bayyinaat

Published time: 23 ,January ,2017      09:49:02
Sayyida Zahara (a.s) ta kasance babban misali abin koyi ga duk wanda yake son tsayawa kyam kan gaskiya da kare hakkinsa da kuma hakkin al’umma yayin da bayan wafatin babanta (s.a.w) ta tsaya ta dage wurin ganin ta kwaci hakkinta da gadonta, da kuma hakkin mijinta na jagorancin al’umma, da hakkokin al’umma na ganin sun samu mai shiryarwa zuwa ga tafarkin gaskiya da hasken shiriya da shari’ar Allah (s.w.t).
Lambar Labari: 12
Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen Sayyida Zahara (s.a) da rayuwarta.
Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.
Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.
Sayyida Zahara (a.s) ta kasance babban misali abin koyi ga duk wanda yake son tsayawa kyam kan gaskiya da kare hakkinsa da kuma hakkin al’umma yayin da bayan wafatin babanta (s.a.w) ta tsaya ta dage wurin ganin ta kwaci hakkinta da gadonta, da kuma hakkin mijinta na jagorancin al’umma, da hakkokin al’umma na ganin sun samu mai shiryarwa zuwa ga tafarkin gaskiya da hasken shiriya da shari’ar Allah (s.w.t).
Ta kasance farkon wanda ya yi shahada kan kariya ga wilayar Imam Ali (a.s) da zuriyarta, da kuma wilayar manzon rahama (s.a.w), da kuma kana bin da ya shafi neman hakkinta wanda yake na dukiyarta ne da annabin rahama (s.a.w) ya ba ta shi kyauta tun lokacin yana da rai, sannan kuma da abin da ya shafi gadonta. Da wannan ne zamu ga ta kasance mutum na farko da ya fara nuna wa duniyar musulmi jajircewa a kan kwatar hakkinsu komai tsanani da wahala.
 Mafi tsananin lamari garta shi ne lamarin da ya shafi jagorancin al’umma bayan manzon Allah (s.a.w) al’amarin da ya sanya ta jaula da gewayawa gidajen ansar domin su ba ta gudummuwa amma ba ta samu wannan ba daga ko da mutum guda. Lamarin ya kai ta ga tattaunawa da halifan farko kan ya ba su hakkinsu amma abin ya ci tura, don haka ne ma aka samu jan daga mai wuyar gaske da musayan kalamai na magana kan wannan lamari tsakanin gidan Annabi (s.a.w) da kuma kuraishawa.
Sayyid Zahara (a.s) ta so ta nuna wa al’umma munin wannan lamarin na canja wasiyyar Annabi (s.a.w) da kawar da jagoranci daga cikin alayensa zuwa ga waninsu, da sakamakon da zai samu al’ummar musulmi na kauce wa koyarwar musulunci ta asali ta asasi. Amma al’umma ba ta amsa mata ba, saboda jahiltar sakamakon abin da ta tsoratar da su, da yawan mutane sun dauka cewa lamarin mulki ne kawai, sai dai abin ya fi karfin hakan kamar yadda ta yi nuni, don sai ga shi al’ummar musulmi ta kasu gida-gida sakamakon sabani kan mene ne gaskiyar hakikanin musulunci, kowa yana bin nasa son ran a matsayin shi ne gaskiya, aka jefar da alayen Annabi (s.a.w) a gefe babu wani mai biyayya ga tafarkinsu sai ‘yan kalilan, wani abin mamaki da takaici ma sai aka bi su da bita-da-kulli da kisa, sannan mai bin tafarkin da suka shata ya zama abin kyama a cikin al’umma.
Fadima (a.s) ta kafa hujja kuma ta yanke duk wani hanzari ga wannan al’ummar yayin da ta nemi su bi ta suka ki, kuma ta nuna musu sakamakon da a yau al’ummar musulmi suke cikinsa na kasakanci, da rarraba, da son rai, da rashin kima da daraja. Ta yi fushi da al’umma amma duk da haka al’ummar ba ta fadaka ba, don haka ne ma ta yi wasiyya da kada wanda ya halarci janazarta sai Imam Ali (a.s) da ‘ya’yanta da wasu kalilan da aka boye sunayensu don gudu kada a tilasta su nuna inda aka binne ta, don haka ne ma ya kasance abin kunya har yau ga duniyar musulmi domin ba su san kabarinta ba!.
Ta kasance mafi muhimmancin mutum da yake misalta mai hamayya da shugabancin Abubakar da duk wanda yake goyon bayansa, sannan kuma mutum mai kwarjini da kowa yake shayi, wasu masu tarihi sun kawo cewa Imam Ali (a.s) ya samu sauki a rayuwarta daga cutarwar masu jagoranci har sai bayan mutuwarta ne aka tilasta masa, aka takura rayuwarsa da kuntatawa mai tsanani!, har ma suna kawo cewa duk tilascin da aka yi masa bai yi bai’a ba sai bayan rasuwarta da ya kasance ba shi da wani mai ba shi kariyar siyasa!.
Ta kasance ita ce ta fi kowace mace kamewa a tarihin matan duniya, don haka ne ta tarbiyyantar da kanta da matan zamaninta cewa; abin da ya fi musu kyawu shi ne su lizimci gidansu sai dai gun lalura. Kamewarta ta kasance hatta da makaho tana sanya masa hijabi domin ita tana ganinsa idan shi ba ya ganinta!.
Ita ce tsokar jikin Manzon Allah (s.a.w), don haka ne dukkan halayensa su ne halayen sayyida Zahara (a.s), kuma hatta da tafiyarsa da maganarsa ba su da bambanci da yadda Manzon Allah (s.a.w) yake yin nasa.
Ta kasance ita ce ta fi kowa ibada bayan babanta da mijinta, domin tana tashi har sai kafafunta sun tsattsage, har ma tana kwana tana ibaba ba ta komai sai ambaton Allah da yi wa makota da al’ummar musulmi addu’o’I, hatta da danta Hassan (a.s) yana cewa: "Ya baba! Kin kwana kina salla amma ban ji kin yi wa kanki addu’a ba sai dai makota? Sai ta ce masa: Ya dana; Makoci sannan gida!.
Wannan ita ce Fadima (a.s) mai ibada da zuhudu, da kin zalunci, da tsoron Allah, da kame kai, da kuma kariya ga al’umma, da neman kafa adalci, da yin tsaye gaban duk wani zalunci.
Salman Muhammadi ya ga faci goma sha biyu a jikin kayanta na gashin tumaki sai ya fashe da kuka yana cewa: ‘Ya’yan sarkin Rum da na Farisa suna cikin alhariri da sundus, amma ‘yar Muhammad annabin Allah (s.a.w) tana cikin tufafi masu kaushi kuma da fashi goma sha biyu!?
Ta kasance tana yin nika da hannunta har sai suna kumbura suna yin ruwa, kuma tana shayar da ‘ya’yanta da kanta, tana sanya tufafin da aka yi da fatar rakuma, babanta mai tsira da aminci ya gan ta a wannan halin sai ya ce: Ya ‘yata ki gaggauta dacin duniya da zakin lahira. Sai ta ce: Ya Manzon Allah, godiya ta tabbata ga Allah kan ni’imominsa da gode masa a kan baiwowinsa.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana fara tafiyarsa da yin bankwana da ita ne, kuma idan ya dawo yana fara shigowa cikin madina da zuwa wurinta ne. Wata rana saboda tarbarsa ta taba sanya wani tufari na Khaibar domin tarbar babanta da mijinta. Yayin da Manzon Allah (s.a.w) ya ga hana sai bai ji dadi ba, da ta fahimci haka, sai ta cire sarkarta da dan kunnenta, da kayan da ta sanya ta aika masa da shi ta ce; ya sanya shi a cikin tafarkin Allah. Yayin da ya ga haka sai ya tausaya mata ya ce: Ta yi abin da ya fi kyawu, babanta fansa ne gareta har sau uku, sannan ya ce: Babu ruwan alayen Muhammad da duniya, domin su an halicce su ne don lahira, an kuma halicci duniya don su ne. A wata ruwayar akwai karin ya ce kuma: Wadannan su ne alayena, ba na son su ci mai dadinsu tun a rayuwarsu ta duniya.
Fadima (a.s) ta kasance matukar gaya wajen ilimi, ta kasance tana amsa tambayoyi cikin sauki, hatta da tambayar da Manzon Allah (s.a.w) ya tambayi sahabbansa game da cewa "mene ne ya fi cancanta ga mace” wata rana suka kasa amsawa sai ita ce ta gaya wa mijinta amsa cikin sauki, shi kuwa ya zo ya gaya wa Manzon Allah (s.a.w) abin da ta ce.
Ta kasance makoma gun mata da maza kan mas’alolin addini, don haka ne ba ta da iyaka ga dukkan mai koma mata don neman amsar tambayarsa. Sannan an ruwaito hadisai masu yawa daga gareta tsira da amincin Allah su tabbata gareta.
 Wata mata ta taba zuwa wurinta ta tambaye ta mas’aloli goma ita kuma tana amsawa, sai matar ta ji kunyar ci gaba da tambaya tana ganin kamar ta tsawaita mata, matar ta ce: Bana son in wahalar da ke da takurawa. Sai Fadima Zahara (a.s) ta ce: Ki tambayi duk abin da kike so, ki sani, ni na ji babana (s.a.w) yana cewa: "Hakika malaman al’ummata ana tayar da su, sai a rika ba su girma daidai gwargwadon yawan iliminsu, da kokarinsu na shiryar da bayin Allah”.
Ta kasance mai tsananin fasaha matuka, A’isha tana cewa: Ban taba ganin wani wanda ya fi kowa kama da Manzon Allah (s.a.w) a magana da zance ba da ya kai Fadima (a.s). Duk wani wanda ya san hikima ya duba hudubarta to zai san kimarta da kimar maganganunta.
Hudubarta mai fasaha da balaga da hikimomi da babu kamarsu ta shahara matuka, alhalin a lokacin ba ta wuce shekaru goma sha takwas ba, amma ta zo da hikimomin da suka dimautar da masu hankula da masu sauraro har a nade duniya, da wannan ne ta cancanci kasancewa kwafi ce ta babanta (a.s).
Kuma ba mamaki gareta domin ita ‘yar babanta ce, kuma matar mijinta, wadanda duniya ba ta haifi kamarsu ba a cikin fasaha da magana ba. Don haka ne maganarta ta kasance mashaya ce da ta bubbugo daga wadannan manyan koguna guda biyu marasa gaba da iyaka, sai ta fesa wannan hasken na hikima da ya mamaye sasannin dukkan ‘ya’yanta tsarkaka tun daga kan Imam Hassan (a.s) har zuwa kan Imam Mahadi (a.s).
Sannan zamu ga abin da ta zo wa duniya da shi na rahama wanda har yanzu kowa yana cin albarkacinsa, yayin da ta nemi a ba ta ‘yar hidima daga cikin bayin da aka kawo da zata taimaka mata a aiki, sai aka ba ta zabi ko tasbihi ko ‘yan aiki, sai ta zabi tasbihi wanda dukkan al’umma zasu amfana da shi har alkiyama ta tashi. Don haka ne bayan salla aka so kowane mai salla ya yi wannan tasbihi, da fara da kabbara 34, da hamdala 33, da tasbihi 33, ga Allah madaukaki wanna kuwa ana kiran sa da tasbihin Zahara (a.s).
Ta ruwaito hadisai masu yawan gaske a kowane janibi da ya hada da; siyasa, tattalin arziki, zaman tare, rayuwar al'umma, hakkoki, hukunce-hukunce, ibadoji, da mu'amaloli, da sauransu. Wannan lamari ne da yake bukatar tsawaitawa don haka ba zamu fada cikinsa ba.
Sayyida Zahara (a.s) ita ce macen da take cikakkiya ta kowane janibi da dukkan mata ya kamata su dukufa wurin neman saninta, da koyi da ita a dukkan janibobin rayuwarta ta zaman al’umma, da ta cikin gida, da ta waje, da ta mu’amala da mutane, da jagoranci da makamantansu.
Matan da suke son zama kammalallun mata masu daraja a duniya to sai su yi koyi da mata masu daukaka kuma su dauki samfurin rayuwar zaman tare daga Imam Ali (a.s) da sayyida Zahara (a.s), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (a.s) ya shiga wajan Fadima (a.s) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu. Sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai”. Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba” Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi” .
Daga Saifu, daga Najmu, daga Abu Ja’afar (a.s) ya ce: "Hakika Fadima (a.s) ta lamunce wa Imam Ali (a.s) aikin gida da kwaba gari da yin gurasa da share gida, shi kuwa ya lamunce mata abin da yake bayan kofa: yin itace, kawo abinci… sai wata rana ya ce da ita: Ya Fadima shin kina da wani abu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama hakkinka ba mu da komai tun tsawon kwana uku ke nan sai dai abin da muka tanadar maka kai kadai, sai ya ce: Me yasa ba ki ba ni labari ba? Sai ta ce: Manzon Allah (s.a.w) ya hana ni in tambaye ka wani abu, ya ce da ni: Kada ki tambayi dan amminki wani abu, in ya zo da shi, shi ke nan, in ba haka ba to kada ki tambaye shi”.
Yahaya da sanadinsa daga Abi Sa'idul khuduri, ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari sai ya ce da Fadima (a.s): Ya Fadima shin kina da wani abu da zamu ci. Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta babu wani abu da ya kwana gunmu da zamu ciyar da kai shi yau, ba ni da komai kwana biyu ke nan sai abin da na zabe ka a kaina da shi da kuma abin da zabi wadannan biyu –tana nufi Hasan da Husain- a kaina da shi. Sai ya ce: Don me ba ki gaya mini ba sai in samo miki wani abu? Sai ta ce: Ni ina jin kunyar Allah in kallafa maka abin da ba zaka iya ba, kuma ka kasa samu .
Daga Abil mufaddal, ya ce : Muhammad dan Ja’afar dan Kais dan Maskana ...da dogon sanadinsa sai a koma wa littafin… daga Abi Sa'idul khuduri ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari mai yunwa, sai ya ce: Ya Fadima, shin kina da wani abu da zaki ciyar da mu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta, ya girmama ka da wasiyya, babu wani abu da ya wayi gari a wajenmu da zamu ciyar da wani mutum shi tun kwana biyu ke nan sai abin da na fifita ka da kai da Hasan da Husain da shi a kaina. Ya ce: Har da ma yara biyu! Me yasa ba ki sanar da ni ba sai in zo muku da shi? Sai ta ce: Ya Abal Hasan, ina jin kunya daga ubangijina in kallafa maka abin da ba zaka iya ba” . 
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (a.s) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado.

Manzon Allah (s.a.w) ya tarbiyyantar da ita, ya yi mata nasihohi, ya kuma nuna mata hanyar da zata bi domin rabauta duniya da lahira. Sai ta bi dukkan shiriyarsa, sai ta kasance malama, mai sanin duk wata mas’ala, kuma ma’asumiya da ba ta taba yin sabo ba, kuma mai shiryayya mai shiryarwa ga al’umma, da al’umma ta bi ta bayan Manzon Allah (s.a.w) da ba a taba samun wani bata ko jahilci ba cikin duniya.
Ta sha wahala matuka a rayuwarta, ba don gudun tsawaitawa ba, da mun kawo da yawa daga cikin hikimomin Manzon rahama (s.a.w) da wasiyyoyin da ya yi mata na juriya kan wahalar da take sha, domin ba ta tarbiyya kan kowane janibi na rayuwa.
Sai dai yayin da zata bar duniya sakamakon abin da ya faru mai daci na zalunci a kanta, ta yi wasiyya ita ma ga Imam Ali (a.s) da ya boye janazarta da kabarinta, kuma ya yi aiki da dukkan wasiyyoyinta hatta wadanda suka shafi rayuwarsa bayan wafatinta. Ta yi masa wasiyya da matar da zai aura bayanta, da kuma raba kwana tsakanin matarsa da zai aura da ‘ya’yanta Hasan da Husain (a.s) da sauran wasiyyoyi masu sanya kuka da hawaye Allah ya sanya mu cikin cetonta.
An yi wa Fadima (a.s) bazata a wata rana da mutuwar Abu Talib ammin Babanta  kuma shugaban Bani Hashim a lokacin ne ta san cewa lallai wani rukuni daga rukunan da Babanta (s.a.w) yakan dogara da su ya rushe saboda haka ta ji muryarsa tana rawa saboda bakin ciki, fukafukin da yakan tashi sama da su guda biyu an cisge dayan musamman saboda tsananin bakin ciki da ya mamaye zuciya da fuska madaukakiya.
Sai ta ga Babanta mai daraja (s.a.w) yana kuka a farkon ganin haka a rayuwarta da hawaye masu zafi da ke kwarara a kumatunsa masu albarka a lokacin duk wanda yake wannan duniya ya san cewa lallai akwai zafi da yake tafarfasa a cikin jini da tsuka na Annabin rahama don haka ne ma sai ta motsa da jiki mai haske da albarka ta sanya fararen hannayen nan da suke daga aljanna ne aka gina su, tana mai share masa hawaye masu zafi da fari da ke gudana suna diga kasa kamar ‘ya’yan carbi dunkule-dunkule, wallahi na so a ce suna zuba ne a jikina domin in shafe su a fuskata domin kada ta samu shafa daga shedan har abada da takan kai ga toshe mahangar tunani, na kuma shafa a jikina domin kada ya sami kuna na wuta!.
Ta kasance tana mai shafewa da hannayenta masu daraja har ta kwantar da zogin da yake ji ta saukar da tafasar nan ta kunkunar juciyarsa ta kawar da abin da yake ji na rashi mai tsanani.
Amma ba a dade ba da ‘yan kwanaki kadan sai ga musiba mafi girma ta sauka ta kasance, alhali ga wancan mikin bai warke ba aka sake tunbuke wa Manzon tsira daya fukafukin da ya rage, alhali da man ya yi rauni da yake zubar jini maras yankewa.
Wayyo Allah!! ba a dade ba sai na ji wata kalma da ta fito daga baki mai haske da kamshin da digonsa ya fi karfin almiskin da yake cikin duniya gaba daya, wace kalma ce? Kalma ce mai nauyi daga haske mai baki mai haske da ake cewa da ita Babar Babanta (a.s) tana cewa: Ina Babata!!.
Saboda haka jin wannan kalma ta sanya Manzo (s.a.w) ya ji wani suka da ya fi sukan kibiya ciwo domin uwa ce ta hakika take tambayar mata ta hakika da suke da wadancan alakoki biyu da mafi girman halitta (a.s) uwa ce kuma ‘ya amma ba tare da an sami abin da masu ilimin falsafa da suke cewa gewayo ba, wato na farko ya koma na karshe, ga hawaye yana zuba kamar ana mamakon ruwa mai kwarara, kai al’umma ku ji wannan kalma mai nauyi da ke kunshe cikin tambayar uwa ga dan da yake uba gareta da take cewa ina Babata?!!.
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi kuka kuma duk wanda yake tare da shi a cikin gidan ya yi kuka, Fadima ta rankwafa ta shiga cikin lullubewar uban (s.a.w) kamar yanda ‘ya’yan kaza suke shiga cikin fukafukan babarsu, kalma ce da tafi abin da ya faru ciwo saboda bakin ciki ne ya sami uwa da take tafi uwa kima domin ita uwa ce daga bakin wahayi daga duniya mai tsarki da nisa daga duniyar ‘yan mariskai, da wannan ma’ana ta duniya da ba mai gane hakikanin ma’anarta sai masu ilimi. Ya girman nauyin wannan tambaya a wannan hali mai wahala da bakin ciki daga gareta (a.s)!! 
Saboda haka sai fiyayyen halitta (s.a.w) ya fada yana mai lallashin halinta da neman kawar da nata bakin cikin da ba bakin cikin da ya kai shi ciwo da zafi, ina iya cewa: bakin cikin da yake ji sai ya ta fi sakamakon ganin halin da take ciki, saboda haka sai hadafinsa ya zama shi ne kokarin kawar da nata bakin cikin yana mai fada da harshe mai laushi da taushin murya domin sanyayawa ga zuciyarta: 
"'Yata hakika Babarki ta tafi aljanna kuma hakika dan’uwana Jibril (a.s) ya ba ni labari cewa tana nan a wani gida na karau ba wahala ba hayaniya a cikinsa ".
Haka nan Fadima ta zama marainiya ba uwa, ta samu daci a rayuwa tana ‘yar shekara takwas dacin da ba ta tada samun irinsa ba sai a lokacin wafatin Babanta (a.s). 
Haka nan aka gaggauta mata fitunu da jarabawowi a rayuwa a shekaru na budurci har zuciyar ta ta tsage saboda rashin uwa!! Bakin ciki ya girgiza ta tana karama mai rauni, ta kusa ta fadi kasa ba don juyawa da Baban (s.a.w) ya yi zuwa gare ta ba da gaggawa yana mai shafe mata hawaye kamar yadda take shafe masa, ta kafu a kan hakuri da juriya!!.
Tana mai dimuwa cikin lamarinta, ba ta san mai zata yi ba; shin zata yi juriya ne da bala’in da ya same ta na rashin uwar da babu wata uwa kamarta ko kuma zata yi wa Babanta da babu uba kamarsa ta’ziyyar rashin matarsa da babu wata mata kamarta ne!.
Nan da nan sai ta zabi ta kasance mai ta’aziyya da lallashi ga uban domin bazatar da aka yi masa na amminsa da matarsa, tana mai yakini cewa ba ya rasa mata maras misali ne kawai ba, har ma ya rasa mai kariya ne mai dauki-ba-dadi da gwagwamarya domin kare hadafinsa kamar yadda amminsa Abu Talib (a.s) yake daya rukunin mai kare shi mai kuma lallashi da tausayi mai juriya, kuma ga shi ya rasa masu ba shi kalmomi masu dadi da ra’ayi mai dacewa. 
Sai Fadima ta yunkura ta motsa a wannan karon ba domin ta tambayi Babanta ba sai domin ta lallashe shi ta kara masa karfin gwiwa ta kawar da bakin cikinsa tana mai shafe masa hawayi daga kumatunsa masu albarka (s.a.w) tana nuna masa kauna irin wacce uwa kan nuna wa danta da kuma son nan da ya rasa daga Khadiza, domin haka ne ta zama Babar banta kuma ‘yarsa a lokaci guda .
Haka nan ta zama uwa ga uban (a.s) a kiyayewa da kauna kuma ‘ya a nasaba da tarbiyyatarwa da koyi amma uwa a kula da kiyayewa.
Haka nan ta fara wata marhala ta rayuwa sabuwa ta fara sabon shafi na rayuwa da Babanta ko zata iya zama kamar khadija ga Babanta (s.a.w) kamar yadda Ali (a.s) ya zama kamar amminsa (s.a.w) Abu Talib (a.s) gareshi. 
Haka nan Fadima ta sha wahala tana mai cire kayoyi daga digadigan Babanta tana mai shafe masa jini daga kafafunsa tana mai wanke hannyansa da shafe masa kasa daga fuskarsa tana mai kawar da bakin cikin nan na ‘ya’yan hanji da kayan ciki daga bayansa da kirjinsa, har shekarar ta ta tara ta wuce.
Babanta ya kasance karkashin zaluncin masu makwabtaka da shi har ta wayi gari tana mai nemansa wata rana sai ta yi kicibis da kazanta a kansa da kasa da kayoyi, saboda haka ta gaggauta tana mai kawar da wannan da hannayenta masu ni’ima tana mai kuka saboda abin da ya sami Babanta na daga cutarwar Kuraishawa da gabarsu da kuma cutarwar makota da makusantansa daga Bani Abdi Manafi, sai wannan ya sanyaya masa zuciya, fushinsa ya kau, zuciyarsa ta kwanta hankalin ‘yarsa ya faranta, tana mai kuka daga halin da ta gan shi a ciki, shi kuma yana mai ce mata: "Kada ki yi kuka ya ‘yata Allah zai kare Babanki”. 
Kafirai ba su kyale Fadima (a.s) ba kamar yadda ba su kyale Babanta ba kamar yadda wani mafi wautarsu Abu Jahal (L) ta ji shi yana zagin Babanta (s.a.w) saboda haka ne ma ta kasa mallakar kanta ta yi raddi ga shi Abu Jahal (L) da kalmomi masu hikima da ke cike da fasahar nan ta Bani Hashim amma saboda Abu Jahal ba shi da kunya da mutunci bai san shi ba har abada, sai ya daga hannunsa ya mare ta a fuskarta yana mai ci gaba da zagi da cin mutunci ga Manzo (s.a.w), Fadima (a.s) ta tafi tana mai bakin ciki da kuka sakamakon abin da yake yi wa Babanta, har ta wuce wuri da Abu Sufyan yana mai jin kukanta da ganin hawaye na zuba a kumatunta (a.s) yana mai tambayar ta me ya same ki ya ‘yar Muhammad!
Haka nan wata rana Fadima (a.s) ta wuce wasu mutane daga manyan Kuraishawa suna shawara kan al’amarin Muhammad (s.a.w) sai ta ji wasu suna cewa: Wallahi ba ma ganin Muhammad (s.a.w) zai daina abin da yake yi, idan mu ka kyale to lallai zai shuna mana bayinmu a kanmu da ma’aikatanmu, kuma zai canza matanmu da ‘ya’yanmu ta yadda babu wata dubara da zata rage garemu, me kuke gani?.
Abu Jahal (L) ya motsa yana mai cewa ina ganin ku kashe shi kawai. Sai wani ya ce: Yaya zamu yi da fushin Bani Hashim da takubban dakarunsu?. Abu Jahal ya ce: Amma yadda za a yi shi ne, kowanne daga cikinku ya dake shi da takobi dukan kwaf daya sai ku yi musharaka a jininsa gaba daya ta yadda Bani Hashim ba za su iya daukar fansa ba sai dai maganar diyya.
Da Fadima ta ji wannan magana sai zuciyarta ta cika da tsoro a kan Babanta, ta lizimci wajan, ta ki barinsa, idanunta suna kula da hanya har sai ta ga Babanta ya bullo da sauri sai ta gaya masa duk abin da Kuraish suka yi  na makirci da kaidi. 
Sai ya gaya mata cewa kada ta damu: "Ki tabbata ya ‘yata Allah ba zai taba ba su dama a kan Babanki ba”. Annabi ya wuce masallaci har sai da ya shiga ya wuce mutanen da suke mitin a kansa domin kashe shi, sai suka yi shiru suka rufe idanunsu saboda abin da suka gani a fuskarsa na haiba da kwarjini, suka mance abin da suka yi ittifaki a kansa dazu, har sai da Manzo (s.a.w) ya tsaya a kansu ya dauki kasa jimki daya ya watsa a kansu yana mai cewa: "Fusaku sun muzanta”.
Sannan ya fuskanci Ka’aba ya yi salla ga Allah madaukaki (s.w.t) a kusa da su, Fadima (a.s) tana tsaye tana ganinsu ba wanda ya motsa daga cikinsu kamar ba wanda ya gan shi, yayin da ya gama sallarsa da munajatinsa sai ya rike hannun ‘yarsa suka tafi gida tare!
Haka nan ta sami wani kunci mai yawa na abin da ta gani wata rana, Babanta yana salla a Ka’aba, ga Abu Jahal (L) da wasu daga Kuraishawa kamar su Asi dan Wa’il Assahami da Haris dan Kais Assahami (L) suna yanka rakumi. Sai Abu Jahal da Umayya dan Khalf (L) suka waiga suka ce da yaransu: Waye zai zo mana da mahaifar rakumin Bani Saham sai ya dora shi a kan bayan Muhammad! (s.a.w) idan ya yi sujada? 
Wannan tunani ya yi wa wasunsu daidai Ukuba dan Abi Mu’id (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L) suka tashi suka dauko tunbi da mahaifar suka dora kan kafadun Manzon Allah (s.a.w) yana mai sujada.!
Fadima (a.s) ta ga abin da aka yi wa Babanta sai ta gaggauta tana mai jin zogi da bakin ciki mai tsanani a kan abin da ta ga ni, hawayenta suna kwarara a kan kumatunta, saboda haka sai ta bayar da duk kokarinta wajan ganin ta kawar da wannan dauda daga kafadun Babanta (s.a.w), Annabi mai girma Uba mai rahama ya daga kansa yana kallon ‘yarsa Fadima (a.s) idanunsa cike da rahama da tausayi da kauna da yarda da bege gareta, tare da dukkan abin da zuciya zata iya nuna wa na nutsuwa da tabbata da hakuri, sannan sai ya rike hannayenta tsarkaka ya tattaro ta zuwa kirjinsa madaukaki ya ce: "Mamakin yadda kika zama babar babanki da wuri haka Ya Fadima” .
Bai bar wannnan waje mai daraja ba tare da ita, wajan da kafiran Kuraish suka bata da dauda sai da ya daga hannayensa zuwa sama yana mai addu’a yana cewa: Ya Allah! ina kai karar Abu Jahal (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L)  a wurinka ka. Ya Allah! ina kawo karar Umayya dan Khalf (L) da Walid dan Utba (L) da Ukuba dan Abi Mu’id (L) da… .
Kada ka so ka ga irin farin cikin Fadima ‘yar Manzo (a.s) a wannan rana sakamakon irin matsayi da ya ba ta na wannan kalma ta (Babar Babanki) da ya daukaka ta zuwa gare shi, kamar yadda ta iya sanya wa a ran Babanta (s.a.w) a wannan ranar da aka samu haduwa a ruhi guda biyu da haduwar kanshi da kanshi, kuma haske da haske, cewa ruhin Baban (s.a.w) mai kira zuwa ga Allah ya samu sanarwa daga ruhin ‘yar mai neman ta zama uwa ga Baban (a.s) cewa ruhinta ruhi ne mai cike kuma kunshe da tausayi irin na uwa ga uban kuma kariya mai karfi mahalarciya a kowane abu da ya faru ga uban (s.a.w), wanda sau da yawa irin wadannan abubuwa suka yawaita bayan Kuraishawa sun samu dama da wafatin Abu Talib!!, sanarwar da ruhin uban ya samu daga ruhin ‘yar shi ne cewa ita uwa ce, don haka ta cancanci wannan kalam ta Babar Babanta.
Fadima (a.s) ita Kadai Ce ‘Yar Annabi (s.a.w) saboda wasu dalilai masu karfi da suka hada da: Na farko: Ambaton ‘ya’ya da jam’i a fadinsa madaukaki cewa: "Ya kai Annabi ka gaya wa matanka da ‘ya’yanka da matan muminai su sassauto da mayafansu wannan shi ya fi da a san su domin kada a cutar da su, kuma hakika Allah ya kasance mai gafara mai rahama.
Wannan al’amari ba ya nuna cewa manzon Allah (s.a.w) yana da ‘ya’ya sama da daya, al’amarin yana kan kaddarawa ne da ba dole ya kasance yana da samuwa ta zahiri ba, kuma akwai da yawa a kur’ani inda aka yi maganar jam’I na gaba daya amma ana nufin abu daya da shi kamar yadda Allah yake fada a cikin ayar mubahala da cewa: "idan suka yi jayayya da kai kan al’amarinsa to ka ce ku zo mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku sannan sai mu yi addu’a mu sanya la’ana kan makaryata” (aali imrana: 61).
Kuma dukkan musulmi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da kawukanmu shi ne Annabi (s.a.w) da kuma Imam Ali (a.s), mata kuma wanda jam’I ne ana nufin Fadima Zahara (a.s) ‘ya’ya kuma wanda shi ma jam’I ne ana nufin Imam Hasan da Husain (a.s).
Na biyu: Malaman Shi'a suna da wani ra’ayi kan wannan al’amari, akwai masu ganin Rukayya da Zainabi da Ummu kulsum ‘ya’yan Annabi (s.a)  ne, wasu kuma suna ganin agololinsa ne kuma ‘ya’yan Hala ‘yar’uwar sayyida Hadiza (a.s) da babarsu ta mutu sai sayyida Hadiza (a.s) ta dauki rainonsu, suna ganin cewa Hadiza ta kasance budurwa ba ta yi wani aure ba kafin Annabi (s.a), kamar yadda aka yada game da ita ba, kuma wannan shi ne ya fi kusa da gaskiya, kuma ita ce magana mai karfi.

Ibn Shahri Ashub ya fada cewa: "Ahmad Bilaziri ya ruwaito, haka ma Abul kasir alkufi a littattafansu, da murtadha a cikin Shafi, da Abu Ja’afar a cikin talkhis cewa Annabi (s.a.w) ya aure ta tana budurwa ne, kuma wannan yana karfafa abin da aka fada a littattafan Alanwar da albida’I cewa Rukayya da zainab ‘ya’yan Hala ‘yar’uwar Hadiza ne” . 
Kuma su ma’abota wannan ra’ayi suna da dalilansu a cikin littattafan hadisai da na nasabobi da na tarihi .
Kuma abin da yake cikin sahihul buhari yana karfafa wannan lamarin cewa: "daga Nafi’u cewa wani mutum ya zo wa Dan Umar sai ya ce; Ya baban Abdurrahman me ya sanya ka kake yin hajji wata shekara wata kuma ka yi Umara ka bar yaki saboda Allah madaukaki, kuma ka san cewa Allah ya kwadaitar game da shi?
 Sai ya ce: Ya kai dan dan’uwana an gina musulunci a kan abubuwa biyar ne: Imani da Allah da manzonsa, da salloli biyar, da azumin watan Ramadhan, da bayar da zakka da hajjin dankin Allah.
Sai ya ce ya kai baban Abdurrahman shin ba ka ji fadin Allah madaukaki a littafinsa ba: "idan wasu jama’a biyu na muminai suka yi fada ku yi sulhu tsakaninsu idan kuwa daya ta yi zalunci a kan dayar to ku yaki mai yin zalunci har sai ta koma zuwa ga al’amarin Allah” (Hujurat: 9). "Ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina addini ya kasance na Allah ne” (Bakara: 193)? 
Sai ya ce: Mun yi wannan yayin da musulunci ya kasance kadan ne, ya kasance ana fitinar mutum daga addininsa ko su kashe shi ko kuma su azabtar da shi har sai da musulunci ya yi yawa babu wata fitina yanzu.
Ya ce: me zaka ce game da Ali da Usman?
Sai ya ce: Amma Usman Allah ya yi masa afuwa amma ku kuna kin yi masa afuwa, amma Ali shi dan Ammin Annabi ne kuma surukinsa, sai ya nuna gidansa ya ce: Wannan ne gidansa kamar yadda kuke gani” .
Ibn Umar yana nunawa da hannunsa zuwa ga gidan Ali (a.s) cewa; ya kasance tare da Annabi (s.a.w) kuma muna iya ganin yadda ya kawo cewa shi ne surukin Annabi (s.a.w) mijin ‘yarsa amma bai fadi hakan ga Usman ba, wanda wannan yake nufin shi mijin agololinsa ne! Madogara: Masa’ilu Majallati JaishusSahaba; Al’ustaz Ali Kurani Alamili
‘Yar Annabi (s.a.w) Fadima Zahara (a.s)
Ita ce Fadima Zahara (a.s) kuma babanta shi ne Muhammad dan Abdullahi, kuma babarta ita ce sayyida Hadiza uwar muminai, mijinta shi ne Imam Ali shugaban wasiyyai, kuma daga 'ya'yanta da jikokinta akwai imamai masu tsarki.
An haifi Fadima ishirin ga jimada sani a shekara ta arba'in daga rayuwar Annabi (s.a.w) kuma ta yi shahada tana abar zalunta a ranar talata uku ga jimada sani shekara ta sha daya hijira, shekarunta goma sha takwas ne.
Imam Ali (a.s) shi ne ya binne ta a Madina ya boye kabarinta da wasiyyarta domin ta kafa hujja kan al'umma da zaluntar ta da aka yi da kuma kwace mata hakkinta. Kuma ta kasance kamar babanta a ibada da zuhudu da fifiko da takawa, kuma Allah madaukaki ya saukar da ayoyin Kur'ani game da ita .
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana yi mata lakabi da "shugabar matan talikai" kuma ya yi mata alkunya da "babar babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta .
Ta haifa wa Imam Ali (a.s) Imam Hasan da Imam Husain da Muhsin (a.s) wanda aka yi barinsa saboda cutarwa da babarsa ta fuskanta, da kuma sayyida Zainab, da Ummu kulsum (a.s).
Wafatin Nana Fatima (a.s): Kamar yadda muka san ice cewa sayyida Zahara (a.s) ta samu kantaa cikin wani hali na bakin cikin rabuwa da Mahaifinta, ta yadda kullum tana cikin kuka da bakin ciki. ta yadda ba za ta iya kamewa ba, wannan hakika yana faruwa ne saboda abu uku:-
Ta fi kowa sanin matsayi da darajar Mahaitinta, muhimmancin rayuwarsa cikin al'umma da abin da wafatinsa ya kunsa na rashi cikin wannan afumma.
Abubuwan da za su sami zuriyarta a baya na kisa da dauri a daidai lokacin da kowa ya juya musu baya, ba su da wani mai taimako sai Allah.
Fitintunu da bala'i da al'ummar musulmi za su dinga shiga. sakamakon barin wasiyyar manzo ta biyayya ga Imam Aliyu ((a.s)) da sabawa wasiyyar Manzo (s.a.w). ta yadda shugabancin musulmi zai koma hannun jabbirai  mashaya giya da sunan khalifancin Mahaifinta bayan wasu lokuta kamar yadda ya faru a daulolin Banu Umayya da Banu Abbas
Ba ka jin komai sai kuka cikin gidan Imam Ali (a.s), mutanen Madina ko'ina sai kuka kake ji. Matan Banu Hashim dukkansu sun hadu cikin gidan suna ta kuka. Imam Aliyu ((a.s)) yana zaune a tare da shi akwai Hasan da Husaini, suna ta kukan rabuwa da mahifiyarsu. Ita kutna Ummi Khulsum ta fita waje tana kuka tana cewa: "Ya Babanmu, Ya Manzon Allah, hakika yau kam mun rasa ka dukkannin rasawa, babu saduwa nan duniya har abada, mutane kuwa sai zuwa suke ba iyaka suna yi wa Imam Aliyu ((a.s)) ta'aziyya.
Sai Abubakar da Umar suka ce: In za a yi mata salla a bari sai sun zo ko kuma a aika musu. Nana (a.s) ta yi wafati ne bayan la'asar zuwa magriba, lokacin da jama'a suka ga dare ya yi ba a yi mata salla ba, sai suka yi zaton jana'izar sai gobe za a yi, don haka sai suka watse. sai wadanda aka sanar da su yadda abin yake kawai suka tsaya. Cikin wannan daren Imam ((a.s)) ya yi mata wanka, Asma'u tana zuba mishi ruwa, sannan ya sanya mata likkafaninta. Lokacin da dare ya yi nisa sosai mutane sun yi barci. sai Imam ya kira jama'arsa suka yi wa Nana ((a.s)) salla. wanda suka hada da: Salmanul Farisi. Ammar Ibn Yassir. Abu Zarri Gifari. Mikdad. Huzaifatul Yamani. Abdullahi Ibn Mas'ud. Abbas Ibn Abdulmuttallib. Fadeel Ibn Abbas. Akilu. Zabair Ibn Ayywam, Buraida da wadansu 'yan jama'a daga Banu Hashim.
Imam Ali (a.s) ya shige gaba don ya yi wa diyar Manzon Allah salla. Yana mai cewa: "Ya Ubangiji 'yar Manzonka ta yarda da ni, ya Ubangiji! hakika ta faku cikin kawaici, ka yaye mata. Ya Ubangiji an kaurace mata ka sadar da lta, Ya Ubangiji hakika an zalunce ta ka bi mata hakkinta, kai ne mafi alkhairin masu hukunci". Sannan sai ya yi mata salla raka'a biyu, ya daga hannuwansa sama yana cewa: "Wannan 'yar Manzonka ce Fatima, ka fitar da ita daga duhu zuwa haske".
An samu ruwayoyi daban-daban dangane da inda kabarin sayyida Zahara (a.s) yake, amma wasu sun tafi a kan cewa yana Bakiyya ne, wasu kuma sun tafi a kan yana cikin dakinta. lokacin aka fadada Masallacin Manzo (s.a.w) sai ya zama yana cikin Masallacin Manzo (s.a.w). Kodai mene ne ya faru an riga an boye kabarin nata kamar yadda ta yi wasiyya da hakan ga Imam Ali (a.s) domin ta nuna zaluntarta da wannan al'umma ta yi na rashin kula da hakkinta da na mijinta.
Wannan al'amarin kawai ya isa ga mai karatu ya yi tunani a kai, me ya sa haka ta faru In ba dalili, me ya sa yanzu ba wani mahaluki cikin al'ummar annabi (s.a.w) da zai iya zuwa  Madina ya ce ga barin 'yar Manzon Allah?!
Bayan haka mata kabari ne, sai Imam (a.s) ya shiga cikin kabarin sannan Abbas da dansa Fadhal suka mika mishi ita ya sanya ta cikin kabarin. Hawaye suna ta zubo masa bi da bi! Bayan ya sanya ta sai ya ce: "Ya kasa ga amana nan na ba ki, wannan ita ce diyar Manzon Allah, da sunnan Allah Mai Rahma, Mai jinkai, da sunan Allah bisa addinin Manzon Allah! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.haidarcenter.com
Saturday, July 31, 2010

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: