bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:35:25
Wajibinmu mu yi addu’a da kuma aiki nagari da kiyaye kawukanmu da tseratar da iyalanmu da kiyaye `yan’uwanmu cikin Imani daga faduwa cikin wannan jarrabawa
Lambar Labari: 196
 
Wajibinmu mu yi addu’a da kuma aiki nagari da kiyaye kawukanmu da tseratar da iyalanmu da kiyaye `yan’uwanmu cikin Imani daga faduwa cikin wannan jarrabawa, ya kamata muyi watsi da tada fitina da kawo matsaloli da shubuhohi, sannan cikin duk wani abu karami ko babba mu komawa masanansa mu je wurin maraji’ai masu girma domin samun fatawa daga garesu cikin kowanne batu gameda raya batun Ashura, kada wani ya yi fatawa ba tare da ilimi ba, lallai yadda al’amarin yake shi ne duk wanda ya yi fatawa babu ilimi to ya yi sauri ya nema wa kansa matsuguni cikin wuta, ya zama wajibi muyi taka tsantsan daga bayyanar da ra’ayi cikin hukunce-hukuncen Allah mu lazimci komawa masana fikihu wanda suke da hakkin yin fatawa da bayanin hukunce-hukuncen Allah, wannan shi ne abin da  lafiayyen hankAli ke karba da dayantattaar hAlinta da da dabi’a wayayya da kur’ani mai girma da irfani madaidaici, menene bayan kin gaskiya da wuce bata.
Kan kowanne dayanmu wajibi ya yi addu’a yana mai tsarkake niyya da Allah ya datar da shi da tsayar da raya juaya yin shuagaban shahidai Imam Husaini (a.s) Allah kuma ya kimsa msa karfi da hakuri da Karin juriya da dauriya kan wannan hanyar, sai muyi koyi dan majibancinmu Imam Sadik (a.s) cikin haka a cikin addu’arsa da yake maziyartan kabarin Imam Husaini (a.s) (Allah ka jikan wadancan fusake da suka sauayasaboda rana* ka jikan wadancan iface iface da ta kasance saboda mu)
Lale lale ga ma’abota ni’ima data ni’imcesu, farin ciki ga wadannan wadanda basu banbance darensu daga ranarsu cikin hidimar Imam Husaini (a.s) da tsayar da raya juya yinsa da shirya ta’aziyya da mimbarori jaje da ciyarwa da shiryarwa da sakafantarwa, Allah ya gwabunta ladanmu da naku kan musibarmu musibar da ta su majibancinmu shugaban shahidai Imam Husaini (a.s) Allah ya kyautata mana ta’aziyya ya sanya mu da su daga cikin masu neman fansarsa tare da magajinsa abin taimakawa Imam mahadi ma’abocin dawowa daga iyalan muhammadu (s.a.w)
`yan uwana cikin Imani da akidar gaskiya abin da yake wajibinmu shi ne mu yi shimfida ga daular Imamin zamanimu (a.s) wanda zai cika ksa da adalci da bayan ta cika da zalunci da danniya, sai mu tashi da aikata wajibinmu kan yadda aka bukaci muyi, mu karu da ilimi da ma’arifa saboda Allah matsarkaki  da kuma muslunci wanda bai da karkata, musammam ma cikin kwanakin watannin muharram da safar, ya zam wajibi kanmu mu karu cikin ilimi da ma’arifa da kara karanta lamarin Imam Husaini (a.s) da juyin juya hAlinsa madawwami, Imani ya kasance kammalalle da aiki nagari tsarkakkakke cikakke kan hasken ilimi da ma’arifa da yakini.
Shin kuwa kasan cewa shin yakini cikin sakafar muslunci cikin makarantar Ahlul-baiti (a.s) ya kasu zuwa martabobi uku, ana kidayasu da jigon martabobi cikin yakini sune: ilimul yakin da ainul yakini da kuma hakkul yakin.
Sannan shi yakini na da ma’anar ilimin da babu shakka ko kokwamto cikinsa, bai girgiza lallai shi kamar misalin kafaffen dutse ne iska da guguwar shubuhohi da ishkaloli da fitintunu da jita-jita da sauye-sauyen yanayi da surutai basu iya motsa shi.
Bara in baka misali cikin sanin wadannan martabobi guda uku:
Duk wanda ya hangi hayaki daga bayan bango to zai ce bayan wannan bango akwai wuta da take ruruta, to ina da ilimin yakini kan haka, idan ya kusanto kusa da wutar har ya dandani zafinta sai ya yanke da samuwar wuta sai dai cewa kuma yanzu ya samu ilimul yakin da samuwar wutar, idan kuma ya ga wutar ido biyu ya jita a jikinsa daga kusa-kusa, idan ma ya shiaga zata konashi to lallai zai kara cewa akwai wuta sai kuma yanzu ya tsallaka zuwa martabar hakkul yakini da dakuma tabbatuwarsa.
Kowanne daga cikin wadanann martabobi guda uku yana fadin wuta wuta, sai dai cewa tsakanin kowacce dayansu akwai nisa sama da kasa a wannan lokaci wanda ya yi Imani da Imam Husaini (a.s) da kuma Imani da bukukuwansa da Ashura lallai wani lokaci zaka sameshi yana ihu yana fadin (na amsa kiranka ya Husaini) sai dai cewa shi yana cikin martabar ilimin yakini kamar misalin wanda ya ga hayaki daga bayan bango, dayan kuma zai ce ( na amsa kiranka ya Husaini) sai dai cewa shi ta hanyar kyawunsa da girmansa (a.s) da kuma jin samuwarsa to shi wannan yana cikin martabar ainul yakin, amma na uku shima zai daga ya ce ( na amsa kiranka ya Husaini) na amsa kiranka ya mai kira abi addinin Allah sai dai cewa hakan yana raye cikin zuciyarsa da zurfafar samuwarsa kai kace yana konuwa da balbalar wutar kaunar Imam Husaini(a.s) da soyayyarsa yana mai cudanya da hakkul yakin.
Na nakashceka wannan kissa a matsayin misali samfuri kan abin da nake fadi:
bukukuwan Imam Husaini (a.s) da alamominsa tsarkaka kamar misalin (sassarfa dawarij) wanda shi ta’aziyya ta al’umma da miliyoyi ke tarayya ciki da ake taso da dawairiji da take karkashin yankin hindiya fuskanin haram mai daraja cikin jam’in da yake cike da jama’a mai ban mamaki suna sassarfa suna dukan kawukansu suan kiran ya Husaini.
An san nau’in wannan jaje da ta’aziyya da ya dayanta da kwarjini wat (Sassarfa duwairij) sakamakon yawan adadin masu tarraya cikinsa basa ma iya tafiya a sannu sannu saboda tsananin turmutsitsi suna sassarfa suna raira waken jaje da ta’aziyya suna bugun kawukansu da hannayesu suna kiran wayyo Husaini har abada ba zamu mu manta da kai ba.
Abin ban mamaki cikin wannan makoki zaka ga kowa da kowa ya yi tarraya ciki daga kowanne bangare tun daga shugabanni da wadanda ake shugabanta da `dan hauza da `dan jami’a da malami da `yan kasuwa mawadaci da talaka kai hatta manyan malamai daga marji’an taklidi cikin yanayin bai daya da tasirantuwa da tasowa suna gudu da sassarfa da kuka da kirarin ya Husaini.
cikin shekarun da suka gabata ya yinda jama’a masu tarin yawa da suka taso cikin ta’aziyya kwatsam sai aka ga maraji’an taklidi cikin wannan gayya ayatollah mahadi baharul ulum ya yarda rawaninsa da alkyabbarsa a gefe ya na tattaki babu takalmi ya dukan kansa yana kiran ya Husaini yana Husaini.
Bayan an gama taron ta’aziyyar sai aka tambayeshi menene ya sanya shi yin haka?
Sai ya ce: ta kaka ba zan aikata haka ba cikin maukibin Husaini bayan na shugabana majibancin lamarina ma’abocin zamani Imamul hujja muntazar (a.s) yana sassarfa babu takalmi a kafarsa cikin ta’aziyya?
 Kamar yadda Imam (a.s) yake cewa: (zan kiraye ka safe da yamma zanyi maka kukan jini mayin hawaye).
Cikin kowanne zamani da wuri cikin kowacce al’umma ya zama dole a samu wayar da kai kan lamarin Husaini da sakafarsa ta zama ita ke jagoranci cikin daidaiku da jama’a sannan kowanne mutum guda daga cikinmu ya zama yana taka wata rawa daga daurorin rayuwarsa cikin kowanne matsuguni ya kasance mai amsa kiran Husaini (a.s) da isar da sakonsa (shin akwai mai taimako wanda zai taimaka mini)  sai ka zamanto daga mataimakn Husaini kamar yadda sahabbansa suka kasance, kamar yadda muke fatan kasancewa madadi cikin mataimaka Imamul ka’im (a.s)
Lallai Imam Sadik (a.s) yana tsayawa kan sahun garin daffi domin ya yi sallam ga shahidan karbala mataimaka Husaini sai ya ce: aminci ya tabbata gareku yaku mataimaka Allah da manzon Allah ya mataimaka sarkin muminai ya mataimaka Fatima ya mataimaka baban muhammadu hassan. ya mataimaka baban Abdullah. babana da babata fansarku kun tsarkaka kuma kasar da aka binneku ta tsarkaka kun rabauta wallahi rabauta mai girma inama na kasance tare da ku in rabauta rabauta mai girma.
Duba fa yanzu tsakaninka da Allah su waye wadannan mutane da Imam Sadik (a.s) ma’asumi mai Magana da har yake fansarsu da babansa da babarsa sannan yake burin ace ya kasance tare da su?
Ya ya suka samu wannan matsayi mai girma da mukami madaukaki? me nene falalarsu menene darajarsu haka ta kaka muma zamu iya kasancewa tare da su daga garesu cikin rayuwarmu da rayuwarsu da mutuwarsu da mutuwarmu?
Allah ya jarraba mataimaka Husaini (a.s) ya gwada su a wurare da dama, lallai da farko-farko mutane masu tarin yawa sun bi Imam sai dai cewa yawancinsu taron bola da shara ne Imam ya gaya musu cewa shifa zaije ya mutu ne ya yi shahada dajin haka sai suka watse wasu sukai gabas wasu kuma sukai yamma haka ma ya jjaraba su a daren goma ga muharram ya musu huduba sai suka amfani da wannan dare matsayin rakumi da suka rika don gudu suka gudu suka barshi kamar yadda sayyada sukaina (a.s) ta bamu labari babu wadanda suka rage wurinsa face yan tsiraru amma a rundunar yazidu sai ga mutum dubu talatin, mazajen na hakika da gaskiya ga akidar Husaini(a.s) bayan koma ya fito sarari kowa ya fuskanci inda Husaini (a.s) ya dosa babu wadanda suka kasance tare da sai su saba’in da biyu (72) wanda tarihi ya yi musu shaida ya kirayesu da (mataimaka Husaini)
Da zaka karanta karbala da daren Ashura da abin da sahabbain da mataimaka suka fadi a mukamin sadaukar da rai da fansar da shi da ka ga abin da mamaki, da kuma abin da Imam Husaini (a.s) ke fadi  (ni bantaba ganin wasu sahabbai mafi cika alkawAli da mafi alheri daga sahabbaina ba* haka ma ban taba ganin iyAli mafi biyayya da sadar da zumunci daga iyAlina ba* baki dayanku Allah ya saka muku da alheri)
 Wannan na nuni da cewa sahhaban Imam Husaini (a.s) sun kasance mafi daukakar martaba da girma da yanayin da wasu basu gabace su ba baku ma wanda zai iya riskarsu, kamar yadda sarkin muminai Ali (a.s) ya bada labari da hakan ya yinda ya isa karbala cikin tafiyarsa zuwa siffaini ya ce: nanne madurkusar matafiya nanne mafadar masoya shahidai, wanda ya gabace su bai iya tsere musu, wanda zai zo daga bai iya riskarsu.
Lallai sun sami darajar shahada cikin tafarkin Allah, sun kuma nuna mafi kayatarwar jarumtaka da sadukarwa a daidai lokacinda wasu suka ja da baya suka sallama karfin dagawa da sakamakon tsananin kiayyarsu ga mutuwa cikin tafarkin Allah saboda son da sukewa duniyarsu da matansu da `ya`yansu da gidajensu.
Hakika daren Ashura ya yayewa sahabban Imam shamaki har sai da ta kai sun ga masukansu a aljanna, dayansu ya kasance yana tunkarar kisa don ya samu damar saduwa da matarsa a aljanna ya rungumeta, hakika Allah ya dage musu labule ya shimfida musu hanya matattakala ya gwabunta musu lada.  
Lallai sahabban Imam Husaini (a.s) mazaje ne da suka gasgata alkawAlin da sukaiwa Allah suka taimaka masa tare da karancinsu suka ba da jininsu sadaka suka tunkari mutuwa da dukkanin maraba da fadadar kirji, suka tunkari kibbai da jikkunansu suka tarbi takubba da fusakensu suka fuskanci mashi da makogaransu suka sadukar da rayukansu domin baiwa Imam Husaini (a.s) kariya suna hAlin fadin bamu da uzuri wurin manzon Allah (s.a.w) idan muka bari aka kasha jikansa Husaini (a.s) alhAlin mu kuma muna raye fatar idaniyarmu na kiftawa, wallahi ba zamu taba barin haka ta faru matukar muna raye har sai an kasha mu muna masu bashi kariya.
Sai daya daga cikin makiyansu wato amru ibn hajjaju ya siffanta su yana mai cewa: (shin kun san da suwa kuke yaki kuwa? Kadai dai kuna yaki da jarumai mahayan dokkai na kasa ma’abota basira masu neman mutuwa`yan gani kasha ni)
 Ranar ashura an cewa wani mutum tare da umar ibn sa’ad: kaiconku shin yanzu kun kashe zuariyar manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: lallai da kaga abin da muka gani da kaima kayi abin da muka yi, wasu ayari sun taso kanmu hannayesu na rike da kawukan takubbansu kai kace zakuna dake kishirwar shan jini, hagu da dama sai kashe mahaya suke sunan tunkara mutuwa basu damu da karbar alakawAlin aminci ba basu kwadayi kudi ko dukiya, babu abin da ya isa ya shiga tsakaninsu daga gangara zuwa tafkin mutuwa da mamaye mulki, kai da mun kame daga yakarsu kankanin lokaci da sai sun cin tsakiyar rundunarmu baki dayanta, to mai kake so muyi da su `dan shegiya)
Hakika haka sahabban Imam mahadi (a.s) suke wanda shi ne zai dau fansar shugaban shahidai (a.s) ya kuma ya cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya
An karbo daga Imam Sadik (a.s) ya yinda Imam Husaini (a.s) ya yi shahada mala’iku sun fashe da kuka suna fadin (yanzu haka za aiwa Husaini zababbenka `dan annabinka? Sai Allah ya tsayar musu da inuwar Imam mahadi (a.s) ya ce musu: da wannan zan daukarwa wannan fansa.
    Mataimakansa suna siffofi da kebantattun abubuwa irin wanda sahabban Imam Husaini (a.s) ke da shi (suna kwana ibada ba tare da bacci su kuma wayi gari kan dokunan yakinsu* sufayen dare don cetae ranarsu* kai kace zukatansu taman karfe ne shakka ba ta cudanyarsu* cikin zartin Allah sunfi garwashi zafi* sannan takensu shi ne ina masu daukar fansar jinin Husaini)
Sabunta Ashura da tsayar da raya bukukuwan ta’aziyyar Husaini a watannin muharram da safar ba wani abu bane face tanadi ga bayyanar Imam mahadi (a.s) lallai shugaban shahidai shi igiyar asadarwa ne tsakanin cika makin annabawa muhammadu da cika makin wasiyyai wanda akai masa suna da sunan annabi Musdafa (a.s)   
Sannan wane sirrine na Husaini da yake tattaro al’ummu a tsawon tarihi da zamani tare da banbancin addininsu da mazhabobinsu da makarantusu na tunani da akidu da yakai ga hatta mawakin zamani ke kada jitarsa don wake waki’ar Husaini wadda ita alamace daga soyayya da ke tare da dan adam.
Hakika Husaini (a.s) shi ne tushe jigo lallai mutumtakarsa na nuna cewa shi cikakken mutum me goyon bayan adalci mai kin zalunci madaukaki kan barin karkata daga tarkacen duniya. Dukkanin zukata masu kin kaskanta da zaluci suna son irin samfurin Imam Husaini (a.s) suna karkata da shiriyuwa da shiriyarsa suna koyi da halayensa madaukaka
Umar Alhassan SAlihu
Faroukumar66@gmail.com
+989335382587




comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: