bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:12:27
Duk wata mata da take muharrama ga namiji ko namijin da yake muharrami ga mace to suna yin hannu tsakaninsu ba tare da wani kariya ba,
Lambar Labari: 192

Hannu da Ajnabi

Yin hannun tsakanin maza ko tsakanin mata shi ne asalin gaisuwa, sai dai an hana yin hannu tsakanin namiji da mace idan babu wani kyalle kamar safar hannu tsakaninsu. Idan mace ko namiji yana da wani kariya kamar safar hannu to zai iya gaisawa hannu da hannu da mace amma da sharadin ka da ya sanya dan yatsa ya sosa tafin hannunta ko kuma ya matse mata hannu da karfi.

Duk wata mata da take muharrama ga namiji ko namijin da yake muharrami ga mace to suna yin hannu tsakaninsu ba tare da wani kariya ba, mutum yana iya yin hannu da babarsa, 'yarsa, 'yar'uwa, 'yar dan'uwa, 'yar 'yar'uwa, amma, goggo, da sauransu. Amma idan mace ta kasance ajnabiiya ko namiji ajnabi wato ba muharramai ba ne, ba ya halatta a yi hannu da su sai da wani kariya tsakani kamar safar hannu ko wata leda ko kyalle sai gun lalura ko yanayi mai haifar da damuwa da tsanani.

Yin hannu tsakanin maza da mata bai kasance kamar yadda yake a shari'a ba, kowace al'umma tana bin al'adarta ne. Misali duk da Musulunci bai haramta ba ya sanya shi a matsayin halal, amma yin sa a wasu al'ummu yakan iya kai ga zubar da jinin wanda ya yi, a wasu al'ummu yakan kai ga dukansa, a wasu kuma ana fasikantar da shi. Kamar yadda kin yin sa kuma ko da babu kariya a wasu al'ummun da suke musulmi ne ana ganin sa a matsayin wulakanta mace. Da yawa irin wadannan hukunce-hukunce har yanzu a kasashen musulmi kallon al'ada ne ya fi karfi gare su ba kallon Musulunci ba[1].

Kebewar Ajnabai

Shari'a ta haramta kebewa tsakanin maza da mata ajnabai, ajnabi shi ne wanda mace zata iya aurensa. Kebewa tana nufin shigar namiji daya da mace daya ajnabai wani wuri da aka kulle kofa ta yadda babu mai iya ganin su ko jin su ko iya shigowa sai dai idan sun bude kofa ne tare kuma da rashin amintuwa daga fasadi, idan babu daya daga wadannan sharadin to bai zama kebewa ba. Da zasu kulle amma kuma akwai amintuwar yin fasadi to bai cika sharudan kebewa ba. Haka nan da zai shiga daki da ita su kulle kofa amma kuma akwai kamara a dakin ana iya ganinsu kamar ya zama wuri ne na intabiyu da shi a radio ko wurin jami'an tsaro, ko ya zamanto sun kebe amma ba shi da wata al'aura kuma ba ya ma sha'awar mata don haka babu maganar wani fasadi ke nan, ko ya zama suna cikin mota suna tafiya ba tare da tsayawa da kebewa wurin da ba a iya ganin su ba, a irin wadannan halayen ba a kiran su da kebewa tsakanin namiji da mace ajnabai.

Kebewar ajnabawa wani abu ne da al'ada ta dauke shi a matsayin abu na wasa, kuma sau tari fasadi yakan samu ne ta hanyar sakaci da wannan dokar ta shari'a. A bisa al'adu gidaje suna zama sakakai, ba su dauki kebewar ajnabai a matsayin wata matsala ta shari'a ba, ita kuwa shari'a tana haramta hakan ko da kuwa babu wani abu da yake gudana tsakaninsu[2].

Tunanin cewa ai babu wani fasadi da yake faruwa sakamakon kebewar kuskure ne domin shari'a ta haramta kebewar ne ko da kuwa babu wani fasadi da yake wakana. Ita kebewar kanta ce shari'a take gani a matsayin fasadi kuma haram a matsayin dokar Allah. Sai dai al'ada ta take wannan dokar ta Allah, sai suka yi sakaci da wannan dokar ta yadda dan'uwan miji da matar dan'uwansa suke kebewa, ko dan dan'uwa da matar amminsa suke kebewa, suka dauki hakan a matsayin ba wani abu ba alhalin shari'a ta haramta abin da ake kira da kebancewa tsakaninsu in dai ba halin larura ba.

Tafiyar Mace

Shari'a ta bayar da tarbiiya mai kyau ga tafiyar mace a hanya, idan mace tana tafiya ana son ta koma gefen hanya ko garu, shari'a ba ta son tafiyar mace a tsakiyar hanya. Kuma ko ba komai a wannan zamanin tsakiyar hanyar yana da hadarin cin karo da abin hawa. Kuma ba a son ta zama tana gaban namiji yayin tafiya, don haka ne idan namiji ya kasance yana tafiya sai ya tarar da wata mace a hanya ko ta tarar da shi idan yanayin tafiyarsu ya kusa zama iri daya ta fuskacin sauri to abin da ya fi shi ne ta tsaya daga bayansa. Haka nan idan suna tafiya da namiji don ta nuna masa wani wuri ko kuma shi ne zai nuna mata wani wuri kamar yadda zamu iya gani a kissar 'yar annabi Shu'aib (a.s) da annabi Musa (a.s).

Shiga Gida

Shari'a ta wajabta wa duk wani wanda yake son shiga gidan mutane sallama da neman izini har sau uku, idan an ba shi izini sai ya shigo idan kuwa ya ji shiru sai ya koma. Hatta da mai gida kansa ba shi da hakkin shiga gidansa sai ya nemi izinin matarsa ta hanyar sallama da neman izini matukar ba su ce ya shigo ba sai ya dakata domin ta yiwu matarsa, 'yarsa, dansa da sauransu suna cikin halin da ba sa son ya gan su a hakan, ko kuma suna da baki da ba sa son ya shigo ba su shirya ba. Haka nan ma matar gida ko yaran gida da suka kai matakin maiyazewa suka san ma'anar tsaraici su ma yana da kyau a sanar da su muhimmancin neman izinin yayin shiga gida. Idan mai gida ya ga ba a ba shi damar shigowa ba ko da lokaci ya tsawaita to ka da ya yi fushi ya nuna ai gidansa ne, na cikin gida suna da hakkin da shi ma yake da shi, don haka ya kiyaye halayen musulunci ya jira har sai sun ba shi izinin shigowa. Haka nan bai halatta ba mutum ya shiga gidan wasu wurin mata sai da izininsu, idan matan suka yi izini sannan sai namiji ya shiga idan kuwa ba su yi izini ba to sai ya dakata ya koma. Neman izini wajibi ne kuma hakki ne na mace, yana hana maza su ga abin da aka haramta na ganin mata, neman izini yana ba ta damar sanya hijibinta kuma ta haka ne za a nisanci ganin haram. Wannan neman izinin ba shi da bambanci ko ina ne, hatta da ajin karatu bai dace ba malami ya fado aji ga dalibansa maza ne ko mata ne sai ya buga kofa sun san cewa malaminsu zai shigo, ya yi sallama, sun amsa, sannan sai ya shiga ajin, kuma wannan lamarin haka yake a kowane wuri kuma ga kowane mutum.

Sai dai bayin mace ko yara da ba su balaga ba suna iya shiga kowane lokaci suka ga dama ko ba izini sai dai a lokuta uku. Duk da bayin mace da yara suna iya shiga kowane lokaci ko ba izini amma sai Musulunci ya sanya musu lokuta uku da dole ne su nemi izinin mace kafin su shiga wurinta, don haka yana da kyau a koyar da yara wannan tarbiiyar a sanar da su lokutan da zasu nemi izini yayin shiga gidan mutane. Lokutan sun hada da; 1)Bayan sallar asuba har zuwa fitowar rana. 2)Lokacin hutun zafin rana yayin da suke cire tufafinsu suna hutawa. 3)Bayan sallar magariba da issha'.

A kowane lokaci neman izinin yana kan duk wani wanda ya balaga, duk sa'adda zai shiga gidan da yake akwai mata to sai ya nemi izinin shiga ko da kuwa muharramai ne. Idan mutum zai shiga gidan babarsa ko zai shiga wurin babansa to sai ya nemi izininsu, sai dai ba dole ba ne kan uba ya nemi izini yayin shiga wurin dansa, haka ma idan zai shiga wurin 'yarsa ko 'yar'uwarsa idan suna da aure, idan ba su da aure ba dole ba ne ya nemi izininsu yayin shiga.

Sai dai a kowace nau'in shiga wurin kowaye hukuncin sallama kafin shiga yana kan mai shiga ko da kuwa uba ne da zai shiga wurin dansa ko 'yarsa. Neman izini a dunkule wani hakki ne na wanda za a shiga wurin wani ko wata don ka da a shigar wa mutum cikin wani yanayi da bai shirya ba kuma ba zai so a gan shi cikin wannan halin ba don haka sai a kiyaye[3].

Dr Sheikh Hafiz Muhammad Sa'id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

hfazah@hotmail.com

www.haidarcenter.com



[1]Duba Hukucin hannu da mace; Usulul Kafi 5: 525.

[2]Duba wasu daga hukunce-hukuncen kebewa; Jami'ul Makasid 12: 44. Mustadrakul Wasa'il 14: 266. Kafi 5: 519.

[3]Duba wasu bayanai: Majma'ul bayan 4: 154. Surar Nur 24: 58, 59. Kafi 5: 528-9.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: