bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      22:07:37
Idan wata najasa ta canja zuwa wani abu daban mai tsarki to ta tsarkaka, kamar idan kare ya kone ya zama toka (to wannan tokar ba najasa ba ce).
Lambar Labari: 265
Rana
 20> (m.184) Rana tana tsarkake kasa da gini da abin da yake jikinsa na daga kofofi da kusoshi ko notuna da makamancinsu na daga abin da suke tabbatattu, bisa sharadin gushewar ainihin najasa daga gare su kafin ranar ta dake su, kuma ya kasance akwai danshi a jikin abin da ya najastun ta yadda bushewarsu za ta zama sakamakon dukan rana kai tsaye, ta yadda za a jingina bushewarsu ga ranar ita kadai.



Canjawa
 21> (m.196) Idan wata najasa ta canja zuwa wani abu daban mai tsarki to ta tsarkaka, kamar idan kare ya kone ya zama toka (to wannan tokar ba najasa ba ce). 
 
Ciratuwa
 22> (m.210) Idan jinin dan Adam ko jinin dabba mai jini mai gudana ya ciratu zuwa dabba maras jini mai gudana, kuma aka dauke shi a matsayin jininta, to ya tsarkaka (ka ga abin da kaska ko kudumus da makamancinsa na daga kwarin da ba su da jini mai gudana, suke sha daga jinin mutum ko jinin dabbar da ke da jini mai gudana, sannu-sannu har ya zama wani bangare na jininsu, to lalle wannan jinin ya tsarkaka). 

Musulunci
Idan kafiri ya yi furuci da kalmar shahada, ya zama musulmi kuma jikinsa da yawunsa da kakinsa da guminsa sun tsarkaka.

Bibiya
Bibiya ita ce tsarkakar wata najasa sakamokon tsarkakar wata najasar daban, shi ne kamar idan giya ta zama tsimi ko kunu, to tukunyar ma ta tsarkaka a daidai lokacin da giyar take zama tsimi a yayin da take tafasa. Haka nan kamar tsarkakar abin da ake wanke mamaci a kansa na daga dutse ko katako da kuma abin da ake suturce al'aurarsa da shi yayin yi masa wanka, haka ma hannun mai wanke shi, duk sun tsarkaka, bayan kammala wanka na uku. 
 
Gushewar Ainihin Najasa
 23-(m.222) Idan jikin dabba ya najastu da wata najasa ta ainihi kamar jini, ko kuma da wani abu najestacce kamar ruwa, to jikin nata yana tsarkaka da gushewar najasar daga jikinta, haka ma cikin jikin dan Adam kamar cikin bakinsa da hancinsa, da zarar ainihin najasar ta gushe to sun tsarkaka.

Tsarkake Dabba Mai Cin Gayadi
Bawali da gayadin dabbar da ta saba cin najasa (da aka fi sani a fikihu da jallal: wato dabbar da ta saba cin kashin mutum) najasa ne, irin wannan dabba tana tsarkaka da yi mata istibra'i ta hanyar hana ta cin bahayan har sai an tabbatar da ta tashi daga sunan mai cin gayadi. Kwanakin tsarkin suna sabawa gwargwadon sabawar dabbobin, bayaninsu dalla-dalla yana can a manyan lattafan fikihu .

Boyuwa Ko Nisantuwar Musulmi
Idan tufafin musulmi ko kwanonsa ko shimfidarsa ko makamancinsu suka najastu, na daga abin da ke karkashin kulawarsa da tasarrufinsa, sannan sai musulmin ya boyu (kamar kwana biyu ba ka gan shi ba ko ya yi tafiya ko ya nisanta) kuma a hankalce aka yi tsammanin ya tsarkake wannan abin da ya najastu, to (sai mu sanya cewa shi wannan musulmin ya tsarkake shi ba dole ba ne kuma mu tambaye shi don haka wannan abin mai najasa a wajenmu zamu yi mu'amala da shi ta abu mai tsarki kuma) ya tsarkaka.
Hukunce-hukuncen Alwala
 24> (m.242) Alwala tsarki ce ta shari'a, kuma ana iya yin ta a kowane yanayi, kuma akwai wasu yanayoyi da alwala take zama wajabi, daga cikinsu akwai salla.
 Wajibi ne wanke fuska da hannaye da shafar gaban kai da saman ko bayan kafafu a yayin alwala, haka nan wajibi ne a yi da nufin neman yardar Allah (S.W.T). Da a ce mutun zai yi alwala da wata manufa daban, kamar sanyaya jikinsa ko tsafta to alwalarsa ba ta yi ba.
 25> (m.243) wajibi ne a yayin alwala a wanke fuska tun daga mafarar gashin kai har zuwa karshen haba ta bangaren tsawo, da kuma wanke abin da babban danyatsa da danyatsan tsakiya suke rutsa shi ta bangaren fadi.
 26> (m.201) Wajibi ne a wanke hannun dama sannan na hagu, bayan an gama wanke fuska, tun daga mararrabar gwiwar hannu har zuwa karshen 'yanyatsu, abin nufi shi ne, wajibi ne a wanke fuska da hannu daga sama zuwa kasa, idan ya wanke sabanin haka to alwalarsa ta baci.
 27> (m.255) Bayan wanke hannaye wajibi ne shafar magabacin kai da danshin da ya rage a hannunsa.
 28> (m.257) Ya isar a yi shafa a kan gashin da ke gaban kai, ba dole ba ne a yi shafar a kan fata. Amma idan gashin kai ya kasance mai tsawo ta yadda ya sakko daga iyakacin inda ake shafawa, to wajibi ne ya shafi tushen kai, ko ya raba gashinsa biyu ya shafi fatar kansa.
 29> (m.208) Bayan shafar kai wajibi ne ya shafi doron ko saman kafafuwasa da danshin da ya rage, tun daga kan 'yan yatsu har zuwa doron kafa. Idan babu sauran danshin da zai yi shafa da shi a hannunsa, wajibi ne ya shafo ko ya goga daga sauran gabbansa na alwala, kuma bai halatta ya dakko daga wani ruwan daban dan yin shafa da shi ba. 
 30> (m.273) Alwala da ruwan kwace da kuma wanda ake kokwanton yardar mamallakinsa, haramun ne kuma ba ta inganta.
 31> (m.277) Ya halatta yin alwala da ruwan randuna da tankunan da suke shagunan da hotel da makamancinsu, idan dama an saba yin alwala da su, koda kuwa mai yin alwala ba mazaunin wajen bane,
 32> (m.283) Idan gabar da ba ta alwala ba ta kasance tana da najasa, wannan ba zai cutar da ingancin alwalarsa ba, sai dai wajibi ne ya tsarkake gabar da ke da najasa don yin salla.
 33> (m.289) Idan rarrabewa tsakanin ayyukan alwala ta tsawaita, ta yadda idan ya yi nufin wanke gaba ko shafa ta, a lokacin gabar da ya wanke ko ya shafa ta daga karshe kafin ya ci gaba har ta bushe to alwalarsa ta baci.
 34> (m.323) Ya haramta ga mai hadasi ya taba rubutun Kur'ani da kowace irin gaba ta jikinsa, ihtiyadi ne kada ya taba da gashinsa, sai dai babu laifi ya taba fassarar Kur'ani mai girma. 
 35> (m.325) Ya haramta ga mai janaba ya taba rubutaccen sunan Allah (S.W.T) da kowane yare aka rubuta shi, kuma ihtiyadi ne wajibi nisantar taba sunayen Annabawa da sunayen Imamai da Fadimatuz zahra'u (A.S). 
 36> (m.326) Idan mutum ya yi alwala ko ya yi wanka kafin shigar lokaci da nufin neman yardar Ubangiji to sun inganta, shin ya yi ta da nufin kasancewa cikin tsarki ko kuma shirin yin salla ko makamancinsu.
Masu Warware Alwala
 37> (m.329) Masu warware alwala su ne:- fitar bawali da gayadi da hutu, wadanda suka fita daga jikin mutum ta mafitarsu ta al'ada. Da bacci da ya rinjayi ido da kunne ko abin da yake gusar da hankali, kamar hauka da maye da suma, da kuma abin da yake wajabta wanka kamar janaba da istihala da haila. 
 38> (m.330-350) Idan ya kasance a sashin wasu daga gabban alwala akwai kurji ko rauni ko karaya, kuma babu bandeji a kansu, idan ya kasance babu cutarwa a gare shi wajen yin amfani da ruwa, to ya wajaba a gare shi ya yi kamar yadda ya saba.
 Idan kuma wankewar da ruwa za ta cutar da shi, to ya yi shafa a kansa da danshin hannunsa in shafar ba za ta cutar da shi ba.
 Idan kuma ya zama da cutuwa ko akwai najasa a jikin ciwon ta yadda ba zai iya gusar da ita ba, to ya wanke gefensa daga sama zuwa kasa.
 Amma idan ya kasance da bandeji a kansa, kuma ba zai yiwu a warware shi ba, ko kuma akwai cutarwa a cikin sanya masa ruwa, to ya wajaba ya yi alwalar mai bandeji (da aka fi sani da jabira): ma'ana ya sanya hankici ko kyalle mai tsarki a kan bandejin ta yadda za a gan shi kamar wani bangare ne daga gare su, sai ya yi shafa a kansa da danshin hannunsa sannan kuma ya wanke sauran gabar.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: