bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:41:14
yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.
Lambar Labari: 255
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. WASU MUTANE UKU A CIKIN KOGO
Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) ya ba da labarin wasu mutane guda uku daga bani Isra'ila: sun kasance matafiya da hanya ta hada su zuwa wani guri. suna tsaka da tafiya sai ruwan sama ya kece, sai suka fake a wani kogo. da shigar su kogon nan sai wani dutse babba ya zamo ya rufe kofar kogon nan, cikin kogon yayi duhu dundun rana ta zame musu kamar dare.
sai ya kasance ba su da tsimi ko dabara face neman taimako daga Allah. Sai daya daga cikinsu ya ce, to shikenan abin da ya kamata mu yi shine, mu yi kamun kafa da wani aiki da muka yi shi tsakani da Allah, ya kasance hanyar tsirar mu daga wannan hali da muke ciki, sai dukkansu suka yarda da wannan shawara.
Daya daga ciki ya fara da cewa: ya Ubangiji Ka sani cewa ina da wata 'yar dan uwana, wadda ta ke kyakkyawar gaske, na kamu da so da sha'awarta sosai, na kasance wani lokaci na same ta ita kadai a daki, har na nufe ta zan keta mata mutunci, a yayin da ta fara magana kamar haka: ya dan kawu, ina maka nasiha da jin tsoron Allah, dan haka ina rokon ka da kada ka keta min hurumi.
Wannan nasiha da tunatar wa ta sanyaya min jiki inda na fi karfin son zuciyata na janye daga aikata wannan mummunan aiki. Ya Ubangiji kamar yadda Ka sani idan na fasa aikata wannan sabo domin Ka, ina kamun kafa da shi da ka kubutar da mu daga halaka, sai kawai suka ga dutse ya matsa gefe kadan har cikin kogon ya dan haska.
Sai mutun na biyu yace: ya Ubangiji Ka sani ina da iyaye wato Mahaifi da Mahaifiya tsofaffi wadda saboda da tsufa har sun rankwafa. Na kasance a kowanne yanayi ina yi musu hidima, na kawo musu abinci wata rana da dare, sai na same su suna bacci, shikenan sai na zauna da abincin nan a hannu har asuba a gabansu ba tare da na tashe su ba dan kada na katse musu baccinsu.
Ya Ubangiji idan na yi haka ne dan neman yarda Ka kadai, to Ka bude mana kofar nan mu samu mu kubuta. A wannan lokaci sai dutsen nan ya kuma matsawa gefe, sai na ukunsu ya ce: ya Masanin dukkan sarari da boye, Ka sani cewa na kasance ina da wani mai yi min hidima, da muddar aikinshi ta kare na ba shi ladanshi, sai ya raina, ya nemi kari daga nan ya tafi abinshi daga gurina ba tare da ya karbi ladan ba. 
Saboda gudun kada na ci hakkinsa, sai na sayi Akuya da kudin, sai na ware ta daban na ci gaba da kula da ita zuwa dan kankanin lokaci ta hayayyafa da yawa. Bayan wani lokaci sai gashi ya dawo neman hakkinsa a gurina. Sai na yi mashi ishara ga akuyoyi, ya dauka ina yi mashi ba'a ne; amma daga baya sai ya kama dukkan dabbobinshi ya tafi.
Ya Ubangiji idan na yi wannan aiki domin neman yardarKa da tsarkin zuciya; to Ka cece mu daga wannan masifa. Sai kawai suka ga dutsen nan ya bude daga kofar kogon nan gabadaya, sai dukkan suka fito zuciya cike da farin ciki, suka ci gaba da tafiyarsu.
Masu karatun masu daraja mu sani cewa sharadin karbuwar aiki shine wadda aka yi shi domin Allah wato da ikhlasi. An ruwaito a cikin al-Kafi cewa: Allah Tabaraka wa ta'ala Ya na cewa da Musa (alaihis-salam), 'ya Musa duk abin da aka yi shi domin Ni, to kadan din shi mai yawa ne. Kuma duk abin da aka yi shi domin wasu, to komai yawan shi kadan ne.' (al-Kafi, mujalladi na 8, shafi na 46, lamba ta 8). Haka kuma Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) yana cewa:
'ka tsarkake zuciyarka, aiki kadan ya isar maka.' (Bihar al-Anwar, mujalladi na 73, shafi na 175, lamba ta 15). Imam Ali (alaihis-salam) yana cewa: 'kyautata aiki da kammala shi ya fi yin aikin, kuma tsarkake niyya daga mummuna ya fi soyuwa akan yin jihadi mai tsawo'. (kamar na baya, mujalladi na 77, shafi na 288, lamba ta 1)
Haka nan ma Imam Sadik (alaihis-salam) ya na gaya wa Mufadhaal bin Salih cewa: 'Lallai Allah Ta'ala Ya na da wasu bayi da suka yi aiki da ikhlasi a asirce, dan haka sai Allah Ta'ala Ya ba su daga ladanShi na musamman, su ne wadanda za su zo a ranar tashin al-kiyama da littafinsu babu komai a ciki, amma a yayin da suka tsaya a gaban Allah Ta'ala sai littafan nasu su cika da kasuwancin da suka yi da Allah a asirce (wato ayyukan da suka yi domin Allah a asirce da ikhlasi).
mufadhaal ya ci gaba da ruwaito wa, sai na tambaya, 'ya shugabana me yasa littafansu su ka kasance babu komai da farko?' sai Imam (alaihis-salam) ya amsa masa cewa: 'Allah Ya killace su ne a matsayi babba da har ta kai ga ba Ya so ko da Mala'iku su san abin da ke faruwa a tsakaninShi da su.' (Uddat al-Da'ai, shafi na 194).
Haka nan Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) ya ce: 'idan za ka yi aiki to ka yi shi tsakani da Allah, saboda kadai Ya na karba daga bayinShi ayyukan da aka yi su da ikhlasi wato domin Shi.' (Bihar al-Anwar, mujalladi na 77, shafi na 103, lamba ta 1).  
2. Munin hassada
A lokacin kalifancin Hadi Abbasi, an yi wani attariji mai kirki a Baghdada. To sai ya kasance a makwabtansa akwai wani mutun shi kuma da yake matukar yin hassada ga dukiyar wannan attajiri. Mutumin ya yi ta mita akan attajirin nan kullum ba dare ba rana, har ta kai shi ga yanke shawarar cewa bari ya siyi bawa ya tarbiyantar da shi yadda yake so domin ya yi mafani da shi wajen haifar wa da attajirin nan matsala.
Wata rana bayan shekara yana tarbiyantar da bawan nan sai yace da shi: ya za ka iya kwatanta biyayyarka ga ubangijinka (mai gidanka)? sai bawan yace: da za ka kunna wuta kace na shiga to zan shiga. Sai mai hassadar nan ya ji farin ciki a ranshi. sai yace: to dama abin da nake ka sani shine cewa ka ga attajirin nan makwabcina, to ba ni da makiyi kamar shi, dan haka ina so ka yi abin da zan umarce ka.
Sai ya ci gaba da cewa: da dare ni da kai za mu hau saman soron attajirin sai ka kashe a kai, ka ga alhakin kisa na sai ya koma a kanshi, dan haka hukuma shi za ta kama ta yanke mashi hukumci kisa, kaga shima ya bar duniyar kenan. Bawan nan ya yi iya kokarinshi na ganin ya kaucewa wannan danyen aiki, amma ina hakan bai yiwu ba daga bangaren mai hassadar.
Dan haka da tsakar dare suka hau saman rufin soron attajirin nan ya sare kan mai gidanshi, ya yi sauri ya dawo shinfidarshi ya kwanta abinshi. 
Kashegari sai aka sami gawar mahassadi a kan rufin gidan attajiri, sai Hadi Abbasi ya ba da umarnin bincikar attajiri; to a cikin bincike sai aka zo ga bawan mahassadi. Bawan nan ya ga cewa a gaskiya attajirin nan ba shi da hannu ko daya a wannan al'amari na kisa; sai kawai ya fadi duk abin da ya faru tsakaninshi da mai gidanshi dangane da hassadarshi ga attajiri.
Sai kalifa ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru na 'yan wasu lokuta, sannan ya dago kanshi yace da bawan: duk ka kashe rai, amma saboda dattakun da ka yi da kuma kubutar da wanda bai ji ba bai gani ba, to zan 'yanta ka, shikenan sai ya 'yanta shi, dan haka cutarwar hassada ta koma wa mai ita wato mahassadi.  
Lallai hasada cuta ce babba wacce take lakwame mai yin ta, kuma ta kan kasance taki ga wanda ake yi wa ita. Allah Ta'ala Ya umarce mu da neman tsari daga sharrin mai hasada a cikin Surar Falaki aya ta 5 inda yake cewa: "Da sharrin mai hasada idan ya yi hasada" (Qur'an: 3:5).
Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) yana cewa dangane da hasada: "Hasada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta ke cinye kirare, sadaka kuma tana gusar da zunubai kamar yadda ruwa ke kashe wuta" (Nahj al-fasaha; hadisi na 1108, shafi na 158). 

To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na bakwai  a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na takwas’.

Hassan Adamu
Ta'alif



Littattafan da aka duba sune:
1. al-Kur'ani mai tsarki
2. Al-Kafi
3. Bihar al-anwar
4. Dastanehay-e-ma, juz'i na 2 
5. Mustadrak al-wasa'il, Juz'i na 3
6. Hikayat'haye shanidani
7. Ghurar al-Hikam
8. Uddat al-Da'ai
9. Nahj al-fasaha
10. 100 moral stories

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: