bayyinaat

Published time: 14 ,March ,2017      16:51:42
Tana karantar da wajabcin tsare hakkokin mutane tsakaninsu a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa. Wannan sura tana magana mai muhimmanci kan munana ayyuka da sakamakonsu da abin da zai zama sakamako a lahira.
Lambar Labari: 75
سورة المطففين


بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai
 
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ 

1. Bone ya tabbata ga masu tauyewa. 

الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُواْ عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ 

2. Wadanda suke idan suka auna daga mutane suna cika mudu. 

وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ 

3. Kuma idan sun auna musu awon kwano ko awon sikeli, suna ragewa.

أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ 

4. Ashe! Wadancan ba sa tsammanin cewa tabbas ana tayar da su ba?

لِيَوْمٍ عَظِيمٍ 

5. Domin yini mai girma. 

يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ 

6. Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta?

كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ 

7. A'aha! Hakika littafin fajirai tabbas yana a cikin Sijjin. 

وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ 

8. Kuma, me ya sanar da kai abin da ake ce wa Sijjin?

كِتَابٌ مَّرْقُومٌ 

9. Wani 1ittafi ne rubutacce.

وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ 

10. Bone ya tabbata a ranar nan ga masu karyatawa. 

الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ 

11. Wadanda suke karyatawa game da ranar sakamako. 

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ 

12. Babu mai karyatawa da ita sai dukkan mai ketare haddi mai yawan zunubi. 

إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ

13. Idan ana karanta masa ayoyinmu, sai ya ce: Tatsuniyoyin mutanen farko ne. 

كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ 

14. A'aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu. 

كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ 

15. A'aha! Hakika, su wadanda ake shamakancewa daga Ubangijinsu ne a wannan ranar. 

ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا الْجَحِيمِ 

16. Sa'an nan, lalle ne, su masu shiga cikin Jahim ne. 

ثُمَّ يُقَالُ هَذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ 

17. Sannan a ce; Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna karyatawa da shi.

كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ 

18. A'aha! Hakika littafin masu da'a yana a cikin Illiyyina?

وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ 

19. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cewa Illiyyuna?

كِتَابٌ مَّرْقُومٌ 

20. Wani littafi ne rubutacce. 

يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ 

21. Mukarrabai ne suke halartar sa. 

إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ 

22. Hakika masu da'a suna cikin ni'ima. 

عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ 

23. A kan karagu, suna ta kallo. 

تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ 

24. Kana sanin walwalin ni'ima a fuskokinsu. 

يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ 

25. Ana shayar da su daga wata giya wadda aka yunke a kan rufinta. 

خِتَامُهُ مِسْكٌ وَفِي ذَلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ 

26. Karshen kurbinta al'miski ne. To, a cikin wannan, masu rige su yi ta rige. 

وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ 

27. Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnim yake. 

عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ 

28. Wani marmaro ne wanda mukarrabai suke sha daga gare shi. 

إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُواْ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ 

29. Lalle ne, wadanda suka kafirta sun kasance suna yi wa wadanda suka yi imani dariya. 

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ 

30. Kuma idan sun shude su sai su dinga yin zunde. 

وَإِذَا انقَلَبُواْ إِلَى أَهْلِهِمُ انقَلَبُواْ فَكِهِينَ 

31. Kuma idan suka juya zuwa ga iyalansu, sai su tafi suna kakaci. 

وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَؤُلَاءِ لَضَالُّونَ 

32. Kuma idan sun gan su sai su ce; Lalle wadannan batattu ne.

وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ 

33. Alhali kuwa, ba a aike su ba domin su zama masu lura da su. 

فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُواْ مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ 

34. To, yau fa wadanda suka yi imani, su ne suke yi wa kafirai dariya. 

عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ 

35. Suna masu kallo a kan karagu. 

هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ 

36. Shin an saka wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa?

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: