bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:46:37
89> Abin da ya kamata a karanta a cikin salla bayan yin niyya da kabbarar harama a jere kamar yadda zai zo ne
Lambar Labari: 326
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Ga Manzon Rahama Da Alayensa Tsarkaka

CI GABAN BAHASIN AHKAM :-

Yadda Ake Salla
 89> Abin da ya kamata a karanta a cikin salla bayan yin niyya da kabbarar harama a jere kamar yadda zai zo ne:
Karanta fatiha: "Bismillahir rahmaninr rahim. Alhamdu lillahi rabbil alamin. Arrahmanir rahim. Maliki yaumiddin. iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in. ihdinas siradal mustakim. Siradallazina an'amta alaihim. gairil magdhubi alaihim waladh'dhalin".
Karatun sura:- "Kul huwallah ahad. Allahus samad. Lam yalid wa lam yulad. Wa lam yakun lahu kufuan ahad".
Zikirin ruku'u:- "Subhana rabbiyal azim wa bi hamdih".
Zikirin sujjada:- "Subhana rabbiyal a'a'la wa bi hamdih".
 Tahiya:- "Ash'hadu anl la ilaha ilal Lah, wa ash'hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluh, allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad".
 Tasbihohi guda hudu:- "Subhanal lah, wal hamdu lillah, wala ila ha illal Lahu, wal lahu akbar".
 Sallama:- "Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu, warahmatul lahi wa barakatuh", wannan mustahabbi ce.
"Assalamu alaina wa ala ibadullahis salihin", Ita wajiba ce idan bai zo da sallama mai zuwa ba nan gaba.
"Assalamu alaikum wa rahmatul Lahi wa barakatuh", ita ma wajiba ce in bai zo da ta daya da ta biyu ba.
 90> (m.1006) Wajibi ne baligi ya san hukunce-hukuncen salla ta yadda ba zai yi kuskure a cikin karatunta ba, wanda kuwa ba zai iya koyon karatunta kamar yadda ya kamata ba, wajibi ne ya karanta abin da ya saukaka gare shi, bai kuma halatta ya bar ta ba a kowane hali.
 91> (m.1002-1016) Wajibi ne namiji ya bayyana karatun fatiha da sura hatta harafin karshe na sallar asuba da sallolin magriba da isha, amma mace tana da zabi tsakanin bayyanawa da boyewa, kuma wajibi ne a kan dukkan namiji da mace su karanta fatiha da sura a cikin sallar azahar da la'asar a boye, haka nan a raka'o'i na uku da na hudu yayin karatun fatiha ko tasbihi.
 Salla tana baci da ganganta bayyana abin da ya wajaba a asirta, haka ma da asirtawa a wajen da ya wajaba a bayyana, sai in ya kasance wanda ya jahilci hukunci ko ya manta.

Mas'alolin Ruku'u
 92> (m.1031) Wajibi ne yin ruku'u a kowace salla bayan gama karatu: yadda ake yinsa shi ne; mutum ya sunkuya ta yadda zai iya sanya hannayensa a kan gwiwoyinsa, kuma wajibi ne ya sukuya zuwa ruku'u daga tsaye.
 93> (m.1049) Bayan kammala zikirin ruku'u wajibi ne ya daidaitu a tsaye har sai jikinsa ya nutsu a tsaye, sannan ya sunkuya zuwa sujjada. Da zai sunkuya zuwa sujjada ba tare da ya daidaita ba ko ya tabbata a cikin nutsuwa ba dagangan, sallarsa ta baci.
 94> (m.1031,1042,1060) Idan ya zo da zikirin ruku'u ko sujjada kafin ya isa zuwa gejin ruku'un ko sujjada, ko kafin jikinsa ya tabbata kuma yana mai gangantawa, ko ya dago kansa daga ruku'u ko sujjada kafin ya kammala zikiri dagangan sallarsa ta baci, amma idan hakan ya faru bisa rafkanwa, sai ya tuna daga baya, to sallarsar ta inganta.

Mas'alolin Sujada
 95> (m.1054) Wajibi ne yin sujjada guda biyu a cikin kowace raka'a daga salloli wajibabbu da mustahabbai.
 Sujjada ita ce sanya goshi da tafukan hannaye da kokon gwiwoyi da kan manyan 'yan yatsun kafafuwa a kan kasa.
 96> (m. 1065) Da zarar ya kamala zikirin sujjada ta farko wajibi ne ya zauna har sai ya nutsu sannan ya yi sujjada ta biyu.
 97> (m. 1085) Wajibi ne yin sujjada a kan kasa ko abin da ya tsuro daga kasa banda wanda ake ci ko ake sawa (tufafi) amma abin da ba za a kira shi kasa ba na daga ma'adinai kamar zinare da azurfa da makamancinsu bai halatta a yi sujjada a kan su ba.
 98> (m. 1074) Wajibi ne bigiren sujjada ya kasance mai tsarki.
 99> (m.1099) Haramun ne yin sujjada ga wanin Allah (S.W.T), don haka abin da wasu ammawa suke yi na sanya goshinsu a kan kasa suna masu fuskantar kaburburan Imamai, idan ya kasance ba da nufin yin shirka ba to babu komai, in ba haka ba, ya haramta.
 100> (m.1102) Wajibi ne gaggauta sujjada ga wanda ya karanta ko ya ji an karanta ayoyin sujjada na cikin surori madaukaka hudu wadanda su ne:- Sajadah, Fusilat, Najami, da Alaki. Idan dai bai yi sujjada ba bayan karanta ayar sakamakon mantuwa, sai ya yi ta duk lokacin da ya tuna.

Mas'alolin Rafkanwa
 101> (m.1118-1121) Idan ya manta dayan wajiban salla, sai ya shiga cikin wajibin da yake bayansa, idan har bai riga ya shiga rukuni daga rukunan salla ba sai ya tuna da abin da ya manta, to wajibi ne ya dawo ya sake wajibin da ya manta, da wandanda ke bayansa na daga wajibai amma idan ya riga ya shiga cikin wani rukuni daga rukunan da yake bayan wajibin da ya manta ba zai yiwu ya riske shi ba. A wannan yanayin idan abin da ya manta rukuni ne sallarsa ta baci, in ba haka ba ta inganta, kuma ya wajaba ya rama bangarorin da ya manta kamar su tahiya sannan ya yi sujjadar rafkanwa.
 102> (m. 1245) Wajibi ne yin sujjadar rafkanwa bayan gama salla saboda wasu abubuwa masu zuwa, daga cikinsu akwai:-
1.    Magana a cikin salla bisa rafkanwa.
2.    Sallama ba a bagirenta ba tare da rafkanwa, kamar idan ya yi sallama bayan raka'a ta daya.
3.    Mance sujjada guda daya.
4.    Mance tahiya (tashahhudi)
5.    Kokwanto tsakanin raka'a ta hudu da ta biyar bayan sujjada ta biyu a cikin salla mai raka'a hudu.
 103> (m.1259) Yadda ake yin sujjadar rafkanwa shi ne: ya yi niyyar sujjadar rafkanwa da zarar ya yi sallama, sannan ya sa goshinsa a kan abin da ya halatta a yi sujjada a kansa, sannan sai yace: "Bismillah wa bilLah wasallal Lahu ala muhammad wa ali muhammad". Ko yace: "Bismillah wa billah allhumma salli ala muhammad wa ali muhammad". Mafifice yace: "Basimillah, wa bilLah, assalamu alaika ayyuhan nabiyyu warahmatul Lahi wabarakatuhu"; Sannan ya zauna, ya yi sujjada ta biyu sai ya yi dayan zikirorin da aka ambata, ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama.

Mas'alolin Kokwanto (Shakku)
 104> (m.1174) shakkun da suke cikin salla guda ishirin da uku ne. Takwas daga ciki suna bata salla, shida kuma ba a la'akari da su, tara kuma salla tana inganta da su.

Shakkun Da Suke Bata Salla
1-    Kokwanton adadin raka'o'in salla, a salla mai raka'a biyu, kamar sallar asuba da sallar matafiyi.
2-    Shakku a cikin raka'o'in magriba.
3-    Shakku tsakanin raka'a daya ko sama da haka.
4-    Shakku tsakanin raka'a ta biyu da sama da haka, a salla mai raka'o'i hudu kuma kafin ya kammala sujjada ta biyu.
5-    Shakku tsakanin ta biyu da ta biyar da tsakanin ta biyu da sama da ta biyar.
6-    Shakku tsakanin ta uku da shida ko tsakanin ta uku da sama da shida.
7-    Kokwanto a cikin adadin raka'o'i hudu ta yadda bai san ko nawa ya yi ba.
8-    Kokwanto tsakanin hudu da shida ko tsakanin hudu da sama da shida.
 105> (m.1175) Bai halatta ba a yanke salla da gaggawa yayin faruwar dayan shakkun da suke bata salla, lalle wajibi ne ya bi a hankali ya yi tunani har sai kokwanton ya tabbata ko ya sami yankewar kaunar samun yakini ko kuma ta yiwu ya samu zato (mai bayar da nutsuwa) game da bagarorin adadin raka'o'in da yake shakku (tayiwu ya gano cewa wannan shakkun) ba a la'akari da irinsa.

Shakkun Da Ba a La'akari Da Su
106> (m.1176) Kokwanton da ba a la'akari da su guda shida ne, su ne:-
1.    Kokwanto a kan abu bayan an wuce mahallinsa, kamar idan ya yi kokwanto a lokacin da ya yi ruku'u cewa ya karanta fatiha ko kuwa.
2.    Kokwanto bayan sallama.
3.    Kokwanto bayan fitar lokacin salla.
4.    Kokwanton mai yawan kokwanto.
5.    Shakkun liman a cikin adadin raka'oin salla, tare da kiyayewar mamu gare ta. Haka ma kokwanton mamu a cikin adadin raka'o'in salla tare da kiyayewar liman gare ta.
6.    Shakku a cikin sallar nafila.

Shakkun Da Salla Take Inganta Tare Da Su
 107< (m.1208) Wajibi ne a bi sannu-sannu wajen yin tunani a cikin yanayoyi tara yayin bijirowar shakku a cikin adadin raka'o'in salla mai raka'a hudu, idan ra'ayinsa ya tabbata da zato ko da yakini a bisa wani bangare sai ya yi gini a kansa ya cika sallarsa, in ba haka ba, ya yi aiki da abubuwa masu zuwa:-
1.    Idan ya yi shakku bayan dago kansa daga sujjada ta biyu bisa cewa ya sallaci raka'a biyu ne ko uku, hukuncinsa shi ne ya yi gini a kan ta uku, sannan ya kara raka'a daya a kai, bayan ya gama salla sai ya zo da wata raka'ar guda ta ihtiyadi¸ ko dai ya zo da ita ta hanyar yin raka'a daya a tsaye ko raka'o'i biyu a zaune da yadda bayaninta zai zo nan gaba.
2.    Idan ya yi kokwanto tsakanin ta biyu da ta hudu bayan ya dago kansa daga sujjada ta biyu, hukuncinta shi ne ya yi gini a kan ta hudu, kuma ya cika sallarsa, sannan ya zo da raka'o'i biyu na ihtiyadi a tsaye.
3.    Shakku tsakanin ta biyu da uku da hudu, bayan ya dago kansa daga sujjada ta biyu, hukuncinta shi ne ya yi gini a kan ta hudu, sai ya cika sallarsa, sannan ya zo da sallar ihtiyadi; raka'a biyu a tsaye, (da kuma) biyu a zaune.
4.    Shakku tsakanin ta hudu da ta biyar ko tsakanin ta hudu da ta shida, ko tsakanin ta hudu da sama da shida bayan da ya dago kansa daga sujjada ta biyu, hukuncinta shi ne; ya yi gini a kan ta hudu, ya cika sallarsa sannan ya yi sujjadar rafkanwa bayan ya kammala salla.
5.    Idan ya yi shakku tsakanin ta uku da ta hudu, a ko'ina ya kasance, hukuncinsa shi ne ya yi gini a kan ta hudu, ya cika sallarsa, bayan haka sai ya yi sallar ihtiyadi, ko dai ya yi daya a tsaye, ko kuma biyu a zaune.
6.    Idan ya yi kokwanto tsakanin ta hudu da ta biyar a lokacin da yake tsaye, hukuncinsa ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama sannan ya yi sallar ihtiyadi raka'a biyu a tsaye ko kuma biyu a zaune (bisa zabinsa).
7.    Idan ya yi kokwanto tsakanin ta uku da ta biyar a yayin da yake tsaye, hukuncinsa ya zauna ya yi tahiya, ya yi sallama, sannan ya yi sallar ihtiyadi raka'o'i biyu  a tsaye.
8.    Idan ya yi kokwanto tsakanin ta uku da ta hudu da ta biyar a lokacin da yake tsaye, hukuncinsa ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama sannan ya yi sallar ihtiyadi raka'o'i biyu a tsaye da kuma biyu a zaune.
Idan ya yi shakku tsakanin ta biyar da ta shida yayin da yake tsaye, hukuncinsa shi ne ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama ya yi sujjadar rafkanwa. Kuma bisa ihtiyadi na wajibi ya kuma yi sujjada ta rafkanwa saboda tsayuwa da ya yi ba a mahallinta ba.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: