bayyinaat

Published time: 25 ,January ,2017      12:11:15
"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32)
Lambar Labari: 18
"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105) 
"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32) 
"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina. (Surar Shura, 42: 10) 
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59) 
"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52) 
"Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46) 
Tun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci wannan kaidin ta kuma yi nasara kan yahudawa da mushrikai da munafukai, albarkacin jagoranci Annabi (s.a.w.a) da kuma lizimtar sahabbansa, zababbu. 
Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa: 
"...Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi...". 
Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance. 
Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi: 
"...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici". 
Da kuma kira zuwa ga riko da igiyar Allah: 
"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba...". 
Da kuma cewa wannan al'umma guda ce: 
"Kuma lalle ne wannan al'ummar ku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku biNi da takawa". 
"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta Mini". 
Kamar haka ne Alkur'ani ya sanya matakan hada kan al'umma kamar haka: 
1. Wanda ake wa bauta Shi kadai ne, kuma abin nema shi ne kadaita Shi da bauta masa. 
2. Manufar addini ita ce tsayin daka da kuma muwafaka da halittar da Allah Ya yi mutane a bisa kanta. 
3. Cewa wajibi ne kan al'umma ta tara karfinta wurin kira zuwa ga Musulunci da tabbatar da al'umma mai kira zuwa ga alheri da umurni da kyakkyawa da hana mummunan aiki, da daukar sakon Allah (S.W.T.) zuwa ga 'yan'Adam baki daya: 
"Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri da kuma hani daga abin da ake ki". 
An umurci musulmi da wannan aikin a madadin rarraba da sabani da jayayya domin kada su halakar da karfinsu kan kokawan cikin gida har ma su raunana su zamo abin hadiyewa ga abokan gaba. 
Alkur'ani mai girma yana kiran hankulanmu domin mu gane dalilan sabani da kuma tabbatar da tushen hanyoyin warware shi: 
(a). Sabani kan shari'a da tunani irin na Musulunci wajibi ne a mai da shi ga Alkur'ani da Sunna. 
"Idan kun yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa...". 
"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah". 
Alkur'ani yana hana mu mayar da jayayya ta ilimi da shar'antawa zuwa wata matsala ta rarraba da sabani da gaba da keta al'ummar musulmi, ya ce: 
"Kuma kada ku yi jayayya har ku raunan, karfinku ya kau....". 
(b). Mas'alolin da suke da alaka da siyasa ko zamantakewa wadanda shugaban al'umma, na shari'a, shi yake tsara su da gudanar da su, to wajibi ne a yi masa biyayya domin kada ra'ayoyi su yawaita a sassaba. Domin dole ne al'ummar musulmi ta zama tana da matsaya guda kan sha'anin siyasa da zamantakewar al'umma. 
"...Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzon Allah da ma'abuta al'amari daga cikinku". 
Hakan kuwa matukar su ma'abuta al'amari sun lizimci hukumce-hukumcen shari'a, kuma suna tabbatar da maslahar al'umma. 
Musulmi a yau - alhamdu lillahi - suna tare da Littafin Allah, wanda barna ba ta shigo masa ko a farko ko a karshe, duk wani mai jirkitarwa bai iso shi, yana nan kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kawo shi: 
"Hakika Mu ne Muka saukar da ambato (Alkur'ani), kuma hakika Mu masu kiyayewa ne a gare shi". (Surar Hijiri, 15: 9) 
Na biyu kuma, Musulmi sun hadu kan kubutar Alkur'ani daga dukkan wani ragi ko kari, kana kuma sun yi imani da shi da kuma Wanda Ya saukar da shi, 
Allah Madaukakin Sarki, Abin nufi da bukata, kamar yadda ya siffanta kanSa cikin wannan Littafi Nasa. 
Na uku, musulmi sun hadu kan gaskata Annabi (s.a.w.a), suna da Alkibla guda, sun yarda da farillolin Musulunci kamar su salla, zakka, azumi, hajji, jihadi, umurni da mai kyau da kuma hani da mummuna da dai sauransu. 
Musulmi sun hadu kan haramcin manyan laifuffuka, kamar su zina, shan giya, luwadi, sata, kisan kai, karya, cin rashawa da dai makamantansu. 
Babu wani sabani tsakanin musulmi cikin ginshikai da tushen imani wadanda suke sanya al'umma ta zama musulma, sun yi ittifaki akan dukkan wadannan gishikai. Saboda haka, wajibi ne a warware mas'alolin ijtihadi da ra'ayoyin ilmi ta hanyar mai da su ga Littafin Allah da tabbatacciyar Sunnar Annabi (s.a.w.a) domin kuwa Annabi (s.a.w.a) ya bar al'ummarsa bisa hanya ma'abu-ciyar haske. Annabi (s.a.w.a) ya ce: 
"Na bar ku kan hanya mai haske, darenta tamkar yininta. Babu mai karkace mata a bayana sai halakakke". 
Al'ummar musulmi a yau tana cikin wani matsayi na tarihinta mai bukatar lura da yanayi na ci gaba mai hadari domin tun da dadewa makiya Musulunci suka yi ta kai hare-hare gare su, kama tun daga yakukuwan Salibiyya (wadanda kiristocin Turai suka yi da musulmi), kawo ya zuwa yau din da muke ciki. 
Su wadannan makiya, kama tun daga su wadannan kiristoci na salibiyya da kuma yahudawan sahyoniya da 'yan korensu, sun fuskanci akidoji da maslahohin musulmi da ruguzawa da kuma makirci, kuma ba su gushe ba tsawon karni na goma sha tara da na ashirin suna babbata wannan al'umma, suna yada rarraba da sabani na siyasa da tunani da bangaranci da jinsi da nahiyanci, ga kuma yakinsu na tunani da kokarin halaka addinin Musulunci. Baya ga haka kuma, ga yada akidojin son duniya kawai da karyata addinai, kamar akidojin jari hujja na Turawan Yamma da gurguzu da dai sauransu. Ga kuma kirkirar jam'iyyu da hukumomi da mahukunta 'yan korensu wadanda suka riki wadannan akidu domin su yaki Musulunci da masu kira da kokarin daukaka shi da shiryar da 'yan'Adam zuwa ga tafarki madaidaici da kuma kubutar da su daga zalunci da bauta wa azzaluman duniya. A waje guda kuma, malaman kwarai suna kiran al'ummar musulmi zuwa ga hadin kai da dawo da martabar musulmi da tabbatar da hukumce-hukumce da tsarin addini, a wani gefen kuwa 'yan koren kafirci, masu sanye da tufafin malamai suna shuka sabani da rarraba da gurbata fuskar Musulunci domin su tabba-tar da hukumcin 'yan koren Turai da sauran makiya Musulunci, masu tsotse arzikin kasashen musulmi da shinfida ikon sahayoniyawa da 'yan jari hujja da 'yan gurguzu. 
Ya wajaba kan 'yan'uwa musulmi da su kiyaye tare da sanin hakikanin masu yada dafin rarraba da sabani cikin musulmi ta hanyar dasisa da karya da kage-kage ko ta hanyar riko da raunana da kagaggun ruwayoyi da suke cikin littattafan hadisai. Irin wadannan hadisai za a samu cewa malamai da masu bincike sun riga da sun fitar da su daga da'irar ilmi, suna ganin sauya su aka yi. Duk musulmi sun san da hakan kamar yadda Manzon Tsira (s.a.w.a) ya gargadi musulmi a hajjinsa na bankwana da cewa: 
"Hakika makaryata sun mini yawa kuma za su yawaita. To duk wanda ya yi min karya da gangan ya tanadi mazauninsa a wuta. Idan hadisi ya zo muku, ku gwada shi da Littafin Allah da Sunnata, abin da ya dace da Littafin Allah, to ku rike shi, abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunnata, to kada ku yi riko da shi( )". 
To idan dukkanmu muna sane da wannan, saboda maslahar waye masu neman rusa addini suke rubuta littattafai da mujallu masu yada rarraba da sabani tsakanin musulmi da kafirta juna da shuka gaba cikin zukata? - domin maslahar wa suke wannan mugun aiki, musamman ma a wannan lokacin mai hadari? Alhali Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: 
"Ba za ku shiga aljanna ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin in shiryar da ku ga wani abu idan kun yi za ku so juna? Ku yada sallama tsakaninku( )". 
Irin wadannan kulle-kulle babu shakka aikin manyan azzaluman duniya ne, masu rawar jiki duk san da aka ambaci hadin kan musulmi da gangamin al'ummar Annabi (s.a.w.a), saboda tsantsar karfin ta na mutane da albarkatu da akida mai karfin gaske. 
Abin da ya dace da malamai da masu tunani da marubuta da masu wa'azi da duk masu daukan nauyin kula da makomar addinin Musulunci masu kyakyawar niyya shi ne su karkata akalar da'awarsu zuwa kalubalantar barnar masu mugun nufi, su kira al'umma zuwa ga hadin kai da warware matsalolinsu na shari'a da tunani bisa dalilai na ilmi. 
An nakalto daga Ibn Shar Ashub cikin littafinsa Munakib Ali Abi Talib cewa: 
"Wata mace ta yi wasicci da sulusin dukiyarta don a yi mata sadaka, aikin hajji, a kuma 'yanta bawa, to amma dukiyar ba ta isa dukkan wadannan ayyukan ba. Sai aka tambayi Abu Hanifa da Sufyan Al-Sauri kan hakan, sai kowanensu ya ce: A nemi mutumin da ya yi aikin hajji amma bai cika ba sai a ba shi kudi ya karasa da wanda yake kokarin 'yanta wuya, amma bai gama biya ba sai a cika masa, sannan a yi sadaka da sauran. Sai Mu'awiyya bn Ammar (yana daga cikin sahabban Imam Sadik) ya tambayi Imam Sadik (a.s.) kan wannan matsala, sai ya ce da shi: "Ka soma da hajjin domin hajji farilla ne, sauran kuma a aikata nafilolin". Sai Abu Hanifa ya yi wannan ya yi wannan fatawar ya sauya ra'ayinsa( )". 
Abu Kasim Al-Baggar ya kawo cikin Musnad na Abu Hanifa, cewa Hasan bn Ziyad ya ce: Na ji Abu Hanifa yana ba da amsar wannan tambayar: Wane ne mafi sani cikin wadanda ka gani? 
Sai ya ce: Ja'afar bn Muhammad. Yayin da al-Mansur ya kawo shi sai ya kira ni, ya ce: Ya Abu Hanifa, mutane sun fitinu da Ja'afar bn Muhammad, saboda haka ka shirya masa tambayoyi masu tsanani. Sai na shirya masa tambayoyi guda arba'in. Daga nan sai ya kira ni alhali kuwa a lokacin yana Hira ta kasar Iraki, sai na amsa masa wannan kira tasa na isa wajensa a lokacin kuwa Ja'afar bn Muhammad yana zaune a damansa. Yayin da na kalli Ja'afar, sai kwarjininsa ya shige ni, tamkar wannan kwarjinin bai shiga Mansur ba. Sai na yi masa sallama, ya amsa mini, sai na zauna. Sai Mansur ya ce: Ya Aba Abdillah, wannan Abu Hanifa ne, sai ya ce: "E, na san shi", sannan sai ya juya gare ni ya ce: "Ya Aba Hanifa, jefa tambayoyinka ga Abu Abdullah". Sai na rika jefa masa tambaya yana amsa mini, yana cewa: "Ku kuna cewa kaza, mutanen Madina suna cewa kaza, mu kuma muna cewa kaza. Ta yiyu mu dace da ku, ta yiwu kuma mu dace da su, wani lokaci kuma mu saba duka. Haka aka yi sai da na gama tambayoyin nan arba'in. Babu abin da ya gaza daga ciki. Sannan Abu Hanifa ya ce; "Lalle mafi sani cikin mutane shi ne wanda ya fi su sanin sassabawarsu( )". 
Wadannan abubuwa biyu da suka faru a tarihi suna nuna yadda ake muhawara ta ilmi bisa tafarki mai tsari, yadda ake bijiro da mas'aloli da binciken hakika da gudanar da muhawara da fito da amsa. 
Irin yadda Abu Hanifa ya yi muhawara da Imam Sadik (a.s.) da tafarkin da suka bi wanda Musulunci ya tabbatar shi ya cancanta malamai da masu bincike su bi domin hakan Musulunci ya sanya ya zama ginshikin isa zuwa ga hakikanin gaskiya. 
Muna iya ganin misalin bin wannan hanya ta ilmi da tunani kubutacce a guri Shaikh al-Azhar, Shaikh Mahmud Shaltut yayin da ya fitar da fatawa cewa ya halalta wa musulmi masu bin mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya da Hambaliya, su bi mazhabar Shi'a Imamiyya kamar yadda ya halalta a bi sauran mazhabobin Musulunci, kuma aikinsu ingantacce ne karbabbe. Baya ga haka kuma Dokta Muhammad Muha-mmad Fahham, daya daga cikin Shehunan Azhar din shi ma yayi amanna da wannan fatawar. 


Mu'assasar Al-Balagh
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: