bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:00:14
Wannan sura da ake kira da suaratul kausar ko mu ce surar alheri mai tarin yawa, ta sauka ne lokacin da mushrikan Makka, musamman A-si bin Wa'il wato baban Amru wanda aka fi sani da Amru xan Aas
Lambar Labari: 237
سورة الكوثر
SUTATUL KAUSAR (SURA TA 108)
DALILIN SAUKA
Wannan sura da ake kira da suaratul kausar ko mu ce surar alheri mai tarin yawa, ta sauka ne lokacin da mushrikan Makka, musamman A-si bin Wa'il wato baban Amru wanda aka fi sani da Amru xan Aas su ke yi wa manzo (SAW) gori kan cewa, 'ya'yan sa basa tsayawa rasuwa kawai su ke xaya bayan xaya, hatta da wanda aka haifa a Madina ma Ibrahim Al'muzzam xan Mariyatul Qibxiyya ya rasu, haka abun ya kasane a Makka su na rasuwa, Manzo (SAW) na da 'ya'ya, su Abdullahi, Axxahir, Al'qasim babban xan sa, duk sun rasu, wacce ta samu tabbata daga cikin su itace Fatima Azzahara (AS), akwai 'ya'yan Hala yayar Sayyida Khadija (SA) da ta xauke su bayan rasuwar mahaifiyar su Hala, su ka girma a wajan sa (SAW) banu umayya na sanya su a matsayin 'ya'yan sa (SAW) irin su Zainab wacce shekarun ta ma sun kusa na Sayyida Khadija (SA), Ruqaiyya da Ummu Kulthum, don haka ne ma wasu daga malaman tarihi har gobe ke sanya su cikin 'ya'yan Manzo (SAW) duk da ba 'ya'yan sa na haihuwa bane, sai Allah ya goge wannan gorin da suke masa na cewa 'ya'yan sa basa tsayawa da nufin ba wanda zai gaji gidan sa da gaya musu ya bashi Sayyida Fatima (AS), 'yar sa ce ta haihuwa sannan zuriyar Manzo (SAW) zata zama ta tsatson sa kamar yadda zuriyar Imrana ta zama daga Saiyyida Maryam (AS), kuma wannan zuriya za ta wanzu tana maxaukakiya har qarshen duniya, wannan sura na da matuqar qima da muhimmancin gaske domin ta sauke don kariya ga Manzo (SAW).
Ba kamar yadda wasu da yawa daga malamai cikin 'yan uwan mu musulmai ke faxa cewa al'kausar na nufin ruwa ne a al'janna da aka baiwa Manzo (SAW), domin ba hikima a baiwa wanda aka yi wa gorin haihuwa ruwa maimakon xa ko 'ya, duk da yake shi kansa ruwan ma babbar ni'ima ce abar godiya ga mahalicci, shi wannan ruwa na al'janna Manzo (SAW) ya kira shi da al-haudh (tafki), shi yasa har yanzu sunan wannan ruwa bai tabbata da al'kausar ba bisa qwaqwqwaran dalili.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ (1) 
Haqiqa mun baka al-kausar (alheri mai yawa).
فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ (2) 
Ka yi salla ga ubangijinka ka sadaukar da rai.
إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ (3)
Lallai mai aibata ka shine mai yankakken baya.
Allah ya yi raddin maganar Asi bin Wa'il, kamar yadda ta tabbata 'ya'yan da ake kira nasa ba nasa bane, domin hatta da Amru xan As xan sa xan Abu Sufyan sabida ba shi kaxai ke je mata ba a lokacin jahiliyayya don haka sai ta zavi xan ya zama na A-si maimakon Abu Sufyan, ya zo a tarihi hatta Mu'awiya wasu lokuta ya kan kalli Amru ya ce kai xan baba na ne sai babar ka ta zavi bada kai ga Amru, ...

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: