bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:30:06
Dangantaka Ta Jini:- Baya halatta ga namiji ya auri waxannan matan: (a) Babanninsa da kakanninsa (na uwa da uba) duk yadda ya yi nisa da su ta salsala; (b) `Ya’an sa da jikokinsa ko mai nisan dake tsakaninsu; (c) `Yar uwarsa; (d) `Yar xan uwansa ko`yar-`yar`uwarsa, ko kuma qanwar babarsa ko wadda suka haxa uwa ko uba.
Lambar Labari: 122
Abubuwan Da Ke Haramta Auratayya Tsakanin Namiji Da Mace:-
1. Dangantaka Ta Jini:- Baya halatta ga namiji ya auri waxannan matan: (a) Babanninsa da kakanninsa (na uwa da uba) duk yadda ya yi nisa da su ta salsala; (b) `Ya’an sa da jikokinsa ko mai nisan dake tsakaninsu; (c) `Yar uwarsa; (d) `Yar xan uwansa ko`yar-`yar`uwarsa, ko kuma qanwar babarsa ko wadda suka haxa uwa ko uba.
2.  Dangantaka ta auratayya (Musahara):- Namiji baya auren:- (a) Babar matarsa ko kakarta; (b) `Ya ko jikar matar da miji ya aura kuma ya take ta da sauransu; (c) Matar da xansa ko jikansa ya tava aura (duk nisansu da jikan); (d) Matar da Babansa ko kakansa ya tava aura.
3. Akwai matan da namiji zai iya aura a mabanbantan lokuta amma ba ya haxa su a lokaci guda. Waxannan su ne: (a) `Ya da qanwa; (b) Mace da`yar uwar babarta ko `yar uwar babanta.
A wannan hukuncin da ya gabata (wato 3b), Shi’a sun  sava da mazhabobi huxu na sunna, Shi’a sun  halatta hakan matuqar matar (wato ‘yar uwar babar wacce za a aura) ta yarda ta haxa miji da `yar-`yar`uwarta, to auren ya inganta.( Sharhul Lum'a na Mohd Ali Attabataba'I ((d. 1231/1816) Riyadil Masa'ilil Tabrizi (Sharhul Kabiru) Tabriz, 1308/1890 – 91, 11, 94.).
In banda ‘yar matar mijin wato agolarsa, - a sauran dagantaka ta auratayya guda ukun da suka gabata - tana haramta ga namiji da zarar an qulla aure, ba tare da sun tara da juna ba. Amma  idan namiji ya yi nufin auren ‘yar matarsa wacce ba su yi jima’i ba, to zai iya ya aurenta, idan ya saki matarsa (uwar agolan). Amma da zarar ya kusanci (ya yi jima’i) da uwar, to ‘yar ta haramta gare shi har abada. Shin hakan ya faru ne sakamakon ingantaccen aure ne ko akasin sa? (`yar ta haramta a gare shi sakamakon tarawa da babarta). Idan namiji ya auri mace da ‘yarta ko ya auri ya da qanwa a lokaci guda to gaba xayan auren (guda biyun) sun vaci. Idan kuma ya fara auren xaya kafin xayar to na farko ya inganta amma na biyun ya vaci.
Mazahabobi sun sava a kan haqiqanin dalilin da ke haramta a auri mace a sakamakon samuwar alaqa ta auratayya.
Hanafiyya sun tafi a kan  cewa haramcin na tabba ta ne idan auran ya zama halattacce, ko yin jima’i da matar ta kowane dalili (wato ta hanyar halattaccen aure ko auren da bai halatta ba, ko kuma zina), kai har da wasannin motsa sha’awa ko ganin al’aurar juna.(Fiqhu 4, 63)
Shafi’iyya sun tafi a kan haramci, in an qulla halattaccen aure ko yin jima’i bayan haramtaccan aure. Shafi’i bai xauki haramci ta dalilin wasannin motsa sha’awa ko zina a matsayin dalilin da zai iya haramta aure ba.(Ibid, 65)
Ra’ayin Maliki ya yi daidai da na Hanafiyya, sai dai kawai a vangaren zina, kamar dai Shafi’i, shi ma Maliki ya tafi a kan ra'ayin shafi’I, saboda baya la’akari da zina.( Ibid, 65)
Shi kuwa Hambali ya tafi a kan haramcin sa a kan haramtaccen aure kamar yadda yake a kan halattacce, ba bambanci, kamar dai yadda halattacce ke haramtawa lokacin da aka sami jima’i (Ibid, 67 – 68), haka ma haramtacce yake haramtawa.
Amma Shi’a sun tafi a kan fahimta irin ta shafi’i sai dai ra’ayoyin malamai sun karkasu a kan zina, wasu sun haramta idan an yi zina wasu kuma sun halatta. (Sharhul Lum'a 5, 176 Riyad, 11 96 – 97)
4. Dangantakar Shayarwa (Ridha'i). Matar da ta shayar da yaro tamkar ita ta haife shi matuqar an kiyaye dokokin shari’a a kan shayarwar (wato ta cika sharuxxan da shari'a ta sanya a cikin shayarwa). Don haka yaron da aka shayar da kuma `ya`yan me shayarwar tamkar suna uwa xaya ne, (dangantakar shayarwa kamar ta jini ce).
 a- Mazhabobin Shi’a da Hanbaliyya sun tafi a kan cewa ya nonon da aka shayar ya wajaba ya zama ya samu sakamakon daukar ciki ta dalilin aure.(Fiqhu 4, 268, Riyad, 11, 86) Shafi’iyya sun tafi a kan cewa abin da zahiri ya nuna na yiwuwar samun cikin ya wadatar a amince da cewa nonon ya samu sanadiyyar cikin, misali, idan da yarinya ‘yar shekara tara wacce aka yiwa aure za ta fara haila sannan  ruwan nono ya fara fitowa, idan har ta shayar da yaro to ya zama tamkar xanta.(Fiqhu, 4, 256) Amma Malikiyya da Hanafiyya sun tafi a kan cewa babu bambanci game da mai shayarwar shin me aure ce ko ma yarinya ce mai qarancin shekaru ko kuma ta yi tsufan da ba zata iya xaukan ciki ba.( Ibid, 253 – 55)
Mazhabar Hambaliyya da shafi’iyya sun tafi a kan cewa idan mai shayarwa ta sami ciki ta hanyar zina (cikin shege) to haramcin auratayya ya shafi dangin matar na jini ne kawai, banda dangin wanda ya yi mata cikin. Amma wannan maganar, Hanafiyya da Malikiyya sun ce har dangin wanda ya yi cikin ma haramcin ya shafe su.(Ibid, 268 – 69) Shi’a kuwa sun ce babu wani haramci a ko wane vangare matukar ta hanyar zina ne domin zina ba abar kimantawa ba ce.(Riyadh 11, 86)
b- Amma mazhabobi hudun (Hanafiyya, Malikiyya, hambaliyya da Shi’a Ja'afariyya),) sun tafi a kan cewa dole sai idan yaron an shayar da shi ne kafin ya cika shekara biyu kafin haramcin aurataiya ya tabbata. Amma Malikiyya sun ce dole sai in bai kai shekaru biyu da watanni biyu ba.(Fiqhu, 4, 253).
c- Dukkanins mazhabobin sun tafi a kan cewa dole sai idan har ruwan nonon ya shiga cikin yaron.
d- Shi’a sun ce dole sai in har yaran ya tsotsi ruwan nonon daga nonon me shayarwa. Don haka idan yaron ya sha bayan an zuba a wani mazubi babu hukuncin haramcin auren.(Riyadh, 11, 86) Amma mazahabobin sunna sun tafi ne a kan rashin banbancin hanyar da yaron ya sha. (ko ya shata hanyar xura ko nonon ya kama).
e- Mazhabobin sun yi savani a kan adadin da za  a shayar da yaron nonon. Shafi’iyya da Hambaliyya sun tafi a kan cewa dole sai an shayar da shi a qalla sau biyar.(Fiqhu, 4, 257) Shi’a kuwa sun ce dole a shayar da shi na tsawan sa’o’i ashirin da hudu ko a qalla sau goma sha biyar, kuma a kowace.
Shayarwa dole ne ta amsa sunan shayarwa. (Riyadh 11, 87)
Amma Hanafiyya da Malikiyya kuwa sun ce zuqa xaya koda kuwa xigo yaron ya sha to haramcin ya tabbata.(Fiqhu, 4, 257)
f- Shafi’iyya da Shi’a Ja'afariyya sun ce: dole ya kasance me shayarwar tana raye lokacin da aka shayar da shi nonon.(Ibid, 256 Sharhul Lum'a, 11, 63) Sauran mazahabobin sun haxu a kan cewa da yaron zai sha nonon bayan rasuwar matar to hukuncin haramci ya tabba ta.(Fiqhu, 4, 254, 255 da 261).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: