bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      21:49:29
Wannan shine karshen tafiyar Manzon Allah (s.a.w) da ya yi da kanshi sannan ya sauka a wurare daban-daban inda musulmai suke
Lambar Labari: 263
ME YA GUDANA A RANAR GHADIR KUM?
Da sunnan Allah Mai Rahama mai jin kai, Tsira da Amincin Allah sukara tabbata ga Shugaban halitta Manzon mu Muhammad dan Abdullahi (A.S.W) da iyalen gidansa tsarkaka wadanda Allah (T.A) ya tsarkake su tsarkakewa.
Sannan abu ne kafin wafatin Manzon Allah (s.a.w)  a shekara ta goma bayan hijira, gaba daya kasashen larabawa sun karbi sakon Manzon Allah (s.a.w) wato addinin musulunci. Manzon Allah (s.a.w) a wannan shekarar ya yi tafiya zuwa aikin hajji. Wanda akafi sani da hajjin bankwana. A nan zamu danyi Magana ne akan wannan hajjin bankwana din muga shin me ya faro a wannan tafiyar ta shi musamman wajen dawuwa daga wannan aikin hajjin.
   Wannan shine karshen tafiyar Manzon Allah (s.a.w)  da ya yi da kanshi sannan ya sauka a wurare  daban-daban inda musulmai suke kuma ya yi musu jawabi. Annabi a wadanan jawaban na shi abinda yafi maida hankali kanshi shine batu akan sanar da mutane wasiyyinsa har zuwa lokacin da zai bar wajen mutanen. Saboda haka ne ma aka lazimtawa mutane taruwa a wannan tafiyar a duk inda Annabi ya sauka, domin ya sanar da mutane wanda zai gajeshi a bayansa domin su yi masa mai’a kuma su yi biyayya a gareshi.
   A wannan tafiyar a kuma wadannan yanku nan wurare biyar aka yi jawabi: na farko: Rana ta 7 ga zulhijja ( yaumu tarwiyya ) a Makka(1) . Na biyu: Rana ta 9 zulhijja  ( A wajen Arfa )(2) . Na uku kuma  Rana ta 10 ( Idul kurban ) a Mina(3) . Na hudu kuma Rana ta 11 zulhijja shima a Mina(4) . Sai kuma na biyar  Rana ta 18 zulhijja a Ghadir Kum.
  GHADIR KUM; WURIN DA AKA NASABTA IMAMU ALI (A.S) A MATSAYIN MAGAJIN ANNABI (S.A.W) RANAR 18 GA WATAN ZULHIJJA HIJIRA NADA SHEKARO 10 DAI-DAI WADAI DA.
   A hanyar dawuwa daga Hujjatul wada ne ( wato hajjin mankwana ) a ranar 18 ga watan zulhijja, a yarin Manzon Allah (s.a.w) ya sauka wani wuri da ake kiranshi da suna Ghadir kum. A wannan wurin ne musulman da suka taho daga Madina, Iraki da kuma Yaman domin sauke aikin hajjin su daga Makka suke sauka, sannan mararrabar hanya ce wacce kowa ke kama hanyar zuwa garinsu. A wannan wurin ne aka yiwa Manzon Allah (s.a.w) wahayi, ayar da tazo a suratu Ma’ida aya ta 67:
 {والله يعصمك من الناس ان الله لا يهدى القوم الكافرين. يا أيّهاالنبيّ بلغ ما أنزل اليك من ربّك, وان لم تفعل فما بلّغت ر سالته}
{Ya kai wannan Annabi ka isar da abin da ya sauka daga Ubangijinka, idan ba ka isar ba kamar ba ka isar da aiken da ya yi maka ba, kuma Allah ne zai kare ka daga mutane, Tabbas Allah baya shiryar da mutane kafirai}(5) .
    Manzon Allah (s.a.w) saboda isar da sakon Ubangijinsa yasa aka tsayar da a yarin a wannan wurin. A nan dai wurin yasa aka tsaya sannan aka jira sauran a yarin da basu karaso ba suka karaso wurin.
  Manzon Allah (s.a.w) a ranar Ghadir, ya yi huduba a wannan rana kamar yadda Ahlussunnah suka ruwaito: { kamar yadda ya zo a Dabri da isnadinsa daga Huzaifa bn Asidil Gaffari ya ce: Lokacin da Manzon Allah (s.a.w) ya dawu daga Hajjin bankwana ya ce: Ya ku mutane! Tabbas Ubangiji shine majibincina ( shugabana ) Ni kuma ni ne majibincin muminai ( shugaban muminai ), kuma ni ne na fisu cancanta  a kankin kansu, To duk wanda na kasance shugabansa to wannan ma shugabansa ne- wato yana nufin Aliyu (a.s). Ya Allah ka taimaki duk wanda ya taimake shi ka kuma yi gaba da duk wanda ya yi gaba das hi…}}(6) .
   Lokacin da jawabin Manzon Allah (s.a.w) ya zo karshe, sai Mala’ika Jibrilu ya sake sauka ya kuma zuwa da wannan ayar kamar haka: 
{ اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتى ورضيت لكم الا سلام دينا.}.{A yau ne na cika muku addininku kuma na cika muku ni’imata a gareku kuma na yardar muku addinin muslunci shine addini }(7) . Wannan jawabin da Manzon Allah (s..a.w) ya yi yana karfafa waccan ayar ta suratul Ahzaba.
   Domin tabbatar da hadisin Ghadir, da farko dai hadisin Ghadir hadisi ne mutawatiri kuma yanada hukuncin a wajen Ahlussunnah, saboda haka zamu iya tabbatar da cewa hadisin Ghadir a mahangar Ahlussunnah haidisi ne mutawatiri. Maruwaita hadisin shi’a da sunna sun tabbar da shi a matsayin hadisi mutawatiri: Hadisi mutawaturi yana nufin daga labarin da ake da yakini da shi sannan kuma wannan ruwayar an kawuta a wurare daban-daban ta yadda ba yanda za a yi idan karyace a ruwaito ta gurare daban-daban haka, haka kuma kai tsaye ba zai yiwu a iya karyata wannan ruwayar ba. Misalin haka akwai hadisin: ( Inni tarikun fikum sakalaini da ya zo a wurare daban-daban da sigar { Inni tarikun fikum sakalaini kitaballlah wa itrati sai a wuri daya da ya zo da sigar wa sunnati wanda malik bn Anas ne kawai ya ruwaito shi a littafinsa na muwadda da wannan sigar wanda hakan yasa hatta da Ahlussunna suma basu karbi wannan ruwaya ba saboda hadisi ne maudu’i) amma Magana akan hadisin man kuntu maulahu hadisi ne mutawatiri saboda haka ba zai yiwu a karyata shi ba.
     Labari muwaturi ya wuce a ce baza a yi aiki da shi ba ko kuma a ce bashi da amfani, sannan labari muwaturi yankan shakku ne a ruwaya, wannan shine abinda malaman hadisi na Ahlussunnah suka yadda dashi, kuma suka tafi a kanshi, domin labari mutawaturi dai-dai yake da ayar kur’ani, duk wanda ya yi inkarin shi ya kafirta za kuma akalleshi a matsayin kafiri, saboda tabbatar da wannan magamar ga abinda Ibn Taimiyya ya rubuta: 
{ والكفرانما يكون بانكار ما علم من الدين ضرورة, او بانكار الاحكام المتواترة والجممع عليها و نحو ذالك:          Ya ce: Kafiri shine wanda yake yin inkarin wani ilimi na addini sannan ne, ko kuma yake inkarin wani hukunci mutawaturi wanda aka yi ijma’i akansa da kuma makamancin haka( 8) . 
  Ta wani bangaren hadisin Ghadir an ruwaito shi da yawan littattafan Ahlussunnah da kuma sunaye dayawa daga masana hadisan Ahlussunnah ta bangare daban-daban. Misali, Ahmad bn Hanbali a littafinsa ko musnadinsa, ya kawu silsila arba’in 40 akan hadisin Ghadir. Bayan ibnu Jarir ya kawu sanadi saba’in 70, da kuma Ibnu Akda, hanya dari da biyar ya kawu 105. Hakama Abu Sa’id Sajastani ya kawu hanya 120, da kuma Abubakar Ju’abi shima ya kawu hanya 125 akan wannan hadisin(9) .
    Wannan yana tabbar mana cewa Hadisin Ghadir mutawaturi ne. kuma wannan maudu’in ya haska mana da yawa daga cikin maruwaitan Ahlussunnah suna I’itirafin wannan hadisin na Ghadir kuma babu wani ishkali akan hakan(10). 
  Daga wannan hasken da muka samu ba zai yiwu a iya canza Hadisin Ghadir ba wai a ce Kalmar maula tana nufin Aboki,  Manzon Allah (s.a.w) a Ranar 18 ga watan zul hijja ya tara mutane da sunan zai sanar dasu muhimmin abu kawai sai ya sanar dasu cewa Aliyu (a.s) Abokinsa ne ko kuma ya sonsa wannan ya sabawa hankali, saboda haka tabbas wannan Kalmar ta maula a hadisin Ghadir na nufin shugaba ba wai Aboki ba.
  Akwai ruwayar hadisin wilaya ma da ya zo a wuri daban-daban daga Manzon Allah (s.a.w) kamar haka: { عليّ ولي كل مؤمن من بعدى, هو ولي كل مؤمن من بعدى, أنت ولي كل مؤمن من بعدى, أنت ولي كل مؤمن بعدى ومؤمنة, فانه وليّكم بعدى, ان عليّا وليكم بعدى, أنك ولي المؤمنين من بعدى, انه لا ينبغى أن أذهب الا وأنت خليفتى فى كل مؤمن من بعدى, فهو أولي الناس بكم بعدى,               
   Duk wanan sai ya zama ba wata manufa saita Abokantaka kenan? Akwai bayanai maban banta akan hadisin Ghadir tunma kafin ranar Ghadir din a wurare daban-daban da aka ruwaito a littattafan shi’a da sunna wanda suke yankan shakku akan Aliyu (a.s) shine Halifa bayan Manzon Allah (s.a.w). zamu dan dakata a nan sai a kasha na biyu zamuci gaba da Magana akan dalilan abinda ya faru ranar Ghadir Kum.
Anan zamu tsaya sai kuma a kasha na biyu inda zamu kawo dalilai akan hadisin Ghadir. Aminci ya tabbata ga wadanda suka ga shiriya kuma suka bita.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: