bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:56:35
Mutane masu hankali da hikima na bawa tarihi muhimmanci na musamman, kamar yadda Imam khimani yake cewa: “Tarihi malamin mutane ne”
Lambar Labari: 330
Gabatarwa
Da yawa daga cikin ayoyin qurnani sun bawa al’amarin tarihi muhummanci na musamman, wannan kuwa sabada cewa Alqur'ani an saukar da shi ne domin shiryar da xan’adam zuwa ga marabauciyar rayuwar duniya da lahira da kuma kare shi daga vata da tavewar duniya da ya lahira ta wanan vangaren, ta xaya bangaren kuma,  a cikin tarihi akwai darasosi da izna masu qima da tasiri wajen shiryar da bil’adama zuwa ga rabauta da kuma nisanta daga shexan.  Saboda haka dalilin da ya sa a ka cirato qissar da yawa daga ckikin Annabawa shi ne don a koya wa mutane masu hankali yadda zasu xauki darasi daga qissoshinsu: {haqiqa a cikin labaransu akwa izna da darasi ga masu hankali} (Surar Yusifa aya ta 111).
Mutane masu hankali da hikima na bawa tarihi muhimmanci na musamman, kamar yadda Imam khimani yake cewa: "Tarihi malamin mutane ne”, don haka a duk lokacin mutun ya buxe shafuffukan abubuwa da suka faru a tarihi yana karantawa, ba tare da aya Ankara ba sai ya sami kansa yana gioyen bayana mutanen da suka riwi gaskiya kuma yana savawa da mutanen da ka riqi bata, kuma sai riqa lakkon abin da ya faru da su a baya yana koyar darisi daga wancanenka kuma yana yin mai amfana da su a cikin rayuwarsa ta nan gaba; saboda haka yanayin mutanen da suka gabata da yanayin sauran mutane duk iri xaya ne, kuma ta yiyu a riqa maimaita abubuwan da suke daidai da waxanda suke na kuskure. bari mju bada misialin, Idan ka duba labarin Annabi Yusif da yadda Yan’uwansa suka riqa yi masa hassada kamar yadda ya zo a cikin Qur'ani zamu fahimci cewa lalle hassada tushe ce ta varna da munannan ayyuka masu yawan gaske waxanda xan’adam yake aiwatarwa a rayuwarsa; ta yadda da wutar hasada zata huru a zuciyar mutum, a lokacin xan’uwa ba zai tava tausayawa xan’uwansa ba, ta xaya vangaren kuma da a ce zai dogaraga Allah Ta'ala ya yi imani da shi har abada Allah Ta'ala ba zai tava barin sa shi kaqai ba; ta yadda a lokacin da Yusif ya sami kansa a tarkon fushin ‘yan’uwansa, sai temakon Allah Ta'ala ya lulluve shi ya kuvutarda shi daga tarkon maqiyansa, kai hatta matarsarki kanta ba ta tava.
Ta xaya vangare kuma, da ace xan adam zai yi imani da Allah Ta'ala kuma ya dogara da shi, lalle Allah Ta'ala ba zai tava bariinsa shi kaxai ba kamar yadda ya yi wa Yusif ya yi da yan uwansa suka cutar da shi, a yayin da ya tsira daga damqar ‘yan uwansa da temakon Allah Ta'ala, ballantana ma haqiqa matar sarki ba ta iya halakar da shi ba, kuma tare da cewa an jarrabce shi da shiga kurkuku na tsawon shekaru amma sai ga shi daba baya ya wayi gari babban wazirin sarkin Misra, kuma ya sami matsayi mai girma matsayin mutane da yawa ke fatan isuwa zuwa gare shi kuma suke fatan matsayin ya zama na su.
Bisa wannan, yin haquri kan musibu da yin juriya da ta shi faxi a gaban wajen yin faxa da vata, da tsayawa qyam a kan yin faxa da gaskiya na sa mutun ya kai ga cin nasara.
Bayan da muka san irin rawar da tarihi yake takawa wajen shiryar da xan adam, tambayar da zata rika jefo kan ta kai tsaye a yanzu ita ce: wane vangare na tarihi ne yake da martaba ta farko wanda karanta shi ke da matukar mihimmanci da amfani?
Amsar wanna ita ce: tun da har karanata ko wane vanbaren tarihi ba abu ne mai yiyuwa ba, ya zama wajibi a zavi vangarorin suka fi ko wane mihimmanci kuma a sararin yake cewa vangaren da ya fi kowanne vangare mihimmanci shi ne vangaren da ya fi taka bbar wara wajen shiryar da xan’adam da nusantar da shi. Kuma da yake tarihin ma’abota addini hakama tarihin jagororin addini da abin da rayuwar su ke cike da shin a daga yanayi na tsanani da na sauki wajen tashi faxin su da kafirai na da rawa mai tasirin da yake takawa a aikace wajen vunqasa da rabautar matemaka gaskiya da adalci; saboda haka karanta tarihi musulunci da tarihin rayuwar Manzon Allah (s.a.w) da tarihin rayuwar halifofi dama abubuwan da suka faru da mabiya musulunci na haqiqa tn daga lokacin gaiba har zuwa lokacin da muke cikin ya zama yana da mihimmanci a mataki na farko kuma yana da mihimmanci na musamman, la’akari da cewa shi ne addini na qarshe kuma makaxaicin addinin da hannun masu canja wa da jinkita wa (wato canja ayoyi da shigar da son rai) bai isa zuwa gare shi ba.
Abu na biyu da ya zama ba kamawa mu yi faxakarwa a kansa shi ne haqiqa rabautaccen kararu ga ko wane littafi ya tsaya ne kan wani salo na musamman, idan har mutun ya yi wa kansa dabaibayi da shi, zai iya amfana da ita sama da yadda zai yiyu ya amfana da wannan karatun, in ba hakaba karatun ya zama tamkar leqa abin da ke cikin litattafi kaxai da bas hi da wani amfani.
Misalin wannan shi ne abin da muke gani na tilawar Qur'ani da wasu ke yi wacce ta taqaitu da furta lafazi da sauti mai daxi, da kuma yadda wasu ke saka dage wajen hardace shi kaxai, kamar yadda wasu ke karanta Qur'ani don su samin lada. A daidai lokacin da wasu jama’a suke karanta Qur'ani don su koya daga tunanin da yake xauke da shi suke wa’aztuwa da nasihohinsa suke saurara hikimominsa don su amfana da su a wajen tafiyar da rayuwarsu, waxannan mutanen ne suke yin aiki da abin da Qur'ani da kansa ya yi wasici da shi, sai kaga suna karanta shi cikin nutsuwar da ke haxe da tuntuntuni da tadabbiri a cikin ayoyinsa don su aiwatar
da shi a aikace a cikin rayuwarsu.
Wannan lamarin haka yake wajen karanta tarihi ma, ta yadda wasu suke karanta shi don ya vebe musu kewa kuma su cenyi lokacinsu kuma su san abubuwan da suka faru kuma su san labarin mazajen wancen lokacin, a daidai lokacin da wasu suke karanta shi don xaukar izna da darasi daga abubuwan da suka wakana a baya don su rayuwarsu ta nan gaba, kuma don su bi tafarkin annabawa (a.s) da Imamai (a.s) da manyan malamai da masana tare da kauce wa ayykan ko - mu ce tafarkin - azzalumai da jahilai.
Yana daga cikin sannan abi cewa wanda yake son xaukar izna daga tarihi ya zama wajibi gare shi ya karantashi da bin diddigi da tuntuntuni, ba ya karanta shi karatu na sama-sama ba, ba tare da waiwayen sakon da zamanin da ya shuxe yake xauke da shi wanda yake son isar da shi ga ‘yan ba ya ba.       

HAIHUWA DA YARINTA DA LOKACIN SAMARTAKA:
An haifi Annabin Musulunci (s.a.w) a shekarar giwaye  (569-570) a garin Makka a Hijaz. Sunan babansa Abdullahi babarsa kuma sunanta Amina. Kimanin wata uku da haihuwar Manzon Allah (s.a.w) mahaifinsa Abdullahi ya rasu a wata tafiyar kasuwanci da ya yi zuwa Madina, sai kakansa Abdulmuxxalib ya xauki nauyin tarbiyyarsa da kula da shi, sannan Halimatus Sa’adiyya mai shayarwa ta dinga shayar da shi har kimanin shekara biyar yana rayuwa a qauye. A lokacin da mahaifiyarsa Amina ta karve shi sai ta tafi da shi Madina, sai dai kash, ba ta wuce wata xaya a Madinan ba ta nufi hanyar Makka don komawa can nan da nan mutuwa ta riske ta a xayan masaukan matafiya da ake kira da Abwa’u, aka binne ta a can.
Haka Manzon Alalh (s.a.w) ya rasa mahaifiyarsa ita ma yana xan shekara shida, xaya daga cikin matafiyan da suka zo Makka ne ya kaiwa kakansa Abdulmuxxalib tare da baiwar babansa (Ummu Aiman). Lallai Abdulmuxxalib ya kyautata kula da jikan nasa, ya kuma nuna masa qauna ta musamman, har ma ya kasance yana ba da labarin cewa nan gaba fa zai sami wani matsayi mai girma.
Bayan nan Manzon Allah (s.a.w) ya sake rasa kakansa yana xan shekara takwas, don haka, sai baffansa ya xauki nauyin kula da shi, wanda shi ne ya zama shugaban Banu Hashim bayan rasuwar Abdulmuxxalib, Abdulmuxxalib mutum ne maxaukaki wanda ake girmama shi a Makkah, kai har qabilar Quraishawa ma suna girmama shi. Abu Xalib ya kasance yana son Manzon Allah (s.a.w) so mai yawa, kai ya fi son sa ma a kan ‘ya’yansa.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: