bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:11:30
Na rantse da ubangiji wanda numfashina ke hannunsa, shedan bai taba haduwa da kai ba kana mai shiga wata hanya face sai ya shiga wata hanyar daba taka hanyar ba. An cirato daga bukhari da muslim
Lambar Labari: 113
Da Gaske Ne Shedan Yana Jin Tsoran Umar Dan Khaddabi Ba Annabi Ba?

Bismillahir Rahmanir Rahim.
Allahumma Salli Ala Muhamad Wa Ali Muhammad.

« وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ مَا لَقِيَكَ الشَّيْطَانُ قَطُّ سَالِكًا فَجًّا إِلاَّ سَلَكَ فَجًّا غَيْرَ فَجِّكَ »
Na rantse da ubangiji wanda numfashina ke hannunsa, shedan bai taba haduwa da kai ba kana mai shiga wata hanya face sai ya shiga wata hanyar daba taka hanyar ba. An cirato daga bukhari da muslim.
Amma shi kuwa Annabi (s.a.w.) sai muka ga ana cewa shedani yana iya kusantarsa har ma kuma yana son ya cutar da Annabi (s.a.w.) adai-dai lokacinda yake yin munajati da ubangijinsa.
بَاب جَوَازِ لَعْنِ الشَّيْطَانِ فِي أَثْنَاءِ الصَّلَاةِ وَالتَّعَوُّذِ مِنْهُ وَجَوَازِ الْعَمَلِ الْقَلِيلِ فِي الصَّلَاةِ
عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ قَالَ
قَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَسَمِعْنَاهُ يَقُولُ أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْكَ ثُمَّ قَالَ أَلْعَنُكَ بِلَعْنَة اللَّهِ ثَلَاثًا وَبَسَطَ يَدَهُ كَأَنَّهُ يَتَنَاوَلُ شَيْئًا فَلَمَّا فَرَغَ مِنْ الصَّلَاةِ قُلْنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ قَدْ سَمِعْنَاكَ تَقُولُ فِي الصَّلَاةِ شَيْئًا لَمْ نَسْمَعْكَ تَقُولُهُ قَبْلَ ذَلِكَ وَرَأَيْنَاكَ بَسَطْتَ يَدَكَ قَالَ إِنَّ عَدُوَّ اللَّهِ إِبْلِيسَ جَاءَ بِشِهَابٍ مِنْ نَارٍ لِيَجْعَلَهُ فِي وَجْهِي فَقُلْتُ أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْكَ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ ثُمَّ قُلْتُ أَلْعَنُكَ بِلَعْنَةِ اللَّهِ التَّامَّةِ فَلَمْ يَسْتَأْخِرْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ ثُمَّ أَرَدْتُ أَخْذَهُ وَاللَّهِ لَوْلَا دَعْوَةُ أَخِينَا سُلَيْمَانَ لَأَصْبَحَ مُوثَقًا يَلْعَبُ بِهِ وِلْدَانُ أَهْلِ الْمَدِينَةِ
Daga Abid-darda'i ya ce : Annabi (s.a.w.) yana tsaye sai muka ji shi yana cewa "ina neman tsarin ubangiji daga gare ka" sannan kuma sai ya ce " ina la'antarka da la'anar nan ta ubangiji " sau uku, sai ya rika mika hannunsa kamar wanda zai kamo wani abu. A lokacin da ya idar da sallah, sai muka ce ya Annabin Allah (s.a.w) hakika mun ji ka kana fadar wani abu wanda ba mu taba jin ka kana fadinsa ba kamin haka, sannan kuma mun gan ka kana mika hannunka. sai ya ce hakika makiyin Allah Ta'ala  Iblis ya zo da tartsatsin wuta domin ya sanya a kan fuskata to shi ne nake cewa {…} amma hakan bai sa ya ja da baya ba, to shi ne na yi nufin na kama shi. Na rantse da Allah Ta'ala ba-daban addu'ar dan uwanmu sulaimanu ba, da sai yawayi gari yana abin daurewa 'yan yaran garin madina suna yin wasa da shi. duba littafin sahihu muslim cikin babin da ya gabata.
Bari mukawo riwayoyi ingatattu wadanda da su ne zasu kara bayyanar mana da yanda hakikanin lamarin yake, ta yanda zamu auna mugani ko zai taba yiwuwa shedani ya iya kusantar Annabi (s.a.w) danufin cutarwa ko kuma abin ba zai taba yiwuwa ba? amma kafin haka muna cewa me ya sa da Annabi (s.a.w)  yake neman tsari daga wancan shedani a wannan lokaci, menene dalilin da yasa wannan shedani bai gudu ba? sannan kuma da alama cewa khalifa Umar bai sami damar halartar wannan salla tare da Manzon Allah (s.a.w) ba, saboda da dai ace yana nan to mun san da wannan shedani ba zai iya XXX samun damar shigowa cikin wannan masallaci na manzon allah (s.a.w.) ba, balantana wannan shedanin ya iya kunsantar annabi (s.a.w.) da tar tsa-tsin wuta, saboda irin tsananin tsoranda shedan yake yiwa umar.
sannan kuma baya ga haka hadisinda aka karbo daga abi-huraira yana cewa kiransa sallah yana sanya shedan yaruga aguje har yaringa sakin tusa. abin tambaya anan shine koshin ita waccan sallah wadda annabi (s.a.w.) yake jan sahabbansa ba'a kirawo mata kiran sallah ba, idan kuma an kirawo meyasa wancan shedani yasami damar shigowa da tar tsa-tsin wuta har cikin masallacin annabi (s.a.w.)?
بَاب فَضْلِ الْأَذَانِ وَهَرَبِ الشَّيْطَانِ عِنْدَ سَمَاعِهِ
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَذَّنَ الْمُؤَذِّنُ أَدْبَرَ الشَّيْطَانُ وَلَهُ حُصَاصٌ

kabiru dfarisa, [24.03.18 17:35]
annabi (s.a.w.) yabaiwa al'umarsa tsari daga shedan ya ce matsawar idan mutum yakaranta wannan abu zai zamar masa tsari daga shedan har izuwa yammaci. ko kuwa kuna ganin cewa shi annabi (s.a.w.) baya neman tsari daga shedanu shiyasa wancan shedani yanufi yacutar dashi? bukhari da muslim sun rawaici haka amma ga riwyar dake cikin bukhari.
64 - باب فَضْلِ التَّهْلِيلِ .
عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ - رضى الله عنه - أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - قَالَ « مَنْ قَالَ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ ، وَهْوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ . فِى يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ ، كَانَتْ لَهُ عَدْلَ عَشْرِ رِقَابٍ ، وَكُتِبَ لَهُ مِائَةُ حَسَنَةٍ ، وَمُحِيَتْ عَنْهُ مِائَةُ سَيِّئَةٍ ، وَكَانَتْ لَهُ حِرْزًا مِنَ الشَّيْطَانِ يَوْمَهُ ذَلِكَ ، حَتَّى يُمْسِىَ ، وَلَمْ يَأْتِ أَحَدٌ بِأَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ بِهِ إِلاَّ رَجُلٌ عَمِلَ أَكْثَرَ مِنْهُ » .
Abin mamaki ga shedan ba ya bin khalifa umar amma zaka samu awurare da dama shedan yana iya kusantar annabi (s.a.w.). daga cikin misalin haka munga yanda ake shigar da kayan shedan har cikin tsakar dakin da annabi (s.a.w.) yake kwanciya (garayar shedan) kai ahlus-sunnah sun rawaici ruwayar dake cewa an ciro zuciyar annabi (s.a.w.) an wanketa sannan kuma an fidda rabon shedan daga cikinta. sune suka rawaici ruwaya dake cewa wai annabi (s.a.w.) yace kowa yanada shedani sai sukace har dakai yarasulallahi? sai yace har dani… sune suke cewa wai annabi (s.a.w.) yace babu wani abin haihuwa face sai shedan ya shafeshi sai maryamu da danta annabi isa (a) kuma wani abin mamaki anan shine sai gashi an tsare shedanu gabarin satar ji daga mala'ikun dake sama don kar suji wani abu daga alkur'ani su iya kawowa bokayensu, amma kuma sai gashi ana iyayiwa wannan annabin da aka saukarwa da alkur'anin asiri yakuma cishi har ya iya aikata abu baisan ya aikata ba.
بَاب تَحْرِيشِ الشَّيْطَانِ وَبَعْثِهِ سَرَايَاهُ لِفِتْنَةِ النَّاسِ وَأَنَّ مَعَ كُلِّ إِنْسَانٍ قَرِينًا
أَنَّ عُرْوَةَ حَدَّثَهُ أَنَّ عَائِشَةَ زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَدَّثَتْهُ
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ مِنْ عِنْدِهَا لَيْلًا قَالَتْ فَغِرْتُ عَلَيْهِ فَجَاءَ فَرَأَى مَا أَصْنَعُ فَقَالَ مَا لَكِ يَا عَائِشَةُ أَغِرْتِ فَقُلْتُ وَمَا لِي لَا يَغَارُ مِثْلِي عَلَى مِثْلِكَ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقَدْ جَاءَكِ شَيْطَانُكِ قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَوْ مَعِيَ شَيْطَانٌ قَالَ نَعَمْ قُلْتُ وَمَعَ كُلِّ إِنْسَانٍ قَالَ نَعَمْ قُلْتُ وَمَعَكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ قَالَ نَعَمْ وَلَكِنْ رَبِّي أَعَانَنِي عَلَيْهِ حَتَّى أَسْلَمَ
… sai annabi (s.a.w.) yace da ita kodai shedaninki ne yazo miki? sai tace daman da akwai shedani atare dani ya ma'aikin allah? sai yace na'am! sai nace atareda kowane mutum? sai yace na'am! sai nace yana tareda kai ya ama'aikin allah? sai yace na'am sai dai cewa ubangijina ya taimakeni akansa har saida ya musulunta. sahihu muslim. kubiyoni kuga wani abin mamaki :
107 - باب مَا يُقَالُ عِنْدَ النَّوْمِ.
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- كَانَ إِذَا أَخَذَ مَضْجَعَهُ مِنَ اللَّيْلِ قَالَ « بِسْمِ اللَّهِ وَضَعْتُ جَنْبِى اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِى ذَنْبِى وَأَخْسِئْ شَيْطَانِى وَفُكَّ رِهَانِى وَاجْعَلْنِى فِى النَّدِىِّ الأَعْلَى ».
wannan riwaya ta zone daga cikin littafin sunan abiy-dauda. annabi (s.a.w.) yakasance idan zai kwanta cikin dare yanayin wannan addu'a, daga cikin abinda yake cewa shine " ya allah ka kaskantarda shedani na "…
da-dai ace imanin wancan shedani ya inganta da annabi (s.a.w.) bazaiyi masa irin wannan bakar addu'a ba cikin kowane dare. sannan kuma gata riwayace ingatacciya.
Alhamdu Lillahi.

KABIR ADAM
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: