bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      22:43:37
Zamu amsa muku da cewa e, haka ne, wannan kuma saboda wasu dalilai da dama
Lambar Labari: 267
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Da yawan mutane suna yin wannan tambayar alhali ba sa buqatar sauraren voyayyiyar amsa, (amsa ta ta gaibu) to mu mun yi imani da cewar Imamai sha biyu gunge ne guda na musamman   ba zai yiwu a mayarwa ko wane xaya daga cikinsu ba, sai dai waxannan masu tambayar suna neman bayanai masu yawa ga wannan matakin ta hanya haqiqoqi bayyanannu ga wannan aiki na kawo babban canji, da abubuwan da ake buqata da za su s aa fahimci ma’anar wannan rana ta alqawari.
A kan wannan tushen ne muka yanke duba na wani xan lokaci a kan kevance-kevancen da muka yi imani da cewa sun cika a cikin halayya da xabi’un waxannan shugabanni ma’asumai,   sai kuma mu jeho tambaya mai zuwa:
Mu dangane da aikin canji mai faruwa game da ranar alqawari, gwargwadon yadda aka fahimce shi bisa ga sunnar rayuwa da gogayyar ta, shin zai yiwu mu kalli wannan doguwar rayuwar ga jagoran da aka ajiye mata a matsayin wani dalili daga dalilan cin nasararta, kuma wannan zai sa shi ya gubatar da wannan aikin ya kuma jagorance shi da daraja mafi girma? 
Zamu amsa muku da cewa e, haka ne, wannan kuma saboda wasu dalilai da dama daga ciki akwai wannan maganar mai zuwa cewa: haqiqa yinqurin kawo babba gyara yana buqata yanayi na ruhi makaxaici ga jagoran da zai ja ragamar yin sa, ya zama yana cike da (hamasa ko) himma da kulawa ... da xaukaka da kuma ganin rashin girman babban aikin da ya sa a gaba wanda aka shirya shi da ya aiwatar da shi da kuma canja tsarin rayuwa a zamanance zuwa wata sabuwar wayewa. 
Gwargwadon yadda zuciyar mai kawo canji take ciki da ganin raunin wannan wayewar da yake yaqa da kuma jin cewa a sarari ita ba komai ba ce face xan xugo a kan dogon layin zanen ci gaban xan’adam, zai wayi gari mafi jin qarfin gwaiwa ta vangaren ruhinsa   kan fuskantar wannan wayewar ko hukumar da kuma dakewa kyam a gabanta da ci gaba da qoqarin tunbuke ta. 
Abu ne a sarari kan cewa lalle gwargwado da ake buqata na jin nauyi na musamman ga  wannan aikin, lalle ne ya zama ya dace da girman shi kansa kawo cnaji da ma kuma abin da ake so a ga qarshensa na wayewa da samuwa, kuma duk lokacin da fito-na-fito don kawar da wani abu ya zama mafi girma kuma ya zama na wayewa ce mafi kafuwa da ta kai qololowa a mbanbantan matakan rayuwa, to haqiqa aikin na buqatar zage dantse mafi girma fiye da yadda ake jin nauyin aikin. 
A yayain da sakon ranar da aka yi  alqawari ta zama ta kawo canji a dukkanin duniyar da ta cika da zalunci da danniya ce, to a xabi’ance dole ne wannan saqon ya nemo mafi girman mutum wanda ke da cikakken sani da jin cewa aikin da ke gabansa ya fi girman wannan duniyar baki xayanta, savanin mutumin da a waccen duniyar aka haife shi ba waxanda suka rayu a cikin inuwar wancan ci gaban da ake nufin canja shi da wani sabon ci gaban adalci da gaskiya, domin wanda ya rayu a inuwar cigaba mai bunqasa, da duniya ta cika da darajarta da tunaninta, to jin kwarjini - zamaninsa - zai rayu a zuciyarsa, domin shi an haife shi a lokacin da wannan wayewar yake cin gashinta, kuma ya taso tun yana xan qarami a lokacin da hukumar take kan ganiyarta, ya buxe idandunansa a cikinta be san wani abu ba sai fuskokin ta mabanbanta. 
Savanin wancan, a ce ga wani mutum, wanda shi mutum ne da ya ke cikin tarihi tsundum ya rayu a duniya tun kafin duniya ta shedi  wannan ci gaban na haske, kuma ya ga babban ci gaba yana jagorantar duniya xaya bayan xaya, sannan suka raunana kuma suka rushe,   ya ga wannan da idanunsa ba karantawa ya yi a littattafan tarihi ba.
Sannan ya ga ci gaban da yake da iko gare shi da ya kasance aji na qarshe daga kissar mutum kafin ranar alqawari, ya ga babbar bishiya tun tana matsayin qaramin iri da ba shi da alamar bayyana.
Sannan ya ganta ta xauki matsayi a cikin mutane tana yin yaxo tana neman dama don ta girma ta bayyana.
Sannan ya rayu da ita wato ya yi zamani xaya da ita a lokacin da ta fara havvaka tana bunqasa wani lokacin tawaya ta same ta wani lokacin kuma ci gaba da dacewa su abotakance ta.
Sannan ya same ta tana bunqasa tana mamaya a hankali a bisa yanayin duniya baki xaya, to ta wannan fuskar xan’adam xin da ya rayu a dukkan waxannan matakan da kaifin hankali da faxaka cikakku yana duba zuwa ga wannan tazgaron - wanda yake so ya yi faxa da shi - daga wancan dogon tarihi mai tsayi wanda ya rayu shi da jikinsa ba ta cukkunan litattafan tarihi kawai ba, yana duba zuwa gare shi ba da ‘yar qaramar sura ba, ba kuma kamar yadda (John Jack Roso)  yake duba zuwa mulkin mallaka a Faransa ba, haqiqa labari ya zo daga gare shi cewa; ya kasance yana jin tsoro da zarar ya suranta kasantuwar Faransa ba tare da samuwar Sarki ba, tare da kasantuwarsa daga manyan masu tunani da hikima kuma yana daga cikin msu yin kira ta fuskancin ci gaban siyasa mai ci a wannan lokacin, domin shi wannan (Rosen) ya rayu ne a inuwar mulkin mallaka, ya sheqi iskar ta tsahon rayuwarsa, amma ka ga Mutumin da ya shiga cikin tarihi to yana da kwarjinin tarihi, da qarfin tarihi da kyakkyawan sani kan cewa abin da ke kewawye da shi na daga kasantuwa da ci gaba wani abu ne da aka haife shi a wani yini daga kwanakin Tarihi, wasu dalilai suka faru gare shi sai aka samar da shi kuma wasu dalilan za su faru sai ya gushe, kuma ba abin da zai wanzu daga gare shi dindindin kai ka ce a jiya ko a shekaran jiya wani abu be faru ba, kuma lallai kwanakin da tarihi ke bawa samuwar wayewa da ci gaba,  duk yadda suka yi tsayi ba wasu abubuwa ba ne face ‘yan kwanaki gajeru a cikin doguwar rayuwar Tarihi.  
Shin ka karanta Surar Kahfi? 
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822. 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: