bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:43:56
Imam Ali (alaihis-salam) yana cewa: Kyautayi ga iyaye shine mafi girma da muhimmancin aiki. (Ghurar al-Hikam, lamba ta 1)
Lambar Labari: 256
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. Malik Ashtar
Wata rana Malik Ashtar zai wuce ta kasuwar Kufa sanye da wasu kaya na tanti marasa kima, kuma da wannan dai yadin tanti yayi rawani, haka ya rika shigewa a yanayi na fakirai. Akwai wani dan kasuwa yana zaune a bakin kofar shagonshi, da ya ga Malik Ashtar a irin wannan yanayi sai ya rika mashi kallon kaskanci, dan haka sai ya boye ya watsa mashi shara mai hade da gwadalon cabi.
Amma Malik bai ko lura da shi ba, ya ci gaba da tafiya abinshi. To akwai wani mutumi wadda yake ya san Malik kuma ya ga abin da ya faru, sai ya ce da dan kasuwar nan: kaicon ka wannan mutumi! ka san kuwa ko wanene ka keta mutuncinshi haka?
ya ce a'a, sai yace: to Malik Ashtar ne, babban kwamandan Ali (alaihis-salam). Nan da nan sai dan kasuwan nan ya kama yin karkarwa yana tsima tare da nadama akan mummunan aikinshi, cikin sassarfa sai ya bi Malik domin ya nemi uzri da afuwa. Sai ya gan shi ya shiga wani masallaci ya na yin sallah, sai ya saurara a gefe guda har Malik ya idar, sai ya matsa kusa da shi ya dora hannayenshi akan hannu da kafar Malik yana ta sumbata, sai ya dago kansa yace: meye haka, me ya faru? sai mutumin ya ce: ina neman uzri dangane da sabon da nayi ne, ban san kai ne ba.
Sai Malik yace: babu wani laifi akanka, na rantse da Mahaliccina ban zo nan ba sai domin nema maka gafara gurin Allah.
 Imam Ali (alaihis-salam) yana cewa: yana daga daukaka da girma hadiye fushi da kawar da kai daga munana war 'yan uwa. (Ghorar al-Hikam).
2. Adu'ar mai ikhlasi karbabbiya ce
Sa'id bin Musayyib ya ba da labari yana cewa: Wata shekara aka yi fari wato kamfar ruwa, sai al'ummar garin suka fita domin adu'ar rokon ruwa. can sai idona ya fada kan wani bawa baki wanda ya ware nesa da jama'a ya tafi can gefe, sai na bi bayanshi, sai na ga labbanshi suna motsi alamun yana yin adu'a, kafin ya kare adu'ar sai na ga hadari na haduwa a sararin samaniya.
A yayin da Bawan nan ya ga hadari na haduwa sai ya yi godiya ga Allah ya tafi abinshi, sai ruwa ya kece sosai har ya kai mun yi tsammanin ruwan zan halaka mu ne. Sai na bi bayan bawan nan na ga inda ya nufa, sai na ga ya tafi gidan Imam Sajad (alaihis-salam). Sai na je gaban Imam alaihis-salam nace: akwai wani bawa baki a gidan nan, ya shugabana ka taimaka ka siyar min da shi. 
Sai yace: ya Sa'id me zai hana na bar maka shi; daga nan sai ya umarci baban mai hidimar gidan da ya tara mashi dukkan masu hidimar gidan, duk ya tattaro su, saidai ban ga wancan bawa da nake nema a cikinsu ba. Sai nace ban ga wanda nake nema ba a duk cikinsu. Sai yace babu wanda ya yi saura kuwa sai wane, dan haka sai ya yi umarni da a kirawo shi, yana zuwa sai na ga shine kuwa wanda nake nufi, sai na ce: wannan ne nake so. 
Sai Imam alaihis-salam yace: ya kai hadimi daga yanzu kai mallakin sa'id ne, dan haka ka bi shi ku tafi. Sai wannan bawa ya dube ni yace: kai kuwa me yasa ka raba ni da shugabana? sai nace: sakamakon tasirin adu'arka da na gani ta ruwan sama. Da bawan ya ji wannan magana sai ya daga hannayenshi ya kalli sama ya ce: ya Ubangijina, akwai wani sirri tsakanin ni da Kai, ga shi kuma yanzu ka bayyana shi, dan haka ina rokon Ka da Ka dauke ni na koma gareKa.
Imam alaihis-salam da wadanda suke gurin da ganin halin da bawan nan ya shiga sai suka hau kuka, nima cikin wannan hali na fita, ina isa gida sai ga dan aike daga Imam alaihis-salam ya ce idan ka shirya sai ka zo jana'izar bawanka..!! na bi wannan dan aike muka tafi na tarar bawan nan ya cika.
Dangane da ikhlasi Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) yana cewa: tsarkake zuciyarka; aiki kadan sai ya iasr maka (Bihar al-anwar, mujalladi na 73, shafi na 175, lamba 15).
Haka nan ya kara da cewa: 'tabbas ga kowacce gaskiya akwai haqiqa, sannan bawa ba ya isa ga hakikanin ikhlasi har sai ya ji ba ya son yabon mutane dangane da duk wani aiki da ya yi shi saboda Allah madaukakin sarki. (Bihar al-anwar, mujalladi na 72, shafi na 304, lamba 51).
Masu karatu da wannan za mu iya fahimtar girman daraja da matsayin da bawa ke kai wa a yayin da ya tsarkake zuciyarshi wajen yin ayyuka.
Imam Ali (alaihis-salam) yana cewa: tsarkin ibada shine ya kasance mutum ba ya fatan samun komai face yardar Allah, sannan kuma ba ya tsoron komai face sakamakon zunubinshi. (Ghurar al-Hikam, lamba 2128).
Imam Sadik (alaihis-salam) yana cewa: tsarkakakken aiki shine aikin da bawa ya yi ba tare da neman yabon kowa ba face Mahaliccinsa Allah madaukakin sarki. (al-Kafi, mujalladi na 2, shafi na 16, lamba 4).
3. Wani Yaro da bishiyar Tufah (apple)
A lokacin da an yi wata katuwar bishiya, wadda wani dan yaro yake jin dadin zuwa gurinta kodayaushe. Ya hau samanta, ya ci 'ya'yanta sannan ya zo kasa ya dan kishingida a inuwarta. Yana son bishiyar, ita ma bishiyar tana matukar son yin wasa da shi. Bayan wasu lokuta yaro ya na tasawa sai ya rage zuwa yin wasan da bishiya kullum.
Wata rana sai yaron nan yazo gurin bishiyar nan fuska a turbune.
"zo mu yi wasa ka ji" tace da yaron.
"na fi karfin nayi wasa a gindin bishiya yanzu ni ba yaro bane" yaron ya ce da ita. "ni yanzu kayan wasa nake so, dan haka kudi nake bukata." ya kuma cewa da ita.
"ayya ka yi hakuri, gashi kuma ba ni da kudi, saidai kuma za ka iya cirar 'ya'ya na sai ka je ka siyar ka samu kudin." tace dashi.
Sai yaron ya ji wani irin dadi, dan haka sai ya ciro duk tufahan da ke bishiyar nan ya tafi da su cikin farin ciki. Saidai tunda yaron nan ya debi tufahan nan bai sake waiwayo bishiya ba, dan haka sai ta ji ba dadi.
Sai wata rana kuma bayan yaron ya zama babban mutum, sai gashi ya kuma dawo wa gurin bishiya, sai ta yi ta murna tace: "zo ka yi wasa da ni."
Sai yace: ba ni da lokacin wasa, ni ta iyalina nake yi. Gida muke da bukata ko za ki taimaka?.
Sai tace: ga shi bani da gida da zan baka, saidai za ka iya sare rassa na in yaso sai ka hada gidan da su. Sai ya sare duk rassan bishiyar nan ya tafi cikin murna. Sai ta ji dadi da ganin shi cikin farin ciki, saidai mutumin bai sake dawo wa gareta ba, haka ta ci gaba da kasancewa cikin kadaici da damuwa.
Sai wata rana da bazara ana zuba zafi mai tsanani, sai ga mutumin nan ya dawo, sai bishiyar ta yi murna sosai. Sai tace: zo mu yi wasa kaji. Sai yace: ni yanzu na tsufa, dan haka ina sha'awar shiga ruwa ne idan za ki bani jirgin kwale-kwale?.
Sai tace: yi amfani da gangar jikina ka hada jirginka, ka ga sai shiga ruwan cikin annashuwa.
Sai ya sare jikin bishiyar nan ya yi jirgin kwale-kwale da shi, ya dauka ya tafi abinshi bai sake ko waiwayarta ba.
sai can bayan shekaru da dama mutumin ya dawo. Sai tace dashi, yi hakuri dana gashi yanzu ba ni da abin da zan baka, babu tufaha kuma babu rassa ko jiki.
Sai yace: ba damuwa ai bani da hakoran da zan tauna, kuma na yi tsufan da zan hau kan bishiya. Cikin hawaye sai tace ba abin da ya yi saura sai ragowar matacciyar saiwata.
"ba wani abu nake bukata a yanzu ba, sai dan gurin da zan dan jingina na huta bayan 'yan shekarun nan," yace da ita.
Sai tace: Yawwa! ai kuwa tsohuwar saiwar bishiya ta fi dadin jingina, zo ka zauna ka jingina da ni, mu zauna mu huta tare. Sai mutumin ya zauna, bishiyar kuma tana ta yin murna da murmushi tare da hawaye.
Wannan labari ne na kowa da kowa. Ita kuma bishiyar a matsayin iyayenmu take. A yayin da muke yara muna jin dadin wasa da su, idan muka yi girma sai mu rabu da su kuma, ba mu waiwayar su sai muna bukatar wani abu a gurinsu ko idan wata matsala ta fuskanto mu. Duk tsanani kodayaushe suna cikin shiri na tallafarmu cikin farin ciki duk lokacin da muka je musu. 
Sai mu ga kamar cewa wancan yaro ya cika zara ko? a'a ba shi kadai bane, dukkanmu haka muke yi wa iyayenmu. Ba mu godewa da yabawa da dawainiyar da suke yi da mu sai bayan babu su. Allah Ya gafarta musu Ya kuma yafe mana a bisa gazawarmu na kulawa dasu, Ya kuma ci gaba da yi mana jagoranci.
Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) yana cewa: Allah Ta'ala ba Zai karbi ramakon ayyukan mutum uku ba, ranar al-kiyama sune: wadanda iyayensu suke fushi da su, da masu taimako a bisa tilasci da kuma masu karyata Qaddara. (Nahjul fasaha, hadisi na 769)
Imam Ali (alaihis-salam) yana cewa: Kyautayi ga iyaye shine mafi girma da  muhimmancin aiki. (Ghurar al-Hikam, lamba ta 1)


To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na takwas  a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na tara’.

Hassan Adamu
Ta'alif



Littattafan da aka duba sune:
1. al-Kur'ani mai tsarki
2. Ghurar al-Hikam
3. Al-Kafi
4. Bihar al-anwar
5. 100 maudhu, 500 dastan
6. Mustadrak al-wasa'il, Juz'i na 3
7. Hikayat'haye shanidani
8. Uddat al-Da'ai
9. Nahj al-fasaha
10. 100 moral stories
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: