bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      07:53:00
Dan Shaikh Zakzaky da ya rage a duniya, Mal. Muhammad; ya rubuta wasikar koke zuwa ga kwamitin kare martabar Lauyoyi (LPP) da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA)
Lambar Labari: 67
Muhammad Zakzaki ya rubuta wasikar koke ga kungiyar NBA da kwamitin LPP na lauyoyi

Harkar musulunci A Nageria

Dan Shaikh Zakzaky da ya rage ya rubuta wasikar koke ga kungiyar lauyoyin Najeriya da Kwamitin LPP, tare da neman a ladabtar da Antoni-Janar na kasa. Dan Shaikh Zakzaky da ya rage a duniya, Mal. Muhammad; ya rubuta wasikar koke zuwa ga kwamitin kare martabar Lauyoyi (LPP) da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) .

 
Dan Shaikh Zakzaky da ya rage ya rubuta wasikar koke ga kungiyar lauyoyin Najeriya da Kwamitin LPP, tare da neman a ladabtar da Antoni-Janar na kasa.

Dan Shaikh Zakzaky da ya rage a duniya, Mal. Muhammad; ya rubuta wasikar koke zuwa ga kwamitin kare martabar Lauyoyi (LPP) da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) dangane da halin ko-in-kula da Antoni-Janar na kasa kuma Ministan shari'a, Malami Abubakar SAN, ya nuna wajen kin yin amfani da aikin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da hukuncin babbar kotun Tarayya da ke Abuja, wacce ta ba da umarnin a saki iyayensa.

Mal. Muhammad, ya yi kira ga bangaren shari'a da su sanya takunkumi tare da daukan kwakkwaran mataki a kan Antoni-Janar na kasa bisa kin bin umarnin kotu da ya yi, duk da cewa kuma ya kasance mai mukamin manyan masana a al'amarin doka (SAN). "Ina kira da madaukakiyar murya ga kungiyar lauyoyi da kuma kwamitin kare martabar Lauyoyi da su dauki duk wani mataki da ya dace a kan Antoni-Janar na kasa, a matsayinsa na jagoran tabbatar da dokoki na kasa sannan kuma masani a kan sha'anin doka a Najeriya, ta hanyar janye duk wata gatar da yake da shi; saboda irin wannan mummunar halayya da ya nuna, sannan su gaggauta daukan mataki domin kwato hakkin Shaikh Ibraheem Zakzaky da Malama Zeenatu Ibrahim Zakzaky," kamar yadda ya ce.

Wasikun koken guda biyu baki daya suna dauke da kwanan watan 28 ga watan Fabrairu 2017 kowacce dauke da taken, "Neman daukan kwakkwaran mataki a kan Antoni-Janar na kasa kuma ministan Shari'a, a matsayin sa na babban masani a sha'anin dokokin Najeriya, a kan irin mummunan halin da ya nuna."

Ya bayyana Najeriya da cewa akwai yarjejeniyoyin kasa da kasa da ke kanta na tabbatar da hakkin dukkan 'yan kasa da kuma kare shi. Ya kuma fadi cewa, gwamnati na karkashin dokokin kasa da kasa na tabbatar da bin dukkan tanade-tanaden dokokin kare hakkin dan Adam na kudurin kasashen Afirka kan hakkin mutane. Ya kuma nuna cewa tunda gwamnatin dimokradiyya ake yi, ya zama wajibi ta yi aiki da kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokokin kasa.

Mal. Muhammad ya ci gaba da bayyana cewa, iyayensa sun shigar da kara a kotun Tarayya ne domin neman a tabbatar musu da 'yancin su na rayuwa, walwala, mutuncin kai da kuma 'yancin rayuwa ta kashin kai, da ta iyali da yanin mallakar dukiya kamar yadda suke a sassa na 33, 34, 35, 36, 37, 40, 41 da kuma 46 (1) da (2) na kundin tsarin mulkin kasa (Kamar yanda aka gyara) na shekarar 1999 da kuma doka ta 4, 5, 6, 11 da 12 (1) na kudurin kasashen Afirka dangane da ‘yancin ‘yan Adam (Kamar yadda aka tabbatar) shekarar 2010 kuma doka ta 11, doka ta xi da kuma xii na ‘yancin kai (hanyoyin tabbatarwa), 2009.

Ya yi bayani ga kungiyar lauyoyi da kuma kwamitin kare martabar Lauyoyi cewa, babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin da ya ba su gaskiya, inda daga karshe ta ba da umurnin sakin su. Dan Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya ci gaba da cewa, maimakon a bi umurnin hukuncin kotun, Antoni-janar kuma Ministan Shari'a, sannan kuma babban masani a sha'anin dokokin Najeriya (SAN), ya ci gaba da tsare iyayensa ba bisa ka'ida ba, abin da ya bayyana a matsayin 'mummunan hali', duk da hakan ya saba wa hukuncin kotun kasa da ta cancanta, sannan kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.

A satin da ya gabata dai, Shugaban Lauyoyin Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Femi Falana SAN; ya rubuta takardar koke ga Mukaddashin shugaban kasar ta Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo SAN, yana neman a gaggauta sakin Shaikh Zakzaky da mai dakinsa ta hanyar bin umurnin hukuncin babbar kotun Tarayya.
Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA 
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: