bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:30:35
Yana daga cikin riko da Sadalu, fadin Malamai cewa: Lallai Sadalu ko ta zamo abin ki ko kuma halas, kuma lokacin da daya daga cikin Malaman Shafi'iyya suka yi kokarin cewa Makaruhi ne, sai wasu suka yi musu Raddi da cewar Imam Shafi'iy
Lambar Labari: 151
Kamun kirji wanda ake ce masa"Kabalu", wato dora hannun dama a kan hannun hagu akan Kirji ya yin sallah.

Cikin yaren Larabci kuwa a janibin Sunna suna kiran wannan aiki da "Al-kabdhu". Amma a bangaren Mazhabin Ahlul-baiti (A) ana kiran wannan kamun kirjin da suna "At-takfiir, At-takattuf, At-taktiif fis-salaat".

Lallai idan muka yi duba cikin litattafan magabata a wannan janibi na Mazhabobin Sunna baki dayansu zamu riski cewa suna riko da wannan lamari ne na Kabalu bisa hujjojinsu na samun wasu maganganu masu kama da Hadisai, sai dai ba Hadisan Annabin ba ne, ma'ana ba maganar da ta fito daga bakin Annabin tsarki Muhammad dan Abdullahi (S) ce ba, maganganu ne na wasu mutane daban, kamar yadda hakan ya zo cikin litattafn Sunnan. Kuma ba dukkanin Malaman Sunna ne suke riko da ita ba, akwai da yawa wadanda suke inkarinta. Amma cikin ikon Allah za mu dan takaice mu kawo wasu daga hujjojin na su, sannan mu yi musu duba na Masana, sai mu ga menene kuma makomarsu.

MAGANGANUN DA SU KA ZO A BANGAREN SUNNA DA SUKE RABA SU DA KABALU

1- A cikin babban Littafin Sunna kuma magabaci daga Litattafan Sunna na farko, wato Littafin Imam Maalik, mai suna Al-muwadda' za mu ga ya kawo a cikin juzu'insa 2, shafinsa na 62:

"Mutane sun kasance ana umartarsu a kan dayansu ya sanya hannunsa na dama a kan hannunsa na hagu a cikin sallah. Sai Abuu Haazim ya ke cewa: Kuma ni ban sani ba (Ma'ana bai san ma maganar ba), sai dai shi Imam Maalik yana nuna daga Manzo ne (S)" (To ashe shi bai san ma maganar ne daga Annabi ba kenan).

2- Haka nan ya zo a cikin Littafin Abuu Abdur-Rahmaan Ahmad bn Shu'aib mai suna Sunanun-Nasaa'iy a cikin Juzu'insa na 3, shafinsa na 452:

"Daga Zaa'idata ya ce, Aasim bn Kulaib ya labarta mana cewa, Babansa ya fada masa cewa, hakika Waa'il bn Hujrin ya ba shi labari yace: Na ce lallai sai na duba na ga yadda Manzon Allah (S) ya ke Sallah, sai na dube shi, sai ya tashi ya yi Kabbara ya daga hannayensa har suka kai saitin Kunnuwansa biyu, sannan ya dora hannunsa na dama a kan tafin na hagu, tare da wuyan tafin hannun da dantsen, ya yin da ya so yin Ruku'u sai ya daga hannayensa ……". Mun zo "Muhallush-shaahid". Hakanan za a iya dubawa cikin littafin Musnadus-sahaabah fii kutubut-tis'ah a musnadin Waa'il bn Hujr.

3- Malam Sulaimaan bnul-Ash'ath Abuu Daawud a cikin Sunan dinsa (Sunan Abu Daawud) Juzu'insa na 1, shafinsa na 274, ko kuma a wani daba'in juzu'insa na 1, shafinsa na 260:

"Daga Zur'ata bn Abdur-Rahmaan ya ce, na ji Ibn Zubair yana cewa: Hada sahu da sanya hannu kan hannu yana daga cikin Sunna". A wannan Hadisin Nasiruddiin Albaniy ya yi Tahkiik ya ce wannan Hadisin Raunanna ne. Kunga shike nan ma ba sai mun ce komai a kansa ba.

4- Hakanan dai a cikin Sunan Abii Daawud din juzu'insa na 1, shafinsa na 274:

"Daga Ibn Mas'uud ya kasance yana sallah sai ya sanya hannunsa na hagu a kan na dama, sai Manzon Allah (S) ya gan shi – sai (Manzon) ya sanya hannunsa na dama a kan na hagu". Albaaniy yace wannan Hadisin Hasanun ne.

5- Malam Buhari kuwa a cikin Sahihin littafinsa juzu'insa na 3, shafinsa na 251, ko kuma a wani Daba'in juzu'insa na 1, shafinsa na 16:

"Daga Sahl bn Sa'din ya ce: an kasance ana umartar Mutane da namiji ya sanya hannunsa na dama a kan dantsen hagu a cikin Sallah. Sai Abuu Haazimin ya ce; ni ban san wannan ba (Daga Annabi), sai dai shi yana jingina abin ga Annabi (S). Sai Ismaa'il ya ce; suna jinganawa, bai ce yana jinginawa ba". To ga dai Hadisin Buhari mafi inganci a wajen Sunna ana ta dabal-dabal – amma duk da haka a ka'ida wannan yana tabbatarwa ne da ba Annabi ne ya ke umarnin ba, ina jin su Halifa Umar dan Haddabi ne.

6- Malam Muslim kuwa a cikin Sahihinsa shi ma wanda Malam Nawawiy ya yi masa sharhi – na Muhyiddiin bn Sharafun-nawawiy a juzu'insa na 4, a Kitaabus-salaat, shafinsa na 39, a wani Daba'in kuwa a juzu'insa na 1, shafinsa na 301, duk dai a "Babin ya dora hannunsa na dama a kan na hagu ……":

"Daga Waa'il bn Hujr ya ce: ya ga Annabi (S) ya daga hannayensa biyu ya yin da ya fara yin Sallah, ya yi Kabbara, ………………, sannan ya dora hannunsa na dama a kan na hagu".

Wadannan sune daga mafi girman hujjojin da Malaman Sunna suke kawowa a cikin Litattafansu na ba su damar yin Kabalu a cikin Sallah, inda wasu suke cewa Sunna ce mai karfi, wasu kuwa cewa suke wajibi ce, wasu kuwa masu saukin ra'ayin da fuskantar abin da suka fuskanta game da wannan maganar da kai tsaye ba bu mai cewa Maganar Manzo ce (S), sai suke cewa babu laifi ka iya aikatawa.


HADISAN SUNNA DA SUKA ZO A KAN YIN SADALU (SAKIN HANNU A SALLAH)

1- Ya zo a cikin littafin Malam Dabaraaniy mai suna Al-Kabiir da lafazinsa kamar haka:

"Manzon Allah (S) ya kasance idan ya zamo yana cikin Sallah yana daga hannayensa har zuwa kusa da kunnuwa, idan ya yi kabbara sai ya sakesu" (Al-mu3jamul-Kabiir: 20/74).

2- Haka nan ya zo a cikin Hadisin Abiy Hamaidus-saa'idiy wanda Malam Buhariy ya fitar da shi da Abu Dauda, kuma na cikin Abu Daudan wanda a ka fitar ta hanyar Ahmad bn Hanbali ya ce: Abu Humaid da wasu Mutane guda goma daga cikin Sahabbai sun yi ijma'i, daga cikinsu akwai Sahal bn Sa'ad, sai suka ambaci sallar Manzon Allah (S), sai Abu Humaid ya ce: ni na fi ku sanin Sallar Manzon Allah (S), sai suka ce: don me? Wallahi kai dai ba ka fi mu yawan kasantuwa da Shi ba (S), haka nan ba ka gabace mu wajen tarayya da Shi ba (S). Sai ya ce: haka ne, sai suka ce: to fadi mu ji, sai ya ce: Ya kasance idan ya tashi yin Sallah yana daga hannayensa har sai ya kai su kafadarsa, sannan ya yi kabbara har sai dukkanin Kasusuwansa ko wanne ya koma mazauninsa, sannan ya yi karatu sai ya yi ruku'u – lokacin da ya gama fada sai suka ce ka yi gaskiya. Wanda sanannen abu ne mazaunin hannaye ya yin da mutum ya ke tsaye shine barukan sa biyun (Wato dama da hagunsa a saki hannayen kasa) ba wai Kirji ba. Hakanan shi Sahal bn Sa'ad maruwaicin Hadisin "An kasance ana umartar Mutane a kan Namiji ya dora hannunsa na dama a kan na hagu" yana cikin mahalarta wajen, da kuma bai kasance ya san shi Hadisin ya bar riko da aikin da shi ba, da sai sun ce masa ka bar dora hannu kan hannu, sai dai kawai cewa suka yi da shi ka yi gaskiya, ba su ce: ba ka fadi Annabin (S) ya dora hannun a kan daya ba. (Sunan Abiy Daawud Juz. 1, Shafi 194, da kuma Ibraamun-nakdh na Muhammad Khidr bn Maayaabiy Al-jakniy Ash-shankiidiy shafi na 18-32).

Haka nan dai Abii Humaid ya na da wata ruwayar daban wajen bayyana yadda SallarSa ta ke (S) a aikace, wanda a cikinta ya bar hannayensa a sake a inda suke, kuma wannan ruwayar ta aiki wacce Dahaawiy ya ambace ta da Ibn Hibbaan kuma Muhammad Khidr bn Maayaabiy Al-jakniy Ash-shankiidiy ya nakaltota a cikin Ibraamun-nakdh shafi na 27.

3- Yana daga ciki abin da Al-Haafiz Ibn Abdul-barr ya nakalto a cikin "Kitaabul-ilm" cewar ya ce:

Hakika Maalik ya nakalto Hadisin Sadalu daga Abdullaahi bnul-Hasan, (A duba cikin littafin Ibraamun-nakdh shafi na 39).

4- Yana daga ciki abin da aka ruwaito na samun Malamai sun tabbatar da samuwar Abdullahi bnuz-Zubair ya kasance ba ya Kabalu, kuma ba ya taba ganin wani mutumin yana yin kabalun sai ya kama hannun ya warwaresu ya mikesu. Wanda kuma Al-Khadib ya nakalto a cikin "Taariikhu Baghdaad" cewar shi Abdullahi bnuz-Zubair ya karbi siffar Sallarsa daga kakansa Abu Bakar Siddik, wanda wannan yana bayyanawa daga gareshi ne cewa Halifa Abubakar ba ya Kabalu. (Ibraamun-nakdh shafina 3, Al-kawlul-fisal shafina 24).

5- Malam Ibn Abiy Shaibah ya nakalto daga Hasanul-Basariy da Ibrahiimun-Nakha'3iy da Sa3iid bnul-Musayyib da Ibn Siirina da Sa3iid bn Jubair, sai ya ce sun kasance ba sa yin Kabalu a cikin Sallah, kuma sun kasance daga cikin Manyan Tabi'ai ma su karbowa daga Sahabbai (R), wadanda a ka sansu da ilimi da kaskan da kai. (Ibraamun-nakdh shafi na 33). Kuma daga misalinsu akwai Abu Mijlaz da Uthmaanun-nahdiy da Abul-jawzaa'. Wanda kuma tabbas wadannan dukkansu sun nakalto a kan tabbas Kabalu ta kebantu ne ga Shugabannin Yahudawa da Kiristochi "Bishop". Wanda an tambayi Ibn Siiriina a kan dora hannun dama a kan na hagu a cikin Sallah sai yace: Lallai hakan ya faru ne ta sanadin Rum, Hasanul-Basariy ya ke cewa: Annabi (S) ya ce: Kamar ina ganin Shugabannin Yahudu sun sanya hannayensu na Dama a kan na Hagu a cikin Sallah (Ibraamun-nakdh shafi na 34 – wanda ya nakalto Ibn Abiy Shaibah).

6- Yana daga cikin riko da Sadalu, fadin Malamai cewa: Lallai Sadalu ko ta zamo abin ki ko kuma halas, kuma lokacin da daya daga cikin Malaman Shafi'iyya suka yi kokarin cewa Makaruhi ne, sai wasu suka yi musu Raddi da cewar Imam Shafi'iy a cikin Al'um ya ce ba bu laifi gareshi ga wanda ba ya wasa da hannayensa a cikin Sallah. Amma shi Kabalu a cikinsa tare da Magana a kan zargi, to ya karkata ne ga abin ki da kuma Magana a kan Hani.

Sai ya kasance (Kabalun) daga abu mai rikitarwa da a ke bukatar barinta da Hadisin da a ka yi ittifaki a kansa shine; Fadinsa (S): "Ita Halas bayyananna ce, hakanan ma Haram bayyananna ce, kuma a tsakaninsu akwai lamura ma su rikitarwa". Wanda kuma haramcin Muhammad Sunusiy ya nakalto shi a cikin littafinsa mai suna: "Shifaa'us-sadr baarii masaa'ilul-ashr", haka nan Al-Haddab da wasunsa suma sun nakalto shi ya yin Magana a kan Kabalu a cikin Sallah.

7- Haka nan dai yana daga cikin dalilan da suke tabbatar da Sadalu Hadisin "Al-musii'u salaatahu" wanda ruwayar Al-Haakim ta ambace shi daga gareshi, wacce kuma tana kan gundarin "Shardush-shaikhaini" – a wannan wajen ne sai na tuna lokacin da muke tattaunawa da Baban Hamdan (Dr. Mansur Sokoto) na kawo Hadisin Ibn Abiy Wakkaas wanda Hakim ya fitar shima ya ce "Kadit-tafakash-shaikhaani", sai ya ke cewa wai ya duba cikin Buhari da Muslim din ba bu Hadisin. Wanda ya bamu mamaki sosai na rashin sanin isdilahin Malamansa a kan wannan jumla, da maganarsa ta ke nuna sam bai sam me a ke nufi da ita ba. "Ash-shaikhaini" dai tana nufin Buhari da Muslim ne, kuma duk Hadisin da a ka fitar da shi ta irin hanyar da Buhari ko Muslim suka fitar ta bangaren ingancin Sanadin, to Sunna suna ce masa a bisa sharadinsu. Misali: ya kasance masu nakalto Hadisin an yi ittifaki a kan thikarsu da isnadin da ya jone da wani Fitaccen Sahabin, ……………… - Wanda a cikin wannan Hadisin na Musii'u Salaatahu, a cikinta akwai farillan Sallar da Mustahabbai, amma ba a ambaci Kabalu a ciki ba. Kuma lafazinsa - bayan ya nemi mai bata sallartasa ya san yadda a ke yin Sallar – Sai Manzon Allah (S) ya ce masa: Lallai ya tabbatar da tsarki, sannan ya godewa Ubangiji ya girmama shi, sannan ya karanta daga Kur'ani abin da Allah ya yi izini a cikinsa, sannan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sannan ya sanya tafukan hannayensa a kan gwiwoyin kafarsa har sai gabobinsa sun daidaita sun tsaya cak, sannan ya ce: "Sami'allahu liman hamidahu", sannan ya tashi ya tsaya kyam har sai kowane kashi ya koma mazauninsa ya tsaya. Sannan ya mike kyam har bayansa ya daidaita, sannan ya yi kabbara ya yi sujjada, da kuma yiwuwar goshinsa daga sujjadar har sai gabbansa sun daidaita sun tsaya cak, sannan ya sake kabbara ya dago kansa ya zauna kyam a mazauninsa har sai bayansa ya mike ya daidaita. Ya wassafa sallar kamar haka har ya gama sannan ya ce: "Sallar dayanku ba za ta cika ba har sai ya aikata ta haka".

Wanda kuma ruwayar wannan Hadisin ta hanyar Al-Haakim ta bayyana a sarari a takaice abin da za a aikata a cikin Sallah daga Farillai da Mustahabbai, kuma ba ta ambaci Kabalu ba. Kuma hakika Ibnul-Kassaar mutumin Baghdaad da wasunsa sun ce tabbas shi wannan yana daga cikin mafi dalilan Sadalu da kore Kabalu a cikin Sallah, a duba cikin (Al-kawlul-fisal na Shehu 3aabidul-makkiy a shafi na 9 – wanda shine Muftin Malikiyyah na Makka can da shudewa).

8- Akwai dai Haidisin da ya zo daga Abu Dauda kuma ya inganta shi, daga Saalimul-barraad ya ce: 3ukbah bn 3aamir ya zo mana sai muka ce masa: ka yi Magana a kan Sallar Manzon Allah (S), sai ya tashi a cikin Masallachi ya yi kabbara, ya yin da ya yi ruku'u sai ya sanya hannayensa a kan gwiwoyinsa sannan ya sanya yatsunsa can kasan gwiwoyin nasa, kuma ya tsayu a tsakanin gwiwowyin hannayensa har sai da komai na gabbansa suka tsaya kyam, sannan ya ce: "Sami'allaahu liman hamidahu", sannan ya tsahi har dukkanin gabbansa suka tsaya kyam, sannan ya yi kabbara sai ya yi sujjada ya dora tafukan hannayensa a kasa, sannan ya tsaya a tsakanin gwiwoyin hannayensa har sai da komai na gabbansa suka tsaya kyam, sannan ya yi kabbara ya dago daga kansa ya zauna har sai da dukkanin gabbansa suka tsaya kyam, ya aikata hakan kumawa dai, sannan ya kawo raka'o'i guda hudu kwatankwacin wannan raka'ar, sannan ya ce: Haka muka gan shi (S) ya ke Sallah. Wanda kuma wannan ya katange ko ya kawo karshe a wajen Malamai, ba bu wani abu saura bayansa da ke nuna neman Kabalu a matsayin Mustahabbi ko Sunna, domin dukkanin Sunnonin sun zo cikin wannan Sallar ta Manzo (S) cikakkiya. Kuma yana nuni ne a kan karshen aikinsa (S) shine barin Kabalu din idan ma ya inganta ya taba aikatawa.

9- Hadisin Hani a kan "Iktitaafi" shi ma yana daga cikin Hadisan da suke tabbatar da Sadalu – "Hadiithun-nahyi anil-iktitaaf fiis-salah" – wanda "Iktitaaf" tana nufin ne Kabalun wato kamun kirji. Kamar yadda ya zo a cikin littafin Al-kawlul-fasl shafi na 35, wanda kuma Hadisin dai Malam Muslim ya fitar da shi. Lafazinsa kuwa shine: Abdullaahi bn Abbaas (R) ya fada ga wanda ya gan shi yana Sallah da Kitso a kansa: Hakika na ji Manzon Allah (S) yana cewa: "Hakika kwatankwacin wannan kamar wanda ya ke Sallah ne hannayensa a kan kirji (Kabalu).


Ga Nassin Hadisin: "Mathalullaziy yusalliy wara'suhu ma3kusun kamathalillaziy yusalliy wahuwa maktuufun" a wata ruwayar kuma "Yusalliy dhaafiran ra'suhu".

Wannan Hadisin ya zo a cikin Littafin Al-amthaal fiil-Hadiith na Abiy Muhammad Abdullah bn Muhammad bn Ja3far bn Hayyaan – wanda a gaban Hadisin Malamin ya ke cewa: "Isnaaduhu, Rijaaluhu thikaat" – Sanadinsa da Mazajen Hadisin thika ne. haka nan dai wannan Hadisin ya zo a cikin Ahmad bn Hanbali juzu'insa na 1, shafi na 316, lambata 2905, da Dabaraaniy daga Ibn Abbaas a juzu'insa na 11, shafinsa na 422, lambata 12196, da dai wasu Malaman da daman gaske).

10- Imam Ahmad ya fitar a cikin Musnadinsa a kan Annabi (S) ya kasance karshen abin da ya ke gareshi shine Hani a kan yarda da Ahlul-kitabi. Kuma wannan bayan ya kasance ne yana son yarda da su a kan abin da bai sauka gareshi ba ne ko kadan, haka kuma Kabalu – kamun kirji a Sallah – na daga cikin aikin Ahlul-kitaab kamar yadda Ibn Abiy Shaybah ya nakalto daga Al-Hasanul-basariy da Ibn Siiriina daga Imaman Sunna kamar yadda ya gabata. (A duba cikin Ibraamun-nakdh shafinsa na 33).

Don haka wannan ya na daga cikin gamsassu kuma ingantattun dalilai da za su isa wajen ingancin abin da ya zo a cikin Al-mudawwanah a kan Karhancin Kabalu a cikin Sallah.

Ubangiji ka kara datar da mu, ka sanya mu matabbata a kan tafarkin da Iyalan Annabinka Muhammad sallallahu alaiHi wa Alihi suke kai har komowarmu gareka, mu kasance Yardaddu ababen yarda, kamar yadda ya tabbata a cikin Kur'ani maigirma, a kan cewa Shi'ar Imamu Aliy su ne "Khairul-bariyyah", kuma su ne: wadanda za su tashi a ranar Alkiyama "Raadhiyatan mardhiyyatan".

Aminci ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya har ya zuwa ranar sakamako.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: