bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:14:33
Dukkanin malaman makarantar khalifofi sun karkata da ra’ayin shafe hukuncin mutu’ah domin su gyara matsayin khalifa na biyu Umar dan Khaddabi, wasu sashensu suka ce an shafe ta da ayar alkur’ani, wadansu suka ce an shafe ta da hadisi.Sai mu kuma muka sabawa bangarori biyun da wadannan maganganun
Lambar Labari: 114
MAGANA TA BIYU: SHIN AN SHAFE HUKUNCIN AUREN MUTU’AH?
Dukkanin malaman makarantar khalifofi sun karkata da ra’ayin shafe hukuncin mutu’ah domin su gyara matsayin khalifa na biyu Umar dan Khaddabi, wasu sashensu suka ce an shafe ta da ayar alkur’ani, wadansu suka ce an shafe ta da hadisi.Sai mu kuma muka sabawa bangarori biyun da wadannan maganganun:
Fadarsu an shafe ayar mutu’ah da ayar Alkur’ani: suna kafa dalilin shafewar da fadin Allah madaukakin sarki "sai dai matayensu da abin da hannayensu ta mallaka (kuyangi) a nan su ba abin zargi ba ne, wanda ya nemi sabanin haka wadannan su ne masu ketere iyaka”. (1)
Sai dai wadannan ayoyi an saukar da su ne a Makkah ita kuma ayar mutu’ah an saukar  da ita  a Madina ne,wanda ya gabata ba ya shafe wanda zai zo daga baya.
Sannan auren mutu’ah, da jin dadi da mace, ba sa kishiyantar juna, da wadannan ayoyi da kuma ayar auren, har ingancin shafe auren mutu’ah ya inganta.
Akwai maganar cewa an shafe shi ne da ayar iddah.Fadar Allah ta’ala "ku sake su a iddarsu” (1) Umarni da iddah a wannan ayar ya shafe hukuncin auren mutu’ah (a fadarsu).
Jawabin shi ne: shi auren mutu’ah ba ai masa togaciya da iddah, kuma ba ai masa togaciya da saki,idan mun tabbatar cewa aure kashi biyu ne a musulunci: na din-din-din da na mutu’ah zai zama ayar saki ta tabbata ne ga auren din-din-din ba na mutu’ah ba,saboda alakar da ke tsakanin auren din-din-din ita ce take bukatar sanarwa a lokacin da za a kare ta saboda samuwar wasu dalilai da za su bijiro ayyanannu.Amma alakar auren mutu’ah ba ta bukatar sanarwa. kawai tana karewa da karewar zamaninta kayyadadde ta hanyar wani tsari wanda aka sanya.Ka ga kenan ayar saki za ta kasance ne abar juyawa zuwa auren din-din-din,ba za a  gwama ta da auren mutu’ah ba har ta zamo abar shafewa.
Akwai Magana ta uku cewa an shafe ta ne da ayar gado, kasancewar ba gado a auren mutu’ah.
A bisa zance da ya gabata ga jawabin da aka mayar musu, martani a kan wannan shi ne rashin wani daga cikin tasirin abu ba ya nufin rashinsa gaba daya.Misali matar da ta yi nushuzi(ta tauye hakkin auratayya) ba ta da hakkin ciyarwa tare da cewa ba ta da hakkin ciyarwa duk da haka tana nan a matsayin mata,kuma sauran hukunce-hukuncen aure za su yi tasiri a kanta.Ahlul kitabi idan ta auri musulmi,ba za ta gaje shi ba tare da haka tana nan a matsayin matarshi sauran hukunce-hukunce da sauran abubuwa za su kasance tare da ita.
Kai yawaitar cece-kuce  kan maganar shafewar dalili ne a kan rashin tabbatarsa.Za mu tabbatar da wannan har ila yau. Sabaninsu a kan lokacin shafewar:
An   ce: An shafe ta ne, kuma Annabi (s.a.w.a) ya hana ranar yakin Khaibar         .
An ce: Hanin ya zo ne a shekarar fatahi Makkah.
An ce: Ta kasance halal amma an hana ne a yakin tabuk.
An ce: An halasta a hajjin ban kwana sannan aka hana.
An ce: An halasta sannan aka shafe sannan aka halasta sannan aka shafe sannan aka halasta sannan aka shafe.An fadi sabani haka. (1)
1.Ahkamul kur’an 2:164-195 babin mutu’ah, Darul kitab ilmi, Sahihul muslim sharhin nawawi 9:179, babin auren mutu’a, Irshad sariy sharhin sahihul Buhari babi na 32: babin hanin manzon Allah(s.a.w.a)auren mutu’a hadisi na 5110, 0119.

Alamu suna nuni da tabbacin rashin shafe ayar, mafi muhimmancin wadannan  a lamu (karina) shi ne bukatuwa tare da yawan maimaitawar maganar shafewar har ta kai Muslim ya sanya jigon babin auren mutu’ah kamar haka.Babin auren mutu’a tare da bayanin an halasta sannan aka shafe har haramcin ya tabbata zuwa ranar kiyama. (1)
Kurdabi ya ruwaito a cikin tafsirinsa abin da ibn Arabiy ya fada, cewar shafewar ya samu a wannan hukuncin sau biyu, sannan sai yai ta’aliki a kan shi da fadarsa: waninsa da ya hada hadisai mabanbanta a kan shi ga abin da yace; shi auren mutu’ah an hukunta halasta shi da haramta shi sau bakwai, sannan aka maimaita adadin shafewar.Sai ya ce: wadannan guraren bakwai sune inda aka halasta mutu’ah sannan aka haramta. (2)
Ibn kayyim Aljauzi ya ce: wannan shafe hukuncin bashi da misali a cikin shari’ah ga baki daya kuma ba a taba samun irinsa ba. (3)
Sannan wane irin ikirari ne wannan da ya bayyana bayan shudewar zamanin sahabbai? Mai ya sa khalifa Umar bai kafa shaida da daya daga cikin wadannan maganganu ba da Kansa kan haramta auren mutu’ah? A bayyane take da a ce ya san wani abu game da haramcin da ya kafa shaida da shi.Ya tabbata daga gareshi cewar ya sabawa Abubakar a cikin yakinsa ga masu hanin zakkah da hadisin Annabi (s.a.w.a) da yake hani da yakar ma’abota shahada, me ya sa a nan bai riko da koyarwar Annabi ba na shafe hukuncin in har ya zamo akwai hujja kamar yadda suke fada? Ko kuwa ma’abota wannan ikirarin sun fi sanin koyarwar(s) fiye da sahabbai ko Umar dan Khaddabi.
1. Sahihul Muslim 2:3 daba’in Darul-fikri Berut
2. Tafsiril kurdabiy 5:130-131
3. Zadu-ma’ad 2:2-3.


Khalifa na biyu bai gamsu da hakan ba sai dai kawai yana cikin wancan bukatar tashi game da auren mutu’ah, saboda musulmi musamman sahabbai ba su yarda da matsayar khalifa na biyu ba, kai sun yi masa martani game da haka, suna masu cewa sun sani an yi lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) da lokacin Abubakar to, da a ce akwai maganar shafewa to da ta bayyana.
Sannan wannan ikrarin ya sabawa maganar khalifa na biyu da kansa ya kasance yana cewa(mutu’oi guda biyu sun kasance a lokacin manzon Allah(s.a.w.a) na kasance ina hana su kuma ina ukuba a kansu,mutu’ar aure da mutu’ar hajji).(1) Da a ce akwai wani abu game da shafewar da ya furta shi,me ya sa ya jingina abin ga kansa.
A kan wannan bayanin zai kasance ikrarin shafewar zai sabawa maganar khalifa da kansa.
Wannan maganar za ta kunyata hikayar shafe ayar mutu’ah har ila yau.An ruwaito daga Dabariy a cikin tarihinsa a cikin abin da ya faru a shekara ta 23 bayan hijira cewa Umar dan Sawadata ya shiga gun Umar dan Khaddabi sai ya ambata masa abin da mutane suke cewa game da abubuwan da aka farar musu kuma ba su yarda da su ba,ciki har da haramcin mutu’ah,sai ya ce: suna cewa ka haramta auren mutu’ah alhali Allah ya sa ta sauki mu ji dadi da damka daya(na dabino) mu yi saki sau uku(daban-daban)lokacin rabuwa!Sai Umar dan Khaddabi ya ce wajen ba da amsa:- Lallai Annabi(s.a.w.a)ya halasta auren mutu’ah lokacin larura,sannan daga baya yalwa ta sami mutane,sannan ban san wani daga musulmi da yake aikata ta ba ko ya koma ga yin ta(mutu’ah), yanzu wanda yaso ya iya auren da damka daya(dabino)kuma zai iya saki daban-daban har sau uku(lokacin rabuwa)ni na dace a kan hukuncin.(2)
1. Sharhu ma’anil asar 2:146, Ahmad dan Muhammad salamata azdiy.
2.Tarikhul-Dabriy, 5:32.

A cikin wannan tattaunawar khalifa na biyu ya kara tabbatarwa cewa matsayinsa a kan auren mutu’ah matsayi ne na kashin kansa,ra’ayi ne wanda ya samar babu fadin manzon Allah(s.a.w.a.) a cikinsa.
Sannan ijitihadin da ya ginu a kan haramta shi a cikin wannan tattaunawar bai cika ba, bacinsa a bayyane yake.Da kansa yake ikrarin cewa Annabi (s.a.w.a.) ya halasta a lokacin larura, to saboda me ya haramta shi kuma ya hana ba tare da togaciya ba, kuma yake azbtarwa a kan shi ba tare da la’akari da larura ba? Tare da cewa Manzo (s.a.w.a) ya halasta shi a lokutan tafiye-tafiyenshi, tafiya wani abu ce daban larura ma wani abu ne daban.

M Hafiz Nig, [03.04.18 22:37]
MAGANA TA UKU: MATSAYIN SAHABBAI DA TABI’AI AKAN AUREN MUTU’AH.
Dalilai a kan rashin shafe auren mutu’ah shine yaduwarsa a cikin sahabbai da tabi’ai da malaman fikihu har zuwa bayyanar mazahabobi hudu a karni na uku da na hudu.
Daga cikin shaidu a kan haka akwai ruwayar Bukhari da Muslim a cikin ingantattun littattafansu daga ruwayar Salamata dan Akwa’u, da Jabir Abdullahi Al-ansari, da Abdullahi dan Mas’ud, da ibn Abbas, da Suburatah dan Ma’abad, da Abi Zar- alghifariy, da Imran dan Husseyn, da Akwa’u dan Abdullahi Al-aslamiy.(1)
Muslim ya fitar a cikin babin auren mutu’ah ruwayoyi masu yawa daga Jabir dan Abdullahi, da Ibn Zubair cewa su suna mutu’ah lokacin Manzon Allah (s.a.w.a.) da lokacin Abubakar, har Umar dan Khaddabi ya haramta.
1.Sahihul Muslim, sharhin Nawawiy 9:179-189, da Sahihul Bukhariy kitabul-tafsir babi na 33 J.4156, Da Kitabun-nikah,      babi 32 J.4724, da kitabul-jitisam babi na 28 J. 6819.

A cikin sahihul Bukhariy (1), ya ce ayar mutu’ah ta sauka a littafin Allah, mun aikata ta lokacin Manzon Allah (s.a.w.a.) alkur’ani bai sauka da haramcin ta ba, kuma bai hana ba har ya bar duniya, kawai dai wani mutum ya fadi son ransa.
Kai manyan sahabbai sun sabawa haramcinta, misalin irin su Imam Ali(a.s) da Abdullahi dan Abbas, Jabir dan Abdullah Al-ansariy, da Abdullahi bn Umar da Abdullahi dan Mas’ud.
Akwai daga malaman sunnah a karni na farko da na biyu wanda ya ba da fatawa da yinta, shi ne Abdul-malik dan Jarih wanda ya mutu a shekara (149) bayan hijira.
Ibn Jazam ya fada a muhalliy "Hakika an tabbatar da halascinta bayan Manzon Allah (s.a.w.a) Jama’a daga magabata, Asma’u bint Abubakar, Jabir dan Abdullahi, Ibn Mas’ud, Ibn Abbas, Mu’awiyah bin Abu Sufyan, Amru bin Haris, Abu Sa’idul-kudriy,da salmata da ma’abad yayan umaiyah dan khalaf, Jabir dan Abdullahi ya ruwaito daga dukkannin sahabbai lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) da lokacin Abubakar har zuwa karshe khalifancin Umar”anyi mutu’ah.
A nan ga jerin sunayen dukkanin sahabbai da tabi’ai daga wadanda suka fadi halascin ta da rashin shafeta, su ne:-
1. Imran dan Husseyn                                          8. Rabi’ah dan Umayyah
2. Abdullahi dan Umar                                         9. Samir-acikin Isabeh-watakila
3. Salmah dan Umayyah                                          Sumrata dan Jundabi.
4. Mu’abad dan Umayyah                                  10. Sadiy
5. Zubair dan Awwam                                         11. Mujahid
6. Khalid dan MUhajir                                         12. Ibn Aws almadniy
7. Ubaiy dan ka’ab                                               14. Anas dan Malik

1. Sahihul Bukhariy 5:185, Darul fikri.

14. Mu’awiyya dan Abu Safiyanu.
15. Ibn Jariy
16. Nafi’u
17. Sabibu dan Abi sabit
18. Alhakamu dan Utaibah
19. Jabir dan Yazid
20. Albara’a dan Azib
21. Sahal dan Sa’ad
22. Almughira dan Shu’uba
23. Salamah dan Akwa’u
24. Zaid dan Sabit
25. Khalid dan Abdullahi al-ansariy
26. Ya’ala dan Umayyah
27. Safwan dan Umayyah
28. Amru dan Dinar
29. Amru dan Haushab
30. Ibn Jarih
31. Sa’id dan Habib
32. Ibrahim Nakha’i
33. Hasanu

Muhd Sani Tiga Hamro, [۲۵.۰۳.۱۸ ۲۰:۳۱]
[Forwarded from HC Ibrahim Irancell]
l Basariy
34. Ibn Musayyib
35. A’amash
36. Arrabi’u dan maisarah
37. Abiy Ibrahim Madruf
38. Malik dan Anas
39. Ahmad dan Hambali,(ta wani yanayi)
40. Abu Hanifah abisa wasu fuskokin.(1)

M Hafiz Nig, [03.04.18 22:37]
Ka koma littafin Ghadir, 7:22, da auren mutu’a a musulunci. 123 da mutu’ah na  Fukaikiy, Hukunce-hukuncen shari’ah a yanayin mutane, 1:28
Wannan Kari ne a kan misalin abin da ibn Amru ya fada cewa sahabban Ibn Abbas na
daga mutanen Makkah da Yamen dukkansu sun ruwaito halascin mutu’ah.
Kurdabi ya fada a cikin tafsirinsa (1), mutanen Makkah sun kasance suna yinta sosai (mutu’ah).
Raziy ya fada a cikin tafsirinsa (2) Sawwad ya fada daga cikinsu cewa ita mutu’ah tana nan a halascinta kamar yadda take.
Abu Hayyan ya fada a tafsirinsa bayan ya nakaito hadisinta (mutu’ah): A bisa wannan jama’ar Ahlul-bait da tabi’ai suke. (3)
Wanda yake son Karin bayani sosai a wannan bigire a fikihance da tarihance da hadisance sai ya koma littafin al’mu’allim (4) na Allamah sayyid Murtada al-askariy.
Idan ka gaskata ikrarin haramcinta daga Annabi (s.a.w.a) to haramcin zai kasance ne ta bangaren hukunci, to hukuncin, hukuncin shugabanci ne na lokaci ba ya nufin ta bangaren shari’a dawwamamme.Saboda haka akwai gudanar makamantan wannan a rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a), kamar haramcin cin naman jakin gida shekarar khaibar, wannan ya kasnce hani ne na hukumah (domin maslaha) ba hukuncin shari’a ba tabbatacce.
Da a ce za mu iya riya shafe hukuncin da haramtashi, mu dauka wadansu sun dace kan yin auren, sai suka saba a kan saki bayan tsawon lokaci to mene ne hukuncin alakarsu? Shin za su yi hukunci ne da haramcinta kuma su dauke ta a matsayin zina? Ko kuwa za su yi hukunci da halascinta? Cewa haramun ce wata ruwaya ce maras dalili;A dauka cewa halas ce ya yi dadai da abin da mazhabar iyalan Manzo(s.a.w.a.) suke a kai.

1. Jami’ul li ahkamul kur’an, 5; 132.
3. Alghadir, 6:222, an ciro daga isti’ab da waninsa   .4. Ma’alimul madrastaini, 2:242-280. 2. Tafsirul-kabir Na Raziy, 3:200
SHIN MUTU’AH ZINA CE?
Amma fadar cewa wai ta yi Kama da zina ko kuma cewar mutu’ah zina ce wannan wani yankin hadari ne ko da kuwa ta kasance abar shafewa.Saboda wannan yana nufin Allah madaukakin sarki ya taba halasta zina sannan ya haramta.Shin musulmi zai yadda da wannan?
Ya riga ya gabata cewa auren mutu’ah aure ne kamar din-din-din, shi ma yana da sharadan da suka dabaibaye shi.Sharuddan su ne akadi, sadaki da ambaton lokaci, da misalin zama mai hankali kuma baligi da kuma rashin hanawa daga shari’ah na daga dalili daga cikin dalilai, ko kuma shayarwa(wadda take haramta aure) da makamantan wadannan.Amma zina ita ba akadi(kulla aure) a cikinta, kuma ba za a riskar da yaron ga ubanshi ba, kuma ba zai gaje shi ba, ba alakar auratayya ba iddah a cikinta(zina).Don haka kamanta mutu’ah da zina maganar banza ce, mai fadarta ma’abocin girman kai ne da jayayya.

NATIJA (SAKAMAKO)
Abin da ya bayyana a gare mu na daga nassosin alkur’ani da sunnar Annabi madaukakiya da nassosin sahabbai da tabi’ai shi ne shar’ancin auren mutu’ah gaba daya da kuma rashin tabbatuwar shafe shi daga manyan sahabbai da tabi’ai, musamman a gurin Ahlul-bait (a.s), su ne ‘Ali’ shugaban wasiyai da ‘ya’yansa Imamai ma’asumai (wadanda basu taba sabo ba) da malamai daga makarantunsu ta fikihu zamani bayan zamani.
Auren mutu’ah aure ne na shari’ah da nassin alkur’ani da sunnah kamar auren din-din-din a shari’ar musulunci, amma auren mutu’ah ya saba masa (da’im) a wasu hukunce-hukunce wadanda muka yi nuni izuwa gare su.
Amma abinda aka samo daga Umar dan Khaddabi ba zai inganta a iya tabbatar da ikrarin shafeshi ba kamar yadda babu wani daga sahabbai ko tabi’ai da yake fadarsa.
Karshen maganarmu shi ne godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

FIRASA
Kalmomin mu’assasah
Gabatarwa
Maganar farko:Auren mutu’ah a alkur’ani da sunnah
Magana ta biyu: Shin an shafe hukuncin auren mutu’ah?
Magana ta uku:Matsayin sahabbai da tabi’ai akan auren mutu’ah
Shin mutu’ah zina ce?
Natija(sakamako)
Firasa

TA DUNIYA 5

DAGA TASKAR AHLUL-BAIT (A.S)
AUREN MUTU’AH

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: