bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      13:01:32
Abu xalib ya tafi Sham tare da Muhammad (s.a.w) a lokacin da yake kan ganiyar samartakarsa a tare da tawagar
Lambar Labari: 331
1- KAKANNIN MANZON ALLAH (s.a.w):
Abdulmuxxalib, Hashim, Abdu Manaf, Qusayyu, Kilab, Murra, Ka’ab, Lu’ayyu, Galib, Fihr, Malik, Nadr, Kinana, Khuzaima, Mudrikata, Ilyas, Mudar, Nizar, Ma’addu da Adnan. Dangantaka ce wacce ba wata dangantaka da ta yi kusa da ita a tsarki da xaukaka da kuvuta daga kowanne irin aibin zamani.

2- TAFIYA ZUWA SHAM:
Abu xalib ya tafi Sham tare da Muhammad (s.a.w) a lokacin da yake kan ganiyar samartakarsa a tare da tawagar
Yan kasuwa masu zuwa Sham. A hanyar tafiya Sham xin sun isa garin Busra, inda suka huta a gefen xakin bautan wani malamin Kirstoci wanda ake ce masa Bahira, babban mabiyin Annabi Isah ne a nan, da wannan mai bautar ya waiwaya ya ga Manzon Allah (s.a.w) sai ya ga wasu alamomi irin na Annabi da zai zo nan gaba da aka ambace su a littafin Kiristoci a tare da Manzon Allah (s.a.w), bayan ya yi wa Manzon Allah (s.a.w) wasu ‘yan tambayoyi shi kuma ya ba shi amsa, sai ya ce wannan saurayin nan gaba zai zama Annabi. Sai ya yi wa baffansa Abu xalib wasiyya kan cewa kar ya yi sakaci da Manzon Allah (s.a.w) kuma ya lura da shi kar Yahudawa su cutar da Annabi (s.a.w), idan suka gane shi da alamomin Annabta.
3- AUREN ‘YAR KHUWAILID:
Khadija ta kasance a cikin manyan matan da suka kevanta da kamewa da hikima, tana cikin babbar qabilar Quraishawa, sau da yawa siffantuwarta da waxannan siffofi ya jawo ake yi mata laqabi da mai tsarki da shugabar Quraishawa. Khadija sun haxa danganta da Annabi (s.a.w) ta wajen kakansu Qusayyu, Khadija ta ji labarin babban matsayin Annabi (s.a.w) da haskensa na nan gaba, don haka ta yi kwaxayin ta aure shi, saboda haka ne ma ta nemi ya aure ta don haka sai ya nemi shawarar baffanninsa, bayan nan ya amince. Ita Khadija a wannan lokacin tana da shekara arbain shi kuma Manzon Allah (s.a.w) yana da shekara ashirin da biyar.

b) LOKACIN DA AKA AIKO SHI A MAKKAH:
1- FARKON AIKO SHI:
Manzon Allah (s.a.w) ya yi rayuwarsa ta quruciya da samartakarsa a cikin mutanen Jahiliyya masu yin shirka waxanda ba su da cigaba, amma duk da haka dauxar shirka da bautar gumaka da xabi’un banza basu tasirance shi ba, duk da watsuwarsu a cikin mutanen Makkah, kai shi fa ya sami tarbiyya a cikin tasrkakakken dangi masu aqidoji da daraja da xabi’unsu maxaukaka, haka kuma kariyar Allah tana kewaye da shi a tsahon lokacin, kamar yadda Imam Ali (AS) ya faxi tarbiyyarsa da xabi’unsa (s.a.w) a wannan lokacin: "Tabbas haqiqa Allah ya haxa shi da Babban Mala’iku, yana sa shi a hanyar manyan xabi’u da kyawawan xabi’u dare da rana tun da aka yaye shi”.
Lokacin da ya kusa shekara arba’in tagogin ilimin gaibu a buxe suke a gabansa, a wani lokacin yana jin saututtuka da kiraye-kiraye daga gaibu ba tare da ya ga wani ba. Manzon Allah (s.a.w) ya kasance a wannan lokacin yana yin halwa lokaci-lokaci a cikin shekara a kogon Hira tare da yawaita yin tunani da ibada. Lokacin da ya kai shekara arba’in, watarana yana kogon Hira sai ga Mala’ikan wahayi ya zo masa yana yi masa magana yana kuma karanta masa Suratul Alaq.
To haka dai Manzion Allah (s.a.w) ya kasance aka aiko shi da Manzanci, a alhalin lokacin bai tava yin karatu a wajen wani ba, kuma bai tava shiga makaranta ba, sai ayoyin Qur’ani suka fara sauka da kaxan da kaxan a cikin shekaru ashirin da uku.

2- SHEKARA UKU ANA YIN DA’AWA A VOYE:
Lokacin da yanayin garin Makka bai yi kama da mai karvar da’awar Musulunci ba, sai Manzon Allah (s.a.w) ya voye da’awarsa har tsawon shekara uku, sai ya dinga kiran wasu mutane a voye don su yarda da Tauhidi da bautawa Ubangiji makaxaici kuma su qauracewa bautar gumaka.
A wannan lokacin Musulunci ya shiga jikin duk wanda ya shirya karvarsa fiye da wanda bai shirya karvarsa ba, a lokacin da kafiran Quraishawa ba su damu sosai ba, ba su kuma yi fito na fito mai tsanani ba har wani lokaci saboda basu san haqiqanin abin da ayoyin Qur’ani da zantuttukan Manzon Allah (s.a.w) da suka qunsa ba.

KIRAN MAKUSANTA:
Bayan shekara uku da fara yin da’awa a voye, sai Allah ya umarci Annabinsa da ya kira makusantansa da danginsa zuwa Musulunci a kevance. Bayan zuwan wannan yumarnin – da ya zo a cikin ayoyi na 214-216 a Surat ash-Shu’ara – sai Manzon Allah (SAW) ya umarci Aliyu (AS) da ya shirya walima ya gayyato ‘ya’yan Abdulmuxxaluib, sai Aliyu ya gayyato makusantan Manzon Allah (s.a.w) nan da nan mutane arba’in suka zo walimar a cikinsu har da Abu Xalib da Hamza da Abu Lahab.
Bayan sun gama cin abinci sai Manzon Allah (SAW) ya miqe ya cewa waxanda suke wurin: "Ya ‘ya’yan Abdulmuxxalib tabbas wallahi ban san wani saurayi a cikin Larabawa da ya zo wa da mutanensa abin da ya fi wanda na zo muku da shi ba. Tabbas na zo muku da alherin duniya da na lahira. Lallai Allah (TA) ya umace ni in kira ku zuwa gare shi. Waye zai taimake ni a kan wannan alamarin ya zama xan’uwana magajina halifana a cikinku?”, amman ba wanda ya amsa kiransa sai Aliyu (AS) wanda shi ne mafi qanqantar mutanen a shekaru, sai ya ce: "Ni ne ya Manzo zan zama mataimakin a kansa”. Nan take Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Tabbas wannan xan’uwana ne kuma magajina halifana a cikinku; ku ji daga gare shi kuma ku yi masa biyayya”.
Ba wannan ne inda Manzon Allah (s.a.w) ya bayyana cewa Aliyu ne halifansa ba kawai, kai ya maimaita faxar haka a wurare daban-daban, za mu yi ishara a kansu a karatu mai zuwa.

A KULA:
Me yasa aka fara kiran makusantan Annabi (s.a.w) zuwa Musulunci sannan daga baya aka kira ragowar mtuane?

4- KIRAN BAKI XAYAN MUTANE A FILI:
Ba a daxe da kiran da Annabi (s.a.w) ya yi wa danginsa don su shiga Musulunci ba saio ga sabon umarnin Allah wanda ya qunshi kiran gaba xayanm mutane zuwa Musulunci, inda Mala’aikan wahayi ya sakko da ayoyi biyu 94-95 a Suratul Hijri.
Don bin umarnin Allah sai Manzon Allah (s.a.w) ya tsaya a cikin mutanen Makka ya ce: "Tababs ni Manzon Allah ne, ina kiran ku ku bautawa Allah shi kaxai ku bar bautar gumakan da ba sa amfanarwa ba sa cutarwa, ba sa halitta basa azurtawa, ba sa rayawa basa kashewa”.
Haka abin yake, Manzon Allah (s.a.w) bai bar wata dama da ta zo masa ba tun daga wannan ranar face sai ya bayyana da’awarsa a cikin taron masu aikin Hajji da maziyartan xakin Allah da wasu wuraren da mutane suke taruwa, ya kasancce yana zuwa masallaci mai alfarma yana kuma karanta Qur’ani da maxaukakin sauti waxannan ayoyin na Allah sun kasacne suna ribace zukatansu tare da sace musu hankulansu, suna kuma sasu su xamfara da wanan mu’ujizar Allah tabbatacciya

GUNDARIN DARASIN:
1-    An haifi Manzon Allah (s.a.w) a shekarar farko ta shekarar giwaye, an aiko shi da Manzanci a shekara ta arba’in bayan shekarar giwaye.
2-    Babansa sunansa Abdullahi bn Abdulmuxxalib, mahaifiyarsa sunanta Aminatu. Abdullahi ya rasu bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w) da ‘yan watanni. Amina ta rasu a shekara ta shida da haihuwar Annabi (s.a.w).
3-    Haqiqa baki xayan kakannin Manzon Allah (s.a.w) masu kaxaita Allah ne, ba wanda dauxar bautar gumaka ta gurvata shi.
4-    Manzon Allah (s.a.w) ya yi tafiya sau biyu zuwa Sham, tafiyar farko lokacin yana yaro, ta biyun kuma lokacin yana saurayi don juya dukiyar Sayyida Khadija.
5-    Annabi (s.a.w) ya auri Sayyida Khadija yana da shekara ashirin da biyar, Khadija tana cikin maxaukakan matan Makka, kai ta ma fi su.
6-    An aiko Manzon Allah (s.a.w) a shekara ta arba’in bayan shekarar giwaye, ya voye da’awarsa har tsawon shekara uku sannan ya bayyana ta bayan shekara ukun.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: