bayyinaat

Published time: 23 ,January ,2017      09:43:31
An ambaci shekarar haihuwarsa da “Shekarar giwa”[1], saboda harin da Habasha ta kai wa Ka’aba domin rusa ta a wannan shekarar. Kuma abubwan mu’ujiza sun wakana yayin haihuwarsa (s.a.w) da suka hada da: 1-Faduwar gumaka akan fusakunsu. 2-Rushewar katangun kisira da suke Shiraz. 3-Mutuwar wutarsu da suke bautawa. 4-Kafewar kogin Sawa. 5-Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne a shekarar miladiya ta 571 ne[2].
Lambar Labari: 10
Muhammad shi ne annabin da Allah a aiko shi a matsayin annabin karshe domin shiryar da dukkan halitta gaba daya.
A lokacin da aka haife shi Makka da Dakin Allah sun kasance a cike da daudar bautar gumaka, sannan kuma Yahudawa da Kiristoci suna rayuwa a Jazirar larabawa.
Daular Farisa tana mallakar gabashin jazirar larabawa, kuma ga daular Rumu a yammacinta maso arewa, kuma da daula ta uku ta Habasha a yamma, kuma a kudu akwai Daular Yemen da ta kasance karkashin mulkin mallakar Habasha a lokacin haihuwar Annabi, da kuma Tekun Indiya.
An ambaci shekarar haihuwarsa da "Shekarar giwa”[1], saboda harin da Habasha ta kai wa Ka’aba domin rusa ta a wannan shekarar. Kuma abubwan mu’ujiza sun wakana yayin haihuwarsa (s.a.w) da suka hada da:
1-Faduwar gumaka akan fusakunsu. 2-Rushewar katangun kisira da suke Shiraz. 3-Mutuwar wutarsu da suke bautawa. 4-Kafewar kogin Sawa. 5-Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne a shekarar miladiya ta 571 ne[2].
Babarsa ita ce Amina ‘yar Wahabi (a.s). Babansa kuma Abdullahi Dan Abdulmudallib (a.s). Kakansa ya ambace shi da Muhammad, kuma ya yi walima, ya yanka tumaki, kuma ya soke rakuma ya ciyar da mutane har kwana uku[3].
Wadanda suka shayar da shi:Babarsa a kwana uku na farko. Suwaiba a wata hudu/ Halimatus’ Sa’adiyya, wacce ta dauke shi kuma ta rene shi. Ta kasance tana da ‘ya’ya kamar haka: Abdullahi. Anisa. Shaima’u.
Ta samu albarka mai yawa sakamon renonsa da shayar da shi: Daukewar fari da ya same su da su da mutanensu. Aminci a cikin al’ummarsu gaba daya. Yalwar arziki da hayayyafar dabbobinsu.
Babarsa ta rasu yana dan shekara shida, sannan sai kakansa Abdul mudallabi ya cigaba da renonsa, shi ma ya rasu yana dan shekara takwas, wanda a sakamakon haka ne baffansa Abu Talib (a.s) da kuma matarsa Fatimatu ‘Yar Asad (a.s) suka dauki nauyin renonsa.
Kasuwancinsa:
Kasancewar gidan Abu Talib yana da karancin yalwa wannan ne ya sanya manzo (s.a.w) ya motsa domin ganin ya dauki nauyin wannan gida, ta hanyar karbar kwadagon kasuwanci na fatauci kamar yadda yake al’amari sananne a wannan zamani.
Manzo ya yi fatauci da dukiyar Khadiza (a.s) da shawarar Abu Talib (a.s), kuma wannan ya samu alheri da yawa da albarka da ba ta lissafuwa.
Sai ya yi fatauci zuwa Sham da dukiyarta ya dawo yana mai cike da hannu mai albarka da kuma amana da ba ta taba gani ba. Musamman daga labaru da ta samu daga mutane daban-daban kamar bawanta Maisara.
Annabi mai girma ya bayar da dukkan ribar da ya samu na hakkinsa na fatauci ga amminsa Abu Talib gaba daya domin yalwatawa ga iyalansa, wannan al’amari ya sanya shi farin ciki mai yawa da abin da dan dan’uwansa Muhammad (s.a.w) ya yi masa na kyauta[4].
Aurensa:
Manzon Allah (s.a.w) ya auri mace mafi kamala a cikin larabawa da mafi yawa daga manyan Makka sun so aurenta amma ta ki amincewa da su saboda kamalarta da kuma yanayinsu na ba tsararrakinta ba ne su a halaye.
Musamman ma wasu suna sonta ne domin wani abu na duniya da take da shi kamar kyawunta ko dukiyarta, wasu kuma ma’abota dukiya maras misali ne amma duk da haka taki amincewa, sai ta yarda da neman da Abu Talib (a.s) ya yi daga gareta na aure da dan dan’uwansa Muhammad, kuma ta amsa masa abin da ya nema, domin kamalarsa da kuma darajar gidansu a cikin larabawa da kuma kamewar Manzo (s.a.w) da rikon amanarsa.
Khadiza (a.s) ta auri Manzo (s.a.w) tana budurwa a lokacin ba ta taba aure ba, tana ‘yar shekara goma sha takwas, shi kuma yana dan shekara ishirin da biyar[5].
Abu Talib (a.s) ya tafi wajan amminta Amru Dan Asad ya nemi aurenta ga manzo (s.a.w), domin an kashe babanta kafin wannan lokacin.
Abu Talib (a.s) yana cewa a yayin da ya tafi neman aurenta ga Manzo (s.a.w): "Godiya ta tabbata ga ubangijin wannan daki (na ka’aba), wannan da ya sanya mu daga tsatson Ibrahim (a.s) da kuma zuriyar Isma’il (a.s)… sannan dan dan’uwana… -yana nufin manzon Allah- ba a auna shi da wani mutum daga kuraishawa a sikeli daya sai ya yi rinjaye, kuma ba a kwatanta shi da wani mutum sai ya fi shi daukaka, … ga shi yana son Khadiza (a.s), mun zo muna neman aurenta a wajanka, da yardarta da kuma umarninta, kuma sadakin yana kaina a dukiyata da zaku nema hannu-da-hannu ko kuma ajalan –na rantse da ubangijin wannan Dakin na Ka’aba- (wannan aure) rabo ne mai girma, addini mai yaduwa, kuma ra’ayi cikakke”.
Sai Muhammad (s.a.w) ya tashi domin ya tafi tare da Abu Talib (a.s) gida, sai Khadiza (a.s) ta ce da shi: ina zaka tafi, ai gidana gidanka ne kuma ni mai hidimarka ce[6].
Haka nan ne ya aure ta (a.s) aka kafa gida mai haske cike da shiriya. Manzo (s.a.w) yana fadi game da ita: Khadiza (a.s) ta yi imani da ni yayin da mutane suka kafirta da ni, ta gaskata ni yayin da mutane suka karyata ni, ta taimake ni da dukiyarta yayin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya arzuta ni ‘ya’ya da ita ya hana ni ‘ya’yan mutane (ta wata matar)[7].
 
Albishir Da Zuwan Manzo (s.a.w)
Hakika an samu albishir da zuwan manzo (s.a.w) tun kafin zuwansa da shekaru masu yawa kamar yadda yake a sunnar Allah ta yin albishir da wani babban abu ga mutane tun kafin zuwansa.
Daga cikin inda aka samu albishir da zuwan manzo (s.a.w) akwai:
Injil; Yohana:
"Idan kun kasance kuna so na to ku kiyaye wasiyyata, ni zan nema daga Uba sai ya ba ku wani abin yabo (Ahmad), domin ya zauna tare da ku har abada[8].
A cikin wannan fakara ya ci gaba da cewa: "Ba zan yi muku magana da yawa ba; domin shugaban wannan duniya yana tafe”. Kuma ya ce: "Amma abin godewa ruhi mai tsarki da baban zai aiko shi da sunana, shi ne zai sanar da ku komai, kuma zai tunatar da ku dukkan abin da na gaya muku”. Da sauran abubuwan da suka zo game da hakan. Idan mun lura zamu ga cewa:
Annabi Isa (a.s) ya yi bishara da wanda zai zo bayansa
Zuwansa an shardanta shi da tafiyar shi Annabi Isa (a.s)
Kuma Allah ne zai aiko shi
Ya san komai
Zai tunatar da mutane abin da Isa (a.s) ya gaya musu
Kuma zai yi shaida ga Masih Isa (a.s)
Hijirar Yahudawa da Kiristocin yankin larabawa musamman Madina da Khaibar domin samun da suka yi a littattafansu game da siffofin annabin karshe cewa zai zauna a wannan yankuna ne, sai suka yawaita hijira domin kwadayin ya zama su suka haife shi.
Samun yaduwar labarin cewa zai zo a yankin larabawa, al’amarin da ya sanya yawaitar kiristoci masu bauta suka warwatsu a yankuna daban-daban na jazirar larabawa domin jiransa da biyayya gareshi idan ya bayyana.
Yaduwar labarin bayyanarsa a ko’ina a kasashe al’amarin da ya sanya wasu mutane yawon neman kasar da zai bayyana, kamar Madina da Makka, kuma misalin irin wadannan mutane da suka shahara akwai Salman Farisi.
Abin da mai bauta Bahira ya gaya wa Abu Talib da ya koma da shi gida, yayin da ya yi tafiya da shi fatauci yana yaro. Bahira ya gaya masa idan yahudawa suka gano shi zasu kashe shi domin hassadar cewa ba a haife shi daga tsatson su ba. Bahira ya tabbatar wa Abu Talib (a.s) cewa ba shi ne babansa ba, domin ba za a haife shi ba sai bayan wafatin babansa (a.s).
Wannan yana nuna mana irin yadda siffofin Annabi suka zama sanannu a wannan yankuna ta yadda har yaruntarsa ba ta iya dusashe wannan siffofin ba da masu bauta a dazuka da tsaunuka irin su Bahira suka iya gano shi tun yana karami. Kuma wannan yana nuna tsananin kishirwa da sanin zuwansa da yake tattare da jama’ar wannan zamanin musamman Yahudawa da Kiristoci da larabawan wadannan yankunan.
 
Hafiz Muhammad Sa’id
www.haidarcenter.com
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@yahoo.com – hfazah@hotmail.com
10 Rabi’ul awwal 1427
20 Parbardin 1385
9 Afrilu 2006
 
[1] Alkamil fittarih: 1/371.
[2] Assiratul Muhammadiyya: 23.
[3] – Siratul mustapha: 42. A’alamul hidaya: 1/25.
[4] – Assiratul muhammadiyya: 41.
[5] – Almusdapha min siratil musdapha: 58.
[6] – A’alamul hidaya: 1/67.
[7] – Sahih Muslim: 7/134. Sahih buhari: 5/39.
[8] – Injilar Yohana: Assihah 14. Wato John: Genesis 14.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: