bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      22:39:32
A watan ramadhana da ya zo na 14h sai umar ya je masallacin tare da wasu cikin mutanensa sai ya ga mutane suna yin nafiloli wasu a zaune wasu a tsaye wasu kuma a zaune, wasu kuma sun yi ruku’u, wasu sun yi sujjada wasu suna yin karatu, wasu suna yin tasbihi wasu kuma suna yin kabbarar harama
Lambar Labari: 152
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

GABATARWA

Wajibabbaun abubwan shari’ar musulunci su ne abubuwan da suka wajaba a kan wanda ya yi imani da Allah da Manzon Allah (s.a.w) da ranar alkiyama zai yi su ne a matsayin abin da ya zama dole a kansa, don samun kamalar da ta dace da shi, domin yin sakacin aikata hakan na nufin sa kamalar sa da ake wa fata ya samu cikin hadari da yiyuwa rashin samun mafi karancin darajojin kamalar da ake masa fata.  
Ana daukar mustahabbi da abubuwan da shri’a ta kwadaita da yin su a matsayin wadancen al’amuran da suke karawa mumini mai riko da wajibai kamala da kusanci zuwa ga Allah Ta'ala.
Sallar da aka wajabti (ta yau da kullum) ba makawa mutum sai ya yi ta a kowane hali, amma dage wa da yin ta a farkon lokacinta ana ganinsa a matsayin falala ce da kamala da kuma nuna himmatuwar mumini da wannan wajibin da Allah Ta'ala ya wajabta masa wacce da ita ne Allah Ta'ala ya daukaka mutum, to haka yin ta ma a cikin jama’a shi ma wani mustahabbi ne, hakan kuma yana tabbatar da wata martaba ta kamala a lokacin da mutum yake yin ta a cikin jam’i. 
Ibadodi sun sha ban-ban a shari’ar musulunci da wasu al’amura, cikinsu, akwai: nau’o’in da suka game lokuta daban- daban da yanayi-yanayi da mutum ke shudewa a tsahon rayuwasa, akwia kuma gamewar ta da mabanbantan lokutan mutum a kowace rana tun daga balagarsa, akwia kuma gamewarsa har zuwa karshen nunfashinsa, wannan ci gaban yana nuna matukar kulawar musulumci da tarbiyar mutum tarbiyar da bata tabbatuwa sai a hankali da kadan da kadan da jarrbawa da gwaji da bada himma da kokari da danfarewa Allah Ta'ala. 
Kamar yanda ibadojin musulunci suka kebanta da sai yadda shari’a ta ce a yi su da kaifiyya kaza da bayani kaza, mutum ba shi da hakkin rage wani abu a ciki ko kara wani abu don ra’ayin sa kai kuma musulmai ma sun yi ijma’i a kan haka. 
Daga nan ne zamu gane wajabcin yin bincike kan abin da wasu musulmai suke yi a watan ramadhana na yin salla da sunan asham, shin Allah Ta'ala mai hikima ya shar’anta ta ne, ya kuma bayyana hukuncinta da bayanan ta filla-filla? Ko ba a shar’anta ta a cikin shari’ar musulnci ba don haka hukuncin ta ya zam bidi’a, bidi’a kuma haramun ce domin ba ta da tushe a Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) madaukakiya.? 

KUR’ANI DA HADISI SUN KORE HALACCIN SALLAR TARAWIHI  
A lokacin da muke karanta Kur'ani ba za mu sami wata alamar sallar tarawihi a cikin ayoyin sa ba. Da da a kwai wani gurbi a Kur'ani da malam mazhabobi hudu sun yi riko da shi, amma sai ga shi ba mu sami wani cikinsu ya kafa hujja a kanta da ayar Kur'ani ba.
Haka ma a lokacin da muka duba sirar Annabi (s.a.w) ba zamu ga wata alamar sallar tarawihi ba, kawai dai zamu sami kwarin gwiwar yin tsayuwar a dare a watan ramadhan, amma da yanayin da ke nuna yi amma a daidaiku ba jam’I ba. 
Hadisai suna karfafa cewa sallar tarawihi fa Annabi (s.a.w) be zo da ita ba, ba a yi ta ba a zamaninsa, kai a zamanin Abubakar ma babu ita, kuma Allah Ta'ala be shar’anta haduwa a yi sallar nafila a cikin kam’I ba, domin nafila na cikin sunnune mustahabbai, banda sallar neman ruwa. (it kadai ce a ka yarda a yi mata jam’i). 
Allah Ta'ala da ya shar’anti yin jam’i a sallolin wajibi kamar farilla guda biyar nay au da kullum da sallar dawafi da sallar kisfewr rana da wata da kuma sallar gawa. 
Manzon Allah (s.a.w) yana tsayawa a dareren ramadhana ya kuma yi sunnonin da ke ciki amma ba a cikin jam’i ba, kuma mutane sun kasance suna yin ta kamar  yadda suka gan shi yana yi. 
Haka al’amarin yake a zamanin Abuuaka da ma har ya rasu 13 h,   Umar dan Khaddabi ma ya hau karagr mulki, ya azumci watan ramadhana na wannan shekarar be canja yadda ake yin salla a wannan watan ba.  

YAUSHE AKA KIRKIRO SALLAR TARAWIHI
A watan ramadhana da ya zo na 14h sai umar ya je masallacin tare da wasu cikin mutanensa sai ya ga mutane suna yin nafiloli wasu a zaune wasu a tsaye wasu kuma a zaune, wasu kuma sun yi ruku’u, wasu sun yi sujjada wasu suna yin karatu, wasu suna yin tasbihi wasu kuma suna yin kabbarar harama, wasu kuma sun sallame, yadda ya gansu be ji dada ba, nan take ya yi nufin gyara lamarin a fahimtarsa sai ya sunnata musu sallar a sham,   a farkon daren watan, ya hada mutanen su yi sallar asham dole, ya rubuta wasika garurawa ya sa liman biyu a madina daya limamain maza daya na mata. A kan wannan an rawaito ruwayoyi masu yawa:- 
Ga abin da bukhari da muslim suka rawaito a sahihansu,   
Cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "duk wanda ya tsaya a ramadhana ya yi sunnonin watan cikin imani da nema lada, an gafarta masa laifin da ya gabata”.  
Manzon Allah (s.a.w) ya rasu al’amarin a haka yake - ai al’amarin tsayuwa a watan ramadhana be canja daga yanda yake kafin rasuwarasa ba (s.a.w), kuma al’amarin ya ci gaba a haka a lokacin halifancin Abubukar da farkon halifancin Umar. 
Bukhari ya rawaito daga a kitabul tarawahi daga Abdullahi dan Abdurrahaman dan Abdulkari’i,   ya ce na fito tare da umar dan khaddabi a daren watan ramadhana zuwa masallaci, sai ga mutane suna salla daban-daban ya ci gaba da cewa sai Umar ya ce ni ina ghanin da zan hada wadannan mutanen su bi liman daya da zai fi sai ya yi nufin hada su karkashin ubayyu dan ka’ab (ya ce) sannan na fita tare da shi a wani dare mutane suna salla a karkashin limami daya sai ya ce: madalla da wannan bidi’ar ......”.
Allama askalani a lokacin da ya zo wajen da maganar umar a wannan Hadisin: "madalla da wannan bidi’ar” sai ya ce: 
"ya ce mata bidi’a domin Manzon Allah (s.a.w) be sunnanta musu yin jam’in ta ba, kuma a zamanin Abubukar ma  ba a yin ta ko a farkon dare ko wannan adadin duk ba a yi.   
Tuhfatul bari da waninsa cikin sharhohin bukhari a kwai kwatankwacinsa sai a duba.   
Allama Abdulwahid muhammad bin Shahna bayan ya ambaton rasuwar umar a abubuwan da suka faru 23H yake cewa a tarihinsa (raudatul manazir): shi ne farkon wanda ya hana siyar da bayi mata da suka haihu, shi ne ya hada mutane jim’in sallar tarawihi. 
Haka ma suyudi ya fada a littafin sa (tarikhul khulafa) cikin abubuwan da Umar ya kirkiro da ya cire daga askari: ya ce: shi ne wanda aka fara kira da amirulmuminina, shi ne wanda ya sunnanta tsayuwa a watan ramadhana, wato sallar tarawihi shi ne farkon wanda ya haramta mutu’a, shi ne farkon wanda ya hada mutane kan kaburbura hudu a sallar gawa. 
Muhammad dan sa’ad ya fadi a tarjamar umar a cikin j 3 cikin dabakat, she ne na farkon da ya sunnanta tsayuwa cikin watan ramadhan, wato yin sallar tarawihi ya sa musu liman, ya kuma rubuta wasika gariururwa hakan kuma ya faru ne a watan ramadhana 14H, ya sa makaranta biyu a madina daya yana yi wa maza limanci daya kuma yana yi wa mata limanci......
Ibni Abdul barri ya fada a tarjamar Umar a cikin isti’ab, Umar ne ya haskaka watan ramadhan da yin sallar tarawihi.   
Sayyid Abdulhasain sharafuddin ya yi ta’aliki kan wadanda suke ganin sallar tarawihi daidai ce. 
Kamar wadannan mutanen Allah Ta'ala ya yi musu afuwa mu da su suna ganin ya gano (da sallar tarawihi) wata hikimar da Allah Ta'ala da Manzon Allah (s.a.w) suka gafala. 
Kai su ne ma suka fi gafala daga hikimar Allah a cikin shari’o’insa da tsarinsa, ya ishe mu a cikin rashin shar’anta sallar Jam’i da nafilar watan Ramadan da wanin Ramadan, mutum ya yi ta a cikin dare a gidansa, ya gana da Ubnangijinsa (AWJ) ya kai karar bakincikinsa da damuwarsa, ya gana da Ubangijinsa da muhimman abubuwa daga wannan sai wancan har ya gama tare da nacewa, yana yin tawassali da yalwar rahamarsa gare shi tare da raja’i da fakewa zuwa ga Alalh, yana mai tsoro da kwadayin rahamar Alalh, tare da komawa zuwa gare shi da yin tuba, yana mai tabbatar da laifuffukansa tare da fakewa da neman tsari, ba zai sami wata mafaka ba daga wajen Allah sai a wajensa ba wajen tsira daga Allah sai gare shi.
Saboda haka ne ma Allah ya bar sunnoni ba sai an yi jam’insu ba. Don mutane su yi guzuri a cikinsu da kadaitaka ga Allah matukar zukatansu sun fuskanto shi kuma gabbansu sun yi aiki don Allah, wanda yake ganin kadan ya yi yana ta ganin karantawarsa, wanda ya yaiwata ya yawaita, tabbas ita ce fiyayyen maudu’i, kamar yadda ya zo a ciin Hadisi daga shugaban Talikai.( ) 
Amma hada ta da jama’a hakan zai iya karance wannan amfanin tare da karanta fa’ida.
Bugu da kari yin sallar nafila a gida zai tabbatarwa da gida rabonsa na samun albarka da daukaka saboda yin salla a ciki, ya kuma tabbatarwa da gida kasonsa na tarbiyyar son yin Sallah da ma nishadin yin ta. Hakan kuma saboda koyi da ayyukan iyaye maza da iyaye mata da kakanni maza da ita a cikin hankulansu da zukatansu, tabbas Abdullahi bn Mas’ud ya tambayi Manzon Allah (s.a.w) meye abin da ya fi yin Sallah a gidana ko yin ta a Masallaci? Sai Manzon Alalh (s.a.w) ya ce: "Shin baka ga gidana yana kusa da masallaci ba, na fi son na yi sallah a gidana a kan na yi a Masallaci ban da sallar farilla ce”. Ahmad da Ibn Majah da Ibnu Khuzaima ne suka rawaito kamar yadda yake a babin kwdaitar da Sallar nafila a Kitabut Targib wat Tarhib na Imam Zakiyuddin Abdul Azim bn Abdil Kawiyyil Munziri.( ) 
An karbo daga Zaid dan Sabit tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ya ku mtuane ku yi Sallah a gidajenku, tabbas sallar mutum a gidansa ta fi, sai dai in farilla ce”. Nasa’i da Ibnu Khuaima ne suka rawaito a littafinsu.
An karbo daga Anas dan Malik ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ku girmama gidajenku da yin wasu sallolinku a ciki”.( ) 
An karbo daga Jabir ya ce: Manzon Alalh (s.a.w) ya ce: "idan dayanku ya gama Salla a Masallaci, to ya sanya wani kaso na sallarsa a gidansa, tabbas Allah zai sa alherin sallarsa a gidansa”. ( ) Muslim ne da waninsa suka rawaito, haka ma Ibnu Khuzaima ya rawaito shi a Sahihinsa da Isnadi zuwa Abu sa’id, Hadisai masu irin wannan ma’anar suna da yawa, wannan shiftar ba za ta iya kawo su duka ba. 
Amman Halifa da yake mutum ne mai tsara abubuwa da kwazo, abin da ya ke cikin sallar jam’i na ibada da ya bayyana da kyakkyaan yanayi tare da fa’idodin jam’i masu yawa sun burge shi abubuwan da manyan malamai sun yi magana sosai a kan haka, kuma dai ka san shari’ar Musulunci ba ta bar wannan bangaren ba, ta kebantar da salloli wajibi da ita, sai ta bar nafiloli don wani bangaren saboda maslahohin mutane (mumini da mumina ba su kasance idan Allah da Manzonsa suka hukunta al’amari ya zama suna da zabi ba).( ) 
RA’AYIN IMAMIYYA KAN SALLAR TARAWIHI:
Tabbas ‘yan Shi’a - saboda bin Manzon Allah (s.a.w) da mtuanen gidansa (a.s) da suke yi - suna yin nafilfilin watan Ramadan ba tare da yin jam’i ba, suna ganin yin ta a cikin jama’a bidi’a ne ba a shar’anta haka ba, hakan ya faru ne a bayan Manzon Allah (s.a.w) ba wata daga wajen Allah kan haka.
Sheikh Dusi ya ce: Nafilfilin watan Ramadan ana yin su ne a dai’daiku, yin jam’i a cikinta bidi’a ne.
Ya kafa hujja kan mazhabar Imamiyya ta ijma’insu kan cewa hakan bidi’a ne. Ga abin da Zaidu dan Sabit( ) ya rawaito daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "sallar mutum a gidansa ta fi sallarsa a Masallaci banda sallar farilla”.( ) 
A cikin Jawahirul Kalam wanda Sheikh Muhammad Hasan Najafi ya wallafa ya ce: Akwai yiwuwar da’awawr tawaturancin Hadisan da ke cewa nafilfilin watan Ramadan bidi’a ne yin su a jam’i.( ) 
Sayyidul Hakim ya rawaito a cikin Mustansak hikayar Muntaha da Zikra da Kanzul Irfan ijma’i kan haka.( ) 

SALLAR TARAWIHI A NASSOSHIN AHLULBAIT (a.s):
Amman imaman Ahlulbait (a.s) kalmarsu ta hadu kan cewa yin jam’in Nafilfilin bidi’a ne mudlakan ba tare da bambancewa tsakanin sallar Tarawihi da wanin Tarawihi ba, akwai ruwayoyi kala biyu da suka zo daga wajensu:
1- Abin da ya ke nuna rashin shar’anta sallar jam’i a baki dayan nafilfili.
2- Abin da yake nuna rashin shar’anta ta a sallar tarawihi. 
Amma bangaren farko za mu fadi ruwayoyi biyu ciki akwai:
1- Imam Bakir (a.s) ya ce: "ba a yin sallar nafila a jam’i don yin haka bidi’a ne, dukkanin bidi’a bata ne, duk bata wuta zai kai mutum”.( ) 
2- Imam Aliyu bn Musa Al-Rida (a.s) ya fada littafin da ya rubutawa Ma’amun: "bai halatta a yi sallar nafila a cikin jam’i ba, don yin hakan bidi’a ne”.( )  
Amma bangare na biyun shi ne tabbas Imam Ja’afarus Sadik (a.s) ya yi magana a kansa yake cewa: "Lokacin da Amirul Muminina ya je Kufa sai ya umarci Hassan bn Ali (a.s) ya yiwa mutane shelar cewa ba a yin jam’in Sallar nafila a watan Ramadan, sai ya yi shelar abin da Amirul Mumionina (a.s) ya umarce shi, bayan mutane sun ji maganar Hasan bn Ali (a.s), sai suka yi kuwwa suka ce: Wayyo Allah Umar! Wayyo Allah Umar, lokacin da Hasan (a.s) ya dawo wajen Amirul Muminina (a.s), sai ya ce masa: Karar me nake ji? Sai ya ce: Ya shugaban Muminai! Mutane ne suke kara suna cewa Wayo Allah Umar! Wayyo Allah Umar! Sai Amirul Mumina ya ce: Ce ne musu: Ku yi Sallar.( ) 
Sau da yawa mai karatu zai yi mamakin maganar Imam da ya ce: "Cene musu ku yi sallar”. 
Ya bar su su cigaba da yin wannan bidi’ar, sai dai idan mai karatu ya koma wajen wasu kalmominsa sirrin barinsu da ya yi su cigaba da abin da suke kai zai bayyana gare shi.
Sheikh Dusi ya ce: Tabbas Amirul Mumina lokacin da ya yi umarnin hani, hana su jam’i ya yi bai hana su yin Sallar ba, lokacin da ya ga al’amarin zai sa mutane su canja su fitunu, sai ya halatta musu yin sallar irin yadda suka saba.( ) 
Abin da Sulaim dan Kais ya raiwaot yana kara nuna haka, yake cewa: Amirul Mumina ya yi huduba ya godewa Allah ya kuma yabe shi, sannan ya yiwa Annabi Salati, bayan nan ya ce: "Dabi’u biyu nake jiye muku, bin son zuciya da dogon buri”. Sannan ya fadi kirkire-kirkiren da suka bayyana bayan Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Da na dora mutane kan su bar su da mayakana sun tarwatse sun barni ni kadai ko da ‘yar jama’a kadan... wallahi tabbas na umarci mutne kar su yi jam’in nafila a watan Ramadan, sai dai sallar farilla, na sanar da su cewa yin jam’in nafilfili bidi’a ne, sai wasu cikin mayakan da suke tare da ni suka ce: Ya ku Musulmai an canja sunnar Umar yana hana mu yin sallar nafila a watan Ramadan! Tabbas na ji tsoron kar su yunkuro su taho inda sojoji na suke...”.( ) 
Tabbas Imam ya hau karagar halifanci da goyon bayan Musulmai ya kuma fuskanci kirkire-kirkiren aka kaga bayan Manzon Allah (s.a.w), ya kuma yi nufin dawo da al’uma zuwa ga zamanin Manzon Allah (s.a.w) a fagage daban-daban, sai dai dabaibayin ya samu kansa a cikin (na al’umma) bai ba shi damar cimma burinsa ba, don haka ya bar wasu abubuwa a yadda suke, sai ya bada himma a kan abubuwa da suka fi muhimmanci idan haka ne ma ya umarci dansa Hasan ya barsu yadda suke don kar tsarin mulki ya lalace, mayakansa su yi masa bore.
Abul Kasim Ibnu kualawaihi ya rawaito  (ya rasu: 369H) daga Imamai biyu Bakir da Sadik (a.s), cewa; su biyun sun ce: Amirul Muminina yana garin Kufa sai mutane suka zo masa, suka ce masa ka nada mana limamin da zai yi mana limanci a watan Ramadan, sai ya ce musu: A’a, ya hana su yin jam’i, lokacin da suka ji haka sai suka fara cewa ku yi wa Ramadan kuka, wayyo Ramadan! Wayyo Ramadan! Sai Harisul A’awar ya zo a cikin mutane ya ce: Ya shugaban Muminai, mutane suna kara sun kyamaci maganarka, sai ya ce: Nan take Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku barsu da abin da suke so, wanda suke so ya yi musu Sallah”.( ) 
Wadannan ruwayoyin suna bayana mana matsayin Ahlulbait (a.s) a kan sallar tarawihi.
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-
MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: