bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      17:00:45
Banbanci nawa ne tsakanin dan gwagwarmayar juyin-juya hali mumini da kuma mumini dan gwagwarmaya
Lambar Labari: 258
Wannan ma’ana na gudana cikin da yawa-yawan wurare masu kama da juna, misali masanin fanni musulmi yana sanya muslunci cikin hidimtawa fanninsa, musulmi masanin fanni ya na sanya fanninsa cikin hidimtawa musluncinsa, haka ma mawaki musulmi, da dan gwagwamaya mumini, da mumini dan gwagwarmaya, lallai shi mumini dan gwagwarmaya yana sanya gwagwarmayar sa cikin hidimar imaninsa, daidai lokacin da dan gwagwarmaya mumini ke sanya imaninsa cikin maslahar gwagawarmayarsa, ka lura sosai. 
Banbanci nawa ne tsakanin dan gwagwarmayar juyin-juya hali mumini da kuma mumini dan gwagwarmaya, lallai na farko ko da larura ta hukunta masa wofinta daga imanin sa lallai shi da wahamansa da hiyalansa zai wurgi da Imani jikin bango, yayi tsammani cewa shi yana kyawunta aiki da aikata hakan, saboda ma’auni da abin la’akari a wurinsa shi ne gwagwarnayarsa, sai yayi kiyasi ya auna kansa da ma’auni da sikelin gwagwarmaya, idan addini da mazhaba da ilimi da fanni suna hidimtawa gwagwarmayarsa lallai zai rikesu a matsayin kayan aiki tsani don cimma bukatar gwagwarmayarsa, amma idan addini da mazhaba sukai karo da gwagwarmayar sa lallai anan ne zaka same shi ya bayyanar da munafuncin sa, ya wofintu daga addini da mazhaba a kimomin kyawawan halaye da madaukakan siffofi.
Dalibin ilimi da Imani:
Idan kana son sanin makomarka da ka jahilta to hakan zai kasance da tunani da zurfafa tunani domin shi tunani shi ne jagoran hankali, idan baka da tunani ta yaya hankalinka zai kasantu, idan tunani ya kasance mara kyawu hankali zai kasance mara kyawu, idan kuma ya kasance mai kyawu to hankali ma zai kasance mai kyawu, kamar yanda hankali yake jagoran zuciya, abin da yake darsuwa kan zuciya kadai dai daga wahayin hankali yake, sannan ita ma zuciya itace sarauniyar gangar jiki, gabbai da jijiyoyi suna bin iradar zuciya da abin da take so da umarnoninta da haninta. 
Duk wanda yake son sanin makomarsa da ya jahilta, daidai lokacin da lallai shi bai sanin meye karshen lamarinsa da karatunsa, to kaka kuma makomar imaninsa, domin lallai daga Imani akwai wanda yake tabbatacce zaunanne har zuwa ranar tashin alkiyama, haka daga Imani akwai wanda yake na ajiya ana kwace shi lokacin fitar rai da mutuwa ko kuma gabaninsu.
Imani na ajiya ana sanya shi wurin mutum kamar matsayin kayan ajiya zuwa wani tsawon lokaci, sai ka samu kufaifayi da alamomin Imani suna bayyana gare shi da alamomin mumini kamar misalin sallarsa da azuminsa da riko da addini, sai dai cewa shi a gobe nan gaba za a cire shi daga gare shi, sai ya koma bayansa, ya shiga da’irar bata ya kasance batacce, idan kuma ya batar da wasu sai ya zama mai batarwa, wannan yana daga tsiyata ta dindin kuma karshensa wuta da azaba.
Wanda kuma imaninsa ya kasance zaunanne har zuwa ranar tashin kiyama, lallai shi guguwa ba ta iya girgiza shi, shi kamar dogon dutse yake, kafarsa na tabbace, mai karfin zuciya da tsaurin Imani, kayace-kayacen duniya basa iya rudar da shi, haka ma dadin siyasa da alfarmar da mukami.
Haka zalika dalibin ilimi cikin hauzozin ilimi, lallai shi bai san me ye makomar rayuwarsa da iliminsa ba, shin zai kasance daga ilimi mai amfanarwa cikin addini da duniya da lahira, ya janyo daukakar darajarsa da kusancinsa zuwa ga rayayye tsayayye, lallai Allah matsarkaki madaukaki daddadan zance yana hawa zuwa gare shi aiki na gari yana daukaka shi, daukaka aiki na tare da daukakar ma’aikaci, lallai shi aiki ma’aluli ne illarsa kuma itace mai aikata shi mai yinsa, idan ya daukaka aiki to babu shakka da kokwanto zai daukaka mai yi aikin, sai ya kasance cikin aljannoni da koramu, cikin matsugunin gaskiya wuroin sarki mai ikon yi.
Misalin wannan ilimin mai cike da haske Allah yana jefa shi a zuciyar wanda ya so shiryar da shi, yana kuma janyo daukakar darajarsa, lallai Allah yana daukaka wadanda sukai Imani daraja daya, domin su bude kofar taskokin aljannoninsu da hakan, sannan yana daukaka masu ilimi da darajoji (yi karatu ka smu daukaka) hakan na kasancewa ne sakamakon neman haske da sukai cikin rayuwa, misalin wannan ilimi zai amfanar da mu a rayuwarmu ta nan gaba da ma bayan mutuwarmu, da cikin kabari da barzahu da ranar tashi daga kabari a taron kiyama da ma cikin aljanna, lallai shi yana daga haske wanda Allah ya sanya shi gare shi cikin rayuwarsa domin yayi tafiya tare da shi, kamar yanda yake kai kawo a gabansa da geffansa damansa ranar kiyama, domin ya dauke shi ya kai shi cikin aljanna, kamar yanda julmar riwayoyi da ayoyi suka zo da bayanin haka.
Sannan lallai wannan ilimi na haske mai cike da albarka, yana sanya kabarin malami cikin dausayi daga dausayoyin aljanna.
Amma ilimi idan bai kasance domin Allah ba bai kasance ana aiki da shi ba, zai kasance mafi girman hijabi zai janyo tsiyata a duniya, kamar yanda zai mayar da kabari ramin wuta.
Duk wanda yake neman ilimi don Allah da Allah zuwa ga Allah jalla jalaluhu, lallai shi da wannan niyya zai shiga hanya zuwa ga aljanna, lallai tabbas wadanda suke sama da kasa zasu dinga nemar masa gafara, kai hatta kifaye da suke ruwa ba a barsu a baya ba wajen nema masa gafara, sannan a sama za a kira shi mai girma.
   A nan akwai wata tambaya ta larura da take bijirowa, shi ne yaya zan san gobe ne ta ilimi, shin ilimina yana daga ilimi mai amfanarwa, ko kuma dai yana daga ilimin da annabi (s.a.w) yake neman tsari daga gare shi 
 (اللّهم إني أعوذ بك من علم لا ينفع)
Ya Allah ina neman tsarinka daga ilimin da ba ya amfanarwa.
Kamar yanda yake cikin addu’a bayan idar da sallar la’asar cikin kowacce rana, sai ka lura, ta yiwu cikin kowacce rana mutum ya jarrabtu da ilimin da bazai amfanar da shi ba, bari dai ma zai cutar da shi ne ya kuma kasance hijabi mafi girma wanda zai hana shi kaiwa zuwa ga Allah, zuwa ga aljanna da ni’imarsa, sai ya zama ya bayyana karara cewa akwai ilimi mai amfani akwai mai cutarwa, akwai ilimi wanda karshensa yake kasancewa dausayi daga dausayoyin aljanna, dayan kuma karshensa rami daga ramukan wuta, ilimin da yake jawo azurtuwa cikin gida biyu, dayan kuma yana jawo tsiyata cikin duniya da lahira.  
 Ilimi ne da ma’abocinsa zai farantawa yan aljanna da shi, dayan kuma ilimi ne da zai cutar da hatta yan wuta daga warinnsa!!
Kamar yanda ya zo cikin hadisi.
wanne ilimi ne wannan da har yan wuta ke cutuwa da shi, ballantana yan aljanna, da har za su roki Allah matsarkaki ya kubutar da su daga wannan malami da aka tashe su daga kabari tare da shi sakamakon doyin da wari da yake yi, lallai hakan yafi tsanani daga azabar jahannama, me yafi girma daga misalin wannan azaba ta ruhi da ta gangar jiki shi kasantuwa kusa da malamin da bai yi aiki da iliminsa ba, wannan wani abu da dalili da kur’ani da dabi’a suke gasgatawa, duk wanda Allah ya bude masa idanunsa na barzahu cikin duniya lallai zai cutu daga malami fasiki lalatacce, ya ji warinsa yayin zama tare da shi.
Farin ciki ga malami mai tsoran Allah, wanda ya koyi karatu don Allah, yayi aiki don Allah, ya koyar don Allah, lallai za a kira shi cikin malakut samawat mai girman matsayi, kamar yanda hakan ya zo daga Imam Sadik (a.s)   
الإمام الصادق×، وبئس العلم والعالم الذي لم ينتفع من علمه، بل كدّس العلوم في ذهنه حتى صار كالمكتبة السّيارة، وكالحمار يحمل أسفاراً، وكان علمه حجابه الأكبر.
Tir da ilimi da malami wanda bai amfanu da iliminsa ba, kadai dai ya taskace ilimummuka cikin kwakwalwarsa har ya zama kamar dakin nazarin karatu mai tafiya, kamar misalin jaki yana dauke da manyan litattafai, iliminsa ya zama hijabi mafi girma.
Yaya zan san makomar ilimina da karshen lamarina cikin duniya ta da lahirata, me zai kasance makomata, daga ina zuwa ina cikin ina, me ake nema daga gareni, mene ne falsafar da hikimar halitta ta da rayuwata, yaya zai zama ban zama kamar malamin da ya tofa yawu kan kur’ani mai girma lokacin mutuwarsa, in kasance daga malamin da zai salati kan waliyan Allah A’imma tsarkaka, kamar yanda yayi sallama ga Mala’ikun da aka umarce su da karbar ransa.
Da yawa-yawan malamanmu sun kasance suna sallama kan wanda suka halarce su daga Mala’iku da A’imma (a.s) lokacin mutuwarsa, shi mai kakakin mutuwar ya kasance shi yana ganin Mala’iku duk da cewar wanda suke kewaye da shi basa ganinsu kamar yanda ya zo a hadisai.
Yaya makoma ta za ta kasance?! Daga wanne sinfi zan kasance daga sinfofi uku wadanda sarki mumini Ali (a.s) ya ambace su ga Kumailu bn Zayad Naka’i (rd), daga cikin malamai akwai malami mai tsoran Allah, daga cikinsu akwai mai koyan ilimi don neman tsaro, kashi na karshe yan abi yarima asha kida, suna amsa sautin dukkanin mai kira suna juyawa tare da kowacce iska.
Malami na Allah dangananne zuwa ga ubangijin talikai, wanda ya tarbiyantu da tarbiyar Allah malakutiyya, hakika yayi zuhudu cikin duniyarsa, ya tsarkake niyya cikin iliminsa, sai da farko in fara da mai neman ilimin don samun tsira, sannan in tsallaka zuwa ga marhalar malami na Allah waliyin Allah in dinga shiryar da mutane zuwa hanyar shiriya, su malamai na Allah jagorori al’ummu magada annabawa da wasiyyai (a.s) sun gaji ilimi da Akhlak da mas’uliyar tablig da isar da sakon sama.  
﴿الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالاتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَهُ وَلا يَخْشَوْنَ أَحَداً﴾ .
Wadanda suke isar da sakon Allah suke jin tsoran sa basa jin tsoran kowa.
Kamar yanda fakihai shugabanni suke shiryar da su zuwa daidai da ayyuka da mafi alherin aiki, ya zuwa hanya mikakka tafarki madaidaici.
Umar Alhassan Salihu
+989196659356
+2348162040719

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: