bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      21:49:29
Idan ma mun xauka waxannan maganganu a kan kuvutar waxannan Annabawa duk sun faru ne tabbas a ranar ta Ashura, to kamar yadda Hadisan baya da suka gabata
Lambar Labari: 262
Da sunan Allah mai Rahama mai jin qai!!!

An samu wasu kaxan daga cikin Malamai suna cewa: ana yin murna tare da Azumi da cika-ciki ne a wannan rana ta goma ga Muharram, don a irin wannan rana ne Allah ya halicci Annabi Adam (A.S), a sannanne ma Allah ya kuvutar da Annabi Musa (A.S) daga Fir’auna, a dai irin wannan lokacin ne Allah ya fitar da Annabi Yusufa (A.S) daga kurkuku ko rijiya, da dai irin waxannan maganganu.
 
Idan ma mun xauka waxannan maganganu a kan kuvutar waxannan Annabawa duk sun faru ne tabbas a ranar ta Ashura, to kamar yadda Hadisan baya da suka gabata suka tabbatar mana da cewa: tun kafin ranar Ashura (wato ranar da aka kashe Imam Husaini) ta zo Annabi (S.A.W) ya ke yiwa wannan ranar kuka, yana zubar da hawayen sa mai tsarki, yana takaici da baqin ciki da abin da zai faru. Tambaya ta anan ya kai Xan’uwa masoyin Annabi (S.A.W) shin da za a ce Manzon Allah ya kawo lokacin da aka yi wannan mummunan aiki na kisan gilla ga Iyalin Sa, a zaton ka Annabi (S.A.W) zai yi murna ne ko kuwa baqin ciki? Nasan dole amsar ka ita ce baqin ciki zai yi, don kuwa tun kafin ma abin ya faru yake zubar da hawaye yake baqin ciki, to ina ga ace ma yana duniyar?
 
Ka sani zuwan Annabi Muhammad (S) ya shafe dukkanin wani abu da wani Annabi yazo da shi a cikin tsarin shari'ar Musuluncin da Manzo (S.A.W) ya zo da shi, muna karvar dukkanin wani Hani ko Umarni, ko koyi daga Annabinmu ne Annabi Muahammad (S.A.W). Don haka abisa nassosin da suka gabata sun tabbatar da Annabi yana baqin ciki da wannan rana ne abisa haka dole ne muma mu taya Annabin mu baqin ciki da wannan bala’i da ya afkawa Iyalinsa, ko da kuwa an samu tarihi ya tabbatar da waxancan abubuwa na falala da suka faru a kan wasu Annabawan (A.S).
 

KAXAN  DAGA CIKIN  FALALAR  IMAM  HASAN  DA  HUSAINI

Manzon Allah (S) yana cewa akan Su:
1- Sune mafifitan dukkanin al’umar duniya, idan aka cire Manzo, Aliyyu, Faximah.
2- Sune shugabannin samarin gidan aljanna (domin daman babu tsofaffi a cikinta).
3- Suna daga cikin danginsa da basa rabuwa da Qur’ani har zuwa Alqiyama, al’uma ba zata vata ba idan tayi riqo da su.
4- Sune waxanda Kakan su yace akan su: Taurari amana ne ga halittun da suke doron qasa kada su vata. Ahalin gida na kuwa amana ne ga halittun dake  kan doron qasa kada su rarraba (Vata).
5- Haka nan suna daga cikin Ahalul-baitin da hawa jirgin ruwan su kuvuta ne, qin hawa kuma halaka ne. (ma’anar Hadisin anan shine Hasan da Husain suna daga cikin jikokin Annabi goma sha biyu da duk wanda ya bisu zai shiga Aljanna, wanda kuma duk bai bisu ba wutar Jahannama makomar sa, Allah ya kiyashe mu).
6- Sune Annabi . yake cewa: Ubangiji ka sani ina son su, don haka kaso su, kuma ina son duk mai son su.
 
Shin kana son Annabi da ‘yayan gidan sa kuwa?! Kana jin za ka ce kana son sune alhalin kana murna da ranar da aka yi wa jikokin Annabin kisan gilla?! Ko kuwa za ka ce kana son sune alhalin kana farin ciki da ranar da Annabi ya ke baqin ciki da ita?! Ko kuwa kana son sune alhalin kana cika cikin ka da abinci a ranar da ‘yayan Annabi suka kasance cikin yunwa da qishirwa?! Ko kuwa kai Annabin ka daban, ba Annabi Muhammad bane?!
 
Ka sani Musulunci ma bai yarda da Mutum ya cika cikin sa da abinci ko abin sha ba dam-dam. Allah Ta’ala yana cewa: "Ku ci ku sha kada kuyi varna haqiqa (Ubangiji) baya son masu varna” (A’araf:31). Anan wasu Malaman tafsiri sun nuna abin da wannan kalmar "varna” take nufi har da cika ciki dam-dam a qoshi.
 
Ka sani cewa Imanin Mutum ba zai tava cika ba, muddin bai so abin da Manzon Allah (S) ya ke so ba. Hakan ne ya sa Malamai suka yi bayani a kan sharaxan cikar  "SO” na gaskiya, sune:
1- Son abin da masoyi ya ke so da yarda da abin da ya yarda dashi.
2- Qin abin da masoyi ya qi da dukkan abin da bai yarda da shi ba.
3- Son masoyan sa da qin duk wanda yake gaba da shi.
4- Jivintar lamarin duk wanda ya jivinci lamarinsa, da gaba da duk mai gaba da shi.
5- Ka tsaya tsaiwar daka wajen taimaka masa, tare da bin abin da ya aikata, wato shine tafiya akan abin da ya tafi akai.
 
Malamai suka ce duk wanda ya sava waxannan al’amura to qarya yake a cikin soyayyar sa, sai mu gasgata faxin wani mawaqi a kansa da yake cewa: "Lau kaana hubbuka saadiqan la axa’tahu li’annal-muhibba lil-habiibi muxii’uhu” ma’ana: "Da son ka ya zamo gaskiya to da ka bi abin son naka, domin kuwa dukkanin abin da ake so ana yi masa biyayya ne”. Idan ka duba cikin littafin "Ajwibatul-mufiidah" za ka taras da waxannan sharaxan na "so”.
 

AZUMIN TASU'A DA ASHURA'

Malamai na gari sun karvo daga jikokin Ma’aiki (S.A.W) cewar; Mustahabbi ne a yi Azumi ranar tara ga watan Muharram (Tasu’a) don xanxanar yunwa da qishirwa don kwaikwayon Jikokin Annabi da suka kasance cikin yunwa da qishirwa a wannan lokacin. Sannan a ranar goma ga watan (Ashura) ana kame baki ga barin ci da sha har zuwa bayan la’asar (domin zuwa bayan la'asar xin ne wannan qishirwa da yunwa suka qare, suka taras da Liyafa daga Kakanninsu a Aljanna Maxaukakiya).

Haka nan a wata ruwayar an so mutum ma ya Azumci gaba xayan watan, domin azumtar watan baki xaya yana kiyaye mutum daga dukkanin munanan abubuwa.

Amma yin Azumi ranar Tasu'a da Ashura ta fuskar neman tabarruki HARAM ne

Allah ka samu daga cikin masoya Annabi (S.A.W) da Ahlul-baiti (A.S), masoya na haqiqa, ka kuma tashe mu tare da su. As-salaamu alal-Husain, Wa- alaa Aliyyib-nil-Husain, Wa-alaa Aulaadil-Husain, Wa-alaa  Ashabil-Husain, As- salaamu Alaikum wa- Rahmatullahi wa- Barakatuh.




comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: