bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:21:37
Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara (samun buxi)
Lambar Labari: 205
TAFSEER        7

سورة النصر
SURATUN NASR (SURA TA 110)
Wannan sura da ake kira suratun nasr ko da hausa mu ce surar taimako, na koyar da mu cewa idan Allah ya yi wa mutun ni'ima ko ni'imomi to ya gode masa, surar na da ayoyi uku.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
إِذَا جَاءَ نَصْرُ اللَّهِ وَالْفَتْحُ (1)
Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara (samun buxi).
Masu tafsiri sun tafi kan cewa wannan nasara/buxi ana nufin fatahu makka ba sulhun hudaibiyya ba, domin shi sulhun hudaibiyya tsani ne zuwa fatahu Makka, tsakanin su sulhun hudaibiyya da fatahu Makka shekara biyu ne.
وَرَأَيْتَ النَّاسَ يَدْخُلُونَ فِي دِينِ اللَّهِ أَفْوَاجًا (2)
Kaga mutane na shiga addinin Allah qungiya – qungiya.
Qololuwar burin Manzo (SAW) shine mutane su shiriya, shigar su addinin musulunci qungiya – qungiya maimakon xaixaiku ba qaramin buxi bane wajan Manzon rahama (SAW) kenan, wannan haqiqanin taimako ne da buxi ga Allah da Manzon sa.
فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ إِنَّهُ كَانَ تَوَّابًا (3)
Ka yi tasbihi da godewa ubangijin ka, ka nemi gafarar sa, domin shi (ubangiji) ya kasance mai karvar tuba.

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: