bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:51:40
Na daya; Tsara Iyali wato daina haihuwa zuwa wani dan lokaci. Na biyu; Tsayar da haihuwa lokaci mai dan tsawo ta yadda za a tsayar da haihuwa a daina samar da dan adam a Duniya wani lokaci. Amma idan ya kasance da ma’anar tsayar da samar da dan adam ta yadda halittar dan adam zata kare ne wannan tabbas haramun ne a shari’a, amma da ma’anar da aka ambata ko kuma daidaikun mutane su tsayar da haihuwa da kansu ta yadda zasu daina haihuwa wannan babu dalili a kan haramcinsa, a bisa ka’ida wannan halal ne.
Lambar Labari: 32
Ba makawa cewa musulunci ya yarda da Tsara Iyali ko kaiyade su idan an sami matsalolin da muka ambata a farkon wannan bahasi ko ba sa samu ba, Sa’annan Kur’ani mai girma ya kaiyade lokacin shayarwa da shekaru biyu, an kuma hana shayar da yaro nonon mai ciki domin yana cutar da mai shan nonon, abin da wannan al’amari yake nunawa kuwa shi ne; tsayar da samuwar ciki har lokacin shayarwa ya wuce. Kamar yadda babu sabani a kan cewa ya halatta a tsayar da haihuwa sabaoda karancin lafiya da rauni da kan iya samun mace ko kare abin haihuwa daga rashin lafiya da yakan dauka daga Uwa kamar Uwa mai cutar tsida. 
Wannan duk yana nuna cewa shari’a mai tsarki tana neman tsari ga iyali da karfafawa ga rayuwa ta gari mai inganci da yalwar rayuwa, da kuma aiki da tsarin da zai kai ga lafiyar al’umma da kiyaye yaduwarta bisa tsari na lafiya da aminci domin kada bala’i ya yadu a cikin al’umma ko lalaci a cikin tsarinta. Wannan kuma yana iya kasancewa ne idan an sami daya daga iyaye yana da muguwar cuta da ‘ya’ya sukan iya dauka, ko dakatar da samun cikin domin uwa ta samu damar shayar da danta da take shayarwa, ko tsoron kada ta kasa tarbiiyatar da ‘ya’ya da biyan kudin karatunsu, ko kula da su idan sun yi yawa da tsammani mai karfi a kan hakan, ko kuma tsoron ciyar da su, duk da akwai sabani tsakanin malamai kan na karshe. 
Amma hukuncin Kaiyade iyali kamar yadda aka yi nuni kala biyu ne; wanda ya shafi daidaiku da kuma wanda ya shafi mutane gaba daya. Wanda ya shafi dan adam gaba daya shi ma kala biyu ne: -
 Na daya; Tsara Iyali wato daina haihuwa zuwa wani dan lokaci. Na biyu; Tsayar da haihuwa lokaci mai dan tsawo ta yadda za a tsayar da haihuwa a daina samar da dan adam a Duniya wani lokaci. Amma idan ya kasance da ma’anar tsayar da samar da dan adam ta yadda halittar dan adam zata kare ne wannan tabbas haramun ne a shari’a, amma da ma’anar da aka ambata ko kuma daidaikun mutane su tsayar da haihuwa da kansu ta yadda zasu daina haihuwa wannan babu dalili a kan haramcinsa, a bisa ka’ida wannan halal ne. 
Wasu jama’a sun haramta hakan saboda wasu dalilai kamar haka: Idan hakan ya zama hakki ne a hukuncin daidaikun mutane to don me ba zai zama hakki ne na al’umma ba? ga shi kuwa hakkin al’umma ya fi hakkin iyaye karfi musamman a wannan zamani na gasar fifiko da karfi tsakanin al’ummu. 
Amsa a kan haka ita ce: Kasancewar wannan hakkin cewa hakkin ne na tilas a kan iyaye babu dalili na shari’a a kansa, saboda haka ba abin da zai hana su kaiyade ‘ya’yansu duk sa’adda suka ga dama. Tare da sanin cewa inda zai kai ga rasa dan adam ne a duniya yake kai wa ga haramun, amma in ba haka ba babu wani dalili a kan haramcin. Kuma yana iya zama abin so idan yawan mutane ya kai ga wani mummunan matsayi a duniya kamar lalacewar tsarin kasashe da fitina mai yawa da yawan al'umma ne ya haifar da ita. 
Dalili na biyu da suka kawo shi ne; Littafi da Sunna sun kwadaitar a kan yawaita haihuwar dan adam. Suna masu cewa: An karfafi Haihuwa da hayaiyafa a musulunci kuma Kur’ani da Sunna sun kwadaitar da haka kamar fadinsa Madaukaki cewa: "Dukiya da ‘ya’ya kawar rayuwar duniya ce” . Haka nan hadisai sun zo suna masu kwadaitarwa a kan haka: Kamar hadisin Bakar dan Salih ya ce: Na rubuta zuwa ga Abul Hasan (a.s) cewa: Ni na nisanci haihuwa shekaru biyar ke nan domin matata ba ta son haihuwa, tana cewa: Yana yi mata wahala ta tarbiiyatar da su saboda karancin abin hannu. Sai (a.s) ya rubuta masa da cewa: Ka nemi haihuwa domin hakika Allah zai arzuta su . Da sauran gomomin ruwayoyi da suke karfafa neman haihuwa da yawaitar al’ummar Manzo (s.a.w) 
Amsa ita ce: Wannan kwadaitawar ba ta kai haddin wajabci da lizimci ba, saboda haka mutane suna da ikon kaiyade ko tsara iyalinsu kamar yadda suka ga dama. Balle ma idan ya kai ga lalacewar tsarin zamantakewar al’umma a nan maganar kwadaitarwa tana karfafa zuwa ga wajabtawa. 
Amma matsalar a yau ba ta neman da na gari ko haihuwa da samurwar al’ummar duniya ta tsayu a kanta ba ne, maganar ita ce, Idan mutane sun yawaita da ya zama ana ji wa al’umma tsoron faruwar wani bala’i a cikin al’umma shin ya halatta a kaiyade iyali ko tsara su. 
Na uku; Wasu jama’a sun tafi a kan haramta Kaiyade iyali kamar Muhammad Dan Habban Al-Basti Mai littafin Assahih Wattasanif shafi na 154 . Da Ibn Hazam Al-Andulusi suna cewa: Kaiyadewar daidai take da zubar da ruwa mai kwarara daga wajansa alhalin filin shuka yana bukatarsa kuma a shirye yake da ya karbe shi domin fitowar tsiro da ‘ya’yan itace na daga abin da yake amfanar mutane da raya halittu da samammu gaba daya. 
Amsa ita ce; Wannan duk abin da suka fada ba ya sanya kaiyade iyali ya zama haram, na’am yana iya zama karahiya idan da yin sa zai haifar da wani abu kamar rashin tsari a al’umma da makamancinsa, hada da cewa sun yi kiyasin farji da gona, mutum da shuka, ruwa kuwa da mani, alhali akwai bambanci mai nisa tsakanin wadannan abubuwan biyu. 
Saboda haka bisa abin da aka ambata Kaiyade Iyali ko tsara su a kan kansa halal ne, kuma suna iya zama wajibi a wani lokaci, amma mun riga mun gabatar da cewa Kaiyade Iyali da ma’anar dakatar da samar da dan adam gaba daya har zuwa wani lokaci ko ma ya kare wannan haramun ne ba mai halatta shi.
Hukuncin Zubar Da Ciki
Kamar yadda muka kawo, cikin hanyoyin da ake amfani da su domin Kaiyade Iyali akwai zubar da ciki, mu sani cewa malaman musulunci gaba daya babu sabani sun tafi a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai domin wannan kisan kai ne da kuma kashe mai rai, kamar yadda duk sun tafi a kan haramcin yin hakan matukar zai kai ga mutuwar uwar ko da ko rai bai shige shi ba. 
Daga cikin dalilai a kan haka shi ne; Haramcin jefa rai cikin halaka da kuma wajabcin kare rai mai alfarma da daraja kamar ran mutum. Amma an yi sabani idan ba a busa masa rai ba wato bai kai wata hudu ba kuma uwa ba zata cutu ba. Fatawar malaman Sunna da yawa sun halatta hakan amma malaman Shi'a mazhabar Ahlul-baiti (a.s) su tafi a kan cewa yin hakan haramun ne a shari’a ko da kuwa yanzu ne ciki ya shiga , sannan akwai wajabcin biyan diiya ga duk wanda ya zubar da shi ko iyaye ne kamar haka: 
1. Idan maniiyi ne dinare ishirin 
2. Idan gudan jini ne dinare arba’in
3. Idan tsoka ce dinare sittin
4. Idan kashi ne dinare tamanin
5. Idan an tufatar da kashin nama dinare dari
6. Idan kuwa halitta ta cika (dan wata hudu) dinare dubu wato diiya cikakkiya . 
Hukuncin Azalu
Halal ne namiji ya yi Azalu ga mace wacce suka yi auren mutu’a da ita, haka nan ga baiwa, amma ‘ya mai aure da’imi da ba na mutu’a ba an yi sabani a kan cewa sai da izininta ko kuwa, wasu malamai sun tafi a kan cewa sai da izininta, in kuwa ya yi ba da izininta ba ya aikata karahiya kamar yadda natijar da aka samu ke nan bayan an hada ruwayoyin da suka hana da wadanda suka halatta masa ko ba izininta. A kan wannan akwai ruwayoyi da yawa da nau’in mata da ko ba izininsu ana iya yin kaiyade iyali gare su kamar haka: 
1- Wacce aka samu yakini ba ta haihuwa 
2- Mai shekaru da yawa 
3- Wacce ba ta shayar da danta in ta haihu
4- Baiwa
5- Mai karancin kunya da rashin kame kai
6- Mai zage-zage da alfahasa
7- Auren mutu’a 
8- 'Yar Zina ko Fasikar Mata
Jinkirta Yin Aure
Wannan ita ce hanya ta uku da ake amfani da ita wajan kaiyade iyali ko tsara su. Wannan hanyar ma halal ce kamar yadda yake gun malamai amma ba a son ta, kamar yadda akwai ruwayoyin da suka yi nuni da mustahabbancin yin aure da wuri musamman ga mace idan ta isa aure da suke cewa in ba haka ba fasadi yana iya faruwa a bayan kasa. 
Kame Kai Ga Barin Jima’i
Hanya ta hudu ita ce kame kai ga barin jima’i shi ma halal ne sai dai ba a son sa a shari’a, har ma an haramta kame kai kwana arbai’in ba tare da an kusanci iyali ba kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da cewa idan ya bar ta kwana arba’in ya yi zunubi. Sai dai wasu suna kauce wa wannan matsalar ta hanyar rashin yin auren ne baki daya domin ka da hukuncin wajabcin kwanciya da matansu ya hau kansu.
Sauran Hanyoyi
Amma sauran hanyoyin da muka kawo a farkon wannan bahasi ba su da hani na shari’a sai dai kawai akwai abin da kan iya haramta su idan sun lizimci haram kamar ajnabi ya ga farjin mace ko sauran jikinta da aka haramta masa gani. Ko da yake ana iya cewa su ma ba a son su ta fuskacin shari’a duk da halal ne saboda ana son yawaita al’umma idan karancinta zai kai ga lalacewar tsarin zamantakewa. Amma idan ya zama yawaitarta yana iya lalata tsarin zamantakewar al’umma a nan ya zama dole a kaiyade ta. 
Saiyid Sadik Rauhani
A littafin fararru da sababbin mas’aloli na Saiyaid Sadik Rauhani shafi 141 . Bayanai game da Tsara iyali ya zo kamar haka ne: Yawaita iyali a musulunci abin nema ne da aka kwadaitar da shi amma kuma kaiyade iyali halal ne, hanyoyin da a kan bi wajan kaiyade iyali su ne kamar haka: -
1-Azalu. 
2-Jinkirin yin aure domin kada a samu saurin tara ‘ya’ya. 
3-Daina jima’i da iyali gaba daya domin gudun kada a samu ‘ya’ya. 
4- Ila’i. 
 Kamar yadda suke su ne hanyoyi hudu da a kan yi amfani da su don kaiyade iyali ko da yake akwai wasu hanyoyin daban. Ganin cewa ni’imar samuwar ‘ya’ya tana neman shiga cikin hadari ne ya sanya coci take neman hanyoyin kai wa ga sanya kaiyade iyali ya zama haram. Ni’imar ‘ya’ya ta zama hadari kuma matsalar karshe da malamai da masu tafiyar da al’amuran duniya suka shagaltu da ita a mafi yawan kasashe, ga kuma matsalar da ake fuskanta ta ninninkawar mazauna bayan kasa a duniya, alhalin gashi a duniya yanzu ana samun karancin mace-macen yara sakamakon maganin cututtukan yara da likitoci suka yi, ga kuma takaitawar yake-yake da sukan salwantar da rayuka masu yawa, sannan ga matsalolin da dauloli da kasashe suke ciki na kasawa da gazawa wajan maganin talaucin da yake addabar Duniyar dan'adam, amma sai ga yawan dan adam yana karuwa mai ban tsoro da yanzu dan adam ya kai biliyan shida a duniya a wannan zamani. 
Bertrand Russell (1872-1970) yana cewa: Adadin mazaunan duniya zai kai biliyan uku da rabi nan da shekaru ishirin da biyar masu zuwa saboda haka wannan yana bukatar tunani na musmamnan kan wannan mas’ala, da farko ana ganin abin kamar mai sauki ne amma bayan lokacin kadan za a fahimci cewa matsala ce babba mai wuyar warwara. 
Cocin Katolika ta yi kokarin hana kaiyade iyali ta kowane hali da duk matakai amma ta yarda da daukar matakin hana daukar ciki daga ma’aurata da gangan. Wannan yana nufin ta yarda da daukar hanyar al’ada domin hana daukar ciki ta hanyar tasiri kan jijiyoyi. Amma matsayin da shari’ar Musulunci mai tsarki ta dauka kan wannan shi ne kallon abin ta mahanga biyu; wato Tsara iyali da kuma kaiyade iyali. 
Saiyid Sistani (H)
Amma Saiyid Sistani a risalarsa ta Minhajus-salihin  yana cewa ne: Ya halatta mace ta yi allurar maniiyin mijinta amma bai halatta ba mai yi mata allurar ya zama ajnabi idan wannan zai kai ga ajnabi ya ga inda bai halatta ba a gani a jikinta ko taba inda bai halatta ajnabi ya taba ba a jikin mace. Sannan ya ci gaba da kawo hukuncin kaiyade da Tsara iyali yana mai cewa: ya halatta mace ta yi amfani da kwayoyin da sukan hana daukar ciki da sharadin wannan ba zai kai ga cutar da ita ba cuta mai tsanani haka yake ko da yardar mijinta ko ba da yardarsa ba. 
A mas’ala ta 71 ya ci gaba da cewa: Ya halatta mace ta yi amfani da (Laulab) wato kwayar da a kan sa a mahaifa domin ta hana daukar ciki amma da kiyaye sharuddan da ka fada na hana ajnabiiyi gani ko taba abin da yake haramun ya gani ko ya taba a jikinta idan sanya shi ya tsayu a kan hakan. Kuma ba a san cewa yana iya kai wa ga barin ciki ba bayan ya zama da a mahaifa, amma idan an san zai kai ga haka to ihtiyadi wajibi a bar shi. 
Haka nan ya yi magana ga yin aiki domin daina haihuwa ko yanke gabobin da sukan haifar da mani da wadancan sharuddan da kuma sharadin rashin cutar da kai. 
Amma game da zubar da ciki yana cewa ne bai halatta ba sai bisa hali daya; ya zama rai bai shige shi ba kuma rashin zubar da shi zai cutar da uwar, amma idan rai ya huru a cikinsa bai halatta ta zubar da shi ba ta kowane hali. 
Saiyid Sabik
Amma Mai Fikihus-Sunna Saiyid Sabik yana kawo wa a juzu’i na biyu na littafin a shafi na 193  a cikin bayaninsa da na takaita shi kamar haka: Musulunci yana son yawaita iyali kuma bai hana kaiyade iyali ba a bisa wasu halaye na musamman kamar ga wanda ba ya iya tarbiiyar ‘ya’yansa tarbiiya ta gari saboda yawan iyali ko talauci, ko mace ta kasance tana da rauni ko saurin daukar ciki. 
Ya ce: A irin wannan halin wasu malamai suna ganin mustahabbi ne kaiyade iyali. Imam Gazali ya kara kan haka da cewa: Haka ma idan mace tana jin tsoron kyawunta kar ya tafi. Sau da yawa mata suna da kyau, amma idan suka haihu daya ko biyu sai kyawunsu ya fara tafiya. 
Ya ce: Wasu malamai sun tafi a kan halaccinsa ta kowane hali suna masu dogaro da hadisai a kan haka. Kamar yadda yake a ra’ayin Shafi’I, da Al-baihaki, da Sa’ad Dan Abi Wakkas, da Abi Aiyubal Ansari, da Zaidu Dan Sabit, da Dan Abbas (R. A) kuma shi ne mazhabar Maliki, da Shafi’i. Ya ce: Ahluz-zahir ma’abota zahiri suna ganin haramcin kaiyade iyali da hana azalu suna masu dogaro da wasu hadisai. 
Bakir Sharif Al-Kurshi
Amma Bakir Sharif Al-kurshi a littafinsa na Tsarin Siyasa a musulunci a shafi na 246 yana kawo tsarin tafiyar da al’amura a musulunci ne, zamu yi kokarin kawo wasu daga cikinsu a nan saboda ya shafi abin da muke magana a kai ta wani bangare . Ya ce: Abubuwan da daular musulunci ta ginu a kansu na siyasarta ta cikin gida su ne: 
1. Tsayar da adalci
2. Kawar da talauci
A cikin wannan a bayanansa ya kawo cewa malaman tattalin arziki sun tafi a kan wajabcin kaiyade iyali domin tsoron yawaitar mazauna duniya da kuma tsoron kada dan adam ya kasa zama nan gaba a duniya. Ya ce: Amma tsarin musulunci ya yi kokarin maganin wannan matsala ta hanya mai sauki wacce ba ta jawo wani halaka ko cutarwa ga kowane mutum daga al’umma sabanin yadda tsarin duniya yake a yau. Hakika tsarin tattalin arziki a musulunci ya wajabta yada yalwa tsakanin al’umma da lamunce rayuwarta, bai bayar da wata mafaka ba ga talauci da rashin kwanciyar hankali. 
Ya ce: Ikbal yana cewa: Bincikena bayan na karanta shari’ar musulunci karatu mai zurfi mai tsawo ya kai ga cewa; duk inda aka fahimci wannan shari’a fahimta mai kyau kuma aka aikata ta kamar yadda ya kamata to hakkin rayuwa zai zama mai sauki ga kowa. 
Ya ce: Matsalar burodin ci tana dada ci gaba, sai dai da dacewar Allah mun sami warwara a cikin shari’ar musulunci da hukunce-hukuncenta. Ya ci gaba da cewa: Zai nuni da wasu daga cikin hanyoyin dalla-dalla: 
1. Aiki tukuru domin samar da kayan masarufi daga abubuwan da kan sanya tabbatar hakan su ne: -
a. Samar da aiki ga al’umma 
b. Dauke Haraji daga kan raunanan mutane talakawa da saukaka shi. 
c. Karfafa ‘yan kasuwa da masu sana’a da manoma da hana abin da kan iya rusa tattalin arziki kamar caca da boye kaya da kudin ruwa da sauransu. 
2. Hana taskace dukiyar kasa a hannun daidaikun mutane, wannan ana iya samar da shi ta wasu hanyoyi kamar haka: 
a. Iyakance nau’in cinikaiya ta hanyar haramta wasu nau’i na cinikaiya a kasa kamar; 
o Hana Boye kaya
o Hana Cin riba
o Tsara Awo da Sikeli
o Haramta Cinikin jahilci, kamar sayar da abin da kowa ya jahilci abin da yake hannun dayan. 
3. Gado 
4. Zakkka 
5. Khumusi: Wannan ana fitar da shi daga abubuwa kamar haka: 
a. Ganima
b. Ma’adinai
c. Arzikin kasan ruwa
d. Halal din da ya cakuda da haram
e. Taska
f. Kasar zimmi da ta cirata zuwa gare shi daga musulmi 
g. Ribar cinikaiya. 
6. Ciyarwa a tafarkin Allah
7. Lamunin zamantakewa, wannan wani abu ne da ya hau kan daula ta samar da shi ga talakawanta kamar haka: -
a. Toshe bukatun talakawa daga Baitul mali, da ya hada da ciyarwa da biyan bashi, da samar da aiki da kayan masarufi na yau da kullum, ko taimakon nakasassu da raunana, da tsofaffi, da marayu. 
b. Shimfida aminci da samar da shi. Wannan yana iya samuwa ta hanyar tarbiiyatar da ‘yan kasa da sanar da su hakkin junansu a tsakaninsu. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: