bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:55:01
Kamar yadda ya gabata ba wasu qayyadaddun shekarun aure balle muce mace ta auri namiji mai shekaru kaza, saidai kawai zamu ambaci bambancin wasu abubuwan
Lambar Labari: 329
1-    LAFIYAR JIKIN SA
Lafiyar jikin namijin da za a aura abu ne muhimmi kuma yana da asali a kan al'amarin aure, haqiqa an yi wasiyya a bisa gwargwadon hali, a kan aurar namiji lafiyayye ta vangaren kwanciya ba marar haihuwa ba.
Haqiqa Imam Ali shugaban muminai (AS) ya yi wani hukunci inda ya jarraba wani yaro xan tsoho mai yawan shekaru, ya haife shi, da sa'annin sa inda aka same shi xan tsohon ya yi rauni wajan gudu da zabura, saboda haka muke cewa qarfi da raunin namiji yana tasiri da a kan qarfi da raunin xan sa.

2-    SHEKARUN SA
Kamar yadda ya gabata ba wasu qayyadaddun shekarun aure balle muce mace ta auri namiji mai shekaru kaza, saidai kawai zamu ambaci bambancin wasu abubuwan, domin samun bambancin shekaru tsakanin ma'aurata yana samar da fifikon fahimta, da riskar abubuwa da lamari mai zurfi da qwarewa.
Sakamakon haka sai ma'aurata su yi yi rayuwa ta xaya na tashin xaya sai ya zama wajibi ne a rayu tare.
Haka idan aka samu bambancin shekaru masu yawa a tsakanin su, shima na kawo savanin riskar  daxin kwanciyar hankali.
Aure wanda hakan kuwa yana haifar da matsala ga ma'aurata, domin kowanne daga cikin su miji ko matar ba wanda zai iya shayar da xan uwan sa shayarwa cikakkiya.
Hakan na yin tasiri ga rayuwar aure inda inda zata zama ta yi sanyi qalau, namiji na kaiwa shekaru 40 yana cikin qarfi da kuzarin buqatar mace koma shekaru 35.
Abinda ya fi kyau ya kasance bambancin shekarun ma'aurata shine shekaru uku ko shida, domin balagar mace daga shekara 9 ta farawa namiji a shekara 15 ya zama ratar da ke tsakanin su shekara shida ce. Ya vangaren girman jiki mace a shekara 13-14, naqmiji kuma daga 17 ya zama ratar shekara uku, idan aka samu bambanci tsakanin ma'aurata ya wuce haka ko ya gaza haka lallai babu daidaitar shekaru a tsakanin su.

3-    TATTALIN ARZIKIN SA
Mumini tsaran mumina ne, aure kuma wani qulli ne mai tsarki saboda haka duk wani sharaxi da aka qulla a cikin sa wajibi ne a karveshi a haka matuqar tun farko an yadda da shi yayin qulla aure, saboda lura da maslahar shari'a wajibi ne a tantance a bisa mtsayin mutum da iyawar sa a bisa daukar nauyi rayuwar aure.
Ruwayoyin musulunci sun qarfafa hakan da cewa auri mutumin da yake da sana'a mai kyau wanda zai iya xaukar nauyin aure da ita, haka kuma an yi wasiyya da rashin aurin rago a kan neman abinci, kada ya kasance wanda yake kallafawa mutane kansa yana xan samun abinda zasu bashi wanda zai xauki nauyin ilalin sa da shi.

4-    WASU SIFFOFIN DA YA KAMATA A LURA DA SU
Daha ciki wasu sufofin da ya kamata mace ta lura da su ga namijin da zata aura  domin cimma burin ta na hadafin yin auren, ciki akwai kunya, kai kawo, kuzari, sadaukantaka, fara'a, barkwanci, kunya da himma, mai madaidaicin kishi, masani kan hukunce-hukuncen addini, mai sabo, gaskiya duk da cewa zai yi wuya a samu dukkan waxanna abubuwan baki xaya ga mutum xaya amman dai a samu mafi yawan su shi yafi a samu ga namiji da za a aure shi.

WASU ABUBUWA MASU QARANCIN MUHIMMANCI
Wasu abubuwan da ba wajibi bane, ko kuma basu da muhimmanci sai xan kaxan, waxanda wasu wawayen ke xaukar su da muhimmanci ko wajibi, kamar kasancewar namiji talaka ko marar kuxi ko matsayi irn na muqami, ko suna hanan ma kyau da sauran su.
Abinda yazo ma wajan neman aure wajibi ne a kula da shi shine, mijin ya kasance mai qoqari wajan nema, amman sauran abubuwan ba muhimmai bane, inda ya kasance mai kuzari ne a kan neman arziki, idan kuma ya zaama ya rasa wannan to ina fa'idar wannan namijin malalaci balle a aure shi.

HANYAR DA ZA A BI A YI BINCIKE
Mun ce wajibine mace ta yi bincike a kan namijin da zata aura muna kuma kawo abubuwan da zata tabbatar a gareshi, amma ta yaya zata yi binciken? Akwai hanyoyin bincike biyu kamar haka :

1-    TA HANYAR TAMBAYAR QWARARRU AKAN LAMARIN AURE
A nan abinda zata yi ta tambayi uba ko uwa ko wani xan uwa daga cikin makusanta mai hangen nesa, ta wajan su zata tattara bayani da kuma son samu abubuwan da ta kasa ganewa  kamar yadda muka faxa a baya, kafin hankali wajan zavan namiji dole ne ya zama ya fi kaifin zuciya domin rayuwa hankali ne ke tsara ta, zuciya kuma na yi mata ado.
Tun da haka ne dole ne a bar hankali ya yi aikin sada farko, in yaso daga baya zuciya da soyayya su biyo baya a lokacin da aka shiga rayuwar aure ba a farkon nema ba.
2-    TA HANYAR ZANCE DA TATTAUNAWA DA SHI
Bayan ta yi bincike ta hanyar tambayar manya da makusanta, sai ta shiga yin bincike ta hanyar tattaunawa da shi, a lokacin yin binciken zata nutsu sosai tya sa tunanin tadon sanin ra'ayoyin sa kuma ta nan ne zata san tunanin sa, kuma zata dinga jarraba shi ta hanyoyi da yawa kamar ta hnayar wasiqa ko magana baki da baki ko ta abokin sa ko 'yan uwan sa da sauran su.

SHARUXXAN MUSULUNCI A KAN MATAR DA ZA A AURA
Ruwayoyi da sharuxxa a kan zavar mace ta fi yawa a kan ta namiji saoda mace ita ce mai xawainiyar iyali musamman xaukar nauyin tarbiyyar yara inda zata hutar da mijin ta, domin mace abar halitta ce mai tausayi wadda  zata iya samar da yara salihai na gari wani lokacin ma ta kan maye gurbin uba lokacin da baya nan.
Musulunci ya yi nuni bisa zavin macen da ta dace a aura, zamu kawo abubuwan da suke wajibi wajan zavar abokiyar zama, kamar yadda ya gabata mun kawo sharuxxan zavar miji wanda kuma sharuxxan mace yafi zama wajibi namij ya lura da su, ya duba cikin 'yan mata ya ga wadda ta tattaraq abubuwan da zamu kawo haha:

1-    ZURIYAR DA TA FITO
A nan akwai wasiyyoyi da ruwayoyi da yawa  kamar yadda muka ambaci wasu daga ciki a dunqule don tsoratarwa a kan aurar yarinyar da ta fito daga mummunan gida.
Manzon Rahama (SAW) ya ce : "na hore ku kadra a dumin, sai aka tambgaye shi, ya rasulillahi menen kadara a dumin? Sai yace kyakykyawar mace a mummunan tsatso"1.
Haka nan an yi wasiyya da aure a iyalan da aka san su da qarfi da kwarjini.
Imam Ali (AS) ya kasance xan uwan sa aqilu ya zavar masa matar da zai aura, domin shi aqilu masani ne a kan salsalar larabawa, yayin da Imam Ali (AS) ya ce masa ka zavamin mace, 'yar larabawa ta haifa min mahayin doki da zai taimaki xana Hussai (AS) a karbala, sai ya ce masa , ka auri Umma Banin, haqiqa babu wanda ya kai babanta sadaukantaka da iya wasa da doki.

2-    IMANI DA AQIDAR TA
Musulmi zai auri mace musulma ba zai auri mushrika ba, sai dai mai addinin da ya sauka daga sama koda an chanja koyarwar sa, shima auren wani lokaci ba na dindindin ba, haka nan musulunci ya yi wasiyya da kada a auri macen da take qiyayya ga Ahlulbait (AS) wato (nasibiyya), Imam Baqir (AS) jikan Manzon Rahama (SAW) ya auri wata mata sai ya sake ta daga baya, da aka tambaye shi dalilin yin haka, sai ya ce nasibiyya ce.
Imanin wadda za a aura wajibi ne ya zama miqaqqe ta zamo tana sa Allah a dukkan al'amuran ta, ta san cewa Allah na ganini ta kuma shi shaida ne a kanta, ta yi imani da ranar qiyama da hisabi, ta san gaskiya da vata, kuma imanin ta ya wuce iya baki da zuciya, ya kai ga aiki a fili.

3-    XABI'UN TA
Ruwayoyin musulunci sun yi hani ga auren mace mai munana xabiu karkatacciya, domin daga dalilin aure shine samun hutu da nutsuwa da jin daxi, su kuma waxannan abubuwan basa samuwa sai da kyawawan xabi'u, domin macen da take da munanan xabi'u bata ganin munin abu,  kamar yadda namiji ke kula da muni fuska,  ido, baki, gashi sauran sassan jikin mace, haka nan ya kamata ya kula da xabi'un ta, domin idan halayen ta suka zamo munana kamar a ce tana da , qarya, munafunci, al'fasha, zama da ita zai juya rayuwa ta zama jahannama mai zafi.
Haka nan an yi wasiyya da kada a auri matar da take qula mummunar alaqa da wasu mazaje a waje domin rayuwar aure na buqatar tsarki da tsarkaka, saboda ba a son a zauna da irin waxannan 'yan matan ballagazazzu.
Haka kuma an qarfafa hani a kan auren mazinaciya sai da idan ta tuba, muddin dai akwai kamammiyar mace tsarkakakkiya ko kuma akwai wata fa'ida, a cikin al'uuam wajan auren ta, a bisa kowane hali wajibi ne namiji ya samu mace tsarkakakkiya, kamammiya, wacce ta nisanta daga mummunan xabi'u ma'abociyar halin girma.

4-    KAIFIN TUNANIN TA
Wajibi ne namiji ya auri mace mai kaifin tunani kuma wadda tunanin ta ya wuce kyale-kyalen duniya kawai, domin idan ya zama kullun tunanin ta ado da sharholiyar duniya, wannan matar ba wadda ta zama abokiyar zama bace, domin ba aminci da tabbas a kan 'ya'yan ta.
Dole tunanin ka ya zama tanade-tanaden gina iyali, saboda shagali da sharholiya ba koda yaushe, kuma ya zama kullium tana tunanin wasu wato ita bata tunanin kanta.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: