bango to zai ce bayan wannan bango akwai wuta da take ruruta, to ina da ilimin yakini kan haka, idan ya kusanto kusa da wutar har ya dandani zafinta sai ya yanke da samuwar wuta sai dai cewa kuma yanzu ya samu ilimul yakin da samuwar wutar, idan kuma ya ga wutar ido biyu ya jita a jikinsa daga kusa-kusa, idan ma ya shiaga zata konashi to lallai zai kara cewa akwai wuta sai kuma yanzu ya tsallaka zuwa martabar hakkul yakini da dakuma tabbatuwarsa.
Kowanne daga cikin wadanann martabobi guda uku yana fadin wuta wuta, sai dai cewa tsakanin kowacce dayansu akwai nisa sama da kasa a wannan lokaci wanda ya yi Imani da imam husaini (as) da kuma Imani da bukukuwansa da Ashura lallai wani lokaci zaka sameshi yana ihu yana fadin (na amsa kiranka ya husaini) sai dai cewa shi yana cikin martabar ilimin yakini kamar misalin wanda ya ga hayaki daga bayan bango, dayan kuma zai ce ( na amsa kiranka ya husaini) sai dai cewa shi ta hanyar kyawunsa da girmansa (as) da kuma jin samuwarsa to shi wannan yana cikin martabar ainul yakin, amma na uku shima zai daga ya ce ( na amsa kiranka ya husaini) na amsa kiranka ya mai kira abi addinin Allah sai dai cewa hakan yana raye cikin zuciyarsa da zurfafar samuwarsa kai kace yana konuwa da balbalar wutar kaunar imam husaini(as) da soyayyarsa yana mai cudanya da hakkul yakin.
Na nakashceka wannan kissa a matsayin misali samfuri kan abinda nake fadi:
bukuwan imam husaini(as) da alamominsa  tsarkaka kamar misalin (sassarfa dawarij) wanda shi ta’aziyya ta al’umma da miliyoyi ke tarayya ciki da ake taso da dawairiji da take karkashin yankin hindiya fuskanin haram mai daraja cikin jam’in da yake cike da jama’a  mai ban mamaki suna sassarfa suna dukan kawukansu suan kiran ya husaini.
An san nau’in wannan jaje da ta’aziyya da ya dayanta da kwarjini wato(sassarfa duwairij) sakamakon yawan adadin masu tarraya cikinsa basa ma iya tafiya a sannu sannu saboda tsananin turmutsitsi suna sassarfa suna raira waken jaje da ta’aziyyam suna bugun kawukansu da hannayesu suna kiran wayyo husaini har abada ba zamu mu manta da kai ba.
Abin ban mamaki cikin wannan makoki zaka ga kowa da kowa ya yi tarraya ciki daga kowanne bangare tun daga shugabanni da wadanda ake shugabanta da `dan hauza da `dan jami’a da malami da `yan kasuwa mawadaci da talaka kai hatta manyan malamai daga marji’an taklidi cikin yanayin bai daya da tasirantuwa da tasowa suna gudu da sassarfa da kuka da kirarin ya husaini.
cikin shekarun da suka gabata ya yinda jama’a masu tarin yawa da suka taso cikin ta’aziyya kwatsam sai aka ga maraji’an taklidi cikin wannan gayya ayatollah mahadi baharul ulum ya yarda rawaninsa da alkyabbarsa a gefe ya na tattaki babu takalmi ya dukan kansa yana kiran ya husaini yana husaini.
Bayan an gama taron ta’aziyyar sai aka tambayeshi menene ya sanya shi yin haka?
Sai ya ce: ta kaka ba zan aikata haka ba cikin maukibin husaini bayan na shugabana majibancin lamarina ma’abocin zamani imamul hujja muntazar (as) yana sassarfa babu takalmi a kafarsa cikin ta’aziyya?
 Kamar yadda imam (as)  ya ke cewa: ( zan kirayeka safe da yamma zanyi maka kukan jini mayin hawaye).
Cikin kowanne zamani da wuri cikin kowacce al’umma ya zama dole a samu wayar da kai kan lamarin husaini da sakafarsa ta zama ita ke jagoranci cikin daidaiku da jama’a sannan kowanne mutum guda daga cikinmu ya zama yana taka wata rawa daga daurorin rayuwarsa cikin kowanne matsuguni ya kasance mai amsa kiran husaini (as) da isar da sakonsa (shin akwai mai taimako wanda zai taimaka mini)  sai ka zamanto daga mataimakn husaini kamar yadda sahabbansa suka kasance, kamar yadda muke fatan kasancewa madadi cikin mataimaka imamul ka’im (as)
Lallai imam sadik (as) yana tsayawa kan sahun garin daffi domin ya yi sallam ga shahidan karbala mataimaka husaini sai ya ce: aminci ya tabbata gareku yaku mataimaka Allah da manzon Allah.. ya mataimaka sarkin muminai ya mataimaka Fatima ya mataimaka baban muhammadu hassan.. ya mataimaka baban Abdullah.. babana da babata fansarku kun tsarkaka kuma kasar da aka binneku ta tsarkaka kun rabauta wallahi rabauta mai girma inama na kasance tareda ku in rabauta rabauta mai girma.
Duba fa yanzu tsakaninka da Allah su waye wadannan mutane da imam sadik (as) ma’asumi mai Magana da har yake fansarsu da babansa da babarsa sannan yake burin ace ya kasance tareda su?
Ya ya suka samu wannan matsayi mai girma da mukami madaukaki? me nene falalarsu menene darajarsu haka ta kaka muma zamu iya kasancewa tareda su daga garesu cikin rayuwarmu da rayuwarsu da mutuwarsu da mutuwarmu?
Allah ya jarraba mataimaka husaini (as)ya gwada su a wuraea da dama, lallai da farko farko mutena masu tarin yawa sun bi imam sai dai cewa yawancinsu taron bola da shara ne imam ya gaya musu cewa shifa zaije ya mutu ne ya yi shahada dajin haka sai suka watse wasu sukai gabas wasu kuma sukai yamma haka ma ya jjaraba su a daren goma ga muharram ya musu huduba sai suka amfani da wannan dare matsayin rakumi da suka rika don gudu suka gudu suka barshi kamar yadda sayyada sukaina (as) ta bamu labari babu wadanda suka rage wurinsa face yan tsiraru amma a rundunar yazidu sai ga mutum dubu talatin, mazajen na hakika da gaskiya ga akidar husaini(as) bayan koma ya fito sarari kowa ya fuskanci inda husaini (as) ya dosa babu wadanda suka kasance tareda sai su saba’in da biyu (72) wanda tarihi ya yi musu shaida ya kirayesu da (mataimaka husaini)
Da zaka karanta karbala da daren Ashura da abinda sahabbain da mataimaka suka fadi a mukamin sadaukar da rai da fansar da shi da ka ga abinda mamaki, da kuma abinda imam husaini (as) ke fadi (ni bantaba ganin wasu sahabbai mafi cika alkawali da mafi alheri daga sahabbaina ba* haka ma ban taba ganin iyali mafi biyayya da sadar da zumunci daga iyalina ba* baki dayanku Allah ya saka muku da alheri)
 Wannan na nuni da cewa sahhaban imam husaini (as) sun kasance mafi daukakar martaba da girma da yanayin da wasu basu gabace su ba baku ma wanda zai iya riskarsu, kamar yadda sarkin muminai ali (as) ya bada labari da hakan ya yinda ya isa karbala cikin tafiyarsa zuwa siffaini ya ce: nanne madurkusar matafiya nanne mafadar masoya shahidai, wanda ya gabace su bai iya tsere musu, wanda zai zo daga bai iya riskarsu.
Lallai sun sami darajar shahada cikin tafarkin Allah, sun kuma nuna mafi kayatarwar jarumtaka da sadukarwa a daidai lokacinda wasu suka ja da baya suka sallama karfin dagawa da sakamakon tsananin kiayyarsu ga mutuwa cikin tafarkin Allah saboda son da sukewa duniyarsu da matansu da `ya`yansu da gidajensu.
Hakika daren Ashura ya yayewa sahabban imam shamaki har sai da ta kai sun ga masukansu a aljanna, dayansu ya kasance yana tunkarar kisa don ya samu damar saduwa da matarsa a aljanna ya rungumeta, hakika Allah ya dage musu labule ya shimfida musu hanya matattakala ya gwabunta musu lada.  
Lallai sahabban imam husaini (as) mazaje ne da suka gasgata alkawalin da sukaiwa Allah suka taimaka masa tareda karancinsu suka ba da jininsu sadaka suka tunkari mutuwa da dukkanin maraba da fadadar kirji, suka tunkari kibbai da jikkunansu suka tarbi takubba da fusakensu suka fuskanci mashi da makogaransu suka sadukar da rayukansu domin baiwa imam husaini (as) kariya suna halin fadin bamu da uzuri wurin manzon Allah (s.a.w) idan muka bari aka kasha jikansa husaini (as) alhalin mu kuma muna raye fatar idaniyarmu na kiftawa, wallahi ba zamu taba barin haka ta faru matukar muna raye har sai an kasha mu muna masu bashi kariya.
Sai daya daga cikin makiyansu wato amru ibn hajjaju ya siffanta su yana mai cewa: (shin kun san da suwa kuke yaki kuwa? Kadai dai kuna yaki da jarumai mahayan dokkai na kasa ma’abota basira masu neman mutuwa`yan gani kasheni)
 Ranar ashura an cewa wani mutum tareda umar ibn sa’ad: kaiconku shin yanzu kun kashe zuariyar manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: lallai da kaga abinda muka gani da kaima kayi abinda muka yi, wasu ayari sun taso kanmu hannayesu na rike da kawukan takubbansu kai kace zakuna dake kishirwar shan jini, hagu da dama sai kashe mahaya suke sunan tunkara mutuwa basu damu da karbar alakawalin aminci ba basu kwadayi kudi ko dukiya, babu abinda ya isa ya shiga tsakaninsu daga gangara zuwa tafkin mutuwa da mamaye mulki, kai da mun kame daga yakarsu kankanin lokaci da sai sun cin tsakiyar rundunarmu baki dayanta, to mai kake so muyi da su `dan shegiya)
Hakika haka sahabban imam mahadi (as) suke wanda shi ne zai dau fansar shugaban shahidai (as) ya kuma ya cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya
An karbo daga imam sadik (as) ya yinda imam husaini (as) ya yi shahada mala’iku sun fashe da kuka suna fadin (yanzu haka za aiwa husaini zababbenka `dan annabinka? Sai Allah ya tsayar musu da inuwar imam mahadi (as) ya ce musu: da wannan zan daukarwa wannan fansa.
    Mataimakansa suna siffofi da kebantattun abubuwa irin wanda sahabban imam husaini (as) ke da shi ( suna kwana ibada ba tareda bacci su kuma wayi gari kan dokunan yakinsu* sufayen dare don cetae ranarsu* kai kace zukatansu taman karfe ne shakka ba ta cudanyarsu* cikin zartin Allah sunfi garwashi zafi* sannan takensu shi ne ina masu daukar fansar jinin husaini)
Sabunta Ashura da tsayar da raya bukukuwan ta’aziyyar husaini a watannin muharram da safar ba wani abu bane face tanadi ga bayyanar imam mahadi (as) lallai shugaban shahidai shi igiyar asadarwa ne tsakanin cika makin annabawa muhammadu da cika makin wasiyyai wanda akai masa suna da sunan annabi musdafa(as)   
Sannan wane sirrine na husaini da yake tattaro al’ummu a tsawon tarihi da zamani tareda banbancin addininsu da mazhabobinsu da makarantusu na tunani da akidu da yakai ga hatta mawakin zamani ke kada jitarsa don wake waki’ar husaini wadda ita alamace daga soyayya da ke tareda dan adam.
Hakika husaini (as) shi ne tushe jigo lallai mutumtakarsa na nuna cewa shi cikakken mutum me goyon bayan adalci mai kin zalunci madaukaki kan barin karkata daga tarkacen duniya. Dukkanin zukata masu kin kaskanta da zaluci suna son irin samfurin imam husaini (as) suna karkata da shiriyuwa da shiriyarsa suna koyi da halayensa madaukaka


Umar Alhassan Salihu 
Faroukumar66@gmail.com
+989335382587

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: