bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      21:41:45
Sama da Qasa sun yi Kuka saboda kisan Husain (A.S). Al-Hafiz Abu Na'iim ya faxa a cikin
Lambar Labari: 261
                               Da sunan Allah mai Rahama mai jin qai!!!
 
"Wanda idanunsa ya zubar da Hawaye a kan kisan Husaini, ko ya xigar da xigo xaya garemu, Ubangiji Maxaukakin Sarki zai sanya shi a Aljanna".

Malaman da suka fitar da wannan Hadisin:
1- Fadhaa'ilus-Sahaabah – Ahmad bn Hanbali: 2/675, Hadisi na 1154, ko wani bugun 3/132, Hadisi na 1118.
2- Wasiilatul-aamaal – Al-allaamah Baakathir Al-Hadhramiy, shafi na 60.
3- Rashfatus-Saadiy na Al-Allaamah As-sayyid Abubakar Al-Hadhramiy shafi na 47, wanda aka buga a Al-Qahira.
4- Da wasu litattafan masu yawa na Ahlus-Sunna.


Mecece ranar Ashura?
 
Ranar Ashura rana ce ta baqin ciki ga dukkanin Musulmi na gari, rana ce ta shiga qunci,  rana ce ta vacin rai, rana ce ta takaici. Rana ce ta tausayi da juyayi ga Iyalin fiyayyen halittu Manzon girma Annabi Muhammad (s.a.w), sakamakon irin gallazawar da aka yi musu na tsare su da aka yi a Dajin Allah babu Ruwa babu Abinci, wanda daga qarshe aka yi musu kisan gilla.
 
Dukkanin Manyan Malamai magabata ba bu wanda ya sava akan cewar an kashe Imam Husaini xan Aliyyu xan Abu Xalib (xan Faxima ‘yar Manzo Allah) da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabin da na Husainin a ranar goma ga watan Muharram. Watan da Hausawa suke kira da watan CIKA-CIKI, kuma suka xauki ranar goma ga watan ranar cika-ciki. Har sukan ce duk wanda bai cika cikin sa ba Ubangiji zai cika masa da wuta Ranar Al-Qiyama.
 
Bayan xora Yazidu xan Mu'awiya xan Abu Sufyan akan Halifancin Musulmai, ya nemi Manyan Sahabban Annabin da su zo su yi masa "Mubaya'a" a kan sun yarda shine Shugaban Musulmin Duniya (wato shine zai ci gaba da bada Doka ta Addinin Musulunci ga dukkan Musulmai). Wasu don tsoron Kisa sun je sun yi Mubaya'ar, wasu kuwa ba su je ba, daga cikin waxanda suka qi yin Mubaya'ar akwai Imam Husaini (A.S), akwai Abdullahi xan Umar, akwai Abdullahi xan Abubakar da wasu daga cikin manyan sahabbai a garin Madina.

Lokacin da Yazidu ya matsa sai Imam Husaini (a.s) ya yi masa Mubaya'a, sai Imam Husain (A.S) yace masa: "Mutum kama ta (Xan Gidan Annabta) ba zai yiwu ya yi wa Fasiqi kamar ka Mubaya'a" ba (wanda babban Malami Ibn Kathir yace: "abu ne sananne cewa; Yazidu ya yi fice wajen shan Giya, kaxe-kaxe, waqe-waqe, wasa da karnuka, wasa da Birai da sauran ayyukan savo da kowa yasan shi dasu. Ya ci gaba da cewa; babu rana xaya da Yazidu ya wayi gari ba a buge da Giya ba. Wanda sanadin mutuwar sa hawa ya yi kan Birinya yana tsalle da ita ta faxo da shi ya karya kwankwaso . . . . . Hakanan Mu'awiya ya yi Hajji ya yi qoqarin karvar Bai'a daga mutanen Makka da Madina, Abdullahi xan Umar ya qi yace: Baza muyi Mubaya'a ba ga wanda yake wasa da Birrai da Karnuka, kuma yake shan Giya yake bayyana Fasiqanci, menene hujjar mu gurin Ubangiji? Ibn Zubair yace: "Ba bu biyayya ga abin Halitta a kan savawa Mahalicci, bayan ya gama vata mana Addinin mu), wanda daga qarshe Imam Husain ya yi hijira ya bar garin Madinah ta Kakansa ya nufi Makkah, yana cikin Xawafi sai ya lura da cewa Yazidu ya turo a kashe Shi, nan take ya fita daga cikin Haramin Allah don gudun kada a keta Hurumin Haramin a zubar da jini a cikin sa. Ya nufi Kufa wato Qasar Iraqi shi da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabi (s.a.w) da Sahabban sa, inda Yazidu ya turo rundunar Yaqi ta riske su cikin Sahara akan lallai Imam Husain (A.S) ya miqa wuya. Anan ma ya kuma maimaita kalmar sa: "Misli laa yubaya'a Misli Yazid", Mutum kamar ni ba zai yiwa irin Yazidu biyayya (Mubaya'a) ba.
 
Anan ne suka tsare su kusa da kogin Furat wanda Ubangiji yake cewa: "wa Huwallazii marajal-Bahraini haza azbun FURATUN wa haza milhun ujaj …." Har tsawon kwana ukun suka hana su shan wannan Ruwan Furat xin, suka kasance babu Ci babu Sha har Yara suka fara mutuwa saboda Nonon iyayensu ya qafe. A kwana na goma ne Dakarun Yazid (L.T.A) suka farwa wannan tawaga ta Imam Husaini wacce bata wuce mutum 70 ba, wacce take xauke da Maza da Mata, Manya da Qananan Yara. A ciki akwai sayyidah Zainab 'Yar Faximah (A.S) 'Yar Annabi Muhammad (S.A.W), akwai 'Yayan Imam Hasan (A.S) Xan Faximah (A.S), akwai 'Yayan Imam Husaini xin, Aliyyul-Akbar, Aliyyul-Asgar, haka nan akwai xan Imam Ali Abul-fadl Al-Abbas, da Sukaina wacce Qarama ce, bayan kisan waxanda aka kashe, ta kasance tana yawaita Kuka tana kiran "Ina Babana?" sai Yazidu yake tambaya Kukan me take yi aka faxa masa, shine ya sa aka kawo ta aka xauko kan Imam Husaini akan farantin Tasa. Yace Yarinya me kike cewa tace " Ina Babana?" Yace "kinga Baban naki" ya xaga yankin da aka rufe Kan Imam Husaini da shi tana ganin sa nan take tayi wata qara bata sake ko shurawa ba ranta ya fita. Akwai Jariri Xan Imam Husain yana ta suma saboda tsananin Yunwa da Qishi ya xauke shi yaje yace su ma bashi ruwan da kansu kada su zaci shine yake son sha, nan take aka sami wani la'antacce ya harbi wannan Jariri da Kibiya.
 
Bayan sun kashe Imam Husain (A.S), sun yanke kansa sun yi sukuwa da Dawaki a kan Jikin sa mai tsarki, sun qone Hemomin da ragowar Mata suke da Yara, sannan suka bi suka kama ragowa suka sanya musu Sasari suka tisa su a qasa har wajen Yazidu. Wanda a ciki akwai Zainab 'Yar Faximah (A.S).
 
An ruwaito daga littafin Musnad Ahmad (3/242, 27/97), da Mu’ujamul-kabiir na Xabaraniy (3/106, Hadith: 2813), da Tarikhu Ibn Asakir (14/197)da wasunsu, daga Anas xan Malik yace: "Mala’ikan da yake kula da ruwa ya nemi izini daga wajen Ubangjinsa yana son ya ziyarci Annabi (S.A.W), sai akayi masa izini, a ranar Manzo (S.A.W) yana xakin Ummu Salamah ne: sai Annabi (S.A.W) yace mata: ya Ummu Salamah ki tsaya a bakin qofa, kada ki bar kowa ya shigo mana: tana nan a bakin qofar sai ga Husaini bn Aliy (A.S) ya shigo. Sai ya buxe qofar ya shiga, anan Annabi (S.A.W) ya rungume shi yana ta sumbatar sa, sai Mala’ikan yace: kana son sa? Yace e, sai yace: al’umarka ce za ta kashe shi,  kanaso na nuna maka gurin da za’a kashe shi? Sai Manzo yace na’am: sai ya danqo danqi xaya na qasar gurin da za’a kashe shi ya nuna masa sai ga qasar ja, Ummu Salamah ta karva ta sanya ta cikin tufafin ta. Thabit yace: sai muka zamo muna cewa Karbala ce".

Haka nan cikin littafin tarihi na Ibn Asakir (14/190, 192), da wanin sa, daga Dawud, yace: "Ummu Salamah tace: Husaini ya shiga wajen Manzon Allah sai ya razana, Ummu Salamah tace: menene ya same ka ya Rasulallah? Sai yace: Jibrilu ne ya bani labarin cewa wannan Xan nawa za a kashe shi ne, Allah ya yi fushi mai tsanani da waxanda suka kashe shi".
 
 
FARKON  KUKA A KAN KISAN  HUSAINI (A.S) ANNABI MUHAMMAD (S) NE

1- Farkon wanda ya fara yin kuka da ranar Ashura tun kafin ma tazo shine Manzon Allah (S.A.W). An fitar cikin littafin Mustadrak alas-sahihaini da Tarikhu Ibn Asakir: Ummul-fadhli bintul-haarith ta ce: ……… yayin da na shiga gurin Manzon Allah (S.A.W) sai naga idanuwansa suna ta zubar da hawaye, sai nace: ya Annabin Allah Babana da Babata fansa a gareka me ya faru? Sai yace: Jibrilu (A.S) yazo mini ya bani labarin al’umata za ta kashe Xana wannan, sai nace wannan? Sai yace: "Na'am, kuma ya zo mini da qasa daga qasarsa Ja" (Mustadrak alas-sahiihain na Haakim: 11/135, Haakim yace: wannan Hadisin Ingantacce ne abisa sharaxin Buhari da Muslim, amma basu fitar da shi ba).
 
2- Imam Aliy xan Abu Xalib baban Husainin shi ma ya yi kukan ranar Ashura tun kafin ta zo. An fitar cikin littafin Sawaa’iqul-muhriqa: Imam Aliy ya bi ta Karbala a hanyar sa ta zuwa Siffin, sai ya tsaya ya kafa takobin sa a qasar gurin yake cewa: anan ne za’a kashe mazajen su, anan ne jinin su zai zuba, anan ne za’a qona hemomin su. A tare da shi akwai Malikul-ashtar da Ammar bn Yasir, sai Malik  yace: ya Shugabana su wanene? Sai Imam yace: sune xana Husaini. Sai mai littafin Sawa’iq yace: anan Imam Aliy ya yi kuka ya yi kuka har sai da qasar gurin ta jiqe da hawayen sa. (Sawaa3iqul-muhriqah ta Ibn Hajar Al-haithamiy: 2/566).

3- Sama da Qasa sun yi Kuka saboda kisan Husain (A.S). Al-Hafiz Abu Na'iim ya faxa a cikin Dala'ilun-nubuwwah (3/211, ko a wani bugun 2/147): Daga Asbag bn Nabaatah ya ce: "Mun je wajen qabarin Husain tare da Aliyyu sai yace: a nan ne wajen ya da zangonsu, a nan ne za su kafa Hemominsu, a nan ne Jininsu zai kwaranya, Samari daga Alayen Muhammad (S) za a kashesu a wannan Dajin, Sama da Qasa za su yi musu Kuka".
 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: