bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:02:53
A wannan bangaren muna son yin bayani game da alakar namiji da mace a mahangar shari'a da ya shafi haduwarsu, kallo, mu'amalar rayuwar yau da kullum kamar kasuwa da ma'aikatu da makarantu
Lambar Labari: 190
Bangare na Shida
A wannan bangaren muna son yin bayani game da alakar namiji da mace a mahangar shari'a da ya shafi haduwarsu, kallo, mu'amalar rayuwar yau da kullum kamar kasuwa da ma'aikatu da makarantu, kebewa tare, kamanni da juna a sifa, sannan kuma sai mu shiga wasu bayanai kan abin da ya shafi soyaiyar da ake yi a wannan zamanin tsakanin samari da 'yan mata da lalacewar da take haifarwa, da fatan mai karatu zai bi mu a sannu a hankali har zuwa karshen bayanan.
Alakar Jinsi Biyu
Alaka wani madauri ne da yake sanya abubuwa biyu a wuri daya ko yanayi daya ko a fahimta daya kamar alakar samarwa da mai samarwa a irin alakar wuta da zafi ko ruwa da danshi ko mahallicci da abin da ya halitta. Haka nan ma zamu ga akwai alaka tsakanin jinsi biyu na mata da maza wacce take alaka ce da take kaiwa ga ci gaban samuwar dan adam a rayuwar wannan duniyar. Kuma saboda neman tsari a kowane abu sai shari'a ta tsara yadda wannan alakara ya kamata ta kasance da iyakokinta da hakkokin kowane bangare, da hanyar haduwa da rabuwa, da sauran lamura da suka shafi rayuwar ma'aurata.
Alaka tsakanin namiji da mace wani abu ne da yake cikin halittarsu don haka alaka larura ce ta rayuwar wadannan jinsina biyu, sai dai Allah madaukaki bai bar ta sakakai babu wata doka ba. Shari'ar Allah ta sanya mana dokoki da iyakoki a cikin alakar namiji da mace, ta sanya mana hadafofi da suka dace ta yadda zai kai ga hadafin duniya da lahira baki daya. Kuma aka sanya tsari ga wannan alakar ta yadda zata kai ga cimma hadafin samun nutsuwar rai da hutun jiki.
Kallon Ajnabi
Kallo ne mafi tasirin abin da yake samar da alakar farko tsakanin namiji da mace, don haka ne shari'a ta muhimmantar da magana kansa da iyakokinsa da dokokinsa. Musulunci yana ganin kallo shi ne matakin farko da yake dasa sha'awa a zukatan masu kallo, har ma ya siffanta shi da cewa shi kibiyar shedan ce da yake haifar da nadama da hasara ga masu kallon da ita. Kuma saboda samar da aminci a cikin al'umma ne shari'a ta yi umarni da runtse ido da rashin kallon mace ta hanyar kura ido. Sai ta yi nuni da cewa mutum namiji ba shi da mallakar kallon farko ga mace, amma yana mallakar na biyu ko sama da hakan, sai ta hana shi mayar da idonsa don kallo da kura ido da niiyar sha'awa da jin dadi .
A daya bangaren kuma sai ta hana mata yin adon da zai kai namiji ga fizguwa zuwa gare su, sai ta sanya kayan mace su kasance wadanda a bisa al'ada ba a lissafa su a matsayin ado mai jan hankalin maza. Duk da kuma shari'a ta ba wa mace da ta balaga kuma ba ta wuce shekarun tsufa ba ikon fito da fuska da tafukanta, amma ba ta bayar da damar yi musu ado da zai jawo hankalin maza gare ta ba. Amma idan mace ta kasance karama ba ta balaga ba, kuma irinta a yanayinta ba ta cikin wacce ake sha'awarta ko kuma ta kasance ta wuce shekarun da aka wajabta mata sanya hijabi, ita ma irin wadannan ba a yarda su yi wani ado da zai ja hankalin mai kallonsu ba ko da kuwa hannayensu da kafafuwansu sun baiyana.
A nan zata baiyana gare mu cewa kallon farko ba shi da laifi domin yana faruwa ne ba da nufi ba, amma kallo na biyu ko sama da haka musamman idan sun kasance da nufin jin dadi, ko kuma zasu iya haifar da jin dadi ko da kuwa ba da nufinsa ba, to su ne suke zama haram ga namiji. Kuma kamar yadda hakan yake ga mace, haka ma yake ga namiji, sai aka haramta wa mace kallon namiji da nufin jin dadi, ko kuma idan ya haifar mata da jin dadi ko da ba ta yi nufin jin dadin ba.
Adon mace da ake nufi ka da ta baiyanar da shi a ayoyin Kur'ani mai girma ana nufin wurin adon, wato sasannin mace kamar kafada, kirji, cinya, wuya, kafa, da sauransu sun haramta ga namiji ya gani, don haka shari'a ta sanya musu dokokin wajabcin rufe su da irin shigar da mutane suke yi bisa al'ada. Wasu sun dauka rufe wadannan mahallin sai da irin tufafin Afganawa ko Larabawa, alhalin tufafin kowace al'umma yana iya zama hijabi ga mace matukar ya rufe mahallin da aka yi musu umarni su rufe, kuma a bisa al'adar mutanen bai fita daban ba ta yadda a al'adar ake ganin sa yana jan hankalin namiji.
Shari'a ta kebance wasu mazaje da ya halatta ga mace ta baiyana adonta (jikinta) gare su wadanda su suna iya ganin jikinta da suka hada da: miji (shi zai iya ganin komai nata), uba, baban miji, da, 'ya'yan miji, 'yan'uwa, 'ya'yan 'yan'uwa, 'ya'yan 'yar'uwa, mace. Wadannan ne mace take iya baiyana jikinta gare su babu wani haramci na shari'a. Amma su ma in ban da mijinta bai halatta ta bude musu daga kirjinta zuwa farjinta ba, mafi kyau sai su takaita da ganin wuyanta zuwa sama kawai, ko kwaurinta zuwa kasa .
Namiji yana iya ganin jikin matarsa (baki dayan jikin matarsa har al'aurarta), da jikin babarsa, uwar matarsa, 'yarsa, 'yar 'yarsa, 'yar matarsa, 'yar'uwarsa, 'yar 'yar'uwarsa, 'yar dan'uwansa. Haka nan ma ta fuskacin mace akwai mazajen da ya halatta ta ga jikinsu in ban da al'aurarsu, wadannan mazaje sun hada da miji (duk jikinsa har al'aura), baban miji, da, jika, dan'uwa, dan dan'uwa, dan 'yar'uwa, dan miji. Akwai wasu mutane da bai halatta su ga jikin mace ba, sai dai a al'ada ya zama ana sakaci game da lamarinsu sabanin shari'a, wadannan mutane sun hada da: dan'uwan miji, mijin goggo, mijin amma, dan ammi, dan goggo. Ko kuma rashin rufe jikin 'yar'uwar mata, ko matar dan dan'uwa, ko matar dan 'yar'uwa ga namiji, wannan duk ba ya halatta a shar'ance domin ba sa cikin maharramai.
Haka nan akwai wasu mutane da ba dole ne mace ta rufe jikinta gare su ba da suka hada da, wawa da ba shi da wata sha'awa ga mata ko yaran da ba su san wani abu mai sunan al'aurar mata ba sakamakon ba su da sha'awa kan hakan kuma ba su san ma'anar sha'awa ba, kuma idan suka ga mace ba komai kamar yadda ba dole ne ta rufe jikinta gare su ba. Kamar yadda babu laifi kallon yarinya ko tsohuwa ba tare da nufin sha'awa ba kuma ba tare da samun sha'awa ba, amma idan ya zama da nufin samun sha'awa ko kuma za a samu sha'awa da yin haka a lokacin ne yake haramta .

Dr Sheikh Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@hotmail.com
www.haidarcenter.com


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: