bayyinaat

Sīrāh
Annabin Daraja
Lalle ni mai barku muku nauyaya guda biyu ne littafin Allah da tsatsona Ahlul baiti matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada lallai su biyun basu taba rabuwa da juna har sai sun gangaro wurina a tafki
Na rantse da ubangiji wanda numfashina ke hannunsa, shedan bai taba haduwa da kai ba kana mai shiga wata hanya face sai ya shiga wata hanyar daba taka hanyar ba. An cirato daga bukhari da muslim
Wahayi a ma’anarsa ta isdilahi yana nufin abin da ake yi wa annabawa da manzanni sakonsa na daga zance ko ilhami da ake kimsa musu (a.s). Kuma shi hanya ce da Allah yake sanar da mutum ubangijinsa da kansa da shiriyarsa domin ya tsara rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran halittu, da kuma yadda zai fuskanci ubangijinsa.
Amma hadisai, cikinsu akwai: “Matsayinka a wajena irin matsayin Haruna wajen Musa ne sai dai ni ba Annabi Abayana”( ). “Kai macibincin duk wani mumini ne a bayana”( ). “Kur’ani na tare da Aliyu ba za su rabu ba har sai zo min a tafkin Alkausara”( ).
Raddin Sukan Yawan Matan Annabi
Amma abin sani game da Manzo (s.a.w), ya auri mata daya ne da ya rayu da ita tun yana shekara ashirin da biyar tana da shekaru arba'in har kusan karshen rayuwarsa yana dan shekara hamsain. Haka ya zauna (s.a.w) da mace daya bai sake aure ba yana ta ibada da tunanin fitar da al’umma daga kangin bautar mutum zuwa ‘yancin bautar Allah. Bai auri ta biyu ba sai bayan yana dan shekara hamsin da uku a lokacin ya manyanta.
1