bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:10:34
Sai kuma halarcin kallon mace sakamakon rayuwar tare, wani lokaci gidan haya ne ake taraiya a cikinsa bisa al'adun zaman gidan haya a tare
Lambar Labari: 191

Alakar Jinsi Biyu_02

Haka nan ya halatta ga namiji ya kalli mace mai baiyanar da jikinta wacce ko da an yi umarni ta rufe ba ta rufewa, sai dai ya kasance kallo ba da nufin jin dadi ba kuma kallon da idan aka yi shi ba za a samu jin dadi ba. Idan ya zama da nufin jin dadi, ko kuma idan an yi kallon ana samun jin dadi to bai halatta ba. Sai dai mahaukaciya duk da tana da wani hukunci shigen irin wannan amma bai halatta kallon gashinta da jikinta da gangan ba.

Sai kuma halarcin kallon mace sakamakon rayuwar tare, wani lokaci gidan haya ne ake taraiya a cikinsa bisa al'adun zaman gidan haya a tare, idan wani ya samu kansa cikin irin wadannan gidajen ko kuma a gidan dangi mai yawan mutane to ya zama dole su kiyaye irin wadannan lamurran gwargwadon iyakar da shari'a ta gindaya musu ko da kuwa ta hanyar aure mai sura ne a bisa ra'ayin malaman mazhabar ahlul-baiti ta yadda zasu zama surukan juna.

Idan kuwa lamarin ya shafi rayuwar wajen gida ne da ya shafi wuraren rayuwar al'umma kamar makarantu, kasuwanni, asibitoci, da saurasu, to shari'a ba ta hana haduwar maza da mata ba, kuma ba ta hanna su kallon juna bisa sharudan da ta gindaya ba. A kan haka ne duk wani abu da yake na rayuwar al'umma ko na larura ya halatta kallon juna, amma mu sani cewa duk da haka ba ya halatta kallo da nufin jin dadi, haka nan idan an samu jin dadi da kallon to sai a yanke shi domin zai zama haram ke nan.

Rayuwar tare ta hada da sheda a kotu ko a shari'a, kamar ta nuna rotsen da aka yi mata a kanta, kuma bai halatta ta boye fuskarta ba don ya zama dole alkali ya kalli fuskarta. Kamar dai makaranta a aji ne da ya zama babu yadda za a sanar da mace tarbiiya da ilimi sai da ganin bayanin da ake iya fahimta daga fuskarta. Da wannan ne zamu ga lokacin da hukumar juyin musulunci ta yi umarni a sanya labule tsakanin malamai da dalibai a makarantun jami'a sai Imam Khomaini ya ba wa dansa Ahmad umarnin cire duk wani labule da aka sanya tsakanin dalibai mata da malamansu da wanda aka sanya shi a motocin bos. Haka nan sanaiya a kasuwa gun cinikaiya a nan ma mace tana kallon namiji shi ma ya kalle ta bisa sharudan da aka gindaya, da sauran mu'amalolin rayuwar al'umma baki daya[1].

Duk wata cakudar samari da 'yan mata a kowane janibi na rayuwa da zata kawo rushewar al'umma gaba daya ba ta halatta koda a makaranta ne ko wajan iyo a ruwa, ko sinima, ko ma'aikata, ko zamantakewa, ko wurin taro da makamancin wannan, don haka ne musulunci ya hana hakan sai dai idan cakuda wacce take akwai cikakkiyar kiyayewa da hijabi da kamewa kamar cakuda a hajji da wuraren ziyara ko wuraren aiki da neman ilimi da sauransu. Musulunci bai haramta wa mace ilimi ko aiki ba, ya ma wajabta mata wannan wani lokaci, kuma ya so mata su wani lokaci. Abin da ya haramta mata shi ne: fita da tsaraici, kamar yadda ya haramta mata aikin da zai hana ta kame kai. Sai kuma bangaren larura yayin magani ko haihuwa domin larura tana halatta duk wani abu da yake haram, kamar yin allura ga mace kuma babu mace da zata iya yi mata, ko ofareshan a asibiti na cuta ko na haihuwa, ko magani a cibiyarta ko kaho a bayanta, da sauran mahallin larura. Wani lokaci kuma mace ce likitan a nan ma babu wata mafita don haka ganin jikin namiji yana halatta gare ta kamar yadda muka kawo ga namiji ya ga jikin mace gun larurar magani.

Sannan a kowane wuri ne ko da kuwa a wruin da ya halatta namiji ya ga mace ko mace ta ga namiji saboda muharramai ne, hatta da uba ga 'yarsa ko dan'uwa ga 'yar'uwarsa babu wani wuri da aka cire ka'idar nan mai cewa: "Ka da kallon ya zama da nufin jin dadi ko ya kasance mai sanya jin dadi ko da kuwa babu nufin jin dadi, idan kuwa ya haifar da jin dadi to ya zama haram". Wannan doka ce ta bai daya a kowane kallo a ko'ina tsakanin kowane irin mutane muharramai ne ko ba muharramai ba, lamarin rayuwar al'umma ne ko na larura ko waninsa. Kiyaye wannan dokar a kowane irin yanayi ya zama wajibi, saboda haka ko da kallo a wani wuri ya zama halal amma idan ya zama ya taka wannan dokar to ya koma haram.

Muryar Ajanbi

Bayan mun gama magana kan lamarin kallon mace ga namiji ko namiji ga mace sai kuma janibin jin muryar juna. Bayan kallo babu wani abu da yake jawo hankalin namiji ga mace da ya kai murya don hake ne kai tsaye bayan mas'alar kallo sai muka fada mas'alar murya domin mu ga me ye shari'a ta ce game da wannan lamarin. Shari'a ta halatta jin muryar mace ajnabiiya haka ma jin muryar namiji gun mace kamar yadda al'adar musulmi da ruwayoyi da tarihi suka tabbatar da hakan. Annabin rahama da alayensa suna sauraron mace kuma ana sauraron mata amma ba su hana ba, hasali ma saiyidar mata baki daya 'yar annabin rahama tana yin huduba a masallaci kan neman hakkinta bayan wafatin babanta.

Abin da shari'a ta haramta shi ne neman jin dadi yayin sauraron muryar mace a kowane yanayi ne na ilmantarwa ne kamar idan mace ita ce malama, ko na larura kamar a likitanci, ko na rayuwa ne kamar a kasuwa ko makota da sauransu. Sai aka hana mata sirantar da murayarsu da tausasa magana da lankwasa ta don gudun ka da ta zama mai jan hankalin maza. Kamar yadda ba a yarda ya kunshi kalmomin da zasu tayar da hankalin namiji ba ko sha'awarsa, dole ne maganar ta kasance a bisa al'ada da man maza da mata suna yin irin wannan muryar. A matakin farko zamu ga wasu daga matan annabi ne aka hana mayar da muryarsu siririya mai laushi don gudun ka da cutar mai ciwon sha'awa ta tashi[2].

Dr Sheikh Hafiz Muhammad Sa'id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

hfazah@hotmail.com

www.haidarcenter.com




[1]Duba; kafi 2: 524. Jawahirul Kalam 29: 89. Almabsut 4: 161. Al'hada'ikun Nadhira 23: 63.

[2]Duba: Tarikh Tabari: Ahdas sanat 11. Da sauran littattafan tarihi. Al'hada'ikun Nadhira 23: 66-67. Jami'ul Makasid 12: 43. Majma'aul Bayan 4: 356. Surar Ahzab 33: 32.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: