bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:02:45
duk wanda ya ziyarci Husain (a.s) yana mai kimanta haka, kuma ba don asharanci da taqama da yin hakan ko da riya da nuna kai ba, Allah zai wanke shi daga zunubbai kamar yanda ake wanke tufa a cikin ruwa daga datti kuma zai rubuta masa a kan kowane taku ladan aikin hajji kuma duk sanda ya daga kafa zai rubuta masa ladan umrah. 15
Lambar Labari: 144
Daga Muhammad bn Muslim, daga Abu-Jafar (a.s) ya ce: "da a ce mutane sun san abin da yake cikin ziyarar Imam Husain (a.s) na falala da sun mutu saboda shauki, da sun gutsure kawunansu saboda hasarar da suke ganin sun yi na rashin zuwa” sai na ce ko menene cikin ziyarar Husainin da zasu yi hakan saboda rashin yin ta? Sai ya ce: duk wanda ya je masa saboda kauna, Allah Ta’ala zai rubuta masa ladan hajji dubu 1000 karbabbiya, da kuma umra dubu 1000 karbabbiya, da kuma ladan shahidai dubu daga shahidan badar, da  ladan masu azumi 1000,da ladan sadaka dubu karbabbiya da kuma ladan ‘yanta bayi 1000 saboda Allah, sannan kuma ba zai gushe ba ana ba shi kariya  a wannan shekarar daga dukkanin cututtuka wadanda suke daga shaidan, sannan kuma Allah zai wakilta masa babban mala’ika da zai rika kiyaye shi daga gabansa da bayansa, da kuma damansa da hagunsa, da kuma kasansa da samansa, to kuma idan ya mutu malaikun rahama zasu zo masa, kuma zasu zo  wajen wanka da wajen sanya likafaninsa, zasu kuma naima masa gafara, sannan su raka shi kabarinsa tare da nema masa gafara, bayan nan kuma za’a buda masa kabarinsa iya ganinsa, sannan za a amintar da shi daga matsin kabari da kuma tambayoyin munkar da nakir, sannan a bude masa kofa kai tsaye zuwa aljanna a kuma ba shi littafinsa ahannunsa na dama, sannan kuma za a bashi wani haske da zai haske tsakanin gabas da yamma, mai kira zai yi kira yana mai cewa :wannan yana daga cikin maziyarta Imam Husain (a.s), babu wani mutum face sai ya yi burin kasancewa cikin maziyartan Imam Husain (a.s)13 

HADISI NA SHABAKWAI
Daga Zuraihu Al-mahrabi ya ce: na fada ma Abu Abdillahi cewa me ya sami mutane na da dangi na wanda a duk lokacin da na ba su labarin ladan wanda ya ziyarci kabarin Imam Husain (a.s) sai surika karyata ni su rika cewa lallai kana yiwa Ja’far bin Muhammad karyane kawai! Sai Imam ya ce: "ka rabu da mutane su rika tafiya yanda suke so, wallahi tabbas Allah yana alfahari da maziyarcin Imam Husain, (a.s) sannan kuma tawagar malaiku makusanta da kuma madaukan Al’arshin ubangiji zasu shiga cikin tawagar maziyartansa har zuwa wani lokaci da Allah zai ce da su: kun ga wadannan maziyartan Husain (a.s) din sun je ziyarar sa ne saboda kaunar su gare shi da kuma kaunar su ga Fatima diyar Manzon Allah (s.a.w) saboda haka ina rantsuwa da daukakata da girmana, tabbas sai na shigar da su Aljannata wacce na tanada musamman saboda waliyyai na da annabawana da manzannina, ya ku mala’ikuna! Wadannan su ne masoyan Husain (a.s) masoyin Muhammad masoyina, kuma duk wanda yake so na to ya so masoyina, kuma duk wanda yake son masoyina to ya so dukkan masoyinsa, domin duk wanda yake kin makiyi na ya zama hakki a kai na, da na azabtar da shi da mafi tsananin azabata kuma na kona shi da zafin wuta ta, kuma na sanya jahannamata ta zama makoma da mazauni a gare shi na azabtar da shi da azabar da ban taba  azabtar da wani daga cikin halittuna ba. 14

HADISI NA SHA TAKWAS 
Daga Kudamatu dan Malik, daga Baban Abdullahi (a.s) ya ce: "duk wanda ya ziyarci Husain (a.s) yana mai kimanta haka, kuma ba don asharanci da taqama da yin hakan ko da riya da nuna kai ba, Allah zai wanke shi daga zunubbai kamar yanda ake wanke tufa a cikin ruwa daga datti kuma zai rubuta masa a kan kowane taku ladan aikin hajji kuma duk sanda ya daga kafa zai rubuta masa ladan umrah. 15
  
HADISI NA GOMA SHA TARA
Daga Harun dan Kharijata, daga baban Abdullahi (a.s) ya ce a lokacin da na tambaye shi,  meye ladan wanda ya je ziyarar kabarin Imam Husain (a.s) yana mai sane da matsayinsa, kuma  yana mai nufar kusanci ga Allah da ita da kuma neman gidan lahira?  Sai ya ce: "ya Harun!  Duk wanda ya je kabarin imam Husain (a.s) yana mai ziyararsa kuma yana sane da matsayinsa kuma yana nufin Allah da ita, Allah zai gafarta masa duk abin da ya gabata na zunubansa da kuma abin da ya jinkirata, sannan ya rantse sau uku yana mai cewa: ashe ban rantse maka ba! Ashe ban rantse maka ba! 16.

HADISI NA ASHIRIN 
Daga Abdullahi dan Maimunal Qaddahee daga baban Abdullahi ya ce a lokacin da na ce masa: meye ladan wana ya ziyarci kabarin Husaini (a.s) dan Ali (a.s) yana mai sanin hakkinsa da matsayinsa, kuma ba tare da da takama ko girman kai ba?  Sai ya ce:” Allah zai rubuta masa hajji dubu (1000) karbabbiya da kuma umrah dubu (1000) karbabbiya, idan kuma ya kasance dan wuta ne za’a rubuta shi a cikin ‘yan Aljanna, kuma ba zai gushe ba ana shigar da shi cikin rahamar Allah har abada. 17

HADISI NA ASHIRIN DA DAYA
Daga Abdullahi dan maskan ya ce: na je wajen baban Abdullahi (a.s) a lokacin wasu mutane sun zo masa daga khorasan sai suka tambaye shi a kan ziyarar kabarin  Imam Husain (a.s) da abin da yake cikinta na falala? Sai Imam ya ce: " babana ya bani labari shi ma daga kakana lallai ya fadi cewa duk wanda ya ziyarce shi yana mai fuskantar ubangiji da wannan aiki, Allah zai fitar da shi daga cikin zunubai kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi, sannan malaiku zasu rake shi aya yin tafiyar shi suna shawagi da fukafukansu a saman kansa cikin sahu har zuwa lokacin da zai dawowa iyalinsa, sannan kuma mala’iku suna nema masa gafarar Ubangiji, sannan kuma rahama ta sauka gare shi daga saman al’arshin Allah, a lokacin mal’iku zasu fada masa cewa lallai ka rabauta kuma wanda ka ziyarta shima ya rabauta. Sannan a tabbatar da kariya gare shi da kuma iyalinsa. 18



HADISI NA ASHIRIN DA BIYU
Daga Muhammad dan Muslim daga baban Ja’far ya ce : " ku umurci y’an shi’armu akan yawan ziyarar Husain (a.s)  domin hakan yana kara arziki kuma yana kara tsayin kwana kuma yana yin kariya daga mummuna, sannan kuma ku sani cewa ziyartansa wajibi ce ga wanda ya yi imani da cewa wilayancinsa daga Allah ne”. 19

HADISI  NA ASHIRIN DA UKU
Daga Abdullahi bin Yahya Al-kahili, daga Abu Abdillahi ya ce: "duk wanda yake so ya kasance cikin karama a ranar kiyama kuma a cikin ceton muhammad (s.a.w) to ya zamo cikin maziyartan Husain (a.s) zai samu lada, falala da karama a wajen Allah, kuma idan ya roki gafarar ubangiji a kan zunubansa koda sun kai kwatankwacin saharar "aalaj” da kuma girman dutsen "tuhama” da kuma kunfar kogi sai ya gafarta masa,  hakika Husain  (a.s) an kasha shi bisa zalunci da cutarwa cikin kishi, shi da iyalai da mabiyansa”. 20

HADISI NA ASHIRIN DA HUDU
Daga Salih An-niyali ya ce: baban Abdullahi  ya ce: wanda ya ziyarci husaini (a.s) bn Ali (a.s) yana mai sane da haqqinsa da matsayinsa,  zai zamo dai-dai da wanda ya yi hajji dari tare da manzon rahama, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. 21

HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR
Daga Musa bin Kasim Al-hadramy, ya ce Abu Abdullahi (Ja’afar) ya sauka a Najaf a farkon imamancin Abu Ja’far (Bakir) (a.s) sai ya ce: "ya Musa! ka tafi zuwa babbar hanya ka tsaya ka jira wani mutum mai zuwa daga nahiyar garin "qadisiyya” idan ya zo kusa da kai kace masa  akwai wani daga cikin ‘ya’yan Manzon Allah  (s.a.w)  yana kiransa, tabbas na san zai zo tare da kai” na tafi na tsaya a kan hanya na jima a tsaye ga zafin rana har na kusa zakuwa na koma domin yin bankwana sai kwatsaham na hangi tahowar wani abu kamar mutum yana tafiya a kan rakumi, ban gushe ba ina kallonsa har sai da ya kusanta zuwa gare ni, sai na ce da shi: ya kai wannan bawan Allah! Ka zo wani mutum daga ‘ya’yan Manzon Allah (s.a.w) yana kiran ka zuwa gare shi, ya kuma siffanta min kai, sai ya ce: kai ni gurinsa, ni ko na iso da shi gurin da suke ya sami guri ya daure rakuminsa kusa da hema, sai imam (a.s) ya ce ya shigo, nima na kusanta na tsaya kusa da hemar ina sauraren maganarsu amma ba na ganinsu, sai Imam Abu Abdullahi ya ce masa : daga ina ka zo?
Sai ya ce: daga nesa, Yemen.
Sai imam ya ce: kai daga guri kaza da kaza da kaza ko?
Sai ya ce eh:  ni daga guri kaza da kaza na zo (ya fadi sunan gurin da imam ya fada). 
Sai Imam (a.s) ya tambaye shi: saboda me kazo nan?
Sai ya ce: na zo nan ne saboda ziyarar Husain (a.s).
Sai Imam ya ce: me kuke gani a cikin ziyararku gare shi?
 Sai ya ce muna ganin albarka a kawukanmu da iyalanmu da ‘ya’yanmu da abubuwan rayuwarmu da biyan buqatunmu.
Sai imam (a.s) ya ce: "shin ba ka so in kara maka wata falalar wannan ziyarar ba ya kai wannan dan’uwan yamanawa?!
Sai ya ce: kara min ya dan Manzon Allah  (s.a.w) . 
Sai imam ya ce: "lallai ziyaran imam Husain (a.s) tana daidai da hajji karbabbe kuma tsarkakke tare da Manzon Allah  (s.a.w) .”
Sai ni kuma na yi mamaki shi ko imam (a.s) ya kara da cewa "kai daidai yake da hajji biyu tare da Manzon Allah  (s.a.w)  ni kuma mamaki na ya karu. 
Sai na ji Imam (a.s) ya kara da cewa dai-dai yake da hajji uku, kai bai gushe ba yana karawa har sai da ya kai ga cewa yana da ladan hajji talatin karbabbiya tsarkakakkiya tare da Manzon Allah (s.a.w)”. 22

HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA
Daga Abdullahi dan Maskan, ya ce: Abu Abdillahi ya ce: "lallai Allah mai girma da daukaka, yana tajalli ga maziyartan Imam Husain (a.s) kafin ya yi tajalli ga ma’abota Arfa, kuma yana biyan bukatun maziyartan Husain (a.s) ya gafarta musu sannan kuma ya ba su ceton wanda suka nema wa sannan ya yiwa ma’abota Arafa hakan. 23.

HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Daga Sulaiman dan Khalid: daga Baban Abdullahi (a.s) na ji yana cewa : " lallai Allah yana da wasu sa’anni, fiye da dubu da yeke yin tanajin azaba ga wanda ya ga dama, kuma ya yi gafara ga wanda yaga dama, kuma yana gafarta wa maziyartan Husain gafartawa ta musamman a irin wadannan lokutan ya kuma gafarta wa iyalansu da kuma wanda suka nema wa gafara a wannan lokacin ko wanene shi, kuma gafara ta har abada, sai na tambayi Imam da cewa, koda wanda zasu nema ma gafarar dan wuta ne? sai ya ce: koda dan wuta in dai ba nasibi ba ne (makiyin iyalan Manzon Allah (s.a.w) ). 24.


HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS
Daga Abdullahi dan Shu’aib At-tamimi, daga baban Abdullahi ya ce: A ranar alqiyama mai kira zai yi kira yana mai cewa: ina ‘yan Shi’an ali Muhammad?!!!  Sai dandazon mutane su riqa mikewa wadanda babu masanin adadinsu sai Allah madaukaki, sai su tsaya gefe guda sannan wani mai kiran ya kara kira da cewa: Ina maziyartan baban Abdullahi (a.s)?!!!  sai da yawa daga cikin mutane su mike, sai Allah ya ba su umurni yana mai cewa ku koma hannun wanda kuke so zuwa Aljanna, a lokacin ne wasu zasu rike hannun wani (wanda ya taba cutar da su)  ya ce nine fa, na taba maka kaza da kaza ranar kaza!  Amma duk da hakan ba zai fasa jagorantarsa zuwa aljanna ba 25.

 
HADISI NA ASHIRIN DA TARA
Daga Isma’il dan Jabir, daga abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Lallai Imam Husain an kasha shi cikin bakin ciki, don haka babu wani bawa da zai je ziyarar sa cikin bakin ciki face Allah ya mayar da shi cikin hali na farinciki 26.


HADISI NA TALATIN
Daga Muhammad dan Muslim, daga Abu Ja’afar (a.s) ya ce: "lallai Imam Husain dan Ali ma’abocin karbala an kasha shi a cikin bakin chiki, cikin kishirwa, cikin bacin rai, kuma hakki ne ga Allah cewa babu wani mai bacin rai ko bakin ciki ko mai zunubi ko mai damuwa ko mai jin kishirwa ko ma’abocin talauci da zai je ziyarar Imam Husain (a.s) sannan ya yi du’a’i a wajensa kuma ya yi kamun kafa da Husain zuwa ga Allah mabuwayi face sai ya tafiyar masa da bakin cikinsa, ya kuma ba shi abin da ya roka ya kuma gafarta masa zunubansa ya kuma kara masa tsayin kwana, ya kuma fadada masa arzikinsa, to sai ku yi la’akari ya ku ma’abota hankali!” 27.


HADIS NA TALATIN DA DAYA
Daga Yunus dan zabyana, daga Abu Abdullahi ya ce; " duk wanda ya ziyarci kabarin Husain (a.s) a ranar arafa, Allah zai rubuta masa ladan miliyan guda na hajji tare da Qa’em (a.s) da kuma ladan Umra miliyan tare da ma’aikin Allah (s.a.w) da kuma ladan ‘yantar da bayi miliyan guda, da dawakai miliyan guda da aka dora kaya kansu aka sadaukar da su saboda Allah, sannan Allah zai kira shi da suna Siddiq (bawa mai gaskata alqawarin ubangijin shi), sai mala’iku su fadi cewa lallai Allah ya tsarkake shi a saman al’arshinsa kuma na kasa zasu rika kiransa da suna "karub” mai yawan juyayi. 28. 


HADISI NA TALATIN DA BIYU
Daga Bashir Al-duhan, ya ce : daga Jafar dan Muhammad ya ce: " Duk wanda ya ziyarci kabarin Imam Husain (a.s) a ranar Arfa yana sane da matsayinsa a gurin Allah, Allah zai ba shi ladan hajji dubu (1000) da umura dubu (1000)  da yaki dubu (1000) tare da Annabi mursali, kuma duk wanda ya ziyarce shi a farkon Rajab Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa kai tsaye. 29.


HADISI NA TALATIN DA UKU
Daga Malik Al-jahani, daga abu ja’afar Albaqir (a.s) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci Imam Husain a ranar ashura har ya tsaya yana kuka a gurinsa, a ranar alqiyama zai sadu da ubangijinsa yana da ladan hajji dubu sau dubu biyu da umura da jihadi tare da Manzon Allah (s.a.w) da kuma A’imma (s.a). 30


HADISI NA TALATIN DA HUDU
Daga Abu Bashir, Daga Abu Abu Abdillahi (a.s), daga Hassanul Mahbub, shi kuma daga Abi Hamza, Daga Ali dan Husain (a.s), sun ce: duk wanda yake son ya yi hannu da Annabawa dubu dari da dubu ashirin da hudu  (124,000) to  ya ziyarci Imam Husain (a.s) ranar nisfu sha’aban, domin kuwa ruhinan Annabawa suna nemo izinin Allah sai a ba su izinin zuwa, daga cikinsu har da Ulul Azmi sai muka tambaye shi su waye Ulul-azmi?  Sai ya ce su ne Nuhu, Ibrahim, Musa, Isa da kuma Muhammad (s.a.w) sai muka kara tambayar sa meye ma’anar kalmar Ulul-azmi?
Sai ya ce sune wadanda aka aikosu zuwa ga dukkan halittun Duniya, na gabashisu da yammacinsu, mutanesu da Aljaninsu”. 31

HADISI NA TALATIN DA BIYAR
Daga Yusuf dan zabyana ya ce: baban Abdullahi ya ce: duk wanda ya ziyarci Imam Husain a daren nisfu sha’aban da kuma eidin karamar sallah da daren arfa na daya daga cikin shekarun rayuwarshi Allah zai ba shi hajji dubu cikakku da umura dubu karbabbu, sannan a biya masa bukatu dubu daga cikin bukatunsa na duniya da lahira.” 32. 


HADISI NA TALATIN DA SHIDA
Daga Abu Sabahi Al-kinani ya ce na ji Abu Abdullahi yana cewa: "lallai a kusa daku akwai wani kabari wanda babu wani mai matsala da zai je masa face Allah Ta’ala ya yaye masa, kuma ya biya masa bukatunsa, kuma lallai a gurinsa akwai mala’iku  dubu hudu wanda suke gurin suke kuka tun ranar da aka karbi ransa, duk idan kuka je ziyaransa sai su raka ku, idan kuka yi ciwo zasu zo ziyartanku, idan kuma kuka rasu zasu raka gawarku. 33.


HADISI NA TALATIN DA BAKWAI
Daga Ali dan Maimun, ya ce: na ji baban Abdullahi yana cewa : "Da dayan ku zai je hajji dubu, amma bai je ziyaran Husain dan Ali ba to zai zama yabar wani hakki ne daga cikin hakkokin Allah madaukaki” sai aka tambaye shi kamar ya? Sai ya ce: hakkin Imam Husain (a.s) farilla ne a kan kowane musulmi. 34.


HADISI NA TALATIN DA TAKWAS
Daga Zaidus-Shahham, daga Jafar dan Muhammad alaihimus salam ya ce:
"Duk wanda ya ziyarci Imam Husain (a.s) a ranar nisfu sha’aban Allah zai gafarta masa abin da ya yi na zunubi da wanda zai yi nan gaba, kuma duk wanda ya ziyarce shi a ranar arafa Allah zai rubuta masa ladan hajji dubu karbabbu, da kuma umara dubu karbabbu, kai duk wanda ya ziyarce shi a ranar Ashura kamar ya ziyarci Allah ne a Al’arshinsa”. 35.


HADISI NA TALATIN DA TARA
Daga Zaidu-Shiham, daga Jafar bn Muhammad Assadiq (a.s) ya ce: duk wanda ya ziyarci Imam Husain a daren nisfu sha’aban Allah zai gafarta masa abin da ya yi na zunubi da wanda zai yi, sannan kuma duk wanda ya ziyarce shi a ranar arfa Allah zai rubuta masa hajji dubu karbabbu, kuma duk wanda ya ziyarce shi a ranar Ashura kamar wanda ya ziyarci Allah Ta’ala ne a kan Al’arshinsa. 36. 


HADISI NA ARBA’IN
Daga Abu abdullahi Imam Sadiq (a.s) ya ce: "duk wanda ya ziyarci Imam Husain (a.s) yana mai sane da matsayinshi Allah Ta’ala zai rubuta shi cikin mafiya daukakan masu daukaka”. 38.


1. Ibn qaulawaih   kamel e ziyaraat 253 v2
2. kamel e ziyaraat 257 H9
3. kulaini kaafi 4;580 hd no. 1
4. kulaini kaafi 4: 581 hd 3
5. kulaini kaafi 4:581 hd5
6. kulaini kaafi 4:581 hd 7
7. ibn kaulawaih kamel e zeyaraat 254 hd 3
8. kamel: 258 hd 3.
9. kamel e ziyaraat 259 hd 1.
10. kamel 260: hd 2.
11. kamel 340 hd 4.
12. Ibn kaulawaih kamel 268 hd 1.
13. Ibn kaulawaih kamel 270 hd 2.
14. Ibn kaulawaih kamel 273 hd2.
15. Ibn kaulawaih kamel 274 hd 3.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: