bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:52:11
Waxannan siffofi ne da Annabi (S.A.W) ya ambata ga Shi'a kuma ko’ina ne aka same su kuma kowane zamani ne.
Lambar Labari: 188
A nan ina son in juyo tunanin Dakta Ahmad Mahmud zuwa ga cewa Shi'a ba sa kafa dalili a kan Shi’anci da samuwar Shi’anci a lokacin Annabi (S.A.W) da abin da ya zo daga gare shi a hadisan sa, mas’alar kamar yadda masu ilimin usul ne suke kiran ta da cewa: Tana matsayin doka ce ba wani abu wanda yake samamme a waje ba, wato ba dole ba ne a same su a wannan lokaci kamar yadda shi Dakta Ahmad Mahmud yake nunawa.
Waxannan siffofi ne da Annabi (S.A.W) ya ambata ga Shi'a kuma ko’ina ne aka same su kuma kowane zamani ne. Amma kafa dalili a kan cewa akwai Shi'a a lokacin Annabi (S.A.W) to ana iya fahimtar sa daga ruwayoyi da kuma qarinoni masu yawa da a kan iya kawo su game da wannan lamarin. Waxannan kuwa Dakta Abdul’aziz Adduri ya kawo wani vangare daga cikin su, kuma ya kawo madogararta , tare da wasu bayanai da kuma wani qaidi da ya kawo kan cewa Shi’anci na ruhi da gina al’umma ne ake nufi a wannan lokaci akwai shi kamar yadda ya kawo a cikin wani vangare na dalilan su wanda a kan haka ne kuma Yahaya Hashim Fargal ya tafi a littafin sa. .
Wasu daga waxannan ra’ayoyi suna komawa ne tun farko zuwa ga lokacin da Shi’anci ya bayyana a rayuwar Annabi (S.A.W) yayin da wasu jama’a suka fifita Ali (A.S) a kan wanin sa na daga sahabbai kuma suka riqe shi shugaba kuma jagora waxanda suka haxa da Ammar xan Yasir, da Abuzar gifari, da Salman Farisi, da Miqdad xan Aswad, da Jabir xan Abdullah da Ubayyu xan Ka’abu, da Abu Ayyub Al’Ansari, da Banu Hashim , da sauran su.
Don haka ne ma yake kuskure ne wani ya kawo bayyanar Shi’anci da cewa ya zo bayan wannan lokaci na Annabi (S.A.W) tare da samuwar su tun a lokacin Annabi mai tsira da aminni. Muhammad Abdullah ya na faxa a cikin littafinsa na "Tarihul Jam’iyyatus Sirriyya" gun bayanin sa da ta’aliqin sa a kan abin da wasu litattafan tarihi  suka ruwaito yayin da Annabi (S.A.W) ya tara dangin sa yayin saukar faxin sa Maxaukaki: "Ka gargaxi danginka makusata", Shu’ara’: 214. Sai ya kira su zuwa ga biyayya gare shi ba su amsa masa ba, sai Ali (A.S) ne kawai ya amsa masa, sai ya yi riqo da wuyan Ali (A.S) ya ce: Wannan xan’uwana ne, kuma wasiyyi na, sannan halifa na a cikin ku sai ku ji daga gare shi kuma ku bi shi.
Muhammad Abdullah ya yi ta’aliqi da cewa: ya na daga kuskure a ce: Shi’anci ya faru ne tun farko a lokacin da Khawarijawa suka ware daga rundunar Imam Ali (A.S), Shi’anci ya fara ne tare da bayyanar lokacin isar da saqon Annabi (S.A.W) yayin da aka umarce shi da ya yi gargaxi ga danginsa makusanta a wannan aya.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: