bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:33:22
Tarihin rayuwar mace yana cike da duhu a cikin al'ummu sakamakon danniya da ta fuskanta a cikinsu, sakamakon haka ne Allah madaukaki ya aiko da 'yan sako a cikin lokuta da marhaloli da zamuna mabambanta, zuwa ga al'ummun nahiyoyin wannan duniyar domin su fitar da su daga wannan duhun zuwa ga haske. Sai dai a ko da yaushe suka juya baya sai al'ummu su sake koma wa cikin al'adunsu, su dulmuya cikin duhunsu, su ci gaba da fandare wa ubangijinsu.
Lambar Labari: 27
A nan muna son kawo wasu bayanai masu takaituwar gaske a dunkule game da irin wannan halaye da mace ta samu kanta ciki na danniya a tsawon tarihin rayuwar dauloli da kasashe don matan da suka samu kansu cikin ni'imar shiriyar Allah su gode masa da kara yabo gare shi. 
Marhalolin Tarihin Mace
Tarihin rayuwar mace yana cike da duhu a cikin al'ummu sakamakon danniya da ta fuskanta a cikinsu, sakamakon haka ne Allah madaukaki ya aiko da 'yan sako a cikin lokuta da marhaloli da zamuna mabambanta, zuwa ga al'ummun nahiyoyin wannan duniyar domin su fitar da su daga wannan duhun zuwa ga haske. Sai dai a ko da yaushe suka juya baya sai al'ummu su sake koma wa cikin al'adunsu, su dulmuya cikin duhunsu, su ci gaba da fandare wa ubangijinsu.
Afrika da Gabas
Sau da yawa akan yi tambaya mene ne hakikanin mace,matsayinta, tasirinta, hakkokinta, tarihinta, da marhalar da ta wuce a cikinal'ummu? Amsar wadannan tambayoyi tana iya baiyana cikin bincike da zamu yi a kan mace a al’ummu, da addinai a takaice. 
Idan muka duba rayuwar mace a al’ummun wasu yankunan Australiya, da wasu yankunan Afrika, da Tsibiran Rasha, da na Tekun Pasifik, da Tsohuwar Amurka, rayuwar tasu tana daidai da rayuwar dabbobi ko ma kasa da hakan,domin a yawacin wadannan yankuna namiji yana da ikon mallakarta ya amfana daga gare ta kamar dabba . 
 A wasu wurare suna ganin kamar an yi ta ne don namiji kawai, samuwarta kafin aure da bayan aure tana bin ta maza ne, a wasu wurare ana sayar da su ne ba aura ba, ana ma iya bayar da rancensu, da aronsu, domin ta haihu ko ta yi wata hidima, har ma ana iya kashe ta kuma babu kisasi. Dukiyarta kuwa ta namiji ce haka ma duka wani abu da ta mallaka, haka ma komai na gida na wahala yana kanta kamar hidimar ‘ya’ya, da bukatun namiji, da sana’a, kuma dole ta jure ba yadda za ta yi . 
Ana iya ganinta ne a taron mata idan ya shafi gida kawai amma duk wani lamari ko taro na addini da ya shafi al’umma gaba daya to a nan wani abin mamaki ne a ga mace. Haka ma ba a san ta ba a lamarin shugabantar kungiya ko taron jama’a sai a wasu wurare. Idan kuwa aka koma fagen ilimi to babu wata kofa da aka bude wa mata. 
Tsofaffin Addinai
 Al’ummu da dauloli suna da al’adu mabambanta, wasu gada ake yi wasu kuma ana tasirantuwa da su ne ta hanyar zamantakewa a wani waje ko kuma daga yanayin dabi'ar wuri. Bari mu ga mace a al’ummu daban-daban da ba su da littafi na doka da aka saukar daga sama, kamar Tsohuwar Kasar Sin, Indiya, Masar, da Farisa, wadanda sun yi taraiya wajan rashin ba wa mace ‘yancinta. 
Mace ba ta da 'yanci ko da na nufi da abin da take so, da na aiki, ko cin gashin kanta, ana tilasata mata taraiya cikin duk wahala, da kebantuwa da aikin gida. Sai dai tana da dan ‘yancin rayuwa cikin al’ummar da take domin a wasu al’ummu ta kan yi gado da aure duk da ba ta da wani cikkakken ‘yanci, namiji ya kan yi aure ba iyaka a wajansu ya kuma kori wacce ya so, idan ya mutu ba ta isa ta yi wani aure ba amma shi namiji yana da hakkin wannan, kuma har ila yau a mafi yawancin daulolin namiji yana iya taskace ta a gida ko duk inda ya so. 
Haka ma Farisa a zamanin da tsarin dabakoki ya haifar wa dangin sarauta halaccin iya auren dangi domin ka da jinin ya watsu a cikin wasunsu, sai aka haramta wa mace auren talaka kuma aka taskace iradarta da abin da gidan sarauta ya ga dama kawai. Ko da yake ta wani bangare wannan tsarin ya rage kaifin zalunci kan dabakar mata saboda damar rike sarauta da tafiyar da al’amuran hukuma da ‘Ya’yan sarki mata suka samu . 
Wani lokaci kuwa zaluncin kwace kyawawan mata da sarakuna suke yi ne ya taimaka wajan haifar da wasu tunani a tarihin wasu al’ummu kamar na ‘yan tunanin Mazdak da saboda zaluncin ne suka yi tawaye suka haifar da wata fikira mai ganin cewa; Ai mace kamar sauran kaya ne don haka duk wacce ka hadu da ita mallakarka ce. 
Kasar Sin da Indiya
A Tsohuwar kasar Sin (Chana) kuwa auren mace kamar saye ne da mallaka, sannan ba ta da gado, kuma ba a cin abinci tare da ita ko da tare da ‘ya’yanta ne, Kuma maza da yawa suna iya taraiya a kan mace daya kamar yadda ake hada hannu wajan sayan doki daya kuma kowannensu yana da ikon jin dadi da ita, sai dai ‘ya’yanta na wanda ya fi saura karfi ne . 
Indiyawa suna da dokokin da suka kebanci mata kawai, a kasar Indiya an hana mace kallon bakar fatar asalin yankin  masu shan wahalar wariyar launin fata, wasu masana suna ganin cewa Ariyawa  sun sanya wannan dokar kan mata ne domin kada mace farar fata ‘yar kabilar Ariyawa ta ji tana son Bakar fata. Ba su tsaya a nan ba sai da suka sake hana mata taba duk wani abu da wadannan kabilu suka taba. Kasancewar hukuncin ya kebanta da mace kawai yana nuna mana irin wariya da mace ta ke fama da ita a fagage daban-daban na rayuwa a Indiya . 
A Indiya mace na bin mijinta ne a samuwa, kuma ba ta da ikon yin aure bayan mutuwarsa, ana kona ta  da ranta ne tare da gawar mijinta abin da aka fi sanin da "Sati" . A Addinin Hindu idan mata suna haila to sun zama dauda haka ma duk abin da suka taba da tufafinsu, kuma dole ne a nisance su, haka nan suna ganin cewa; ita wata halitta ce tsakanin mutum da dabbobi . A Littafinsu na dokokin addini mai suna "Manu Dhrama Sastra” a Babin bayani game da mace ya zo cewa: 
Dole ne mace ta zama ba ta da zabi a kan kanta ko yarinya ce, ko tsohuwa, ‘ya ta ubanta ce, kuma mata ta mijinta ce, uwar marayu tana karkashin ‘ya’yanta ne. Mace ba ta isa ta ci gashin kanta ba har abada, kuma dole ta yarda da wanda babanta ya zaba mijinta har abada, ta yi wa miji hidima har mutuwa kuma ba ta isa ta yi wani miji ba idan ya mutu ko ta yi tunanin wani miji bayan mutuwarsa. 
Kuma dole ne yayin nan ta bar duk wani abu da take marmari ko kwadayi na ci mai dadi ko tufafi mai kyau da duk wani ado har rayuwarta ta kare, idan mijinta ba ya son ta yana bin wata matar kada ta sake ta ji haushi kuma ba ta da ikon takaita masa hidima da neman yardarsa. Aljannarta  tana karkashin mijinta kada ta yi wani abu sai da yardarsa. Uban yarinya kada ya ci sadaki ko yaya daga ciki, in ko ya yi haka daidai yake da wanda ya sayar da ita. 
Duba ku ga yadda mace ba ta da ikon tunani ko sanya mai kyau ko cin abin da take marmari ko aure don mijinta ya mutu, wato da ana an gwanci ya mutu shi ke nan ta gama aure har ta mutu koda kuwa za ta shekara dari a Duniya, sannan kuma ba ta da ikon tunani a kan makomarta.
WASU DAULOLIN
Al’ummu masu ci gaba da dokoki game da abin da ya shafi mace kamar Kaldaniyawa, Rumawa da Yunaniyawa (Girika) duk ba su tsira daga irin wannan ba, saboda haka zamu yi kokari mu kawo misalai game da matsayin mata a cikin irin wadannan al’ummu. 
Kaldaniyawa
A littafin Kaldniyawa na shari’a mai suna "Hamurabi” sun kafa dokar bin mace ga miji da rashin ‘yancinta faufau har ma a cikin nufi, irada, aiki, da bukata. Idan da zata saba masa ko ta yi wani abu na kashin kanta to yana da hakkin fitar da ita daga gidansa ko ya yi mata kishiya ita kuma ya yi mu’amala da ita a matsayin baiwa. Haka ma da zata yi barnar abinci yana iya kaita kotu, idan kotu ta tabbatar da haka to za a nutsar da ita a ruwa har mutuwa . 
Rumawa
Amma Rumawa suna daga cikin al’ummar da ta dade da kafa dokokin zamantakewa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa (a.s). A wajansu mai gida shi ne Ubangijin gida da matan zasu bauta masa kamar bayinsa, kuma yana da cikakken zabi, ba ya shawara da mace domin ita ribar kafa ce ta zaman tare kawai da duk abin da ya ga dama shi zai yi, yana iya kashe matarsa da ‘ya’yansa mata idan yana ganin maslahar hakan kuma ba mai ganin ya yi wani laifi, mata, ‘ya, da ‘yar’uwa, duk suna cikin mawuyacin hali. 
 Har a Falsafarsu ba a ganin mace wani bangare na al’umma, ba a zartar da cinikinsu ko alkawarinsu, ba su da hakkin zabe ko wasa, amma ‘ya’ya maza koda na tabanni ne suna da daraja domin suna maza. Kuma idan mace ba ta haihuwa miji yana iya kashe ta saboda ba ta kawo ‘ya’ya maza a al’umma, idan namiji ya gane shi ne ba ya haihuwa yana iya bayar da aron matarsa ga wani dan’uwansa idan ta yi ciki ta haihu da namiji sai ya yi alfahari ya samu da. 
 Kuma ana iya bayar da rancen mace kamar kaya, sayarwa, bayarwa kyauta, biyan bashi, ko a matsayin haraji, haka nan ba ta tsira daga duka ko kisa ba. 
Daga cikin dokokin Rumawa: Mace ba ta dariya, ba zata ci nama ba, ba ta da ikon magana, shi ya sa ma akan sanya mata mukulli a baki, sannan suna ganin ba ta da komai sai hidima ga miji ko ubangida, kuma suna ganin ta a matsayin wasila ce da shedan yake amfani da ita wajan halakar da mutane . 
Larabawa
Amma Yunan da Yankin Larabawa da Tsohuwar Iran a wajansu gida da maza ne ake lissafinsa ba da mata ba, har ma kusancin da a kansa ake gado  da maza ne ake la’akari ba mata ba, babu kusancin da ya shafi mace da ake kiyaye shi koda na uwa ne, ko ‘ya, ko ‘yar’uwa. Kusancin mace da ake kiyaye wa kusanci ne na saduwa, haihuwa, da aurataiya. 
A al’adun Larabawa idan ‘ya tana gidan uba ko miji suna iya yin duk abin da suka ga dama da ita, kimar mace hatta ta ranta ba ta da wani alfarma, a sakamakon mace ba ta da wani hakki da ake kiyaye shi sai farkon shahidi a Musulunci ta zama mace. Dukiyar mace ta namiji ce koda kuwa sadakinta ne ko ta kasuwanci da ta yi balle gado da haramun ne a gare ta, uba ko dan’uwa shi ne zai aurar da ita ko ta ki ko ta so. 
 Jaririya kuwa ko yarinya ba ta tsira daga binnewa da ranta ba, "Kuma idan wacce aka turbude ta da rai aka tambaye ta. Saboda wane laifi ne aka kashe ta ". Suna ganin halittar mace aibi ce da musifa da bala’i gare su  musamman ma idan an ribace ta a yaki a wajansu wannan wani aibi ne da babu kamarsa, don haka a binne ta ma da rai don kada ta taso ta zama aibi ga al’ummarsu. 
 An ce farkon wadanda suka binne ‘ya mace su ne Banu Tamim sannan sauran larabawa suka dauka, wannan ya kasance ne sakamakon ribace su da sarki Annu’uman dan Munzir ya yi ne , sai wannan abu ya fusata su suka fara binne na raye da ransu. Haka nan idan aka yi wa wani albishir da ‘ya mace sai ka ga yana buya daga mutane don kunya na abin aibi da ya samu. "Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka kirin yana mai bakin ciki. Yana mai buye kansa daga mutanen saboda munin abin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne cikin wulakanci ko kuma zai turbude shi a cikin turbaya ne, hakika abin da suke hukuntawa ya munana" . Amma idan namiji ne aka haifa masa sai ka gan shi yana mai farin ciki komai yawansu, wannan ma ba ya isar sa har sai ya yi da’awar dan zina ma cewa nasa ne, har ma ya kan iya kai wa ga yaki ko fada a kan ‘ya’yan zina . 
 Koda yake wasu lokuta wasu gidajen sukan ba wa mace damar ta auri wanda take so, ko ma yaya dai, mu’amalarsu da mata mu’amala ce da ta cakuda da ta al’adun daulolin da suke kewaye da kasashen larabawa kamar Iran da Rum. 
 A yankin Larabawa mace wata kalma ce ta wulakanci a gaya wa namiji ita kuma kalma ce ta kaskanci. Haka nan mace a wasu al’ummu ta zama murhu ne kawai na dafa abinci ko wanke kaya da yara sai kuma idan bukatar namiji ta taso, amma duk abin da ya shafi ci gaban al’umma wannan wani abin mamaki ne a ga mace a ciki. 
Yunan (Girika)
Amma a Yunan  al’amarin mata ba shi da bambanci da na Rumawa da suna la’akari da namiji ne a dokokin zamantakewa, komai na namiji ne ba abin da mace take da shi amma a bangaren laifi ana hukunta ta. Haka nan in ta jawo wani abu na amfani to wannan na namiji ne, suna ganin mace kamar kwayoyin cuta ne masu cutar da al’umma, amma ta wani bangare abu ce ta amfanin al’umma, kuma idan ta sake ta yi laifi ko yaya yake, to ta shiga uku. 
Mafi yawancin al’ummu ba sa ganin aikinta karbabbe ne a wajan Allah, a Yunan ana cewa da ita dauda daga aikin shaidan, wasu daga Rumawa da wasu Yunanawa suna ganin ba ta da Ruhi irin na namiji. Suna ganin mace kamar wani ribataccen yaki ne da yake kurkuku wanda idan ta kyautata amfani ba nata ba ne, idan kuwa ta munana ta dandani kudarta, kuma ba a gode mata, suna ganin tunaninta sharrin ne kawai, saboda haka ba ta isa a bar ta a kan tunaninta ba. 
Haka nan maza su ne kawai al’umma, shi ya sa gidan da babu maza hukuncinsa a rusa shi, don haka idan wani ya ga ba ya haihuwa to dole ya ba da aron matarsa don ta samu namiji, in ba a samu namiji ba sai ya yi tabanni da dan wani ko dan zina ko da kuwa ta hanyar runton da ne da jayaiya. Saki da aure a wajensu iri daya ne da na Rumawa, kuma akan iya auren mata ko nawa aka so amma daya daga ciki ita ce bisa doka sauran kuwa ba bisa doka suke ba . 
Ma'abota Littafi
Yahudawa suna da dokoki da ba su dace da kimar mace ba, idan mun duba zamu ga suna da dokar cewar idan da namiji ya auri yarinya sai ya yi da’awar ya same ta ba budurwa ba kuma babanta bai yarda ba to baban yana iya kai jini a kyalle kotu ya ce: An yi wa ‘yarsa kazafi, idan ya ci galaba sai a ci mijin tarar azurfa dari kuma bai isa ya sake ta ba har abada, amma idan aka tabbatar da haka to ita kam za a kai ta bayan gari ne a jefe ta har mutuwa. Yaya aka san cewa zina ta yi?. Ko kuwa babu wata hanyar zubewar budurci sai ta zina?!. 
 Idan mutum ya saki matarsa sai ta auri wani shi ma ya sake ta to na farkon ba shi da ikon sake aurenta domin an najasta ta !. Don me ya sa mace ce kawai ta zama najasa ban da shi namijin?!. 
Idan dan’uwa ya zauna da dan’uwansa a gida daya sai shi mijin ya mutu ya bar matarsa to ya zama dole kan dan’uwansa ya aure ta. Idan kuwa ya ki, sai ta kama hannunsa ta kai shi gaban dattijan gari ko yanki ta cire takalminsa ta tofa masa yawu a fuska, sannan a rika kiransa da sunan: Mai tubabben takalma!. Tambaya a nan idan ba ta son sa fa? Shin ya zama dole ke nan ta aure shi?!. 
Game da gado kuwa matukar uba yana da da namiji to mace ba ta da komai!. A nan ina batun hakkin mata ke nan?. Don me ya sa ba su da komai?!. 
Amma game da dokarsu babu wani adadin matan da aka iyakance za a iya aura !. Ke nan babu mai bakin sukan Musulunci da ya iyakance su da hudu kawai?! . 
Idan muka duba Kiristanci kuwa zamu ga babu wani bambanci sosai a mafi yawan dokoki tsakanin Kiristanci da Yahudanci, misali game da hukuncin lullubi da hijabi wanda akwai shi a Yahudanci da Kiristanci amma sai suka sassauta hukuncinsa, wanda a farkon Kiristanci rashin sanya shi laifi ne kuma aibi ne mai girma da saba doka. Duba ka ga abin da ya zo a Risalar Bulus zuwa ga mutanen Korentis da umarnin a aske gashin duk wata mata da ba ta da hijabi (lullubi) don ta ladabtu! . Hakan nan suka sassauta shi saboda faruwar juyin juya halin masana’antu a kasashen turai da sunan saukaka aiki ga mace don ta ji dadin yin aiki a gona da ma’aikatu, sai abin ya yi yawa har coci ta yi muwafaka da shi. Tambaya a nan don me coci ta yi shiru kan takura mata masu lullubi da ake yi a yammancin duniya da hana su wasu hakkoki har da na ilimi?!. 
A nan ya kamata mutane su yi hukunci tsakanin irin wadannan dokoki da na musulunci, kuma su kwatanta su ga ni’imar da Allah ya tanada a cikin addinin musulunci da kamalarsa, da kula da hakkin mata da ba a taba samunsa irinsa ba a tarihin rayuwar dan'adam . 
Yammacin Duniya
Amma mace a yammacin duniya muna iya cewa: Yammacin duniya sun kwaikwayi musulunci ne amma sai suka dauki wanda ya yi musu da zai taimaka musu a duniyance suka cakuda shi da al’adunsu, wato sun dauki samfur ne amma suka ki yin aiki da duk abin da ya kunsa. Koda yake a wasu mahangai nasu da yawa sun sha bamban dari bisa dari da musulunci, domin shi ya tsakaita dokokinsa ne a komai, ya kuma dora shi bisa maslaha da hadafin halittar dan'adam ne, amma su sun dauki mutum a matsayin shi ne ma’auni saboda haka sai ya zama tamkar shi ne Ubangijin kasa wanda komai ya so shi ne daidai don haka ba a hana shi cimma abin da ya sa gaba. 
Yamma da suke ganin cewa sun daidaita mace da namiji a komai a nazarinsu da mahangarsu amma sai muka ga sabanin haka a aikace  domin har yanzu ba a samu wata mahanga ba mai iya yiwuwa a aikace in ban da mahangar musulunci. Sannan ga take hakkin mata ta yadda hatta da ma dankwali da mayafi da zata sanya a kanta da ganin damarta amma hakan yana iya haramta mata shiga ajin karatu don yin ilimi har abada. Abin mamaki yayin da namiji ya kan shake wuyansa da nektayel yana sanye da dogon wandonsa da ya rife shi gaba daya, amma mace idan ta yi hakan ta lullube jikinta gaba daya wannan abin yaka ne a wajansu. 
 A yamma da ake da'awar an daidaita mace da namiji a hakkin komai ba tare da la’akari da dabi’ar kowanne da Allah ya halicce shi a kan ta ba , sai ga shi a aikace ya nuna sabanin haka ko ma ba za a iya aikata shi a aikace ba. Yau shekara fiye da dari biyu da kafa kasar Amurka amma mutum nawa ne mace ta rike shugaban kasa, mataimakinsa, shugaban majalisa, ministan shari’a, kai ko da na harkokin waje nawa ne, da wasu mukamai da dama da ka kan iya kwatantawa? Haka ma a aikin soja mata nawa ne kuma maza nawa ne? Da yawa mun ga mata sun zama kayan talla abin biyan bukatar sha’awar maza a irin wadannan kasashe . 
A taron Faransa ne fa a shekarar 586 bayan kaikawo da sabani mai tsanani an tabbatar da cewa mace mutum ce sai dai an halicce ta ne domin ta yi hidima ga namiji. A Ingila kuwa nan da shekaru dari baya ba a lissafa ta a cikin kidayar al’umma . 
Mahangar Musulunci
Mahangar musulunci ta girgiza duniya a wancan zamani da ta shelanta cewa babu bambanci tsakanin mace da namiji sai da tsoron Allah a daidai wannan lokaci a duk fadin duniya daga gabas har yamma babu inda mace take da wata kima ko wani hakki muhimmi a cikin al’ummarta. Haka nan ya zo a Kur’ani mai girma fadin Allah madaukaki: "Ya ku mutane! mu mun halicce ku maza da mata… mafi girmanku a wajan Allah shi ne mafi tsoronku gare shi... ”.  Sannan sai ya nuna wani jagoranci da maza suke da shi a kan gida domin kowace tafiya tana bukatar jagora. Allah madaukaki yana cewa: "Lallai su mata suna da kwatankwacin abin da ke kansu na hakkoki, da kyautatawa, kuma maza suna da wata daraja a kan mata" . 
Sai dai domin gudun ka da namiji jagoran gida ya dauka yana da ikon mamaye komai, sai Allah mabuwayi ya yi nuni da cewa Allah ya sanya muku baiwa da ya yi wa kowanne, a wani fagen mata sun fi daukaka, a wani fagen kuwa maza ne suka fi daukaka, don haka ka da namiji ya yi burin samun wasu darajoji na mata don ba zai iya samu ba, haka ma mace ka da ta yi burin samun wasu darajoji na maza don ba zata samu ba. Wanda ya mamaye halittunsa da rahamarsa yana cewa: "Kuma kada ku yi burin abin da Allah ya fifita sashinku da shi a kan sashi, mazaje suna da rabo da sakamako na daga abin da suka aikata, suma mata suna da rabo da sakamakon abin da suka aikata. Ku dai ku roki Allah daga falalarsa"  (maimakon burin abinda ya fifita sashinku da shi a kan sashi). 
Mace da namiji a musulunci duk daya ne sai dai a aiyuka da Allah ya bambanta su daidai gwargwadon yadda halittarsu take, amma ta bangaren ruhinsu babu bambanci tsakanin mace da namiji, bambancin ya shafi bangaren jiki ne. Haka nan musulunci ya duba maslaha a cikin dokokinsa; misali a hukuncin gado musulunci ya kiyaye masalahar duka ne domin dukiyar miji tana komawa ga matarsa da ‘ya’yansa ne, amma ta mace ta kebanta da ita ne. Kuma bai wajabta mata yaki ba sai ya wajabta shi a kan namiji, haka nan ciyarwa tana kan namiji ne, ita kuwa ba ta fita daga gida in ban da larura ko wani abu na wajibin fita sai da izininsa. 
Matsalar da take faruwa a kasashen musulmi ta al’ada ce ba musulunci ba, misali a wasu wurare idan mace ta yi zina aibi ne da gori ga ‘ya’yanta sabanin namiji. Haka ma auren dole ba safai a kan yi wa namiji ba, amma mace da yawa ya kan faru a kanta, wannan kuwa yana komawa al’adu ne ba musulunci ba. Amma musulunci ya daidaita mace da namiji a irada, iko, mallaka, girmamawa, rike mukami, kasuwanci, ibada, aure cikin yarda , Ilimi, hankali, likitanci, injiniyanci, kasuwanci, tare da fahimtar juna da mijinta. 
Musulunci yana kiyaye maslahar duka bangaren mata da maza a dokokinsa, misalin dokar halarcin auren mace sama da daya, da babu wannan dokar da mata sun samu kunci a cikin rayuwa kamar maza, kuma da an sami yaduwar fasadi mai yawa a kasashe. Shari’a ta sanya dokokin daidai da dabi'ar kowanne, misalin saki a bisa ka’ida ta farko yana hannun namiji ne sai dai idan da sharadi tsakaninsu na cewa tana iya sakin kanta , saboda mace idan ta fusata tana da saurin yanke hukunci, don maslaha sai musulunci ya sanya irin wannan abubuwa a hannun namiji. Haka ne musulunci ya gina dokokinsa bisa hikima da maslaha domin cimma hadafin gina al’umma ta gari mai iya isa zuwa kamalar da Allah ya ke so ta kai zuwa gare ta. 
Musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne tausaya wa mace a tarihin dan'adam, kuma yana ganin rayuwar iyali ba ta cika sai da wahala a wajen gida da cikin gida, don haka ne ma ya raba rayuwar gida biyu domin ya karfafi soyaiya da kaunar juna ta taimakekeniya, don haka sai ya ba wa namiji aikin wajen, ya kuma ba wa mace aikin cikin gida. Ya sanya aikin cikin gida a hannun mace, domin mace ta fi namiji iya tafiyar da al'amuran cikin gida musamman kula da yara. Ita ce ta fi cancanta da yanayin tarbiiyar yara ta fuskacin tunani da tausayi da lafiya. Yana ganin da an ba ta aikin namiji da yake wajen gida da wannan yana nufin a dora aikinta da yake cikin gida a kan namiji ke nan, don haka ne sai ya bar aikin wahala na wajen gida a kan namiji ita kuma ya ba ta aikin cikin gida . 
Allam Saiyid Diba’diba’i yana cewa : "Bambanci tsakanin 'yan'adam mace ko namiji ne ba ya fitar da wani daga cikinsu daga nau’in da suke ciki na ‘yan’adamtaka, kuma samun kamala ga kowanne daga cikinsu abu ne wanda yake mai saukin yiwuwa ga duk bangarorin biyu ta hanyar kamalar halaye, tsarkin zuciya, imani, biyaiya, neman kusanci, don haka mafi kyawun kalma a nan ita ce fadin Allah cewa: Ba na tozarta ladan aikin mai aiki daga cikinku namiji ne ko mace, sashenku daga sashe yake. Wannan al’amari ya saba da abin da ya zo cikin Attaura da take fada a cikin Sufurul Jami’a: "… sai na samu mafi daci daga mutuwa ita ce macen da take cikin daki…”. 
Sukan musulunci a yammacin duniya ya taso ne saboda gafala da rufe ido game da tarihin musulunci lokacin da ya rike duniya ya wayar wa yamma da gabas kai, ya zo da tsari da babu kamarsa, da adalci da ake buga misali da shi, da tsarin rayuwa mafi kamala a tarihin dan'adam, domin tsari ne da ba a kwatanta shi ko kusa da sauran tsaruka. Ba don Yakin harin Salib (crusade) da yamma suka kai shi kan duniyar muslulmi suka samu littattafansu ba, hada da albarkacin makarantar Bagdad da Andulus, da yammacin duniya bai gano ilimi mai yawa ko wayewar ilimi ba. 
Malaman da kuka samu albarkacinsu irin su "Farabi” da "Al-kindi” malamai ne mabiya alayen manzon Allah (s.a.w), haka nan mutumin da kuke wa kirari da mafassarin ilimi mai girma "Ibn sina” ya amfana daga koyarwarsu kuma musulmi ne mai biyaiya ga Ahlul-baiti (a.s), haka ma "Ibn Rushdi” bamalike babban malamin Falsafa a Andulus. Amma sai kuka dauki wanda ya amfani al’adunku a duniya kuka jefar da wanda bai yi muku ba. 
Lallai Musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne tausaya wa mace a tarihin dan Adam, kuma yana ganin rayuwar iyali ba ta cika sai da wahala a wajen gida, da kuma zama a cikin gida, sai ya raba rayuwar gida biyu domin ya karfafi soyaiya da kaunar juna ta taimakekeniya, ya ba wa namiji aikin wajen, ya kuma ba wa mace aikin cikin gida. Ya sanya aikin cikin gida a hannun mace, domin mace ta fi namiji iya tafiyar da al'amuran cikin gida musamman tarbiiyar yara da kuma kula da lafiyarsu. Ita ce ta fi cancanta da yanayin tarbiiyar yara ta fuskacin tunani da tausayi. Addinin musulunci mai hikima yana ganin da an ba ta aikin namiji da yake wajen gida da wannan yana nufin a dora aikinta da yake cikin gida a kan namiji ke nan, don haka ne sai ya bar aikin wahala na wajen gida a kan namiji ita kuma ya ba ta aikin cikin gida duk da bai hana ta yin aikin waje ba bisa sharudansa. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: