bayyinaat

Published time: 09 ,August ,2018      23:57:24
Haqiqa wannan tsarin wakilcin da mutane ke bi tun a farkon musulunici aka gina shi
Lambar Labari: 198

A-    Imamanci Imami daga Ahlulbaiti (a.s) be zamo wani bangare daga vangarorin hukuma ba, kuma be zama irin iko ko mulkin da ke ciratuwa daga  mahaifi zuwa xa ba, irin wanda tsarin mulki ke ba shi kariya, kamar imamancin halifofin faximawa da halifancin abbasawa ba, kaxai (irin wannan ikon) ya kasance yana tabbata ta hanyar samun biyayya daga mutane ta hanyar wakilansa da mutane masu yawa ke bi tahanyar yin tasiri a zukatan mutane da da gamsar da tunaninsu a kan wannan tsarin da nuna sun cancanci shugabancin musulunci da jagorancin sa ta vangaren ruhi da tunani.
B-    Haqiqa wannan tsarin wakilcin da mutane ke bi tun a farkon musulunici aka gina shi, sannan ya girmama ya yaxu a lokacin Imam Baqir da Sadiq (a.s), kuma makarantar da waxannan Imamai biyu suka kafa ta wayi gari a cikin wannan tsarin a tana xauke da wani tunanu faffaxa wanda ya yaxu a cikin a duniyar musulmai, kuma wannan tsari ya tattaro xarurawan faqihai da malaman Kalam da na tafsiri da ma malamai a cikin fagagen lilmi Musulnci da na Xan’adam din da aka sani a waccen zamanin, har sai da Hasan xan Aliyyul Washa ya ce: haqiqa na shiga masallacin kufa sai na ga shehunnai   xari tara dukkaninsu suna cewa Ja'afar xan Muhammad  (a.s) ya zantar da mu.
C-    Haqiqa sharaxan da wannan makarantar ta xoru a kan su ita da abin da yake kamantata na daga wakilcin mutane a cikin marayar al’ummar musulmi, sun yi imani da su kuma suna qayyadantuwa da abin da suka qunsa wajen ayyana Imamai da sanin cancantarsa a matsayin Imami, an gindaya sharaxai masu tsanani, domin sun yi imani da cewa Imami ba zai tava zama Imami ba sai ya zama ya fi kowa ilimi a zamaninsa.   
D-    Haqiqa wannan makarantar ita da jagorancinta na jama’a ta kasance tana gabatar da babbar fansar da kai (mabiyanta sun sadaukar da kansu sun bada jini da tsoka) a hanyar ta ta ganin ta tabbata kan aqidarta ta imamanci; saboda ta kasance babar barazana a mahangar hukumar da take ci, ko da kuwa ta vangaren tunani ne kawai, al’amarin da ya sa hukumar wancen lokacin ta ci gaba da kai musu hari na kar a bar iri, sai aka kashe wanda aka kashe aka xaure wanda aka xaure kuma xaruruwa suka mutu a cikin duhun kurkuku, kuma wannan na nufin imaninsu da imamancin Ahlulbaiti (a.s) yana jawo musu musiba,   kuma ba shi da wani abu da yake da shi wanda ake samun qarawa ( ta wani abin duniya ) da shi face abin da mai aqidantuwa da shi yake ji ko yake tsammani na kusanci da Allah Ta'ala da kuma samun matsayi a wajensa.
E-    Haqiqa Imamin  da wannan (tsarin na wakilcin) gugun  al’umma ya tabbatar da imamancinsu, ba su kasance sun kevance kansu daga jama’ar ba, kuma ba su kai kansu can tsororruwar matsayi a cikin manyan gidaje kamar dai yadda sarakuna suke yi wa jama’arsu ba, kuma (imamai) ba su tava yarda an sa shamaki tsakanin su da jama’a (mabiyansu) ba, sai dai in hukumar da ke mulki ce ta shiga tsakanin su (da mabiya) ta hanyar jefa su (imaman) kurkuku ko nisantasu, kuma wannan abu ne da muka sani ta hanya adadi masu yawa na marawaita da masana hadisi game da ko wane xaya daga cikin Imamai goma sha xaya, da ma ta hanyar abin da aka cirato na daga wasiqun da suka kasance tsakanin Imam da waxanda suka yi zamani da shi, da kuma tafiye-tafiyen da Imam yake yi ta wani vangaren, da kuma abin da ya kasance yana yaxawa ta hanyar wakilansa a mabanbanta sasannin Duniyar musulunci da wani bangaren daban, da ma kuma abin da Shi’a suka yi sabo da shi a kansa na bibiyar yanayin da imamansu suke ciki da kai musu ziyara a madina mai haske yayin da suke dafifi zuwa gidaje masu tsarki don gudanar da faralin hajji.   Dukkanin waxannan a sarari sosai suna tabbatar da kaikawo mai ci gaba tsakanin Imam (s.a) da wakilansa da suka yaxu cikin faxin sassan duniyar musulunci bisa mabanbantan matsayinsu na daga malamai da wasunsu.
F-    Haqiqa masarautar da ke ci wacce ta yi zamani da Imamai ta kasance ta na kallon su kuma tana kallon wannan shuganacin na su na ruhi a matsayin babban haxari kan samuwarsu da ikonsu, bisa wannan ne suka zage dantsensu wajen ganin sun yi kaca-kaca da wannan shugabancin kuma suka yi ta aikata munanna abubuwa saboda haka wani lokaci ma sukan nuna qeqashewar zuciya da xagawa idan haka ya zame musu larura wajen kare kujerarsu ta mulki, kuma xauri da kora sun kasance abubuwan yau da gobe da su kansu Imamai  suka yi ta fama da su, duk da abin da hakan ke sabbabawa na jin damuwa da kyamar da masulmai da mutanen mabiya - Ahlulbaiti (a.s) - ke bayyanawa a bisa mabanbantan matsayinsu.
Idan muka kalli waxanna nuquxuxin guda shida da idon basira waxannan suke tabbatatun abubuwa ne na tarihi, da ba shakka a cikinsu zai iya yiyuwa mu fita da sakamako kamar haka: Tabbas samuwar imamanci na wuri lamari ne a fili wanda yake da tabbacin samuwa, kuma be kasance wahami da wahamomi ba, domin imamin da ya bayyana a fage aiki yana qaramin yaro ya kuma shelamta kansa a matsayin Imam na ruhi da tunani ga musulmai ba ki xaya, kuma dukkanin waxannan tarin jama’ar suka zama suna yi masa biyayya a matsayin Imami, babu makawa sai ya kasance yana da wani matsayi bayyananne abin la’alari kuma ya zama yana da matsayi a ilimi da sani mai faxi sasanni kuma ya zama yana da kwarewa a fiqihu da tafsiri da aqida domin idan har be zama haka ba, da ba zai yiyu wannnan gungun jama’ar su yarda da imamancinsa ba, tare da cewa Imamai sun kasance a wajen da zai yiyu ga mabiyansu su su yi ma’amala tare da su kuma a yanayoyi mabanbanta zasu iya yin tasiri a rayuwarsu da ma ma’aunin mutuntakarsu. Shin kana ganin zai yiyu wani xan qaramin yaro ya yi kira zuwa imamancinsa, kuma ya xora kansa a matsayin alamin musulunci - ta hanyar imamamnci - alhali yana kan ido  da majiyar mutanen da suke yi masa biyayya, sai su yi imani da shi sannan su sadaukar da abu mai qima a kansa na daga abincinsu da rayuwarsu ba tare da sun kallafawa kansu gano haqiqanin sha’aninsa ba, kuma ba tare yanayin imamancinsa na yarinta ya girgiza su ba, don su sami masaniya kan haqiqanin matsayinsa ta hanyar gudanar da gwaji da jarraba wannan yaron Imami ba? Kuma ka qaddara cewa mutane ba su motsa wajen sanin yanayinsa ba, shin zai yiyu matsalar ta shuxe tsawon kwanaki da watanni ba tare da haqiqa ta bayyana gare su ba, dun da kai kawo da alaqa ta xabi’a mai ci gaba tsakanin wannan yaron da sausan mutane? Kuma shin hankali zai karvi cewa ga shi yaro ne a tunaninsa da aikinsa da gaske amma kuma hakan be tabbata a kansa ta hanyar doguwar alaqa ta yau da gobe ba?
Idan kuma muka qaddara cewa lalle tsayin al’umma kan imamancin Ahlulbaiti (a.s) bai bada dama su gane haqiqanni lamari ba to don me ya sa masarauta mai ci ta yi shiru ba ta yi qoqarin bayyana haqiqa ba idan har tana da riba kan hakan? Ya tsananin sauqin yin hakan ga masarauta mai ci da ace Imami yaro, yaro ne shi a tunani da wayewa kamar yanda aka san yara, ya isa ya zama mafi cin nasarar hanya idan aka gabatar da wannan yaron ga Shi’arsa da waxanda ma ba Shi’arsa ba kan haqiqar yadda yake, kuma ta tabbada da dalili kan rashin cancantar sa ga imamanci da shugabancin mutane a ruhi da tunani, idan har ya zama yana da wahala a kasa tabbatar da rashin cancantar mutumin da yake xan shekara arba’in ko xan shekara hamsin saboda ya kewaye sani da wani babban gwargwado a wayewar zamaninsa kan yanda ake xarewa kujerar imamacni, ke nan babu wata wahala wajen tabbatar da rashin cancantar yaro na al’ada duk yanda ya kasance mai kaifin basira da hazaqa kan imamanci da ma’anarsa kamar yadda Shi’a imamiyya   suka san shi, kuma da hakan ya kasance mafi sauqin hanya (wajen kawo qarshen Shi’a ) fiye da bin hanya mai murxiya da bin tafarkin yin kof xaya da ta’anatin da masarautar wancen lokacin ta zava kuma ta yi ta bi (don ta kawo qarshen shi’anci).   
Kaxai fassarar da za a bayar kan yin shirun hukumar wancen lokaci ga barin yin wasa da lamarin   ita ce cewa  ta riski cewa imamanci tare da qarancin shekaru lamari ne na gaskiya ba abu ne da aka qirqira ba.
Kuma bisa haqiqa hukuma ta gane haka a aikace bayan da ta yi qoqarin yin wasan kura da wannan lamarin na imamanci sai ya zamana ta gaza yin komai a kai, kuma tarihi sheda ne kan waxannan qoqarce-qoqarcen da kuma gazawarsu   a daidai lokacin da ko sau xaya ba a tava ba mu labarin girgizar matsayan imamancin yaro ba ko kuma aka ce Imami mai qarancin shekaru ya fuskanci wani yanayi na tsanani da ya fi qarfinsa ko ya sa amincin mutane da shi ya yi rauni ba.
Wannan muke nufi a lokacin da muke cewa haqiqa imamancin qaramin yaro lamari ne na haqiqa a rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba kawai rayawa ba ne kamar yadda wannan lamarin yana da tushensa da yanayoyinsa masu kamanceceniya a cikin kundin abin da aka saukar da sama wanda ya shuxe tsahon tarihin manzanci da shugabancin da Allah Ta'ala yake naxawa.
Kuma Yahaya (a.s) ya isa misali kan tabbacin lamarin imamancin yaro daga Ahlulbaiti (a.s) a cikin taskar ubangiji, yayin da Allah Ta'ala yake cewa: {ya Yahaya ka riki littafi da qarfi kuma mun ba shi hukunci yana xan karamin yaro}  
A lokacin da ya tabbata cewa imamancin wanda ke da qarancin shekaru lamari ne na haqiqa kuma ya tabbata a aikace a cikin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba wata ja-in-ja da zata yi saura kan lamarin imam mahdi (a.s), da halifancin sa ga babansa a lokacin yana xan yaro   "  .
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: