bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:12:34
Abdullah bin Ja'afar (mijin sayyida Zainabul kubra 'yar Sayyida Fatima salamullahi alaihima), yana daga cikin mafifitan masu kyauta da sadaukarwa na zamanin shi. Wata rana zai wuce ta wata gonar Dabino, sai ya ga wani Bawa yana aiki a gonar, a daidai lokacin kuwa an kawo wa Bawan nan abincinshi, ya dakata da aikin ya tawo inuwa domin ya ci abincin, sai ga wani Kare yazo gurin yana kada bindin shi alamun yana jin yunwa.
Lambar Labari: 145
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

SADAUKARWAR WANI BAWA
Abdullah bin Ja'afar (mijin sayyida Zainabul kubra 'yar Sayyida Fatima salamullahi alaihima), yana daga cikin mafifitan masu kyauta da sadaukarwa na zamanin shi.
Wata rana zai wuce ta wata gonar Dabino, sai ya ga wani Bawa yana aiki a gonar, a daidai lokacin kuwa an kawo wa Bawan nan abincinshi, ya dakata da aikin ya tawo inuwa domin ya ci abincin, sai ga wani Kare yazo gurin yana kada bindin shi alamun yana jin yunwa.
Sai Bawan nan ya sanya wa karen nan balli daga abincin, karen nan ya cinye, sai Bawan ya dada ballar masa, karen nan dai ya cinye alamun yana jin matukar yunwa, sai Bawan nan ya tura masa dukkan abincin.
Sai Abdullah ya tambayi Bawan cewa: Abincin Rana nawa kake dashi? Bawan yace: wannan dai da ka gani shikenan. Sai Abdullah ya kuma tambayar shi: to me yasa ka gabatar da kare a kanka? Bawan yace: wannan karen daga nesa yake kuma yana matukar jin yunwa, dan haka bani son in bar gurin nan na bar shi cikin wannan hali na yunwa, ba zan sami nutsuwa ba.
Abdullah ya ci gaba da tambaya: To kai kuma ya zaka yi da yunwar yau? Da wanne abinci zaka magance ta? Sai Bawan ya ce: Da hakuri da juriya zan lallaba zuwa dare. Da Abdullahi ya ga irin wannan dattaku da sadaukarwa ta wannan Bawa, sai yace: wannan Bawa yafi ni sadaukarwa; saboda yabawa da kuma karfafa aikin alkhairi, sai Abdullah ya Sayi wannan Gona da duk abin da yake cikinta da kuma Shi kanshi Bawan, daga gurin mai su, sannan ya 'yanta Bawan ya kuma bashi gonar da duk abin cikinta.
Allah Ya azurtamu kuma Ya bamu zuciyar kyautatawa mabukata.
Wannan labari sai ya sake tuna min da labarin wani bawan Allah mai matuqar kyauta da taimako a gurin da ya DACE, ana ce mashi Hatami Ta'i, wadda har ana buga misali da shi, shi Hatami Ta'i ya kasance mai matukar yin kyauta, to da Allah Yayi mashi rasuwa, sai dan uwanshi yace sai ya gaji irin halin dan uwanshi na kyauta.
Da jin haka sai mahaifiyar su, tayi badda kama (kamar tsohuwa mai yin Bara), sai taje wajenshi tana neman taimako, yasa aka bata, da ta fito sai dan anjima kadan ta kuma komawa, yasa aka kuma bata, an kuma dan jimawa sai ta koma a karo na uku, sai yace wai wannan ba tsohowar da tazo dazu bace? Sai yace baiwar Allah kinzo kin kuma zuwa haka!!!
Sai ta bude fuskarta, tace dashi: ai na gaya maka Marigayi Dan uwanka ba nan ba!!! Domin sai da na gwada shi kamar haka har sau saba'in, amma bai kosa ba, wato duk zuwa sai ya bani, duk da ya shaida mutun daya ne yake zuwan mashi haka.
***


IDAN ANYI MAKA MUMMUNA; KA MAYAR DA KYAKKYAWA
Wata rana wani mutumi yaje gaban Imam Sajad (AS) -daya daga cikin jikokin Annabi (Sallallahu alaihi wa Alihi), a gaban mutane yana basu tarbiyya. Mutumin ya fara gaya mashi maganganu munana, wato zagi da cin mutunci.
Amma sai jikan Annabin nan bai tanka mashi ba, wato bai bashi jawabi ba, bayan mutumin ya gama ya tafi, sai Imam Sajad (AS) yace da 'yan majlisin: Kun ji dai abin da mutumin nan ya fada min yanzu ko? Suka ce Eh! Sai yace: To ku biyo ni muje gurinshi ku ji amsar wannan batanci da yayi min.
Duk suka tashi kuwa, suna cewa lallai kam bai kamata a qyale shi ba, muje a bashi jawabi!!! Sai Imam Sajad (AS) ya dau hanya suna biye dashi, yana tafiya yana karanta wannan Ayar mai tsarki:
"Wadanda suke ciyar wa a cikin sauqi da tsanani kuma suke masu hadiyewar Fushi, kuma masu Yafe wa mutane laifi. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa". (Sura Aa'li Imran aya ta 134).
Wanda ya ruwaito wannan al'amari yace, tunda muka ji Imam yana karanta wannan Ayar muka san cewa, Imam da kyakkyawa zai maida mashi amsa.
Bayan da Imam (AS) ya isa kofar gidan mutumin, ya kira shi, yana cewa ku gaya mashi, Ali dan Husaini ne yake sallama dashi. Da mutumin nan yaji, sai a zatonshi shine Imam yazo ne ya mayar mashi da kamar yadda yayi mashi koma fin haka!
Da Imam yaga mutumin sai yace dashi:
Ya kai dan uwa kaje wajena ka fadi wasu munanan maganganu dangane dani, idan daga cikin munanan da ka fada akwai su a tare dani, to ina rokon Allah da Ya gafarta min, kuma idan duk abin da ka fada basu tare dani, to kai kuma Allah Ya gafarta maka.
Da jin haka sai mutumin nan ya Sumbaci goshin Imam yana mai cewa: duk abin da na fada maka babu su a tare da kai, nine mafi sifatuwa da hakan.
Allahu Akbar!!! 'Yan uwa mu dubi rayuwar mu ta yau da kullum da junanmu, mu kyautata zamantakewarmu da yafiya a tsakaninmu, sai muga mun sami ingattacciyar rayuwar gidaje biyu (Duniya da lahira).
Allah Yasa mu rabauta amin.
***



FALALAR ALLAH TA GAME KO'INA
An taba yin wani mutun mumini a zamanin da can. Matanshi ma su biyu muminai masu kyawawan dabi'u. Sai wata rana a mafarki yaga wani mutun yana cewa dashi, Allah madaukakin sarki Yayi maka alk awarin tsawon rayuwa a wannan duniyar.
Amma rabi daga cikin tsawon rayuwar za ta kasance Sassauka da walwala tare da yawan arziki. Ita kuma daya rabin, zata kasance cikin kunci da talauci. Dan haka yanzu sai ka zaba, wanne bangare ne kake so ya kasance a farko, kuma wanne bangare zai kasance a gaba? Allah Ya baka zabi akan wannan al'amari.
Sai muminin nan yace, to a bashi dama ya tuntubi matanshi domin yayi shawara dasu, dan suma bangare ne na rayuwarshi.
Kashegari da safe sai ya zayyanawa matan nan nashi abin da faru gareshi, sai matan suka shawarceshi da ya nemi kyakkyawar rayuwa a farko, inyaso sai yayi kyakkyawan amfani da ita. Allah zai iya yi musu lutfi, Ya cika musu sauran rayuwar su da falalarShi mara iyaka.
A dare na gaba sai ya kuma ganin shi waccan mutumin dai da yazo mashi jiya a mafarki. Ya tambaye shi, kamar haka: to yaya wanne ka zaba? Sai muminin yace mashi, na zabi kyakkyawar rayuwa a farko.
Sai kuwa daga sannan duk rayuwarsu ta canja, arziki ta ko'ina da walwala.
Sai matan nashi suka kuma shawartashi da yayi amfani da abin da Allah Ya bashi domin Shi Allah din, ta hanyar kula da kyautatawa dangi, makwabta da sauran mabukata bayin Allah. Suka ci gaba dai da bashi shawarwarin yadda zai yi amfani da dukiyar da ni'imar da Ubangijinshi Ya bashi ta kyakkyawar hanya.
Ana haka a kwana a tashi sai rabin rayuwar tashi yazo karshe, dan haka yanzu saura daya rabin wadda rayuwarshi za ta kasance cikin Wahala da Qunci.
To sai waccan mutumin ya kuma zuwar mashi a mafarki yana gaya mashi cewa: Allah mai lutfi da rahma Ya mayar da daya rabin na rayuwarka shima zai kasance cikin walwala da yalwar arziki, domin ya zama daga cikin ladan ka na kyakkyawan ayyukan ka da kyautatawarka da kayi da lafiyar da arzikin da Allah Ya baka a rabin farko.
Allah Akbar!!!
Allah kenan Buwayi gagara misali, mai kowa mai komai, Wanda Taskarshi bata karewa, Shine mai bayarwa a Da Can da Yanzu, kuma Bai daina bayarwa ba. Wanda baya yin Bacci ko gyangyadi, kodayaushe Qofar rahmarshi da kyautatawarshi a bude take ga kowa. Shi ba marowaci bane.
Rabbana a'tina fiddunya hasanatan wa fil a'khirati hasanah.
***


QWAQWALWA BA TA YIN QASA A GWIWA WAJEN KARBAR GASKIYA
Shi kuwa labarin mu na yau na wani Sarki ne da aka taba yi a zamanin da can. Sarkin kuwa ya quduri aniyar ya gina Dan qaramin birni ne, wadda ba a taba samun kamar shi a haduwa ba, kuma wadda ba za a iya samun wani mai kallon qurilla din da zai iya ganin ko fitar da aibu ko naqasun wannan birni ba.
Hakan aka yi kuwa, Yasa aka qera mashi wannan birni wadda komai yaji ta fuskar kamala da haduwa. Mutanen qasar kuwa suka bayar da shaida cewa, lallai kam ba a taba samu ba a baya da yanzu birni hadadde kamar wannan.
Amma sai wani mutum daya da yace: inda zan sami aminci daga dukkan cutarwa ko barazana, da na fadi aibu ko naqasun wannan birni.
Sarki yace mashi, ka aminta. Fada mana matsalarshi. Sai mutumin yace wannan birni yana da naqasu guda biyu:
Na farko shine, Kai sarkin wannan birni, wata rana zaka mutu kuma shi wannan birni zai koma hannun wasu ne.
Na biyu shine bayan kai din kuma, Shi wannan birni wata rana zai LALACE.
Sai sarkin nan yace: kash!!! Me yafi wannan al'amari muni kuwa! Sai ya cewa mutumin, to yanzu gaya mana yadda za a iya gujewa wadannan aibobi biyu.
Sai mutumin yace:
ka gina gidan da, zai kasance bashi da naqasu kuma ba zai lalace ba, kuma ba zai gushe ba har abada, kuma wadda kai ma zaka iya rayuwa a cikinshi, rayuwa ta har abada kana kuma kana matashi babu tsufa.
Bayan Jin haka, a yayin da Sarki ya shiga cikin gida, sai yake bai wa 'yarshi labarin abin da ya faru, sai 'Yar tashi ta gaya mashi cewa: LALLAI BA A TABA SAMIN MUTUMIN DA YA FADA MAKA GASKIYA BA IRIN WANNAN MUTUMIN A WANNAN FADAR TAKA.
Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya dada mana himma da kuzari na muhimmantar da dayar duniyar tamu akan wannan. Ameen!
***
Littattafan da aka ciro wadannan Qissoshi sune:

1- Yek sad Maudhu’ 500 dastan (Sayyid Ali Akbar Sadaqat)
2- Hayat Al-Qulub (Allama Majlisi)
3- 100 moral stories (Akramullah Syed)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: