bayyinaat

Published time: 15 ,June ,2018      19:38:33
Aure samar da wata alaka ce mai karfi tsakanin namiji da mace da yakan halatta wa junansu duk wata alaka da ta kan iya kaiwa ga samar da zuri'a, da hawan wasu hakkoki kan junansu.
Lambar Labari: 133
Rayuwar Ma'aurata
 
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki, tsira ya tabbata ga zababben halittar Allah annabi Muhammad da alayensa tsarkaka

"Su tufafi ne gare ku, haka ku ma tufafi ne gare su". Bakara: 187. 

Aure samar da wata alaka ce mai karfi tsakanin namiji da mace da yakan halatta wa junansu duk wata alaka da ta kan iya kaiwa ga samar da zuri'a, da hawan wasu hakkoki kan junansu. Aure wata ni'ima ce da Allah ya sanya ga bayinsa da babu mai samu sai da ludufinsa (s.w.t). Babu wani mutum da zai yi aure da wata ko wata ta auri wani sai Allah ya rubuta musu hakan. Aure hanya ce da ake samar da muminan bayi, shari'a ta yi bayanin cewa babu wani mumini da za a samar ba ta hanyar aure ba, don haka tsarkin haihuwa ana samun ta ne ta hanyar aure kawai. Musulunci yana ganin halaccin aure kuma yana karfafawa kan hakan, kuma yana umarni da shi kuma yana murna da aure da wuri, wannan kuwa yayin da kowanne mace da namiji ya cika shekarun kamalarsa, ga mace da namiji, a lokacin ne yake karfafa yin aure domin kada alfasha ta wakana. 
Mutum halitta ne na al'umma da zaman cikin iyali wanda yake shi ne mafi karancin haduwar zaman tare, amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wanda wannan asasin an gina shi ne da namiji da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da aiyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyaiya mai karfi da alaka tsakanin iyali. Shin kuwa mutum ya san wajibi ne a kansa ya daukaka himmarsa zuwa ga Allah (s.w.t) domin ba a yi shi don ya damfaru da duniya ba, "Ina zaku ne" . Shin kuwa mutum ya san cewa yana da wani nauyi da ya hau kansa? "Ku kare kawukanku da iyalanku daga wuta, wacce gumagumanta su ne mutane da duwatsu" . 
Littafin "Rayuwar Ma’aurata”  ya kunshi bahasosida suka shafi "Mace a Al’adu da Musulunci” da yake kunshe da bayanai ne game da marhaloli da mace ta kasance a ciki daga zamanin da zuwa yau a takaice, don hadafin fahimtar ni’imar da Allah (s.w.t) ya yi mana a wannan Addini da ya aiko mafificin halitta Manzo Muhammadu (s.a.w) da shi, sa’anan kuma zai taimaka wajan sanin matakai da marhaloli na tarihi da mata suka wuce a sauran al’ummu da suka gabata. Sai bahasin "Auren Mace Fiye da Daya” don hadafin kariya ga hukuncin musulunci da manzon rahama (s.a.w) kan abin da ya shafi auran sama da mace daya da yawaitar matan Mafificin halitta. Sai kuma bahasi na uku "Rayuwar Ma'aurata”  wanda yake bayani da nuni kan namiji ko macen da za a zaba don zama tare. Tare da bayanin nauyin da ya hau kansu, da yadda ya kamata su rayu, da sauran bayanai da suka shafi rayuwar ma'aurata. 
Musulunci addini ne mai fadi da ya himmantu da warware duk matsalolin dan'adam, don haka ne ya kalli duk wani janibi na rayuwar mutane, saboda haka ne muka yi imani da cewa babu wani abu da musulunci bai yi magana a kansa ba. Sai dai an samu takaitawar musulmi wurin ba wa komai hakkinsa sai suka himmantu dawasu bangarori suka manta da wasu. Da zamu kalli fagen siyasa, zaman tare, tattalin arziki, tsaro, kotu, dauloli, da alakoki, rayuwar iyali, babu wasu bayanai masu yawa da zaa samu. 
Takaitawar yin bayaninsa ya sanya wasu al'ummu suna daukarsa a matsayin addini tauyaiye da ba shi da wani abin cewa a kowane fage sai na ibadoji da wasu mu'amaloli kamar aure, ciniki, haya, saki, rantsuwa, da makamancin hakan. Suna masu jahiltar iliminsa da hikimominsa masu kima da darajada zasu iya fitar da wannan duniyar daga kangin da take ciki, da bayar da warwara ga duk wani dan'adam a kowane fage. Rashin fadada magana kan hikimar da hukuncin addini yake kunshe da ita ya sanya hatta musulmi sun jahilci mafi yawan hikimomin hukuncin addini a kan kowane lamari. 
Littafin ya kalli al'adun mutanenmu na kasar Hausa da yadda suke rayuwa domin neman gyara cikin wannan al'ummar tamu da ilmantarwa ko tunatarwa game da wasu muhimman bayanai da ya kamata su mayar da hankali kansu game da gyara zaman tare domin samun al'umma ta gari. Sannan ya kunshi takaitaccen bayani ne game da yadda ya kamata gida ya kasance, da siffofin ma’aurata, da kuma yadda ya kamata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hakkin juna kamar yadda musulunci ya gindaya ba tare da ketare iyaka ba. 
A musulunci an yi umarni da yin aure ba domin biyan bukatar duniya ko ta sha’awa ba kawai, akwai bukatar gina al’umma saliha da zata ci gaba da daukar nauyin isar da sakon Allah a duk fadin Duniya, wannan yana bukatar taimakekeniya tsakanin ma’aurata, sa’annan akwai samun nutsuwar ruhi da dan'adam yana bukatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata. Komai ilimin da mutum (namiji ko mace) suka samuko wata ni'ima ta duniya idan ba su samu mai debe musu kewa ta fuskacin zaman aurataiya ba to akwai wani gibi babba da ba su cike shi ba wanda ba ya samuwa sai ta hanyar aurataiya . Sai dai idan ba a samu dacewa da abokin zama nagari ba ta yadda aka mayar da kauna da so suka koma kiyaiya da gaba, to rayuwa takan gurbace ta koma gwara rashin abokin zama. 
Ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matukar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan kasa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo a ruwaya . Mu sani akwai kamalar da ba ta samuwa sai ta hanyar aure, irin wadannan abubuwansun hada da: sanin ma’anar ciyarwa, yafewa, soyaiya, hakuri, juriya, daukar nauyin mutane, reno, tarbiiyar ‘ya’ya, fahimtar kimar iyaye, tunanin gida, da sauransu. 
 Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: Sau da yawa daga cikin abubuwa kamar ma’anar soyaiya, da kauna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma’anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wadanda ta hanyar zaman banza da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hakikaninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai . 
 Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga rayuwar al’umma baki daya, ta yadda zai zama sanadi na gina al’umma saliha da ci gaban duniyar musulmi. Daga karshe ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga iyaye da duk bayin Allah salihai malamaina da duk wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Web Site: www.haidarcenter.com
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: