bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:30:13
Husaini yana jawo ukuba mai girma da kunyata duniya da lahira, saboda haka akiyaye akiyaye daga shiga azabar wuta da nadama da hasara a ranar da nadama bata wani amafani.
Lambar Labari: 195
Daga cikin hakkin dukkanin musulmi da musulma da duk wanda ya yi Imani da manzon rahama da ya yi koyi da shi cikin raya zaman makokin ashura da girmama ibadunsa ka da ya damu da shubuhohin da ake kawowa ciki domin nufin suka da kawo ishkAli kan ta’aziyar Husaini da masu ta’aziyya da masu gangara maukibinsa.
A bayyane yake cikin tabbatattun lamurra kamar yadda bakin ciki kan shaugaban shahidai baban Abdullah Husaini (a.s) da ta’ammuli cikin lamarinsa da girmama ibadunsa da dukkanin hidima cikin tafarkin raya majAlisin ta’aziyya da musibu, lallai digon hawayen da ya zuba kan Husaini (a.s) tana kashe fushin Allah mai girma da daukaka hakama akasin haka, lallai yin tawaye da isgili kan raya lamarinsa da wulakanta masu raya lamarinsa da raunajna su da sanya kaya kan hanyarsu ta Husaini yana jawo ukuba mai girma da kunyata duniya da lahira, saboda haka akiyaye akiyaye  daga shiga azabar wuta da nadama da hasara a ranar da nadama bata wani amafani.
kada ka sake ka bar raya lamarin Husaini wadda cikinsu akwai ziyararsa baban Abdullah (a.s).
Ya zo cikin littafin alkamilul ziyarat babi na 40 sh 116 da isandinsa daga Imam Sadik (a.s) cewa: kada kabar ziyarar kabarin Imam Husaini (a.s) saboda tsoro lallai wanda ya bar ziyararsa zai ga daga hasara abin da zai fatan inama ace kabarins ya kasance kusa da kabarin Imam.
Idan ya zamanto wannan shi ne hAlin wanda ya yi kasa a gwiwa ya takaita kan sha’anin ziyartarsa ya kake tunanin hAlin wadanda ke kawo shubuhohi da cikin sha’aninsa da yin tawaye da jayayya kan rayar alamominsa da bukukuwansa tsarkaka, sannan bomi bomi ga wanda ke yakar wadancan bukukuwa da alamomi yana ta’addanci kan maziyarta Husaini (a.s) yana mai kokarin dusashe hasken Allah da yake tajalli cikin fitilar Imam Husaini shiryayya,sai dai cewa Allah yaki yarda sai ya cika haskensa koda kuwa kafirai da munafukai sunki.
    Ya zama wajibi kan kowannenmu da dukkanin abin da Allah ya bashi da tashi ya raya lamarin Husaini da dukiyarsa da alkalaminsa da kafafuwansa da dukkanin ikonsa domin ya karu cikin da lada da dacewa.
 Na’am ya zama dole ai gyara da sauye sauye a wuraren da ke bukatar hakan ya zama dole a kyawunta niyya da kyawuntar mai aiki da kyawunta aikin, kyawuntar niyya bai isarwa tare da rinjayar aiki da barnarsa lallai kyawuntar niyya bata isarwa cikin ta’ammuli raya al’amarin Husaini (a.s) lallai dole shima rayawar ya zamanto anyi shi cikin kyawawan yanayi, lallai mafi kankantar kuskure koda kuwa bada ganganci akayi shi ban a iya tasiri mara kyawu cikin raya lamarin Husaini (a.s).
Wajibi ne kan dukkaninmu gwargwadon sha’anin kowannenmu kamar yadda malami ya mallaka da iliminsa mawaki da wakens `dan kasuwa da kasuwancinsa sarayi da karfinsa mace da rayuwarta mai huduba da hudubarsa kai kowanne nau’I daga cikinmu ya zama wajibi su kara sadaukarwa cikin wannan hanya ta Allah da kuma abin da ya fi falala da kamala da tsarkaka da yawa da girma da iklasi suna mai tsarkake niyya da izinin Allah madaukaki.
Ya zama dole mu kayyadantu da hukunce-hukuncen Allah da tsantseni daga bayyana ra’ayi matukar mu ba ahAlin hakan ba bane bamu cancanci ba da ra’ayi ba da ijtihadi kamar misalin maraji’ai ahAlin haka, lallai wajibi ne mu mayar da lamari zuwa ga ahAlinsa wadannan masana fikihu ma’abota girma da wanda suke da hakki cikin fitar da fatawa da alkalanci, ka da mu sake mu ketare iyakokin Allah gwargwadon silin gashi lallai su hukunce-hukuncen Allah suan da gman gaske daga wAliyansa, shin shahadar Husaini (a.s) wani abu ne da ya wuce raya addinin kakansa musdafa (s.a.w) lallai daiann har addinin muhammadu bai tsayuwa sai an kasheni to yaku takubba ku kamani.
ashe manzon Allah (s.a.w) ba shi ne mafi darajar hAlittu ba kuma ba shi ne dAlili samuwar duniya da fadinta da cikarta ba, da shi aka farab da shi aka rufe, lallai shi yana kyawawan dabi’u, ya kasance tsakanin zira’I biyu ko kuma mafi kusa daga haka daga madaukaki mafi daukaka, ai dai lokacin da lamari ya isa ga hukunce-hukuncen Allah to Allah madaukakin sarki ya ce:    
 
﴿ وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الأَقَاوِيلِ (44) لأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ (45) ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ (46) فَمَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ ﴾
          da ace zai kirkiri ba’arin wasu maganganu kanmu* da mun damkeshi da dama* sannan da mun yake masa laka.
Yana daga cikin sanannen al’amari cewa labari da akai ma sharadi gasgatacce ne tare da rashin gasgatuwar mukaddima da kuma natija da zata zo bayansa a ilimi mandik. Lalla babu kokwanto cewa manzon Allah (s.a.w) bazai aikata haka sai dai cewa Allah madaukaki ya yi nufin bayyanarwa da bada labari cewa kan lamari mai muhimmancin gaske ba komai bane wannan al’amari da ya wuce girman hukunce hukuncen Allah madaukaki da girmamar alfarmar fatawa da haramcin yenta ba tare da ilimi da ma’arifa ba.
Lallai raya ashura cikin kowacce shekara na nuni zuwa ga rayuwar mazhabar Ahlul baiti (a.s) da wanzuwarsa daga nan kuma mu’amala treda da la’amarin Imam Husaini (a.s) da dukkanin shakAli da yanayi lallai Allah zai bada lada mai yawa ga wanda ya yi haka, kamar yadda dukkanin wanda ya tsaya gaban yaduwar lamarin Husaini Allah zai masa ukuba da ukuba mai radadi zai kuma dusashe ambatonsa wannan sunnar Allah ce kuma bazaka taba samun sauyi daga sunnar Allah ba.
Idan ranar ashuara ta kasance a shaekara 61 daga hijra rundunoni biyu zasu gwabza da juna rundunar yazidu da rundunar Imam Husaini (a.s) to haka lamarin yake cikin kowanne zamani runduna biyu na kwamawa da juna, duk wanda ya kasance cikin hanyar Imam Husaini (a.s) zai amu lada da kuma rahamar Allah, wanda kuma ya kasance kan hanyar Yazidu ba’umayye lallai ya cancanci ukuba da fushin Allah     
 
و﴿ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ ﴾
Ranar ne zasu rarrabu.
Irin wannan rarrabuwa za ta ci gaba har tashin kiyama.
Hakika habibu ibn Muzahir ya kasance daga mutanen Kufa kamar yadda Shimru ibn Zul jaushin ya kasance daga mutanen Kufa, dukkaninsu daga gari daya suka fito sai dai cewa makomar kowanne daya daga cikinsu tayi nisa daga dayan a ranar Ashura, hakika shi Habibu rayuwarsa mai albarka tayi karshe mai kyawu cikin sahun Imam Husaini (a.s) shugaban shahidai jagoran rundunarsa, amma wancan tsinanne wanda ya kasance daga gayyar makiya Imam Husaini (a.s) daga makasansa jagororin munafunci da kafirci.  
nawa ne daga mutane daga wadanda sukai ta’ammuli mai kyawu da al’amarin Husaini da alamominsa da ta’aziyyarsa sai ya zamanto ya garar rahama ya azurtu cikin makomarsa da karshensa.
  misalin zuhairu ibn kainu sananne da kasantuwarsa a farkon sha’aninsa ya kasance mabiyin usman masoyinsa ya kasance ya na imanin cewa lallai na kashe Usmanu bisa zalunci kuma sarkin muminai Ali (a.s) yanada hannu cikin kisansa, ga irin misalin wahab wanda shi kacokan da kirista ya kasance sai dai cewa su biyun sun kai ga matsayin samun ceto da martaba mai girma a ranar Ashura kai hatta kowanne daya daga cikinsu ya kasance kamar ragowar shahidan karbala miliyoyin maziyarta na kai ziyara kabarinsu tsarkakka domin su karanta musu(raina dana mahaifana fansarku) maziyarta sun kasance suna karbar fansarsu da mahaifansu, cikin wannan maziyarta nasu zaka samu manya manyan malamai  da masana fikihu da manya-manyan maraji’an taklidi da muminai masu falala.
Lallai Imam Husaini (a.s) ya kira zuhuiru sai zuhairu yam kiransa ya azurtu duniya da lahira, haka ma ya kirayi ubaidullah ibn hurru ju’ufi don tallafa sai ya ki amsa kiran Imaminsa ya wayi gari cikin asararru ya yi hasara duniya da lahirarsa.
Imam Husaini (a.s) da bukukuwan juya yinsa cikin zamaninmu kadai sun kasance ma’auni majarrabta masakar sanin gaskiya da banbanceta daga karya da tantance haske daga duhu da alheri daga sharrri da falala daga kaskantuwa, akwai daga wAliyan Allah da shi’ar Imam Husaini da masoyansa da zasu fitinu cikin Imam Husaini (a.s) ya kasance yana musu addu’a a cikin kunutun sallarsa yana rokon ubangijinsa (ka tsare wAliyyanka daga fitinuwa cikina).
Lallai ita Ashura itace masukar jarrabwa da gwaji. Lallai daga mutane akwai wadanda suka rabauta cikinta suka samu riba, akwai kuma wadanda suka fadi suka asarantu, haka lamarin zai ta wakana har zuwa tashin kiyama.
Akwai wanda ke hidima da dukkanin abin da yake da shi daga karfinsa kuma ya sadaukar da rai mai tsada cikin tsayar da raya bukukuwan juya yin Husainiyya zuwa ga bayyyana ibadojin Allah, ya kasance daga rundunar Imam Husaini (a.s) cikin sahun habibu da su zuhairu da wahab da hurru ibn yazid rayahi, akwai kuma mai tada fitina da kawo shubuhohi da sanya kayoyi da shinge kan hanya da dawwamarta sai ya dinga kawo shakka da yin isgili ga masu raya bukukuwan to wannan mutui ya kasance cikin sahun su shimru ib zul jaushi da harmala da umar ibn sa’ad da yazidu ibn mu’awiya sai ya fadana cikin fitina, sannan addu’ar Imam Husaini (a.s) ga wAliyan Allah wadda yake yinta cikin kunut ba zata tattaro da shi ba.
 Shin kasan kuwa cewa mutane dubu suka kasance cikin maukaibin Imam Husaini (a.s) a kan hanyarsa zuwa karbala kafin wayewar garin goma ga muharram sun kuma ka suna sallah a bayansa suna sunbatar hannayensa masu albarka suna tamabayarsa ilimin addininsa da mas’aloli sai dai cewa ranar Ashura basu ci jarrabawa ba sun fadi yasassu babu wadanda suka rge daga cikinsu face mutane saba’in da `yan kai, domin su sun nemi duniyar Imam Husaini (a.s) ya yinda suka tsinkaya suka gano cewa Imam shahada zaiyi wayewar garin goma ga muharram sai suka kunyata shi suka warware mubaya’a suka koma zuwa ga duniya yazidu ibn mu’awiya tsinannnen Allah. lallai sun kasance bayin duniya addini wani abune da yake damfare a fatar bakinsu. Suna karkata duk inda rayuwarsu ta karkata, idan an jarrabce su da bala’i sai ma’abota addini su karanta bawanda suke ragewa face kadan daga bayin Allah masu godiya. adadinsu yakai mutum dubu talatin koma fiye da haka basu fusknata basu ganewa kamar dabbobi koma ace sun fisu bata wadancananka suna daga gafalallu. sai ku sanya idaon basira ku lura yak u ma’abota hankAli. bafa mai rabauta da samun nasara daga wannan jarrabawa face `yan tsiraru, sai agargadu agargadu hakika Allah ya tsaresu daga fitinuwa cikin shugaban shahidai (a.s)
   


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: