bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:24:27
Ana ganin sadaka da kuma taimako a matsayin rahama ne daga ubangiji izuwa ga Talikai, wacce ya sabbaba ta kuma ya koro ta izuwa muminai, domin ya basu lada akan ta. Kuma ya kamata ga wanda yake so ya bawa mutane sadaka a matakin farko ya fara ta kan mabukata daga cikin ahlin sa da ya`yan` sa da kuma yan uwansa.
Lambar Labari: 119
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

"DORON KASAR RANAR TASHIN  ALKIYAMA DUKKANIN SA WUTA CE, IN BANDA INUWAR MUMINI, HAKIKA SADAKAR DA YAKE YI ZATA YI MASA INUWA”.

SADAKA DA TAIMAKON MUTANE DA KUMA BIYAN BUKATUN SU.

 
Sadaka ita ce: ka taimaki talaka da dukiya ko abinci ko abin sha ko tufafi ko mazauni, kai dama dukkanin abinda wani zai iya bukata ko yake bukata, wanda ba zai iya samun sa da kansa ba, saboda karancin abin da yake dashi, kuma gashi wannan abin zai taimake shi a rayuwar sa.

Ana ganin sadaka da kuma taimako a matsayin rahama ne daga ubangiji izuwa ga Talikai, wacce ya sabbaba ta kuma ya koro ta izuwa muminai, domin ya basu lada akan ta. Kuma ya kamata ga wanda yake so ya bawa mutane sadaka a matakin farko ya fara ta kan mabukata daga cikin ahlin sa da ya`yan` sa da kuma yan uwansa.
An ruwaito daga Manzo (S.AW.A.) cewa: "Babu sadaka alhali makusanci yana cikin bukata” (2).  Kuma kada ya wulakanta mabukaci da fadin wata kalma ko kallo ko motsin da zai bakanta masa ko ya wulakanta shi.  Allah Ta'ala ya ce: {kyakkyawar Magana da yin gafara, sun fi sadakar da cutarwa ke biyo mata baya}. Da kuma fadin sa madaukakin Sarki: {ka karbi sadaka daga cikin dukiyoyin su, wacce zaka tsarkake su da ita}.  Manzo (S.AW.A.) ya ce: Yayin da aka tambaye shi waye mafi soyuwar mutane a wajen Allah sai ya ce: "wanda yafi amfanar da mutane”.  Kuma ya ce: "Dabi’u guda biyu na alkairi, babu wani abu na biyayya da yake sama da su: "Imani da Allah da kuma amfanar da bayin sa”.
An karbo daga Manzo (S.AW.A.) cewa: "sadaka tana bice zafin kabari ga ahlin ta, kuma, kadai musulmi zai shiga inwar sadaka ne a ranar Alkiyama”. Manzo (S.AW.A.) yace: "hakika sadaka tana bice fushin ubangiji”.   An karbo daga Imam Sadik (A.S) yace: hakika Allah Ta'ala yana cewa: "Babu wani abu, face sai na sanya masa wanda yake karbar sa, ba ni ba, in banda sadaka, lalle ni nake tarbar ta da hannu, na kuma karba”. Ya kai dan`uwa mai kyashin ya taimaki dan uwan sa, ka sani cewa: abin da zai amfane ka shi ne, wanda ka gabatar, wanda ka temaki dan`uwan ka ko wani da shi, amma wanda ka ke ajiyewa ba komai ba ne, face na magada wanda kai kuma hisabi za’a yi maka a kansa.  Bayin Allah na kusa-kusa sun kai matakin da idan wani ya nemi wani abu a wajen su ko kuma suka bashi wani abu ya karba, sai sun gode masa!! Sun kasance idan suka ga mabukaci, sukan ce: "madalla da wanda zai wuce da guzuri na”. Da wannan ne suke ganin cewa, kai da ka bayar aka karba, kai yafi cancanta da ka gode fiye da wanda kabawa, domin shine ya zama hanyar ka izuwa Aljanna, kaga kuwa wanda ya zame maka sanadin shiga Aljanna shi yafi cancanta da ka godewa fiye da wanin sa.  Don haka ne ma suke ganin batun ka ji ma cewa ka yi wani abu ma sam bai taso ba!!!. Da wannan ne nake cewa: Ya yan`uwa na! ku taimaki mabukata saboda Allah, tun kafin damar ku ta kure, a lokacin da ba kuda shi a duniya, ko kuma ba ku da dammar yi domin kun raga kun bar ta a baya, a can duniya.  Ballatana ma hanyoyin taimakawa, masu muhimmanci a wannan zamanin suna da yawan gaske, kamar misalin temakawa masu karatu wajen biyan kudin admission, ko sai musu litattafai, ko biya musu kudin jarrabawa. Ayyukan da amfanin su da kuma ladan da zai rika zo maka a sakamakon su, ba za su taba karewa ba har izuwa tashin  alkiyama.{ya ku wadan da kuka yi imani kar dukiyoyin ku da ya’ya’yen ku su shagaltar da ku daga ambaton Allah………..* kuma ku ciyar (temaka a kowane irin fage na taimako) daga abin da muka azurta ku da shi tun kafin lokacin da mutuwa za ta zowa dayan ku, sai yace: ya ubangiji ina ma za ka jinkirta mini izuwa wani lokaci makusanci da na bada gaskiya kuma da na zamo daga cikin salihai} wace amsa ka ke tsammani Allah Ta'ala  zai bawa wadannan mutanen?!!! Ka koma suratul munafikun. Allah ya kiyayemu Nadama alokacin da bata da amfani. Amin summa amin.             
 WAFATIN ZAHRA (A.S)
A ranar 3 ga watan jimada ula ne, sayyida Fatima Azzahra (A.S) ta bar duniya, a shekara ta 11 daga hijira. Ta rasu bayan wasu kwanaki da rasuwar baban ta Shugaban halitta baki daya: Manzo Muhammad (S.A.W.A).  Hakika Fatima itace Bishiyar da ba’a samu ba, kuma baza ‘a taba samun kamar ta ba. Itace shugabar mata baki daya tun daga farkon duniya har karshen ta.  Sayyida iyaka ce a kowane fage da zaka iya yin tunani ko Magana akai, idan ka tabo bangaren Ilimi, Ibada, Akhlak, Karamci, da dai sauran su, zaka ga cewa babu kamar ta. Me ka ke tsammani ga wacce ta amsa tambayar da dukkanin sahabbai suka kasa amsawa?, wannna ya faru ne alokacin da Manzo (S.A.W.A.) ya tambaye su cewa: "menene yafi ga mace” sai dukkanin su suka kasa amsawa, yayin da Fatima taji labari sai tace da inanan da nace: "kar taga namiji kuma kar shi ma ya ganta”. Akhlak din ta kuwa, ka zantar ba tare da damuwa ba, ita ce wacce idan tana sallar dare take yi wa makwabtanta addu’a acikin dukkanin addu’o’in ta, har sai yayin da dan ta Imam Hasan (A.S.) ya tambaye ta, yaya ba ta yiwa kanta addu’a, sai makwabtanta kawai? Sai ta ba shi amsa da cewa: ya da na "MAKWABCI SANNAN GIDA”  Wani makaho ya nemi izinin shiga wajen ta (A.S), sai ta sa hijabi sai Manzo (S.A.W.A.)  yace: "don me za ki sa masa hijibi alhali makaho ne?”, sai ta ce: "in har shi baya gani na ai ni ina ganin sa, kuma yana jin kanshin iska”, sai Manzo (S.A.W.A.) yace: "na shaida cewa ke tsoka ce daga gareni.”  Karamominta kuwa, sun fi karfin guntun alkalami irin nawa, domin ita ce wacce ta cika duniya da karamomi, ya isheka misali, yin hirar ta da babar ta tun tana ciki, da kuma hore mata mala’iku wadanda suke taya ta aiki, da sauran su wadanda suke cike da litattafan tarihi.
Sayyyidah ta gamu da mummunan bakin ciki bayan wafatin baban ta, al’marin da ya girgiza tarihin duniya da ma na dan adam baki daya, lamarin ya kai ga cewa a yanzu dinnan ba’asan takamemen inda kabarin Fatima yar ma’aikin Allah yake ba. A yanzu a ce duk duniyar nan babu wanda zai iya nuna maka inda kabarin yar Manzon Allah yake, wacce ita kadai ce ya bar mana?
Menene amsar mu ranar alkiyama, idan muka hadu da Manzo  yace: "yaya kuka riki ahli na a baya na? Shin a she son su da yi musu biyayya, ba shi ne ladan  sakon da Manzo (S.A.W.A)  yazo mana da shi daga Allah Ta'ala, kamar yadda ya fadi acikin littafin sa madaukaki ba? Daya daga cikin manya-manyan Bayin Allah, Sufaye wanda ake kira Ayatullah Mar’ashi Annajafi, wanda ya sami ismullahil a’azamu ya nemi a nuna masa inda kabarin sayyida Fatima yake, sai akace masa ba zai samu wannan ba, domin an kebanci Imam Mahdi (A.S.) da wannan a lokacin da ya bayyana, shi ne kadai zai bayyana inda kabarin nata yake.
 Nasiha ta gare ka/ki ya dan uwa da yar uwa mai karatu, mu koma tarihin musulumci domin mu san daga ina muka fara kuma ina zamu kare, domin in har ba mu san mafarar mu ba, to ba yadda za’ayi musan makarar mu. Sannan ga wanda yake so ya san yanayin da yake ciki a yanzu, ya zama wajibi ya san abin da ya wuce acikin tarihin da ya gabace shi, im ba hakaba, babu makawa zai fada cikin rudani da dimuwa. Allah ya shiryar da mu tafarkin sa madaidaici.
TUSHEN AKIDA
Sau da yawa idan ka tambayi mutane menene yafi komai mihimmaci a musulum ci? sai yace maka sallah, yana mai dogara da hadisan da suka yi nuni akan mahimmancin ta, da kuma kasantuwar ta ginshikin addini, ba tare da waiwayawa izuwa, shin ita ginshiki ce a tushen addini (akida), ko kuma a ressan addinin, (furu`a), da kuma rashin lura da cewa ita sallar nan akwai fondishin (tushe) wanda ta doru akan sa wanda kuma idan ba mu kyautata shi ba, ta zama aikin ka banza!
Hakika akwai aiki ja a gaban mu ta bangaren fahimtar da al’ummar mu wajibi na farko sannan me bi masa sannan me bimasa…..! Shi wannan addinin da muke gani lissafaffen abu ne mai tsari, wanda babu wani abu da ya kai shi tsari. In ka so, ka dauki misalin sa tamkar a matsayin bishiya ce, wacce take da tushe da ressa da ganye da kuma ya’ya. Bani labari ya kai dan’uwa na, ya kake  gani idan ka sare tushen bishiya kabar ta da ressan ta, ganyen ta da kuma yayan ta, shin kana tsammanin zata ci gaba da rayuwa saboda kabar mata mafi yawan abin ke jikin ta? Babu shakka amsar za ta zama a’a, amma da za ka bar mata tushen ta ka cire sauran baki daya, sannan ka kyale ta, tabbas zata ci gaba da rayuwa kuma ta ma maye su da wasun su.
Wannan zai sa ka fahim ci cewa: a she idan mutum ya sami matsala a cikin tushen addinin sa to komai ma ya sami matsala, har sallar da yake takama da ita. Da wani yaren idan tushen addinin da mutum ya doru a kan sa ba daidai ba ne, imma, saboda bai je makaran ta ba, ko kuma bai fahimce shi daidai ba, ko kuma shi kansa tushen ba daidai bane, a wannan yanayin, dukkanin ayyukan sa na ibada batattu ne. "bisa ijma’in malamai addini musulumci baki daya”
Ashe kenan ya zama wajibi mu fara tsaida tushen addinin mu, sannan mu tsaya kyam akan rassansa. Wanda sune su salla azumi da sauransu. Daya daga cikin babbar matsalar da mulkin mallaka na turawan yamma ya kawo, shi ne, raunana koyarwar addini, da kuma fifita karatun da ba na addini ba akan sa, ako wane mataki. Yanayin ya kai ga cewa, mafi yawan makarantu, ba a koyar da addini kamar yadda ya kamata, ta yadda yawancin daliban ba sa iya bambamce maka tsakanin tushen bishiyar addini{akida} da reshen ta {furu’a}.
Wadannan matsaloli sun jawo mummunan koma baya acikin lamarin addinin alummar musulmi na wannan nahiyar, kai dama duniya baki daya. Wanda bai san tushen addinin sa ba shin za’a karbi salla, azumi, zakka da sauran ibadun sa, ko kuwa?
Wai shin a tun asali an yarda da musulumcin wanda bai san tushen addinin sa ba ko kuwa?
Wane matsayi malamai suka ajiye wanda yake yin addini saboda ya sami iyayen sa da kakannin sa akai?.
Wadannan amsoshi da ma makamantan su  duk za mu tattauna su a fitowa ta gaba.
[MUNA YI MU KU FATAN ALHAIRI]
 MAKOMAR BINCIKE

•    KARAMATUZ-ZAHRA’U
•    AL-ASRARUL-FATIMIYYA
•    AL-AKHLAKUL-ISLAMIYYA
•    BUGYATUL MUSLIMINA
•    RISA LATUL-HUKUK
•    AKAIDUL-IMAMIYYA
•    SHARHI UMMUL-BARAHIN.

AMINCI YA TABBATA GA MANZO MUHAMMAD DA ALAYENSA DA SAHABBAN SA.

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= muniruddin875@yahoo.com
Whatsapp da telegram +2348038557822

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: