bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      17:03:00
Matafiyar dalibin ilimi shi ne da farko ya yi kokari ya nesantar da kansa daga biyewa sha’awe-sha’awen dabbanci, ya samu iko kan danne fushin sa da sha’awarsa cikin
Lambar Labari: 259
Shugabanci da jagoranci nagari kadai suna hannun malamai nagargaru da fakihai yardaddu, abin nema daga dukkanin wani dalibin ilimi cikin Hauza ilimiyya, shi ne ya kasance kan mustawar da ake bukata daga gare shi, daga malamai na Allah wadanda zargin mai zargi bay a damun su cikin Allah, musammam ma siddikai, kalamansu kalamai ne na rabautattu, masu raya dare masu zama fitila manara da rana, masu riko da igiyar kur’ani da tsatso tsarkaka (a.s) suna raya sunnonin Allah da manzon sa, zukatan su na cikin aljannoni jikkunansu na cikin aiki.
Matafiyar dalibin ilimi shi ne da farko ya yi kokari ya nesantar da kansa daga biyewa sha’awe-sha’awen dabbanci, ya samu iko kan danne fushin sa da sha’awarsa cikin samuwarsa, da sanya hankali da adalci da hikima, sannan ya kasance mai neman ilimummukan Allah domin neman tsira, haka ma ya hau jirgin tsira, jirgin Muhammad da iyalan sa (s.a.w) sannan misalin Ahlil-baitin gidan annabi mafi girma kamar misalin jirgin annabi Nuhu (a.s) duk wanda ya hau ya tsira duk wanda ya juya baya ya nutse cikin teku ya halaka, makomar sa ta kasance tsiyata da wuta da azaba, sannan cikin marhalar ta uku ya kasance daga malamai na Allah ya jagoranci mutane ya zuwa bakin gabar amintuwa da aminci ya zuwa ni’ima da aljannoni.
Anan ina da tambaya kai ma kana da tambaya dukkanmu muna tambaya, yaya zan kasance malami na Allah ta yaya zan lamintar da makoma ta wacce take jahiltacciya ban santa ba?!
Tsoro da fata: 
Babu kokwanto cikin kasancewa lallai shi mumini yana rayuwa tsakankanin tsoro da fata, shi tsoro da fata haske ne guda biyu cikin zuciyar mumini da za a auna daya kan daya da bai rinjaye shi ba, ba a san makoma da goben dalibi ba tun farkon shigarsa Hauza Ilimiyya, ta yiwu nan gaba ya zama kamar misalin Mirza Ali Muhammad Bab wanda yayi da’awar na’ibantakar Imam Mahadi (a.s) sai ya zamanto ya bace ya kuma batar da mutane, shi ne wanda ya haifar da kungiyar Baha’iya ta wannan zamani domin yakar shi’anci, ko kuma ta iya yiwuwa ya zama kamar Shaik Muhammad bn Abdul-Wahab Najadi wanda ya assasa mazhabar wahabiyanci masu kafirta musulmai, ta yanda yake kafirtar da duk wanda bai bin mazhabarsa shin daga shi’a yake ko daga sunna kamar misalin Ash’arawa da sufaye babu banbanci.
Muhammad bn Abdul-wahab ya kasance cikin dangi ma’abota ilimi mahaifinsa yana daga cikin manyan shehunai haka ma dan’uwansa, kai farkon ma wanda ya fara inkarin mazhabar sa ya bayyana shi a matsayin bataccce mai batarwa shi ne dan’uwansa Salman bn Abul-wahab, wannan Magana tabbatacciya ce a muhallinta.
Bai buya ba cewa yan mulkin mallaka suna cin amfanin misalin wadannan dalibai cikin Hauza Iimiyya, domin su batar da mutane da rusa addini da mazhaba da sunan addini da mazhaba, kadai suna daukar su aiki da jan hankalinsu da kudade masu yawa da mata da alfarma da mukami, sakamakon raunin da suke da shi da karkacewar tunani da yake cikin badininsu.
Babbar musiba itace sakamakon hura wutar fitina da bata yan mulkin mallaka kamar misalin kasar birtaniya, sai ka samu kowacce da’awa ta samu mabiya, da’awar ta yadu cikin mutane kamar ruruwar wuta cikin kirare, kamar cikin wannan lokaci da muke ciki ta yanda muke iya ganin wahabiyawa yan sunna da baha’iyawa daga shi’a basu gushe ba suna taka rawa cikin bata da batarwa, asasin wadannan mazhabobi biyu na bata daga daliban ilimi ya kasance, wannan shi ne abin da muke jin tsoro cikin nan gaba a hauzozin ilimi, lallai da sunan addini za ka samu wani daga dalibai ya assasa sabuwar mazhaba ya rarraba kawukan al’ummar musulmi, ya shuka fitina da munafunci da sabani da rigima da kiyayya da gaba tsakanin musulmai, wanda wannan shi ne kololuwar abin da makiya addini yan mulkin mallaka suke fata, daga mummunar siyasarsu ta nuna kiyayya da suke cewa (raba kansu sai ka mallake su) sai suna mulkin kasashen  musulmai ta hanyar rarrabawa kawukansu da yada sabanin cikinsu da rigingimu na zubar da jini domin su  samu iko kansu, da iko kan dukiyoyinsu, a irin wannan hali ni da nake  dalibin ilimi yaya zan amintar da kaina da makoma ta, yaya zan katangeta da samun lamini kan tsiranta a nan gaba.
Ya zama dole a yi tunani da sanya wayewa da taka tsantsa, sannan kuma muyi riko da nauyaya guda biyu littafin Allah da tsatso tsarkaka (a.s) lallai matukar munyi riko da su ba zamu taba bata ba har abada kamar yanda manzon Allah (s.a.w) ya bada labari cikin hadisin Saklaini wanda bangarori biyu suka nakalto shi.
Ya zama dole a koma komawa ta gaskiya zuwa ga Ahlil-baiti ma’asumai (a.s) lallai zancensu haske ne, lamarinsu shiriya ne, wasiyyarsu tak'wa ce, aikinsu alheri ne, al’adarsu ihsani.
Idan kana son sanin makomarka da gobenka kan hasken makarantar Ahlil-baiti (a.s) to abin da ya zo daga sarkin mumi Ali (a.s) a littafin Nahjul Balaga ya isar maka:      
 (إذا إشتبهت عليكم الأمور فيعرف أواخر الأشياء بأوائلها).
Idan al’amura suka rikice muku to ana sanin karshen abubuwa daga farkonsu.
 Wannan yana daga cikin mafi kayatarwar abin da ake fadi cikin sanin goben da aka jahilta, lallai kamar yanda yake a cikin ilimin mandik (natija na biye mafi karancin mukaddima) duk sanda dukkanin mukaddimomi suka kubuta daga sugrayat da kubriyat a wannan lokaci natija za ta kasance lafiyayya kubutatta ingantacciya da za a iya dogaro da ita da jingina gareta, za kuma a kafa hujja da ita a mukamin kawo hujja. 
Duk wanda yake son sanin karshen karatunsa da neman ilimin muslunci da yake yi, da kasantuwarsa mai neman ilimin don samun tsira, sannan ya kuma kasance malami na Allah da yake shiryar da bayi, kadai zai san hakan tun ranar farkom shigarsa Hauzar ilimi.
Me ya sanya shi bari garinsa da zuwa wata kasa mai nisa don neman ilimi me ya sanya ya zabi karatun Hauzar ilimi mai albarka, me yake nema da wannan karatu da yake da koyarwa da wallafe-wallafe da tabligi, da dukkanin abin da yake cikin sha’anin malaman addini cikin jama’a, shin ya sanya mafara da manufa ga Allah matsarkaki kuma don shi
 (إنّا لله وإنا إليه راجعون)
Daga Allah muke gare shi za mu koma.
Ko kuma dai don duniya da tarkacenta da alfarma da mukami da riya da alfahari yake yin karatun. 
Bai buya ba cewa yawancin daliban Hauza daga manisantan garuruwa da kasashe suke zuwa sun bar Ahalinsu da iyalansu don neman ilimi, sun yarda da talauci da bakunta da radadi da bakin ciki, dukkanin hakan domin su kasance makamai na Allah, su koma ga mutanensu domin gargadarsu dammaninsu su gargadu, kamar yanda Allah matsarkaki cikin littafinsa mai cike da hikima mai girma.
Ta yanda musulmai suka kasance farko-farkon muslunci da cikin zamani annabi mafi karamci, dukkaninsu suna fita zuwa jihadi saboda kaunar jihadi da shahada, sai matsarkaki madaukaki ya ce: 
﴿وَمَا كَانَ الْمُؤْمِنُونَ لِيَنفِرُوا كَافَّةً فَلَوْلا نَفَرَ مِنْ كُلِّ فِرْقَةٍ مِنْهُمْ طَائِفَةٌ لِيَتَفَقَّهُوا فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُوا قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُوا إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ﴾.
Bai kamata dukkanin muminai su fita jihadi ba saboda haka me zai hana wata jama’a daga kowanne bangare ba zasu rage a gid aba domin su nemi ilimi cikin addini su gargadi mutanensu iadan sun dawo gare dammaninsu sa gargadu.
Idan Allah aka nufa, lallai shi yayiwa wadanda suke jihadi cikin tafarkinsa alkawari da cewa tabbas zai shiryar da su zuwa ga tafarkinsa madaidaici, da kuma tabbatar da diga-digansu
﴿وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ﴾.
Kuma wadanda suka yi kokari don neman yardarmu tabbas zamu shiryar dasu tafarkinmu lallai Allah yana tare da masu kyautatawa.
Idan niyya ta kasance ta gaskiya tsarkakka, abin nufi da neman ilimi shi ne neman kusancin Allah matsarkaki, ya kuma kasance mai kira zuwa ga tafarkin ubangijinsa da hikima da kyakkyawan wa’azi, da kuma jayayya da abokin rigima da wacce tafi kyawu, wannan shi ne abin da ake nufi da kyakkyawan karshe a dunkule, saboda ana sanin karshen abubuwa ta hanyar farkonsu.
Duk wanda ya kasance mai komawa ga Allah kamar yanda Ibrahim (a.s) ya kasance cikin kiransa zuwa ga hajji
 (هلّموا إلى الحج) 
Ku taho ku taho zuwa ga hajji.
Kumar kamar yanda shugaban shahidai ya kasance cikin kiransa ranar Ashura 
(هل من ناصر ينصرني) 
Shin akwai wani mai taimako da zai taimakeni.
Lallai kiransu su biyun kira ne na Allah da annabta, ku amsawa Allah da manzonsa idan suka kira ku zuwa ga abinda zai raya ku.
Umar Alhassan Salihu
Faroukumar66@gmail.com
+2348162040719
+989196659359

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: