bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:53:52
Haqiqa musulmai sun yi savani a cikin wannan mas’alar, ita makarantar mazhabobi huxu ta sanya halifanci da imamanci da shugabanci daga cikin sha’anin shari’a da ayyukan mukallafai, a yayin da makarantar Ahlulbaiti (a.s)
Lambar Labari: 197
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
 ‘Yar Matsaya Tare Da Masu Musantawa
Ya bayyana a sarari daga abin da ya gabata cewa mas’alar mahdawiyyanci ma’ala ce ta aqida tun kafin ta kasance mas’ala ta tarihi kuma dalilin da ke tabbatar da ita dalili ne na Aqida kafin ya kasance dalili na tarihi, kuma ya bayyana a sarari cewa akwai tarin dalilan da suke tabbatar da ita kuma ya bayyana cewa tabbas boyayyen lamari na gaibu kamar irin na Imam Mahdi (a.s) a al’adance ya gaji fuskantar masu musanta shi, domin abin da ke boyuwa daga idanuwan mutane na da manufa daga manufofi, wanda abin da ake nufi da hakan kar wani daga cikin mutane ya gan shi ta yanda idan an tambayi mutane a kan sa zasu ce: ba mu ganshi ba, ko da kuwa suna daga cikin mafi kusancin mutane zuwa gare shi, kuma mun faxi cewa musantawar irin waxannan mutanen ga abin da yake voyayye ba zai zama ingantaccen dalili kan rashin samuwar abin ba, wannan ce mararraba ta asasi wacce masu musanta haihuwa da samuwar Imam Mahadi (a.s) suka faxa ciki, domin su sun tafi suna ta binciken iran wannan nau’in madogarar a cikin tarihi, a yayain da suka kasa samun wani abu daga irinta (madogarar) sai suka xauke shi a matsayin dalili kan rashin haihuwa da samuwar Imam Mahdi (a.s), tamkar dai savanin Shi’a kan lokacin da aka haifi Imam Mahdi (a.s) da sunansa da shaidar Ja'afar maqaryaci baffan Imam Mahdi (a.s) ta cewa xan’uwansa ya rasu be bar magaji ba.
Kuma asasin tattaunawar mu tare da waxannan shi ne cewa haqiqa tafarkin nan na tarihi za a iya yin hukunci da shi kan mas’alolin da ake iya riska (da hawas guda biyar) waxanda tun daga farkon su har karshe sun faru ne a idon muruwaita da marubuta tarihi misalin waqi’ar siffin da waqi’ar karbala.....da sauransa, kuma ba daidai ba ne a hukunta mas’alolin gaibu na akida da wannan ma’aunin (na ruwayar tarihi) kan asalin samuwarsu ba,  kuma wannan lamarin na da hasken da ake iya riska a wajen zavavvavun mutane ta yadda, da za a tambayi mutane game gari kan wannan lamarin da sun musanta shi. To ta yaya kuma zamu xauki musanatawar game gari daga mutane a matsayin dalili kan rashin samuwar wani lamarin da masu shi tun tuni suka yi imani da cewa ba abu ne da za a iya gani ba, in ba ga xaixaikun zababbaun mutane ba?
Haqiqa abin da ya kamata ga wanda yake so ya yi jayyaya kan mas’alar Imam Mahdi (a.s) ya fara ne tun daga tushen mas’alar ta aqida ba ya xauke ta daga wani yankin ta da ya danganci tarihi ba, domin lamari ne da ya zama, da gangan ake so ya zama boyayye a asirce daga idanuwan mutane mafiya kusanci, ta yadda da ba za a rasa samun savani a kan wasu vangarorin lamarin ba, na daga irin savani da aka samu kan lokacin haihuwar Imam da savani kan sunan mahiafiyarsa, kuma sheda irin shedar Ja’afar maqaryaci ba zata cutar ba, domin a xabi’anci amsar da za a bayar a irin wannan yanayin ita ce: haqiqa savanin kan shekarar haihuwa da sunan mahaifiya, wannan abu ne na xabi’a a sarari sakamomakon dagewar Imam Hasan Al-askari kan voye yadda lamarin yake  dalla-dalla cikakkiyar vuyewa daga idanun mafiya kusanci makusanta, Don toshe kafar isar labarin zuwa mahukunta Abbasawa, kamar yadda shedar da Ja'afar maqaryaci ya bayar kan cewa xan’uwansa ya rasu be bar baya ba (wato be bar xa ko ‘ya ba), ta faru ne sakamakun haka, ta yadda Imam Hasan Al’askari ya so ya voye haihuwar xan’sa ga xan’uwansa, sai Al’amarin ya zama a wajensa kai ka ce Imam ba shi da magaji  a baynasa kuma wannan matakin da Imam ya xauka a kan xan’uwansa ya yi daidai da hankali  ko da kuwa xan’uwan na sa be zama maqaryaci da aka yi masa sheda da fasiqanci ba, ta yaya kuwa!, ballantana ma an shedi Ja'afar maqaryaci da yin haka.  

Kevance-kevancen na biyu Imamamanci a qananan shekaru

Daga cikin abin da ke xamfare da imamancin Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) qudurcewar su da imamanci Imam mahda (a.s) tun yana da qarancin shekaru (yana yaro), kuma waxannan kevance-kevance wani lokaci mun kalle su da mahangar musulunci da nufin kafa hujja da ije abin da zai yuyi a ije shi na daga ishkali a addinance, wani lokaci kuma mukan kalla su da mahamgar haqiqa da bayanin cewa lalle wannan imamancin imamanci ne na gaskiya da ya tattaro dukkanin abubuwan da suka tabbatar masa da nagarta gamsashshiya kuma ba imamanci ba ne na rayawa ko na jeka-na-yi-ka ba.  
Kuma Idan muka kalle shi da mahanga ta musulunci zamu ga ya zama larura mu tantance mas’alar imamanci tun a farko da cewa shin ita mas’ala ce ta aqida? ko kuma mas’alar shari’a ce? Idan ta kasance mas’alar aqida kamar yadda Shi’a suka qudurce zamu ga qur’ani na bayyana tabbatuwar Annabtar qaramin yaro a sari -wacce ita mas’ala ce ta aqida- Allah maxaukakin sarki ya ce: {ya Yahaya ka riqi littafi da qarfi kuma mun ba shi hukunci yana xan yaro}   
Idan kuma mas’alar ta kasnce ta shar’a to lalle yana daga cikin fayyatattun lamuran musulunci cewa an kange yaro, kuma duk wanda aka kange shi to ya rasa walicci a kan kansa, kenan ta yaya zai iya zama waliyyin waninsa don haka waliccin yaro ba zai tabbata ba kenan.
Haqiqa musulmai sun yi savani a cikin wannan mas’alar, ita makarantar mazhabobi huxu ta sanya halifanci da imamanci da shugabanci daga cikin sha’anin shari’a da ayyukan mukallafai, a yayin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da cewa wannan mas’ala ce ta aqida kuma tana daga cikin tushen addinin da take daga cikin sha’anin ubangijin talikai, kuma ba ta daga cikin abin da ya kevanci mukallafai kuma ba ta gada cikin abin da ya kevanci ayyukan bayi, don haka makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imanin da imamancin yaro na wasu adadi daga Imamai, wanda daga cikinsu akwai Imam Mahdi (a.s), saboda haka aqidar ta dace da abin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da shi a wannan mahallin ba wani ishkali da zai zo mata ta vangaren aqida mutuqar qarara qur’ani ya tabbatar da Annabci Annabi Yahaya (a.s) yana yaro, haka ma basu ishkali ta vangaren shari’a mutuqar dai  a mahangar Ahlulbaiti (a.s) wannan mas’alar ta fita daga iyakar shari’a ta faxa shingen aqida, kuma hukuncin shari’a na babin kange yaro tana xanbbaquwa sannan tana gudana ne kan mukallafai, kuma ba ta xabbaquwa kan Allah Ta'ala, domin ita shari’a dakon Allah Ta'ala ce da ya xora wa mukallafai.
Da haka ne zai bayyana a sarari cewa, da muka kafa hujja da Annabcin Annabi Yahaya (a.s) abin da muke nufi shi ne, mu yi bayanin cewa, Imamanci kamar Annabta yake shi ma mas’ala ce ta Aqida kuma lalle ita mas’alar aqida ba ta xoruwa kan qiyasin (wato ma’aunin) mutane, ballantana ma ba ta xoruwa hatta a kan qiyasin shari’ar da ta zo don ta tsara rayuwar mukallafai, don haka be inganta a xabbaqa ta a kan ubangijin talikai ba, domin Annabtar Annabi Yahaya (a.s) tana fa’dantar da mu cewa lalle mas’alar Aqida ta tsayu ne kan dalili da hujja, idan hujja ta aqida ta tsayu kan imamancin yaro qarami, babu makawa sai mun yi imani da ita kamar yanda muka yi imani da annabcin yaro qarami a yayin da dalili na aqida ya tsayu a kanta, a wannan lokaci ba shi da ma’ana a ce kafa hujja da annabcin Annabi Yahaya (a.s) ba shi da mahalli, domin an anbace shi a sarari a cikin qur’ani savanin mas’alar Imam Mahdi (a.s).
Daga nan ne ibni Hajar Asqalani Al-haisami shi da makamancisa suka qalubalanci imamancin Imam Mahdi (a.s) da cewa ba ta da asasi kwata-kwata. A yayin da ya rubuta hakan da salon be dace ba, yana mai cewa: "sannan abin da ya tabbata a shari’a mai tsarki lalle waliccin yaro baya inganta, ta yaya ya yiyu ga waxannan wawayen su yi da’awar imamancin xan shekara biyar ......”   
Haqiqa ya bayyana cewa wannan ba ya daga cikin abin da shari’a ta tabbatar kaxai dai yana daga cikin abin da fiqihun su ya tabbatar wanda be inganta su lazimta mana shi ba. (Wato su hukunta mu da shi ba).
Kuma idan muka kalli lamarin ta vangaren Tarihi za  mu samu cewa lalle Mahdi (a.s) ya gaji babansa a shugabancin musulmai yana xan shekara biyar, kuma wannan yana nufin lalle ya kasance Imami da dukkanin abin da imamanci ya tattaro na tunani da ruhi tun da wurwuri a cikin rayuwarsa maxaukakiya.
Sayyid shahid Assadr yana faxi a kan wannan lamarin imamanci a qananan shekaru qanana a sarari lamarin da da dama daga cikin mahaifan Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka rigaye shi a kai, ka ga Imam Muhammad  xan Ali Al-jawad, ya hau imamanci yana xan shekara takwas a rayuwarsa  , kuma Imam Ali xan Muhammad  Al-hadi (a.s) ya karbi imamanci yana xan shekara tara   a rayuwarsa, kuma Imam abu Muhammad Hasan Al-askari (a.s)   mahaifinimam Mahdi (a.s), ya karvi jagoranci yan axan shekara ashirin da biyu, idan an lura za a ga cewa riqe muqamin imamanci da qarancin shekaru ya kai qoqoluwarsa da matuqa a cikin Imam Mahdi (a.s) da Imam Jawad (a.s), kuma mun ambace ta da mabayyanin abu wato abu na sarari wanda da aka saba gani saboda idan aka danganta ta da wani adadi na mahaifan Imam Mahdi (a.s) tana tabbatar mana da wani abu na sarari na ilimi da musulmai suka rayu da shi, kuma suka kiyaye shi a cikin gogayyar rayuwa tare da Imami da wannan yanayin ko wancen. Kuma ba zai yiyu a nemi mu tabbatar da wani abu na sarari ba wanda yake mafi bayyana kuma mafi qarfi fiye da gogayyar al’umma ba,   kuma da sannu zamu bayyana haka bisa jeri mai zuwa.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: