bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:17:37
Ta tsananta lamarin har ta yi umarni da fitar da masu irin wadannan halaye daga gidajen musulmi . Muhimmin lamari shi ne ma'aunin kamantuwa da maza ko kamantuwa da mata
Lambar Labari: 194
Kamanni Da Maza
Allah ya halicci maza da mata kuma ya bambanta tsakainsu, kuma ya sanya iyaka kan kowannensu namiji ne ko mace sannan ya sanya wa kowane jinsi siffofin da suka kebanta da su. Hatta motsin jiki da yanayin aiyuka, magana, karfin jiki, zama, tafiya, tufafi, al'adu, da sauransu sai da aka samu bambanci tsakanin namiji da mace, sai wannan ya wajabta wa kowane jinsi tsayawa iyakarsa. Shari'a ta haramta kuma ta la'anci mai kamantuwa da maza daga cikin mata da kuma namiji mai kamantuwa da mata. Ta tsananta lamarin har ta yi umarni da fitar da masu irin wadannan halaye daga gidajen musulmi . Muhimmin lamari shi ne ma'aunin kamantuwa da maza ko kamantuwa da mata, kuma mafi muhimmaci shi he kowace al'umma ta koma wa al'adanta domin kowace al'umma tana da al'adarta, akwai wacce shigar mazanta ita ce shigar matan wata al'ummar da akasin hakan.
Sai dai sabanin da ake ciki shi ne mene ne mai kamatuwa da daya jinsin? Kuma shin idan namiji ya yi aiki ya koma mace ko mace ta yi aikin da ya mayar da ita namiji hakan yana cikin kamantuwa da aka haramta ko kuwa? A nan ne zamu ga yana da muhimmanci kowa ya koma wa mazhabarsa domin sanin ma'anar hakan gun malaman mazhabarsa. Malamanmu sun bayar da amsar cewa wannan ba ya ciki, kuma babu wani dalili da suke da shi kan haramcin hakan. Domin kamantuwa da mace shi ne namiji yana namiji ya kamantu da ita, kamar yadda kamantuwa da namiji shi ne mace tana mace ta kamantu shi. A nan kuma ya koma mace ne kai tsaye ko ta koma namiji ne kai tsaye, kuma ba mu samu haramcin hakan ba a shar'ance.
Idan aka samu wani mai raddi ga malamanmu kan hakan yana mai kafa dalili da ayar canja halittar Allah yana mai jahiltar mahangar malamanmu kan wannan ayar? Sai mu ba shi amsa da cewar: Halittar Allah da shedan ya kawo a wannan ayar yana nufin hukuncin Allah da addininsa  kamar yadda ya zo a ruwayoyin Ahlul-baiti (a.s).
Mas'alar kamantuwar maza da mata ko akasin haka tana doruwa kai tsaye bisa al'adun mutane ne, idan sanya sarka ko dan'kunne ya kebanta da mata a wasu al'adun, to a wasu al'adun da hakan bai kebanta da mata ba sai ya zama halal ga namiji ya sanya dan kunne da sarka. Amma idan ya kebanta da mata ta yadda za a ga namiji ya yi shigar mata bisa al'ada to a nan bai halatta ga namiji ba. Kamar dai tufafi ne, da zamu ga mata ne suke sanya wando maza su sanya zani a wasu kasashe irin su Indunisiya, amma sai hakan ya zama akasi a kasashen hausa ta yadda maza ne suke sanya wando mata su sanya zane. Ko da yake yanzu ma mata suna sanya wando a al'adun bahaushe, kuma a bisa gaskiya wando ne ya fi dacewa da mace domin ya fi ba ta kariya, babu wata iska da zata daga mata zani ko ta yaye mata kwauri, don haka ina kira ga bahaushe ya samar da juyin tufafi musamman ma wando ga mata a cikin al'adunsa.
Sannan tun da wannan hukunci ya kebanci al'umma ne ba ya shafar tsakanin miji da matarsa, idan mace da miji su kadai ne a gidajensu, kuma tana son ta yi kwalliya da kayansa shi kuma ya yi mata kwalliya da kayan mata babu wani abu da zai hana su yin hakan. Idan zasu fita sai su canja kayansu idan sun dawo daga unguwa suna gidansu sai kowa ya ba wa kowa kayansa, sai ya yi mata shigar mata ita kuma ta yi masa shigar maza.
Sumbuntar Yara
Musulunci ya karfafi iyaye da sumbutar 'ya'yansu kamar yadda ya karfafi maza da sumbuntar matansu mata kuma da sumbuntar mazansu, sai dai wannan bai zama al'ada gun bahaushe ba har yanzu har ma wasu suna ganin sumbunta a matsayin wani rashin ladabi. Idan muka duba hukuncin abubuwan da shari'a ta halatta sau tari wasu aububwan suna saba wa da al'adun wasu al'ummu, kuma yawancin al'ummu sun fi riko da al'ada fiye da addini sai su ga halaccin addini mummuna su ga halaccin al'ada kyakkyawa.
Sai dai Musulunci ya sanya karhancin sumbuntar yarinyar da ta kai shekaru biyar ko shida ga mutanen da ba iyayenta maza ba, ana son ma nisantar sumbuntar ta idan ta wuce shekaru biyu. Karahiya ne ga namiji ya sumbance ta idan ta kai wannan shekarun idan babu sha'awa a sumbuntar, amma idan ma da sha'awa ne to ya haramta kai tsaye. Haka nan ma mata ajnabai ga yaro an karhanta su sumbanci yaro idan yakai shekaru bakwai .
Ya fi kyau ka da a saba wa yara su taso da al'adar sumbuntar yara 'yan'uwansu tun farko, ta yadda idan suka kai shekaru biyar zuwa bakwai ba zasu wahala wurin barin ta ba. Sau tari idan mutum ya saba kan wani hali da ya taso a kansa yakan yi masa wahalar barinsa da wuri, don haka tun farko ka da su saba da wannan halin shi ya fi. Sumbunta wani hali ne da idan ya yadu tsakanin samari da 'yan mata shi ne babban mukullin shedan na yada fasadi, kuma kasashen yamma babban misali ne wurin lalacewa sakamakon irin wadannan munanan al'adun.


Dr Sheikh Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@hotmail.com
www.haidarcenter.com




comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: