bayyinaat

Published time: 12 ,May ,2018      07:33:01
Ita wannan kalmar "shi'a" tana da ma'anar nabiya da mataimaka kamar yadda ya zo a littafin kalmomi "kamus" na kusan dukkan "kamus' din larabci, Fairuz abady a cikin kamus ya ce kalmar "shi'a" ... "shi'aturrajul" na nufin mabiyansa ko mataimakan sa, haka nan ma'anar su daya da firka, tana doruwa kan mutum daya, biyu
Lambar Labari: 124
Akidun Shi'a 1
Akidun Shia Daga Bakunan Su
بسم الله الرحمان الرحيم
وصلي الله على محمدوءاله
GABATARWA
Ina mai gidiya ga Allah da ya bani damar fara aiko rubutu a karo na farko kan akidun Ahlulbait (AS) domin bada wata yar gudunmawa daidai gwargwadon iyawata tare da neman Allah ya karb koda harafi daya ne daga gareni a matsayin bada wata gudunmawa ga wannan mazhabi, da fatan Allah ya sanya wannan rubutunawa ya amfanar wajan yada haske da ma'anar wannan mazhabin gaskiya tsantsa na gidan annabta, ina kara rokon Allah ya karfafi duk wanda ke kokarin ganin wannan mazhabi ya bayyana a siffarsa ya sanya ikhlasi cikin dukkan ayyukan sa tare da kare shi daga sharrin halittu ya karba daga gare shi ya kareshi da kyakkyawar niyya, Allah ya dankwafar da dukkan mai yi wa wannan mazhabi zagon kasa bisa son rai ya sanya kokarin sa wajen yin hakan ya zama sanadin faduwar sa, ya tabar da shi ya hana shi abinda yake buri, Allah ya karemu da ikhlasi ya sanya mu karbar gaskiya daga ma'abocin ta ba tare da duban wanda ke gaya mana ba.

MANUFA
Na fara wannan rubutu ne don ganin yadda aka bar wannan al'umma a baya wajan sanin dayawan abubuwan da ke kewaye da ita daga kowane bangare kamar: Al'adu, Addinai, Bangarorin Addinan, Kabilu, Tarbiyya, Zamantakewar Iyali da sauransu, sai na ga bari na yi amfani da wannan dama don kokarin kare wani dan duka daya daga cikin miliyoyi da fatan Allah ya bamu dacewa.

SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan dan aikin da nai ga ruhin Marigayiya mahaifiyata Rahama Hussain da yar'uwa ta ta jini Zahra'u Muhammad Sa'id da fatan Allah ya rahamsheta ya sanyata cikin ceton Sayyida Zahra (AS),
GODIYA
Ina godiya ga iyaye na, Malamai na, Abokaina da sauran dukkan yan uwa da abokan arziki da sauran 'yan uwa muminai bakidaya,

WANNAN ITACE SHIA DAGA BAKIN 'YAN SHI'A

HAKIKANIN SHIA DA FARKON TA.
Kalmar  "SHIA"
Ita wannan kalmar "shi'a" tana da ma'anar nabiya da mataimaka kamar yadda ya zo a littafin kalmomi "kamus" na kusan dukkan "kamus' din larabci, Fairuz abady a cikin kamus ya ce kalmar "shi'a" ... "shi'aturrajul" na nufin mabiyansa ko mataimakan sa, haka nan ma'anar su daya da firka, tana doruwa  kan mutum daya, biyu, jam'in maza da jam'in mata, Wanannan Kalma ta Shia amman daga baya sai ya zama a na gayawa wanda ya jibinci Imam Ali da mutanen gidan sa, har ma sunan ya zama kamar na su ne su kadai, jam'in kalmar shi ne "ashya'u" da "shiya'u". wannan ce ma'anar kalmar shi'a, ina fatan wannan ma'anar ba zata rikitar da ku ba daga yau.

Kalmar "shi'a" a magana: suna ne da ake gayawa mabiya Imam Ali bin Abi Dalib (AS) da mataimakan sa tun daga zamanin Manzon Rahama (SAW) ba wanda ya sa musu wannan sunan sai Manzon Rahama (SAW), daga litattafan Ahlus sunna kamar yadda zamu kawo inda su ka zo a nan gaba.
kamar yadda Allah ya fada game da manzon sa (SAW) {baya fadin son zuciya ba abinda yake fada sai wahayin da aka yi masa} suratun Najm aya ta 3-4.
Haka ma Manzon Rahama (SAW) ya ce : "shi'ar Aliyyu sune rabautattu" malaman sunna sun rawaito wannan hadisin da ire-iren sa a litattafan su da tafsirsn su a tafsirin ayar da ta gabata Kamar Haka:
1-    Hafiz Abu Nu'aim ya rawaito a littafin sa "hilyatul auliya'u " da sanadin sa daga ibni Abbas ya ce : lokacin da wannan madaukakiyar ayar ta sauka {hakika wadanda suka yi imani da ayyuka na gari sune fiyayyun halitta} suratul Bayyina aya ta 7. sai Manzo (SAW) ya yiwa Imam Ali bin Abi Dalib (AS) magana ya ce masa : "ya Aliyyu! kai da mutanen ka zaku zo ranar alkiyama kun yarda da Allah shima ya yarda da ku".Abu Mu'ayyad Muwakkaf Ahmad al kuwarizmi ya rawaito a fasali na 17 cikin klittafin manakib littafin "tazkiratul kuwwasul ulama'u"  na sibd ibnil jauzi. (al-manakib, hadisi na biyu daga hadisi na 18 cikin bayanin abinda ya sauka game da Ali (AS).
2-    Babban malamin tafsirin Sunna da aka sani da Hakimu Ubaidullahi Al'haskani ya rawaito cikin littafin sa "shawahiduttanzil" daga Hakima abi Abdullahil Hafiiz da sanadin sa zuwa Yazid bin sharahital ansary, ya ce : na ji Aliyyu (KW) na cewa : Manzon Rahama (SAW) ya bani labari cewa : "ya Aliyyu baka ji Allah na cewa : {hakika wadanda suka yi imani suka yi kyakykyawan ayyuka sune fiyayyun halitta} ba? (ai kai da makiyan ka ne, mahada ta da ku tafkin alkausara, idan al'uImam Ali bin Abi Dalib (AS)a suka zo wajan hisabi za'a kira ku a karrama ku kuma jikin ku na ta haske".
3-    Abu Mu'ayyad Muwakkaf Ahmad al kuwarizmi ya rawaito a "manakib " cikin fasali na tara daga jabir bin Ab dullahil ansari, ya ce : muna zaune wajan Manzon Rahama (SAW), sai Imam Ali bin Abi Dalib (AS) ya fuskanto sai Manzon Rahama (SAW), ya ce : "hakika dan uwana ya zo muku" sai ya waiwaya wajan ka'aba ya dake ta da hannun sa sannan ya ce : "na rantse da marikin raina hakika wannan da mabiyan sa sune ma rabauta a ranar kiyama, kuma shine farko a imaniu kuma ya fiku cika al'amarin Allah, kuma ya fiku dagewa da lamari Allah, ya fiku adalci a cikin mutane, ya fi ku raba abu daidai, sannan ya fi ku daraja a wajan Allah". Sai ayar : {hakika wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari sune mafiya alkhairin mutane} Suratul Bayyina aya ta 8, ta sauka.
Mai ruwaya ya ce : sahabban Manzon (SAW) sun kasance idan sun ga Imam Ali bin Abi Dalib (AS) ya fuskanto su sai su ce : fiyayyan mutanen Annabi (SAW) ya zo. (manakibi Aliyyin (AS) fasali na 9, hadisi na 10).
4-    Jalaluddin assuyudy babban shahararren malamin sunna ma haka ya fada game da wannan aya da ta gabata, har ma ana ce masa mujaddadin ahlussunnah wal'jama'a a karni na tara kamar yadda aka fada  a "fat'hul makal" ya rawaito a tafsirin sa "addurrul mansur" daga ibni askar addimashky, ya rawaito daga Jabir dan Abdullahil ansary ya ce : wata rana muna zaune a wajan Manzon Rahama (SAW) katsam sai ga Aliyyu bin Abi Dalib ya shigo, sai Manzo (SAW) ya ce : "na rantse da marikin raina, hakika wannan da mabiyan sa sune masu rabauta ranar al'kiyama", sai aya ta sauka : {hakika wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau wadannan sune fiyayyun halitta}.
Haka nan ma ya kuma zuwa cikin durrul "mansur" a tafsirin ayar da ta gabata, daga bin Addi, daga bin Abbas ya rawaito cewa : lokacin da wannan ayar ta sauka Manzon Rahama (SAW) ya ce da Imam Ali bin Abi Dalib (AS) cewa : "kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'kiyama kun yadda da Allah, shi ma ya yarda da ku".
5-    Ibni Sabbag al'maliki ya rawaito a littafin sa "fusulul himma Babi na 122, daga dan Abbas ya ce : lokacin da ayar : {hakika wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau wadannan sune fiyayyun halitta} Suratul Bayyina, aya ta 8, ta sauka.  sai Manzon Rahama (SAW) ya ce da Imam Ali bin Abi Dalib (AS) : "ai kai ne da mabiyan ka, kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku, makiyan ka zasu zo cikin fushi an bankare su".
6-    Ibni Hajar a cikin sawa'ikul muhrika babi na 11, ya rawaito daga Hafiz Jamaluddin, Muhammad bin yusuf azzarandy almadani, har ma ya kara a ciki : sai Imam Ali bin Abi Dalib (AS)  ya ce : su waye makiya na? Sai Manzo (SAW) ya ce: "duk wanda ya yi maka bara'a ya tsine maka!".
7-    Allama Shamhudy a cikin littafin sa "jawahirul ikdaini ya rawai to shi daga Hafiz jalaluddin azzarandy, ya yadda abinda aka kawo a sama (6).
8-    Shahararren Malamin sunna Mair Saiyyid ya rawaito a littafin sa "mawaddatul kurba" daga Ummu Salama uwar muminai matar Manzon (SAW) ta ce : Manzon Rahama (SAW) ya ce : "Aliyyu kai da tawagar ka yan Al'jannah ne, kuma kai da tawagar ka yan Al'jannah ne".
9-    Hafiz ibnul magazili shaf'iy  al-wasidy ya rawaito a
litttafin sa "Manakib Aliyyu bin Abi Dalib (AS)" da sanadin sa daga Jabir bin Abdullahi ya ce : lokacin da Ali (AS) ya dawo daga yakin khaibara sai Manzon Rahama (SAW) ya ce masa : "Ya Aliyyu ba don kada mutane cikin al'umma ta su fadi irin abinda nasara suka fada a kan Annabi Isa (AS) ba, da na fadi wata maganar da idan ka wuce ta kusa da musulmai, za sun dinga diban kasar kafarka da ragowwar ruwan alwalar ka, don su yi magani da su, saidai ya isheka cewa matsayin ka wajena kamar matsayin Haruna ne a wajan Musa, sai dai ba annabi bayana, kaine zaka sauke nauyin da ke wuyana ka suturta addini na, kuma zaka yaki mutane kan sunna ta, gobe kiyama ka fi kowa kusanci da ni, kuma kaine halifana a tafkin al'kausara, kuma mabiyan ka suna kan membarin haske, fuskokin su sun yi haske a gefe na, sannan sune makota na a gidan al'janna, wanda ya yakeka ni ya yaka haka ma wanda ya yi zaman lafiya da kai to da ni ya yi".
Mun karanta a muwaddatul kurba da abinda muka nakalto wannan maganar ga ta : an rawaito daga Manzon Rahama (SAW) ya ce ya Aliyyu , : "kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'kiyama kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku,  makiyan ku na cikin bacin rai an bankare su".
Mun karanta a "mawaddatul kurba" kan abinda muka fada hadisin da ya gabata cewa : an rawaito cewa ; Manzo (SAW) ya ce : "ya Aliyyu, kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'kiyama kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku,  makiyan ku na cikin bacin rai an bankare su".

'YAN SHIA DAGA CIKIN SAHABBAI
Ya zo a kitabuzzeena na ibni Hatim arrazy malamin snna ya ce : "Shia" shine sunan farko a musulunci na wasu jama'a a lokacin Manzon Rahama (SAW), har sahabbai hudu sun shahara da wannan suna, su ne :
1-    Abu Zarril gifari.
2-    Salmanul farisi.
3-    Mikdad bin Aswad.
4-    Ammar bin Yasir.
Tambayar da zata zo z nan itace: ta yaya sahabban Manzon (SAW) guda hudu na kusa da shi wadanda ya ke ji da su za'a dinga kiran su da shi'a alhalin ya na ji yana gani kuma bai hana wannan ba!
Amsa itace: Manzo (SAW) shine wanda ya sanya Ali (AS) a matsayin Halifansa a bayan sa, domin ya shiryar da mutane musuluncin gaskiya a bayan sa.
Wadannan dalilai masu inganci da suka fito daga wajan mashahuran malaman sunna kan karfafa zancen Allah ta hanyar hadisai masu inganci a daga malaman sunna, wannan kuma kadan ne daga cikin dubunnan da su ka zo daga bangaren sunna, Ina fatan mai karatu zai bincika sannan ya fahimci Hujjar shia na fifita Ali (AS) a kan kowa bayan Manzo (SAW), da fatan bayan haka ba wanda zai sake tuhumar Shia kan fifita Ali (AS) domin ba su ne su ka fifta shi ba, Allah ne da Manzon sa (SAW) su ka fifita shi.
 Abin bakin ciki da yawa daga masu kiran kansu malaman sunna, da fatan yan uwa yanzu sun gane cewar duk musulmin kirki ya wajaba ya yi riko da wannan fifkon Allah da Manzon sa su ka yi, domin allah da Manzon sa sun fi kowane dayan mu cancatar a kan sa,
Idan mu ka waiwaya a manyan litattafai zamu samu hadisai da yawa da suka zo daga wadanda ke da tsananin ikhlasi daga sahabban Manzo (SAW) cewa : sun ji Manzon Rahama (SAW) ya na cewa : "mabiya Aliyyu sune fiyayyun talikai, sune masu rabauta don hakane ma suka yi alfahari da hakan har ma suka shahara a cikin sahabbai da sunan "shi'ar Aliyyu".


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: