bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:24:54
Akwai dalili na akida kan wannan fahimta a cikin daruruwan hadisan da suka zo daga Manzon Allah (s.a.w) wadanda suke yin nuni kan tantance wanene hakikanin Mahdi (a.s) da kuma kasancewarsa daga Ahlulbaiti (a.s)
Lambar Labari: 149
Da Suanna Allah Mai Raham Amai Jin Kai

Mahdiyanci a wajen Ahlulbaiti

Imamai goma sha hudu su ne sirrin fahimtar mahdawiyya

Hakika asalin akidantuwa da bayyanar mai kubutarwa wanda shi ne tushe (zinariyar) mahangar mahdawiyanci a musulunci, ana ganin sa a matsayin wani abu da ya shafi bil’adama baki daya, kuma lamarin ba ya kebanta da wani addini ayyananne ko mazhaba ayyananniya, kuma wannan hakika ta samu ta temaka wajen yin wurgi da shubuhohi hudu kan mas’alar mahdawiyyanci a lokaci guda.
Wannan hakika bayani ce, kan:- 
Na farko: bata shubuhar da ke da’awar cewa al’amarin Imam Mahdi (a.s) ya kebanta da ‘yan Shi'a alhali musulmai sun yi ittifaki a kai. 
Na biyu: tana yin bayani kan bata shubuhar tatsuniyar da ta tsayu kan ccewa lalle fikirar ko akidar mahdawiyanci tatsuniya ce da aka tsamo ta daga kirkira ko yin tunani bisa rayawa domin ita tatsuniya rayawa ce, da ta doru kan shirme da sakarci da aka cirato daga wani tabbataccen abu wanda ya gabata ko na wasu al’umma ko wasu jama’a, alhali babu wata tatsunuya da ta rabauta da samun karbuwa daga baki dayan dukkanin addinan sama da wadanda ma ba na sama ba, wacce ta zama tana bayini da harshen dukkanin Dan’adama kuma malamai da falasifa suka doru a kanta.
Bayani na uku: bata shubuhar da ke da’awar cewa yahudawa sun taka rawa wajen samar da tunanin mahdawiyyanci, to idan har abin da tunanin shi’ance yake kunshe da shi ya kasance yana da samuwa a cikin yahudanci kuma akwai shi a cikin dukkanin addinan sama, to saboda me zama riga ganin cewa lamarin ya shallake tunani in ya zama akwai shi a cikin musulunci, lalle abin da tunani da hankali suka hukunta shi ne ya zama musulunci yana kunshe da wannan mahangar a cikinsa da mafi bayyanar sura, kuma mafi kamala, kamar yadda yake a sarari a cikin makaratar mazhabar Ahlulbaiti (a.s).
Don haka, yana daga cikin alamomin kamala ga wannan addini da ma wannan mazhabarar kanta kasantuwarsu suna dauke da tunanin mahdawiyanci, ashe dukkanin addinnai ba su kasance sun hadu kan wasu daga cikin tushen akida da wasu daga hukncin shari’a kamar hajji da azumi da salla da makamancinsu ba? kuma shin kasantuwar yahudawa sun bayyana kudurcewarsu a sarari - su da ma wasunsu - kan iri-iren wadannan lamuran, shin hakan zai sa musulunci ya zama ya nisanta daga gare ta ke nan? ko kuma hakan na hukunta musulunci ya tabbatar da samuwarsa a cikinsa tare da gabatar da shi da mafi kyau sura mafi kamala? Hakika wannan shubuhar na tabbatar da tawaya ga ma’abotan ta kuma tana tabbatar da kamala ga musulunci da shi’anci. 
Bayani na hudu: Kamar yadda zai bayyana a sarari a Bayani na hudu, an kore shubuhar da take cewa: matsi da tsananin da mabiya Imamai Ahlulbaiti (a.s) suka sami kansu a ciki a karkashin masu mulki, shi ne dalilin da ya haifar da wannan fikirar ko wannan mahangar ta mahdawiyyanci, alhali khawarijawa ma sun fuskanci tsanani da matsin da be gaza wanda mabiya Ahlulbaiti (a.s) suka fuskanta ba, kuma da ace akwai wata ka’ida da ta hukunta haka hakika wadanda aka zalunta da wadanda aka raraka a duniya suna da yawa tare da cewa ba’a san su da wata akida da take kunshe da mahdawiyanci ba, kuma da yawa akwai mutanen da suka yi imani da akidar mahdawiyyanci ba tare da sun kasance cikin zalunci da raraka ba, kuma da ace akidantuwa da Mahdi ya samo asali ne daga zalunci da takurawa da raraka to don me zai sa akidar ta wanzu cikin mutanen da suka zo daga baya-baya wadanda su ba su dandani kudar raraka ba.
Na’am, abin da za a iya kudurcewa da shi shi ne matsanancin matsa da takura na iya zama dalilin da zai karfafa mutane ya iza su ga yin riko da mahdawiyanci sosai, ba wai ya zama dalilin da zai sa su kirkiri wannan tunanin tun asali ba.
Hakika addini shi ne mafi kamalar bayani kan hakikanin Dan’adam shi kuma musulunci shi ne mafi kyan bayani game da hakikanin addini kuma makarantar Ahlulbaiti (a.s) ita ce mafi kamalar bayani kan hakikanin musulunci.
A daidai lokacin da addinai ke yin shela kan mahangar mai kubutar da Duniya hakika wannan na bayyana hakikanin abin da ke bunne a cikin samuwar dan’adam da mafi kamalar yanayi da kammaluwa, fiye da kasancewar sa bayyanar da boyayyen abu, kuma a lokacin da musulunci ke shelanta wannan fikirar kadai yana shelanta wata hakika ta addinin mai karfin gaske da mafi kyan salo fiye da yadda addinai sama magabata suka bayyana, kuma a lokacin da Ahlulbaiti (a.s) suke bayyana wannan mahangar kadai suna gabatar da mafi kamalar bayani dangane da hakikanin musulunci kan wannan dunkalallen lamarin (na mahdawiyya). 
Don haka, banbanci da ke tsakanin makarantar halifofi da makarantar Ahlulbaiti (a.s) kan fahimtar mas’alar mahdawiyanci, banbanci ne tsakanin makarantu biyu da ke yin mafi takaitukar bayani kan wannan hakikar da kuma makarantar da ta fitar da mafi gamewar bayani kan hakikanin musulunci a mafi girma da daukakar mataki, sai makaranta ta farko ta dauka cewa makaranta ta biyu ta shi ge iyaka, ta wuce matsayarta, kuma ta yiyu sirrin shahara Shi'a da mahdawiyanci ta yanda ya zama tamkar wani abu da Shi'a suka kebanta da shi kai ka ce ba akida ce ta dukkanin musulmai ba, yana komawa zuwa ga cewa Shi'a sun kebanta da sanin mahdawiyanci zuwa gejinsa na kamala, kuma Shi'a suna da fahimta tilo kan kebance-kebancen mahdawiyanci wanda da shi ne kadai ma’anar mahdawiyanci ta hakika take bayyana.
Wadannan kebance-kebancen sun samo asali daga tushe Daya wanda shi ne yanda Ahlulbaiti (a.s) suka fahimci hakikar mahdawiyanci bai takaitu da kallon abin da zai zo nan gaba kadai ba, kuma mahdawiyyanci ba lamari ne na bada labarin abin farin cikin da zai faru nan gaba ga Dan’adam kawai ba ne, kamar yanda makarantar halifofi take gani, kafin nan tabbas akidar mahdiyanci wani bangare ne da ba zai yiyu a fitar da shi daga cikin ilimin akida imamiyya isna ashariyya ba, mazahabar da samaniya ta (ubangiji ya) kaddara mata samuwa a tsawon tarihin tun daga lokacin wafatin Manzon Allah (s.a.w) har ya zuwa mintinan karshe na rayuwar Dan’adam a doron kasa, da wani yaren, wannan mas’ala ce da ta shafi Imami na goma sha biyu wanda imamancinsa ya fara tun daga shekara ta 260 bayan hijiran ma’aiki har zuwa yau din nan kuma zai ci gaba har lokacin da zai bayyana ya yi a karshen duniya. 
Mu (‘yan Shi'a) a lokacin da muke bahasi kan mas’alar Imam Mahdi (a.s) a mahangar Ahlulbaiti (a.s) ya zama lalle mu mayar da hankali mu kalle ta a matsayin ta na lamarin akida, ta wane bangaren kuma mu kalle ta ta fuskacin kafa kujja da dalili, a wani karon kuma ta bangaren kebance-kebancen da ke tattare da ma’alar, ta wani bangaren kuma bisa kimar da mas’alar take da it a matakin akidar da take tattare da ita.



Tabbatar Mahangar Mahdawiyyanci A Akidance A Wajen Ahlulbaiti (a.s)

Akwai dalili na akida kan wannan fahimta a cikin daruruwan hadisan da suka zo daga Manzon Allah (s.a.w)  wadanda suke yin nuni kan tantance wanene hakikanin Mahdi (a.s) da kuma kasancewarsa daga Ahlulbaiti (a.s)  ..... da kuma cewa shi da ne gun Fadima (a.s)  daga zuriyar Imam Hasain (a.s)   kuma shi ne da na tara daga ‘ya’yan Husain (a.s)  da kuma cewa lalle halifofi guda goma sha biyu ne  . 
Wadannan su ne ruwayoyi guda biyar daga cikin ruwayoyi masu yawa da suka zo kan bayanin manufar mahdawiyya kuma suka bayyana wanda shi ne hakikanin Imam Mahdi (a.s) kuma duk wanda ya kalle su, zai ga yadda aka bi mataki bayan mataki aka fara daga babban jigo zuwa mafi kankanta har zuwa ayyana shi kansa Imam din. 
Hakika Sayyid Shahid sadr ya yi la’akari da cewa wadannan ruwayoyin sun kai wani irin babban adadi kuma sun yadu duk da kokarin dankar matakin kamewar da Imamai (a.s) suka yi wajen kin yin maganar a fili a gaban mutane, don kare rayukan ‘yan baya daga zuriyarsu masu zuwa daga kisan sarakuna ko kuma saurin kawo karshen rayuwarsa  Kuma yawan adadin wadannan ruwayoyin ba shi ne asasin da ya sa aka yarda da ingancin su ba, ballantana ma kari a kan haka akwai wasu darajojin da manuniya da suka isa zama hujja kan ingancinsu, don haka hadisin nan na Annabi (s.a.w) wanda yake magana kan Imamai ko halifofi ko amirai a bayansa da kuma cewa su halifofi ko Imamai ko amirai goma sha biyu ne, tare da sassabawar matanin haidsin, ta hanyoyi mabanbanta- hakika wasu daga cikin marubuta sun kididdige ruwayoyinsa sai adadinsu ya kai sama da dari biyu da saba’in , an ciro su daga mafi shaharar litattafan hadisai na Sunna da Shi'a, na daga abin da ya hada da Bukhari  da Musulim  da Turmuzi  da Abidauda  da Musnad din Ahmad dan Hanbali  da mustadrak alas sahihaini  na hakim, kuma an yi la’akari da cewa bukhari wanda shi ne ya cirato wannan hadisin ya rayu a zamanin Imam Jawad (a.s) da Imamai biyu Alhadi da Askari (a.s) lalle a cikin wannan akwai babbar izina domin hakan ya tabbatar da cewa lalle wannan hadisin an karbo shi daga Annabi (s.a.w) tun kafin abin da yake kunshe a cikin sa ya tabbata a sarari, wanda hakan ya sa mahangar nan ta imamai sha biyu ta zama cikakkiya, wannana na nufin cewa babu wata dama ta yin shakka kan cewa an cirato hadisin don ya zama ya dace kuma ya tabbadar da ingancin imamancin imamai sha biyu har ma hadisin ya zama yana tabbatar da wannan mahangar; domin hadisan da aka jinginawa Annabi (s.a.w) na karya ba su kasanace ba face sai don ana kokarin tabbatar da wata mahanga ko bawa wasu uzuri na wani abu da ya faru daga baya wanda a da babu labarin wadannan hadisan kuma ba a taba ganinsu ba a cikin hadisin litattafan hadisi ta yanda za a iya auna shi da hakikanin abin da hadisan suke yin bayani ba, kuma matukar muna da dalili a hannu kan cewa lalle hadisin da aka ambata ya rigayi - lokacin- silsilar tarihin rayuwar imamai sha biyu daya bayan daya kuma ya zama akwai shi a cikin litattafan tarihi tun kafin lamarin ya faru a sariri (tun kafin zuwan imaman daya bayan daya), wanda zai ba mu dama mu tabbatar da cewa wannan hadisin ba yana bada labarin abin zai faru a zahiri ba ne, kadai hadisi ne da yake bada labarin lamarin ubangiji, da ya zo daga bakin da baya furuci bisa son rai , yana mai cewa "hakika halifofi a baya na buga goma sha biyu ne”   . Kuma  sai wannan hakika ta imamanci ta tabbata a sariri farawa daga kan imam Ali (a.s) har zuwa tukewarsa kan Imam mahdi (a.s), don ya zama tabbaci kuma tilon abin da haknkali zai iya karba, kan fassarar wannan hadisi madaukaki, ko kuma ka ce: hakika hakan ya kasance shi ne abin da ya yi daidai da abin da ya zo a wannan hadisi madaukaka da ya zo daga Annabi  a aikace wanda hankali zai karba . 
Hakika Muslim ya fitar a cikin sahihinsa ta hanyar kutaibatu dan Ssa’ad, daga Jabiru dan Samrata, ya ce:  "Mun shiga wajen Annabi Muhammadu (s.a.w) ni da babana sai na ji yana cewa: "hakika wannan lamarin ba zai zo karshe ba har sai shuwagabanni goma sha biyu sun ja ragamar al’amarinsa”. Sannan sai ya fadi wata magana da ma’anar sa ta buya a gare ni (ban san me yake nufi ba) sai na tambayi baba na sai ya ce min ya ce: "dukkanin su daga kuraishawa suke”.  
Sannan ya fitar da shi daga Ibnu Abi Umar daga gare shi daga haddab dan Khalid daga gare shi daga Nasru dan Ali bajahdhame, daga gare shi kuma daga Muhammad  dan Rafi’u daga daga gare shi ta kowace hanaya. 
Kuma ya fitar da shi daga Abibakar Dan Abi Shaiba daga gare shi ta hanyoyi biyu, haka ma daga Kutaiba dan Sa’ad dag agare shi ta wasu hanyoyi buyu na daban. 
Wadannan hanyoyi guda tara kenan a cikin sahihu Muslim, ina kuma ga sauran hanyoyin da suka zo cikin sauran litattafan hadisi na sunna da na shi’a.  

ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:- 

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: