bayyinaat

Published time: 10 ,August ,2018      00:11:04
“Sallar dare biyu-biyu ce, idan kaga Asuba za ta riske ka ka yi wutiri da raka’a xaya”, ya halatta ya faxa raka’o’i ya yi sallama xaya, saboda Hadisin da Aisha ta ruwaito cewa
Lambar Labari: 200

Abu Yusuf da Muhammad sun ce: "Kar mutum ya qara sallama xaya a kan raka’a biyu da daddare”( ).
Ya faxa a cikin Muhazzab cewa: "Sunna dai ita ce ya yi sallama a duk raka’a biyu, saboda Hadisin da aka ruwaito daga Ibnu Umar (RA) tabbas Manzon ALlah (s.a.w) ya ce: "Sallar dare biyu-biyu ce, idan kaga Asuba za ta riske ka ka yi wutiri da raka’a xaya”, ya halatta ya faxa raka’o’i ya yi sallama xaya, saboda Hadisin da Aisha ta ruwaito cewa tabbas Manzon ALlah (s.a.w) ya kasance yana yin raka’a 13, raka’a biyar a cikin su ne wutiri, sai ya zauna a ta qarshen ya yi sallama, lallai ma ya yi wutiri raka’a da bakwai da raka’a biyar bai raba tsakaninsu da sallama ba”, idan mutum ya yi taxawwa’i da raka’a xaya ba laifi, saboda an ruwaito Umar (RA) "Ya wuce ta wani masallaci sai ya yi raka’a xaya, nan take wani mutum ya bishi, ya ce masa ya shugaban muminai ai raka’a xaya ka yi, sai ya ce: Ai taxawwa’i ce duk wanda ya so ya qara, wanda ya so ya rage”.( )
Sai Nawawi ya ce:
"A cikin Mazhabobin malamai mun faxi cewa hakan ya halatta a wajen mu mutum ya haxa raka’o’in nafila da yawa ya yi sallama xaya duk da yake abin da ya fi mutum ya sallama a raka biyu-biyu a sallar dare da rana, wannan ne abin da Malik, Ahmad, Dawud da Ibnul Munzir suka faxa, an hakaito daga Hasanul Basari da Sa’id xan Jubair, Abu Hanifa ya ce: A duk raka’a biyu ko huxu ake yin sallama a sallar wuni, duk xaya ne a falala, Kar ya qara a kan haka, sallar dare raka’a biyu, huxu, shida takwas da sallama xaya, ba zai qara kan takwas ba, Ibnu Umar ya kasance yana yin raka’a huxu da rana, wannan ne abin da Ishaq ya zava”.( )
Yaya bayan duk waxannan maganaganun da ra’ayoyi za a yi da’awar cewa ba wani da ya ce makaruhi ne ko haramun ne yin raka’a uku da sallama xaya ba, kamar yadda mu’utazili ya faxa ya tabbatar, ya saki maganar kai tsaya a matsayin haka take?
Sheikh Yusuful Bahrain ya faxa a Hada’iqun Nadira:
Ba kokwanto cewa Salla ce fiyayyen duk wani batu, sai dai duk lokacin da baligi ya qudurce wani al’amari qari a kan abin da hujjojin nan suka nuna, kamar kevantaccen adadi da kevantaccen lokaci da kevanacciyar kaifiyya da irin haka wanda dalilin shari’a bai tabbata a kansa ba, tabbas hakan ya haramta, ibadarsa kuma ta zama bidi’a, bidi’ancin bana vangaren sallar bane, bidi’ancin na vangaren wannan aikin nan da ya qudurce a wannan lokacin da adadi da kaifiyya ba tare da wani dalili ya zo a kansa ba”.( )
2- Yunqurin Alqali Abduljabbar Al-mu’tazali a littafinsa almugni, inda yake magana a kan sallar Tarawihi: "Idan Tarawihi tana jawo yin salla da qarfin hadda Qur’ani, to me zai hana a xauke ta a matsayin Sunna”.( )
Wannan maganar ta sa tana dawowa ne zuwa ga maganar Ibnu Abil Hadid Al-Mu’utazili a natijar da aka samu, a wannan lokacin amsar dai ita ce amsar, tabbas salla ibada ce, ibada tana buqatar nufin ibada, nufin ibada baya cike sai bayan tabbatar da samuwar umarnin Allah, sallar Tarawihi a yanayin da ake yinta da irin yadda kaifiyyarta da ake yi ake, shari’a fa ba ta bada umarnin haka ba, to yinta a matsayin ibadar haramun ne, bidi’a ce, abar qyama a cikin Addini.
3- Yunqurin Ibnu Taimiyya da ya xauki maganar Umar xan Khaxxab kan sallar Tarawihi da yace bidi’a ce, wai bidi’a ce a lugga ba a shari’a ba, tabbas musulmai sun yi sallar Tarawihi a zamanin Manzon Allah, tabbas Annabi (s.a.w) ya fito ya yi sallar a dare xaya ko biyu tare da su, sannan ya bari saboda dalilin da ya faxa, wato, ba abin da yake hanani in zo wajen ku sai don gudun kar a farlanta muku ita, ku yi salla, a gidanje gidajenku”, don haka ma aka gane ganar Ibnu Taimiyya cewa tabbas abin da ya tabbatar da fuitowar yaa nan, tabbas ba don tsorn farlantawa ba da ya taho wajensu. A zamanin Umar kuma sai ya sa musu makaranci xaya (wato Liman) ya kuma haskaka masallacin da fitila sai suka dinga haxuwa a masallacin suna yin salla a qarqashin liman xaya ga hasken fitila – abin da da basa yi, Umar ya kirata da sunan bidi’a don a lugga haka ake cewa duk da yake a shari’a ba bidi’a ba ce”.( )
Wannan sunan da Umar ya sa mata bai dame mu ba, sunan shari’a ne ko na lugga ne, abin day kae da muhimmanci a wajenmu shi ne furucin da ya yi na ravawa shari’a wani abin da musulmai ba su sanshi ba a baya, abin da ya rava shi xin nan kamar yadda Ibnu Taimiyya ya faxa da kansa shi ne haxuwarsu a masallaci a qarqashin liman xayam, ya kuma haskaka musu masallacin, hasken fitilar ba shi ne ya dame mu ba domin bayan cikin ibada, abin da yake da muhimmanci shi ne haxuwarsu a salla a qarqashin inuwar limami xaya, akwai tsammain Ibnu Taimiyya ya ambaci haskaka masallacin da fitila don ya kawai da tunanin mai karatu cewa abin da Halifa ya yi aiki ne wanda bai shiga cikn gundarin ibada ba, tabbas haxuwa a masallaci a qarqashin inuwar liman xaya shima kamar haskaka masallaci ne, kamar yadda ba a lissafa haskaka masallaci a matsayin bidia ba, saboda baya cikin gundarin ibada, haka ma ba a lissafa haxuwa don yin sallar da yinta a cikin jam’i a matsayin bidi’a. Natijar maganarsa dai ita ce tabbas Umar bai qirqiro bidi’a a cikin shari’a ba, kawai ya qago wasu abubuwa ne a wajen Sallah, kamar haskaka masallaci, wannan voye gaskiya ne da yaudara.
Tabbas daga bayanin yunqurin da ya gabata ya bayyana cewa tabbas yin Sala a cikin jam’i al’amari ne  na gundarin ibada, ba zai yi wu bawa ya yi karambani a ciki ba, ba makawa dole ya bi umarnin shari’a a ciki, savanin haskaka masallaci da fitila, wannan baya cikin ma’anar ibada, ba za a ce haskaka masallaci bidi’a banme.
Amma da’awar da ya yi cewa tabbas Manzon Allagh (s.a.w) lallai ya fito yin sallar tarawihi a dare xaya ko a dare biyu, sannan ya yanke tabbas daga abin da ya gabata ya bayyana cewa jam’in tarawihi ba shi da inganci, hakan kuma yana warware maganar Umar: "Madalla da wannan bidi’ar”, tabbas wannan maganar tasa, tana nuna rashin yin sallar Tarawihi a baya, saboda yin aiki bayan yankewarsa ba a ce masa bidi’a.
4- Yunqurin karkasa bidi’a, a kan hukuncehukunce guda biyar.
Wannan ne mafi munin yunquri da nisancewa gaskiya da ruhin shari’ar Musulunci, yunqurin nan yana hasko tsakanin tosorn da masu yunqurin suke da shi a kan mas’alar sallar tarawihi, da maganar da Umar xan Khaxxab ya yi a fili cewa bidi’a ce.
Tabbas sun ce: Lallai bidia’ ta kasu kashi-kashi, bidi’ar haramun, makaruhiya, wacce ta halatta, wajiba da mustahabbiya.( )
Taqatacciyar amsa a fili a kan wannan yunqurin: Tabbas bidi’a ma’anarta xaya ce a fili; shigar da abin da baya cikin addini a cikin addini, tabbas Musulmai sun yi ittifaqin haka ‘yan sunna da ‘yan shi’a. Wannan ma’anar ba ta xaukan karkasawa dai-dai da hukunce-hukunce guda biyar. Ba za ta kasu a kan qa’idar yau da muni ba ne da bidi’a tana da ma’anoni da yawa, da zai yiwu mu suranta hakan a kan ta sai dai ma’anarta xaya ce wato ma’ana mara kyau da aka faxa a cikin Hadisi, ma’anar da Annabi (s.a.w) ya tsoratar ya kuma yi barazanar yin mafi tsananin azaba a kai. Dama dai masu karkasa bidi’a kashi biyar ko kashi biyu suna kafa hujja da aya ko Hadisin Annabi da yake goyon bayan maganarsu.
Ba za su iya haka ba, domin a littafin Allah da Sunnar Annabi ba wannan kashe-kashen, saboda wannan karkasawar korarriya ce a hankalce, kamar yadda ba zai yiwu a kasa zalunci ace akwai mai kyau da mara kyau ba, to ta hakan ma ba zai yiwu a karkasa bidi’a da mai kyau da mara kyau, don bidi’a abin da take nufi shi ne qirqirowa shari’a wani abu da jingina mata abin da baya cikinta a cikinta, wannan ma’anar mummuna ce, mara kyau ba za su rabu ba ala ayyi halin, alhalin wannan karkasawar da aka faxe ta, tana tabbatar da yiwuwar bambancewa tsakanin bidi’a da abu mara kyau da yiwuwar samuwar bidi’a mai kyau. Wannan ya faru ne sanadiyyar mahangar karkasa wannan da take aiki da ma’anar lugga, wato; abin da aka qirqiro ba tare da an kwafa ba, tabbas wannan qirqirowar zai yiwu ta zama mai kyau ko ta zama mara kyau, wannan ba ja-in-ja a kai, mu ba muna magana a kan ma’anar lugga ba ne, muna magana ne a kan ma’anar shari’a, lallai suna faxawa cikin manyan mugalaxoxi a lokacin da suke magana a kan bidi’a da ma’anar shari’a, sannan suke da’awar cewa tana iya karkasuwa, nan take za ka ga sun karkasa ta amman fa a ma’anar lugga.  

TATACCIYAR MAGANA:
Tabbas Sallar tarawihi ba ta da asali a cikin littafin Allah da Sunnar Annabi (s.a.w) Imaman Ahlul Baiti (AS) sun qarfafa cewa tana cikin bidi’o’in da Allah mai hikima bai sharanta ba, kamar yada ba ta kasance a zamanin Annabi (s.a.w) da Abubakar da wani lokacin mulkin Umar ba, kai fa ita bidi’a ce ta bayyana da umarnin Halifa na biyu Umar xan Khaxxabi, tabbas duk wani qoqari da yunqurin da ake ta yi na kare ta daga zama bidi’a yunquri ne mara nasara.

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: