bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      21:38:47
Lambar Labari: 260
Gabatarwa:
Da Sunan Allah mai Rahama mai Jin Kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa. Allah Subhanahi wa Ta’ala ya halicci halittu daban-daban masu tarin yawa, amma duk a cikin halittunsa bai halicci wanda ya girmama ya karrama kamar dan adam ba. 
Lallai dan adam halitta ce da Allah ya yi matukar karramawa tare da girmamawa ya kuma yi masa matsayoyi masu tarin yawa, sai dai duk da irin wannan karamcin da matsayoyin nan da aka yi masa, za ka same shi a wani janibin na halilittarsa yana da rauni da gajiyawa, dan karamin misali a nan shi ne cewa za ka ga ‘ya’yan sauran dabbobi irinsu tinkiya ko saniya zai yi wahala su wuce minti talatin daga haihuwarsu ba tare da sun iya mikewa su tattaka da kafafunsu ba, kai har da iya yin ‘yan tsalle-tsalle. Amma yayin da ka kalli dan adam sai ka samu cewa saboda tsananin rauninsa daga lokacin haihuwarsa sai a kwashe kusan shekara daya zuwa biyu ana dawainiya da shi kafin ya fara kokarin iya zama, rarrafe, tsayuwa sannan har ya kai ga iya tafiya, wanda dukkan wadannan matakan da yake bi, za ka samu yana da bukatuwa ne ga wani wanda zai hidimta da tallafa masa.
Mene Ne Ma’anar Hidima:
A takaice hidima tana nufin: Yunkurawa wajen yin wani aiki ko fuwace wani abu da nufin amfanar da wani abin halitta ko wasu jama’a.  
Karin Bayani Dangane Da Ma’anar Hidima:
Wato abin da ake son mai karatu ya fahimta a nan shi ne cewa: Duk wani yunkuri da wani aiki da sadaukarwar da wani mutum zai yi ko ya samar domin amfanin waninsa – shin wanin nan nasa mutum daya ne ko jama’a da yawa ne ko kuma sauran halittu ne ma – su wadannan duk sun shigo cikin abin da ake kira da hidima.
Don haka za mu iya cewa kowane nau’i na aiki ga jama’a, shin ilimi ne mutum yake da shi sai ya sadaukar da ilimin ta hanyar koyar da yara ko manya maza ne ko mata da dai sauran jama’a domin su amfana, ko kuwa wata wadata ce ta kudi da dukiya yake da ita ya dauki wani bangare na dukiyar nan ya tallafa wa jama’a, kamar ya gina masu makaranta, ko dakin shan magani, ko gyara wata hanya a unguwa, ko gina rijiya da dai sauransu, ko kuma yana da fuska ne a idon mahukunta da masu mulki, sai ya yi amfani da wannan damar ya nema wa wasu matasa karatu a makarantu ko aikin yi a ma’aikatu, da dai sauransu; to duk wadannan su ma sun shigo cikin abin da ake kira da hidima.  
Kashe-Kashen Hidima:
1- Hidima wadda ake karbar lada (kudi).
2- Hidima wadda ba a karbar lada (kudi).
Amma mu a cikin wannan dan gajeren rubutun za mu mayar da hankali ne a kan hidima kashi na biyu, fa’idodinta, kwadaitarwar da ayoyin Qur’ani da hadisan Ma’asumai (as) suka yi a kanta da kuma sakamakon da ake sa ran wanda ya tsayu da yinta zai samu a duniyarsa da lahirarsa.
Lallai hidima kashi na biyu tana daya daga cikin muhimman abubuwa a addinin musulunci musamman a bangaren akhlak, wato mutum ya zama yana kulawa da mutane, taimaka masu gwargwadon iko da tausaya masu, jin cewa matsalar dan uwanka kai ma matsalarka ce, ta shafe ka kamar yadda ta shafe shi, yin himma wajen warware wani hali na kunci da wani dan uwanka ya shiga, musamman ma a ce kana hidimta wa muminai ne da salihan bayin Allah.
Idan muka koma cikin Qur’ani mai girma da ruwayoyin Ma’asumai (as) da sirarsu da ta waliyyai, za mu samu cewa bayan sauke wajibai, to babu wani lamari da ya kai hidimta wa al’umma kima, matsayi da kusantar da bawa zuwa ga Allah Ta’ala. 
Ayoyin Qur’ani Mai Girma Masu Magana A Kan Hidima Ga Halittu:
Kafin mu fara kawo ayoyin Qur’ani mai girma, za mu so mu dan yi shimfida kamar haka; Al-Qur’ani mai girma ya yi nasiha tare da kwadaitarwa ga dan adam a kan ya kasance mai hidimta wa ‘yan uwansa ababen halitta raunana muminai da wasunsu. To sai dai Qur’ani mai girma ya yi amfani ne da kalmomi daban-daban wadanda suke ishara zuwa ga ita wannan kalmar ta hidima ko hidimtawa, kamar irinsu: albir (alheri) Ihsan (kyautatawa), Ikram (girmamawa ko karramawa), Infak (ba da tallafi), Kardh (ba da rance), Ta’awun (taimakekeniya), Isar (Sadaukarwa) da dai sauransu, wadanda da sannu za mu je ga ayoyin masu albarka wadanda suka yi magana a kan hakan.
Allah subhanahu wa Ta’ala yana cewa:
بسم الله الرحمن الرحيم : [لَيْسَ الْبِرَّ أَنْ تُوَلُّوا وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ وَآتَى الْمَالَ عَلَى حُبِّهِ ذَوِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ وَالسَّائِلِينَ وَفِي الرِّقَابِ….] (سورة البقرة : آية 177).
 Tarjamar Ayar: Alheri ba shi ne (a lokacin sallah kadai) ku juyar da fuskokinku bangaren gabas da yamma ba, sai dai alheri shi ne mutum ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littafin (Allah) da Annabawa, sannan ya ba da dukiya alhali yana sonta ga makusanta da marayu da talakawa da wanda yake a kan hanya da masu roko da kuma ‘yanta bayi, kuma ya tsayar da sallah ya kuma bayar da zakka… (Sura: Albakara, aya 177).
Ya zo a tafsirin al-Amsal cewa: Albir: Tun a asali yana nufin yalwatawa, sannan aka yi amfani da kalmar a kan nau’oin alheri da kyautatawa, domin mutum ta hanyar kyautatawa ne yake fita daga da’irar zatinsa, domin ya samu yalwatuwa har ya kai ga cewa alherinsa da kyautarsa su iya kai wa ga sauran jama’a.
Sannan: Albar, (wato idan aka yi wa kalmar wasalin sama), aikatau ne na albir, wanda shi kuma a asali yana nufin sahara da kuma wuri yalwatacce; to amma sai a ka yi amfani da ita a kan mai kyautatawa, bisa la’akari da ainahin jawabin da ya gabata.
Sannan sai Qur’ani ya yi bayanin mafi muhimmancin asulla na alheri da kyautatawa, wadanda suke guda biyar, yayin da ya ce: "Sai dai alheri shi ne mutum ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littafin (Allah) da Annabawa”.
Wannan kuma shi ne asasi na farko: Wato imani da mafara, da makoma, da kuma malai’ku wadanda suke ‘yan sakon Allah, sannan kuma sai tsarin Ubangiji, sannan sai Annabawa wadanda suke kira zuwa ga wannan tsari din. Lallai imani da wadanda al’amuran yana haskaka samuwar mutum, haka ma yana samar masa da wani karfi wanda zai dinga tunkuda shi zuwa ga gina kai da aikata kyawawan ayyuka.
Sannan ci gaban ayar yana magana ne a kan infaki: Shi ciyar da dukiya ko infaki ba al’amari ne sassauka ga kowa da kowa ba, musamman idan lamarin ciyar da dukiyar ya taka wani matsayi wato ma’ana ya zama ya kai ana batun sadaukarwa ne. Domin kuwa son dukiya wani abu ne samamme a cikin zukata sai dai yana a mataki-mataki ne. Kuma lallai fadin Allah cewa: "Ba da dukiya alhali yana sonta”, yana nuni ne a kan wannan hakikar. Sai dai su wadancan (muminan) suna ciyar da dukiyarsu ne, tattare da cewa suna son abarsu, ba don komai ba sai  domin neman yardar Allah Ta’ala.
(Kuma wani abin karin muhimmanci a cikin ayar dangane da yin alheri ko hidima ga al’umma, sai ya zama Allah subhanahu wa Ta’ala), A mataki na farko ya fara da ambatar makusanta, sannan marayu da talakawa, sannan sai wadanda bukata ta bijiro masu ta dan lokaci kadan, kamar matafiyin da ya shiga yanayi na bukata (misali guzurinsa ya kare, alhali yana nesa da garinsa), sannan daga baya sai ayar ta ambaci masu roko, wanda hakan yake nufin cewa ba dukkan mabukata ne suke yin roko ba .
Wannan aya mai girma, za mu ga irin yadda ta muhimmantar da yin alheri ko taimakawa da hidimtawa raunana, farawa daga makusanta har zuwa matafiyin da guzurinsa ya kare. Kuma wani babban abin lura a cikin wannan ayar shi ne cewa, irin yadda Allah Ta’ala ya gwama yin alheri da yin imani da Shi (s.w.t.a), ranar lahira, mala’iku, littafin (Allah) da Annabawa, wanda hakan yake kara fito mana da girman yin alheri da matsayinsa a wajen Allah Ta’ala.
Za mu ci gaba insha Allah.
Jamil Yusuf.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: