bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      22:58:06
Abin da jamhurin masu bahasi suka tafi a kansa na cewa Shi’anci ya bayyana ne ranar Saqifa, kuma wannan ya na nuna dalilin samuwar sa a lokacin Annabi (S.A.W) ke nan, domin ba zai yiwu ba a hankalce a ce
Lambar Labari: 189
Dalilai A Kan Faruwar Shi’anci A Lokacin Annabi (S.A.W)
1- Litattafan tarihi da suka zo da siffofin wasu jama’a a lokacin Annabi (S.A.W) da ake kiran su da Shi'a kuma mun riga mun yi nuni da wannan, don haka ne Hasan xan Musa Annubkhati yake da wani bayani game da Shi'a ya na cewa:
Shi'a su ne jama’ar da suka bi Imam Ali xan Abuxalib (A.S) a lokacin Annabi (S.A.W) sannan sai ya qirga wasu mutane ya ce: Su ne farkon waxanda aka kira da Suna Shi'a, don sunan Shi’anci daxaxxe ne ga mabiya Ibrahim (A.S) (Alfiraq wal maqalat na nubkhati: Babin ta’arifin Shi'a.).
2- Abin da jamhurin masu bahasi suka tafi a kansa na cewa Shi’anci ya bayyana ne ranar Saqifa, kuma wannan ya na nuna dalilin samuwar sa a lokacin Annabi (S.A.W) ke nan, domin ba zai yiwu ba a hankalce a ce: ya havaka cikinsati gudakwai tsawon muddar ranar qarshen rayuwar Annabi (S.A.W) zuwa gama lamuran shirin zanajarsa bayan wafatin sa, wai sai aka samu wasu mutane da suke da wani tunani da fikira da aqida ta musamman.
Wannan kuwa lamari ne da ba zai yiwu ba, domin samuwar irin wannan jama’a tana buqatar lokaci ba qanqani ba, kuma dukkan wanda yake da masaniya kan lamarin Saqifa da matsayin da waxanda suka qi yin bai’a ga Abubakar da hujjojin su a kan wannan lamarin zai samu yankewa da yaqinin cewa wannan matsayi da suka xauka na qin bai'a ga Abubakar da biyayya ga Ali (A.S) ba ya faru ba ne a gajeren lokaci da gaugawa haka daga wafatin Manzon Allah (S.A.W) zuwa ga binne shi, saboda lamarin ya nuna akwai samuwar wannan fikira da aqida mai asali tun farko kan wannan lamarin tun farkon musulunci.
3- Wasu suna ganin cewa ba zai yiwu ba a hankalce a samu zuwan wasu hadisai daga harshen Annabi (S.A.W) da suke fifita shi sannan sai a samu wasu musulmi sun qi yarda da hakan suna masu yin kunnen shegu da wannan, alhalin suna masu imaninsu da biyayyar su ga Manzon Allah (S.A.W). Sai dai amma tarihin musulunci ya nuna mana faruwar hakan a wurare daban-daban da zamu ambata maka wasu daga ciki:
A- Matakin Farko:
Yayin da faxin Allah Maxaukaki ya sauka, "Ka yi gargaxi ga jama’arka makusanta", aya ta 214 daga surar Shu’ara’. Masu tarihi suna cewa Annabi (S.A.W) ya kira Ali (A.S) ya umarce shi da ya yi abinci ya kuma kira alayen Abdul Muxallib, adadin su a wannan rana mutane arba’in ne, bayan sun ci sun sha daga nonon da ya tanadar musu sai Annabi (S.A.W) ya miqe tsaye ya ce: Ya ku ‘ya’yan Abdul Muxallib ni wallahi ban san wani saurayi da ya zo wa Larabawa da fiye da abin da na zo muku da shi ba, na zo muku da alherin duniya da lahira, kuma Allah ya umarce ni da in kira ku zuwa gare shi, waye a cikinku da zai taimake ni a kan wannan lamari a kan ya kasance xan’uwa na kuma wasiyyina kuma halifana a cikin ku,. Sai mutane suka tage gaba xaya, babu wanda ya bayar da amsa. Ali (A.S) ya na cewa: Sai na ce: -alhalin nafi kowa qarancin shekaru a cikin su kuma na fi su qananan idanu, na fi su girman ciki, na fi su shafaffen dudduge- Ni ne zan kasance wazirin ka a kan hakan ya annabin Allah. Sai ya riqi wuyan riga ta, sannan sai ya ce: Wannan ne xan’uwana kuma wasiyyina sannan halifa na a cikin ku, ku ji ku bi daga gare shi, sai mutanen suka kwashe da dariya suna cewa da Abuxalib: Ya umarce ka ka ji ga xanka kuma ka yi biyayya (Tarihin Xabari: j2, shafi: 216. da tarihin bin asir, j 2, shafi: 28).
B- Mataki Na biyu:
Abu Rafi’i alqibxi bawan Annabi (S.A.W) ya na cewa: Na shiga wajen Annabi (S.A.W) ana cikin halin yi masa wahayi, sai na ga wata macijiya, na kwanta tsakaninta da Annabi (S.A.W) domin kada wata cutarwa daga gareta ta isa zuwa gare shi, har sai da wahayi ya qare daga gare shi, sannan ya umarce ni da kashe ta, sai na ji shi ya na cewa: Godiya ta tabbata ga Allah da ya kammala wa Ali (A.S) burin sa, farin ciki ya tabbata ga Ali da fifitawar da Allah ya yi masa. Wannan kuwa bayan ya karanta faxin Allah Maxaukaki: "Kawai majivancin lamarin ku su ne: Allah da manzon sa da waxanda suka yi imani waxannan da suke tsayar da salla suna bayar da zakka, alhalin suna masu ruku’u. Aya: 55, Ma’ida. Kuma malaman Ahlus-sunna da na Shi'a duk sun tafi a kan cewa wannan aya ta sauka ne ga Ali (A.S), daga cikin su akwai Suyuxi a Durrul Mansur gun tafsirin ayar da aka ambata, haka nan ma Arrazi a cikin Mafatihul Gaibi, da baidhawi a cikin tafsirinsa, da Zamakhshari a cikin Kusshaf, da Sa'alabi a cikin tafsirin sa, da Xabarasi a cikin Majma'al Bayan da wasunsu daga malaman tafsiri da masu hadisi.
Daga abin mamaki sai ga shi Alusi a cikin tafsirin sa na Ruhul Ma'ani ya tsaya a kan wata matsaya da take mai muni da rauni ya na mai hana saukar wannan aya game da Ali (A.S), ya na kuma faxawa cikin vangaranci da yakan kai mutun ga faxawa cikin qiyayya da gaba da gaskiya, da faxawa cikin magana mai karo da juna da warwara maras ma’ana. Mutum yakan yi mamakin wannnan mutumin, domin sau da yawa mukan gan shi da matsayin warware magana da suka ga Imam Ali (A.S), wani lokaci ya ba shi haqqin sa, wani lokacin kuma ya tsaya ya na mai musun sa, kuma dukkan wanda ya karanta rubuce-rubucen Alusi ya san shi da hakan.
C- Mataki na uku:
Matakin da Annabi (S.A.W) ya xauka ranar Gadir-Khum, yayin da ayar nan ta sauka: "Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijin ka, idan kuwa ba ka aikata ba, to ba ka isar da saqon sa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane" Ma’ida: 69. Yayin nan sai Annabi (S.A.W) ya tsayar da matafiya kuma aka yi masa mimbari daga kayan raquma sai ya yi huxuba a kansa da huxubar nan tasa mashahuriya sananniya sannan sai ya riqe hannun Imam Ali (A.S) ya ce: Ba ni ne na fi cancantar jagorantar muminai ba fiye da kawukan su? Suka ce: Haka ne. Sai ya maimaita sau uku, sannan sai ya ce: "Duk wanda nake jagoran sa to Ali wannan jagoran sa ne, Ubangiji ka jivanci wanda ya jivance shi, ka qi wanda ya qi shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka kuma tavar da wanda ya tavar da shi" sai halifa na biyu ya haxu da shi ya ce: Farin ciki ya tabbata gare ka ya kai xan Abuxalib, ka zama shugabana kuma shugaban dukkan wani mumini da mumina.
Kuma Razi ya kawo fuskoki goma daga cikin sababin saukar wannan aya: kuma daga cikin akwai cewa ta sauka kan Imam Ali (A.S) ne, sannan sai ya qara da bayanin bayan haka da cewa: Wannan shi ne faxin Ibn Abbas, da Barra’u xan Azib, da Muhammad xan Ali, -yana nufin Imam Muhammad Baqir (A.S) (Tafsirin Arrazi, j 3, sahfi: 431) -. Kuma hadisin Gadir jama’a da yawa sun ruwaito shi daga mahardata hadisai na Ahlus-sunna, kuma Ibn Hajar ya ruwaito shi a cikin littafin sawa’iq xin sa daga sahabbai talatin, kuma ya kawo cewa dukkanin tafarkin sa ingantacce ne, kuma wasu kyawawa ne (Assawa’iqul muhriqa, babi na biyu daga fasali na tara).
Ibn Hamza Alhanafi ya kawo shi daga Abixxufail Amir xan Wa’ila kamar haka ya ce: Usama xan Zaid ya ce da Ali: Kai ba jagorana ba ne, kawai jagorana shi ne Manzon Allah (S.A.W), sai Annabi (S.A.W) ya ce: Kamar dai ni an kusa kira na sai in amsa, kuma haqiqa ni zan bar muku nauyaya biyu, xaya ya fi xaya girma, littafin Allah da kuma Ahlin gidana, ku duba yadda zaku maye mini a cikin su, ku sani ba zasu rabu da ni ba, har sai sun riske ni a tafki, kuma Allah shi ne shugabana, kuma ni ne shugaban dukkan mumini da mumina, kuma duk wanda na kasance shugaban sa, to Ali (A.S) shugabansa ne, ya Ubangiji ka agaza wa wanda ya bi shi, kuma ka qi wanda ya qi shi (Albayan watta’arif, j 2, shafi 136).


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: