bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:56:15
labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya
Lambar Labari: 257
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. Da Annabi Musa (AS) ya roki Allah
Wata rana Annabi Musa (alaihis-salam) ya yi roko ya ce: ya Ubangijina Allah, ina so ka nuna min wannan halittar taka wadda ta tsarkake kanta domin ambatonKa kuma take yi maka da'a ba tare da algusu ba.
Sai ya ji sauti cewa: ya Musa! je ka bakin ruwa kaza, ni kuma zan nuna maka abin da ka nema. Sai Annabi Musa (alaihis-salam) ya tafi bakin tekun da aka ce ya je, da isar shi sai ya ga wata bishiya a bakin ruwan, sai ya ga wata tsuntsuwa akan wani reshe na bishiyar nan wadda ya tankwaro kasa-kasa ya kusa taba ruwan, tana ta ambaton Allah.
Musa (alaihis-salam) ya tambaye dangane da labarinta, sai tace: tun da Allah Ya halicce ni nake akan wannan reshen bishiyar nake yin ibada kuma ina ambatonShi kuma daga duk zikrina guda daya zikri dubu ne yake tsira (fita) daga shi. Ta ci gaba da cewa abincina da nake ci na ji na koshi shine dadin ambaton Allah.
Sai Musa (alaihis-salam) ya kuma tambayar ta yace: to yanzu daga duk abin da ke duniyar nan akwai wani abu da kike da burin samun shi? sai tace: Eh, burina na sha digo daya daga ruwan wannan teku. Musa (alaihis-salam) yana al'ajabi yace: ya ke baiwar Allah to ai tsakanin bakinki da ruwan babu wata tazara mai yawa, me yasa ba za ki dangwalo ba? sai ta ce: ai ina tsoron kada dandanin ruwan ya katse min dadin ambaton Ubangijina. Dan haka sai Musa (alaihis-salam) ya dora hannayenshi biyu a kai saboda mamaki da al'ajabi. (khazinatul-jawahir, shafi na 318).
Lallai da ambaton Allah ne zukata suke samun nutsuwa. Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa alihi wasallam) yana cewa: kada ku kuskura ku fifita wani abu akan ambaton Allah, saboda Ya ce,"tabbas ambaton Allah shine madaukaki". (Bihar al-Anwar, mujalladi na 77, shafi na 107, lamba na 1).
Imam Ali (alaihissalam) shima yana cewa: "ambato ko tuna Allah shine asasin babban jin dadi ga masoya Allah". (Gurar al-Hikam, lamba ta 670).
2. Wani dankoli ya ci amana
Wata rana wani ya shiga garin Baghdada a matsayin bako, ya saka wata sarkar wuya ta kimanin dinare dubu a kasuwa domin siyar wa amma bai samu mai siye ba. To da yake yana tunanin zai wuce zuwa Makka ne, sai ya shiga neman wani amintacce da zai ba shi ita ya ajiye mashi.
Sai mutane suka yi mashi ishara da wani dankoli wanda wai suka ce mai tsantseni ne shi. Sai ya bashi ajiyar wannan sarka, ya tafi Makka abinshi. Yayin da zai dawo daga can har da tawo wa da dankolin nan tsaraba ta musamman.
Da ya zo gurin dankolin ya bashi tsarabar, sai dankoli ya nuna bai san shi ba, yace: ni ban san ka ba, kuma babu wata ajiya da ka bani, sai suka kaure da takaddama har hankalin mutane ya yo gurinsu, sai aka zo aka fitar da mutumin daga rumfar dankoli.
Mutumin nan ya sake komawa gurin dankolin nan amma duk sanda yaje ba abin da yake samu sai maganganu marasa dadi. Sai wani yace dashi: ka rubuta kara ka kai gurin Amir Adhdul daulah Dailami tabbas zai yi wani abu akai, sai ya rubuta wasika zuwa ga Amir, Adhdul daulah ya bashi amsar wasikarshi yace: kayi kwanaki uku a jere kana zuwa kofar rumfarshi kana zauna wa, ni kuma a rana ta hudu zan shigewa ta gurin, zan yi maka sallama kai kuma abin da za ka yi kawai shine amsa sallamata. sannan kuma kashegarin ranar sai ka kuma neman sarkarka a gurin shi, daga sai ka bani labarin sakamakon abin da ya faru.
A rana ta hudun sai ga Amir da tawagarshi cikin daukaka yazo zai wuce ta kofar shagon dankolin nan, idonshi na fada wa kan bakon nan, sai ya yi mashi sallama ya yi matukar girmama shi. Bakon nan ya amsa wa Amir, dama za ka zo Baghdada amma ko ka sanar da mu, dan kada mu yi maka hidima ko, sai Bakon ya amsa mashi da cewa: ai da yake ban yi niyyar tsaya wa a garin haka ba.
A duk wannan lokacin dankoli da sauran mutanen gari suna jin su, sai suka cika da mamaki cewa wannan bako waye shi; dan haka dankoli sai ya razana ya kidime. Amir yana tafiya, sai dankoli ya fuskanci bako ya tambaye shi yace: dan uwa yaushe ka bani waccan sarka da kake magana akai, kuma ya kamanninta yake? sake gaya min ko zan tuna. Sai bako ya sake fadin sifar ajiyarshi, sai dankoli ya dan dudduba kadan sai gashi ya dauko ta ya ba shi; yace: Allah Ya sani na manta ne.
Sai bako ya tafi gurin Amir ya gaya mashi duk abin da ya faru, sai Amir ya karbi sarkar daga hannunshi sai ya rataya ta a wuyan dankoli, sannan ya ba da umarni a zagaya da dankoli cikin gari a haka ana fadin cewa wannan shine sakamakon wanda zai karbi amana daga baya kuma sai ya yi inkari.
Bayan wannan horo sai aka mayar wa da bako sarkarshi, ya kama hanya ya koma garinsu.
Amana tana daga cikin babban ma'auni da ake gane mutum na gari  da ita. Kamar yadda Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) yake cewa: ana gane munafuki ta hanyar sifofi guda uku: mai yin karya, wanda yake saba alkawari da kuma mai ha'inci a amana. (Nahj al-Fasaha, hadisi na 81).
Sannan ya kuma cewa: ka aminta da dan uwanka (na imani) idan ka samu ukun nan a tare dashi: kunya, amana da kuma gaskiya; ka yanke kauna daga gareshi wanda ya rasa su. (Nahj al-fasaha, hadisi na 278).
3. Mala'ikan rahma
Wata rana lokacin haihuwar wani jariri ya gabato, sai ya tambayi Allah cewa, "an gaya min za tura ni duniya gobe, to amma ya za ayi na rayu a can alhali na kasance karami rarrauna?" sai Allah Ya amsa masa: "daga cikin dinbim mala'ikun da nake da su na zaba maka daya, za ta jira ka kuma za ta kula da kai".
Sai jaririn yace: "to amma gaya min ya zanyi alhali a nan ba abin da yake sa ni farin ciki daga wake sai murmushi!" Sai Allah Ya ce dashi kada ka damu, mala'ikan za ta yi maka wake kullum, kuma za ka ji dadin soyayyar da za ta nuna maka.
Sai jaririn ya kuma cewa, to ya zan fahimta idan mutane za su yi magana da ni, idan ban iya yarensu ba? wannan mai saukine, Allah Ya ce dashi, mala'ikan taka za ta sanar da kai zakaka kuma mafi kyawun kalaman da ba ka taba ji ba, kuma tare da hakuri da kulawa za ta koya maka yadda za ka yi magana. Jariri ya kuma cewa: to ya zan yi idan kuma ina so nayi magana da kai? Sai Allah Ya ce mala'ikan za ta koya maka yadda za ka yi adu'a.
Jaririn ya kuma cewa, na ji ance a duniya akwai gurbatattun mutane. To wa zai kare ni daga cutarwarsu? Allah Ya mayar masa da cewa: ita dai mala'ikan nan ce, kuma ko da hakan zai kasance barazana ga rayuwarta! sai jaririn nan ya tabe fuska yana cewa: saidai kodayaushe zan kasance cikin bakin ciki tunda ba zan sake ganinka ba. Sai Allah Ya mayar masa cewa: Mala'ikan taka ai kodayaushe za ta rika yi maka maganata kuma za ta koya maka yadda za ka dawo gare ni, duk ma dai kodayaushe zan kasance tare da kai.
A daidai wannan lokaci yana cikin aminci, amma sai ga shi yana jiyo wani sauti daga duniya.
Sai jaririn cikin sauri a hankali yace: ya Allah, ga shi kuma na kusa tafiya amma saidai ba ka gaya min sunan mala'ikan nawa ba?! sai Allah Ya ce masa jin sunanta ba shi da wani muhimmanci sosai amma za ka iya kiran ta da 'Uwa'!
Lallai matsayin uwa ba karami bane idan muka yi la'akari da yadda take sadaukar da dukkan jin dadinta kawai domin wanzuwa da walwalar 'ya'yanta. 
Shi yasa ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) yake cewa: la'ananne ne wanda yake zagin mahaifanshi. (nahj al-fasaha, hadisi na 432). Hakanan ya kuma cewa: Maigida (miji) shine mafi hakki akan matarshi; ita kuma uwa itace mafi hakki akan 'ya'yanta. (hadisi na 940). Akwai inda yace kuma: A kula da uwa! a kula da uwa! sannan uba sai kuma 'yan uwa (hadisi na 1317).
Allah Ya gafarta wa iyayenmu mata Ya kuma gafarta wa mahaifanmu maza, Ya kuma kara mana kumazin kyautata musu idan suna raye.


To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na tara  a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na goma’.

Hassan Adamu
Ta'alif



Littattafan da aka duba sune:
1. al-Kur'ani mai tsarki
2. Ghurar al-Hikam
3. Al-Kafi
4. Bihar al-anwar
5. 100 maudhu, 500 dastan
6. Mustadrak al-wasa'il, Juz'i na 3
7. Hikayat'haye shanidani
8. Uddat al-Da'ai
9. Nahj al-fasaha
10. 100 moral stories
11. khazinatul-jawahir

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: